Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

IMAAN 15-16

 

15..

 

Ammi ce xaune parlon inna ta sanadin aikawa da innar tayi a kirata, ta fi minti sha biyar parlon amma inna bata ce da ita komai ba sai goge gogen kayan kallonta take, Ammi ta bukaci ta yi mata goge gogen inna tace ta bar shi, bayan wani minti biyar din Ammi tace "Inna na daura girki ne wllh...." Inna tace "Kin daura girki? Tabdi... Toh ita warcan 'yar da kika bari meye amfaninta da baxata dinga

duba maki girkin ba, ina ce yau alhamis babu islamiyya" Ammi tace "Barci na baro ta tana yi" Inna ta tabe baki tace "A haka dai kullum, Allah dai ya mana tsari ya fidda d'a na kunya, amma gaskiya ni tunda nake tafasasshen ruwan Imaan bai taba shiga baki na ba, toh uwar me xata je ta dafa ma mijin ma idan tayi aure, kullum ayi ta laka ma yarinya ciwo ana daure mata kugu wai bata da lafiya, to ni dai ba ruwana ba wanda xai xagi d'a na, idan ma an samu to Allah ya isa" Ammi dai bata ce mata komai ba, Inna ta xauna tace "Tana yar yarinya da ita tayi ta langwabewa, tana abu salalo salalo, ana ma ciwo sharri to ni dai ba ruwana, dama magana nake son yi mama ke da Amina, to Aminar bata ga damar xuwa ba har yanxu, tana can sai ta mula ta mulmule sai kace xata ma Maryam haka....." Inna bata rufe baki ba Anty ta shigo da sallama, Tace "Sannu inna..." Inna ta tsuke fuska tace "Yauwa" Anty ta xauna tana kallon Ammi tace "Uwar Imaan kwana biyu" Ammi tayi murmushi tace "Ae kam duk mun buya" Mikewa inna tayi ta ci gaba da goge gogenta, Anty tace "Goge goge kike Inna" a fusace Inna tace "Toh baxan yi goge goge ba in mutu cikin wari yar nan, ko ke baki ga ko ina tsaf ba, ko hancin ki bai ji kamshin dake tashi parlon ba, wllh tun safe ban xauna ba ina ta aiki baki ji bayana ba kamar ya balle in huta, ke hatta simintin da kika tako kika shigo nan sai da na goge sa fess yau, ai kazanta bata da kyau, ni dai in sha Allahu cikin kamshi xan mutu ba ruwana, kuma tirr da kazami, ai ina lura duk cikin jikokina babu wanda ya dauko tsafta ta sai Mujaheed" Anty da Ammi dai sai kallonta suke, ta xauna tace "Yo Mujaheed mana, shi kadai ne Allah ya ceta ta wannan fannin, duk inda kazanta take ma shi bai xuwa, kullum tsaf xaka gansa abunsa, baxa ku yarda da xance na ba sai kun shiga dakinsa, ko don raino na ne shi din oho, ga shegen kyankyamin tsiya.... shi kuma wannan katon Isuhu ba shi da aiki sai saka gogaggun kaya da fesa turare amma duk kika basa abinci to wllh a nan xai bar maki kwanon ya tsallake ya wuce, to ina tsafta a nan, ai ta nan ake gane kazami, dakinsa kuwa karkari ya kakka6e gadon ya kara gaba, ita ko wannan mai laluran Imaan ga dai gashi har gashi amma ba gyara malam, kullum gashin nan a kume xa ki gansa sai ta fi sati da sattuka bata sharce ba, to ina tsafta a nan, da an mata magana sai tace xafi yake mata, ai duk mace ta gashi ake gane kazantar ta ni kwarkwata ma nake guje mata wllh, sannan babu tattali kullum sai ta bar min adikonta a nan idan ta xo, ga su can na tara yafi kala dari yanxu, Ko uwarta xan ci da su oho, ni ce ma Bukar xan yi ma ya daina siya mata turmin atamfa gwara a siya falle a mata riga da sket banda dankwali, Atoh shi kenan yayi ta asaran dukiya atamfa dai masu tsada amma tayi ta walakanta adiko, Maimoon kuwa dama kayan datti sai ta tara ta tara taga babu sarki sai Allah, babu wanda xata saka sannan xata kwashesu ta hau wanki duk su cika gida, to ina mace a nan, babu kazantar da ya fi wannan wllh, sauran yan matan kuwa ni wani lkcn ma sai in ji kamar wari suke wllh...." Murmushi Anty tayi, Inna tace "Wallahi ba batun dariya ba, to dai kowa tasa ta fishshesa a gidan nan ba ruwana da kowa ta kaina nake, yanxu dai abinda yasa na kira ku ba wani abu bane...." sai kuma ta yi shiru, su dai kallonta kawai suke, tayi kasa da murya tace "Ku lissafa min daga ranan asabar xuwa yau kwana nawa kenan" Ammi tace kwana shidda" Inna tace "Toh yau kwana shidda rabon Mujaheed da Imaan su xo min nan su gaisheni, yanxu fisabillahi daga sun min ba dai dai ba na nuna bacin raina sai su kullace ni, meye laifina don nace ban yarda shanye min fura da suka yi ba" Anty ta bude baki tace "Gaskiya basu kyauta ba har kwana shidda" Inna ta fara matsar kwalla tace "Ni fitinata har ya kai Mujaheed ya ki takowa nan yau har kwana shidda, daga gyara kayanka sai ya xamo sauke mu raba? Ke Amina na kira ki ne a matsayin uwarsa don ba ruwana da wancan katuwar da ta haifesa, ke kuma Aisha saboda Imaan yar ki ce" Anty tace "Amma Inna ca nake kince kada su sake xuwa maki idan ba haka ba xaki bar gidan" Inna xaro ido tace "Oh oh Allah kaji wata magana don Allah, to Amina idan na bar gidan nan ina da gidan uban da xanje in tsugunna, duk ba xance bane dai da tsorata mutane, bacin rai ai babu abinda bai sawa, don nace kada su sake xuwa kowa yasan fada kawai nayi, me suka min da xan hanasu xuwa nan?? Allah ya tsine ma fura da nonon in dai saboda shi xan kori jikokina, meye kuma wani fura da nono kamar mayyar bafillatana" Anty na danne dariyar ta tace "Ahh to gaskiya basu kyauta ba" Inna ta kalli Ammi tace "Ke kuma Aisha kinyi shiru kina kallona ko baki da abun cewa ne?" Ammi tace "Kiyi hakuri Inna, ina komawa xan sameta" Anty tace "Nima Mujaheed na dawowa aiki xan samesa In sha Allah" Inna ta gyara xama tace "Toh, sai ku ji dalilin da yasa xa su min haka su kaurace min, yanxu duk saukin kai na su basa gani, ni ba mafadaciya ba, ni ba fitinanna ba, ni ba mai sa ido ba, ni ba mai kwadayi ba, ni ba mai mita ba, toh meye xasu wani dauke kafa daga magana dai ta fahimta, to sai dai idan Ahmadu ne ya hure masu kunne ya masu hudubar tsiya, banda haka su har wani wayo garesu da xasu dauke kafa daga xuwa inda nake" Anty ta fara dariya, Ammi kam murmushi kawai tayi, Inna tace "Aa don Allah ku duba xancen da kyau, wllh xuge su aka yi, kuma ba kowa xai yi hakan ba sai mutumin nan Ahmadu don Bukar baya haka shi, ni gaskiya na ma daina sa Ahmadu a lamarina daga yanxu tunda tsanata yake cusa ma yaran a rai, anjima kuma xan sa kira min Bukar yaji abinda ake ciki, kwana daidai har shidda fa" Ammi ta mike tace "Ki yi hakuri Inna ina komawa xan mata magana bari in je in duba girki na" Inna tace "ke ta girki ma kike ga maganar al'ajabi ana yi a nan Ahmadu ya xuge yara, haba don Allah abinci dai abinci dai kamar ana yunwa Amina" Ammi ta nufi kofa tace "Toh sai dai anjima inna" Inna tace "Toh Allah bamu alkhairi, ki dai tsitsiyeta kiji dalili" fita Ammi tayi parlon bayan ta ma Anty sallama. Inna ta tabe baki tace "Kinga bafillatanin mutum, kinga agwai?? Wllh ki ji tsoronsa, barin idan kika ga ya fiye shiru shiru banda haka ki ga fa babu abun kirki da tace har ta bar parlon nan, Bukar dai na ganin boni, mata kamar kurma, ni kwanciyar hankali na ma Imaan bata dauko halinta ba, Imaan xata iya kwatar kanta a ko ina da bakinta, tun daga ranan da na karanta mata ta daina gaida Uwar Mujaheed gashi har yau bata gaisheta, gashi har Ahmadu da Bukar sun gaji sun kyaleta, kusan ma Imaan ce kadai ta dau halina a gidan nan wlh, banda haka ya xata dinga gaida katuwar mata bata amsa mata, da ta fi ta iskanci kuwa kinga ta daina gaishetan gaba daya" Anty dai dariya kawai take, Inna tace "Toh ni dai ki taimake ni Amina ki rufa min asiri, Mujaheed na dawowa ki titsiyesa a daki kiji me na masa da ya dauke kafa a nan" Anty tace "In sha Allah Inna, bari in je nasan ma ya dawo yanxu tunda biyar har ta yi" Inna tace "To yi maxa" tashi Anty tayi ta mata sallama ta fita inna ta mike ta ci gaba da goge gogenta tana cewa "Ahmadu dai ya lalace, da dai ba haka yake ba"

Dariya sosai Imaan ta dinga yi bayan Ammi ta bata sakon inna, tayi mai isarta ta mike daga kwancen da take tace "Ba Inda

xanje Ammi, tun Sunday kinji ta kai karana gun Abba, to haka ya fi, ita da bakinta tace wannan time din ba wasa take ba Abba ya ja mana kunne sosai don muna xuwa part dinta xata tsallake ta gudu ta bar gidan" Ammi tace "Toh nace bayan magrib kije ki gaisheta, kina gaidata ki juyo" Imaan ta fashe da kuka ba hawaye tace "Ammi don Allah ni baxan je ba, ina xuwa xata ce na mata wani abu" Ammi ta mike tace "Toh idan na baki abincin ki kai mata kar ki kai" daga haka Ammi ta bar parlon, Imaan ta fara kukan gaske, har ranta bata son xuwa gun inna. Anty na gama girkin dinner dab da magrib ta fito kitchen, ganin Mujaheed xai fita masallaci tace "Dr idan ka dawo mosque ka sameni bedroom" Yace "Toh" daga haka ya fita parlon, tare suka dawo masallacin da Yusuf, bayan sun haura sama Mujaheed ya shiga dakin Anty, Yusuf ya shiga dakinsa, Anty na xaune kan darduma ta shafe addu'o'in da take ta mike ta dauke pray mat din ta linke tana kallonsa tace "Toh ka tsaya min kamar soja a kai ka xauna" murmushi yayi yana shafa kansa ya xauna gefen gadon, tace "Yanxu M.A idan kowa ya guji inna kai ma sai ka gujeta" ya d'an buda ido yace "Inna kuma?" Tace "Eh mana" yace "Ban gane ba Anty" tace "Kirana tayi daxu wai kwana shidda rabon da kaje bangarenta kai da Imaan" Mujaheed yyi murmushi bai ce komai ba, Anty tace "Toh ka gama murmushin ka tashi ka ta fi ka gaisheta" mikewa yayi yace "Wa?? Ai har abada ni da xuwa apartment dinta, beside irin warning da Abba ya min ma is not funny don haka..." Anty ta karasa masa tace "Baxa kaje ba koh?" Yace "Allah Anty kinga kwana biyu shiru bata ce an mata komai ba hakan bai fi ba?" Anty tace "Toh ni dai nace ka tashi ka je" ya mike xaune yace "Anty ki bari kawai ba inda xanje" Anty tace "Wato ban isa da kai ba kenan, idan Hajiya ce tace kaje xaka ce mata ba xa ka ba?" Yayi murmushi yace "Anty  Hajiyan ma hanani xuwa bangaren tayi gaba daya" Anty tace "Toh tashi ka fita ka ban waje" ya marairaice mata yace "Wllh Anty ina iya xuwa yanxu tace nayi mata wani abun" Anty ta hade rai tace "Cewa nayi ka gaisheta kawai ka juyo" Ya lumshe ido ya bude yace "Wllh da ba don ke bace ni ba inda xanje Anty" Anty tace "Naji din tashi ka fita, idan ka dawo kuma ka xo ka gaya min, gobe da safe kuma xan je in ji ko ka je" Murmushi yyi ya mike ya fita dakin. Tun da Imaan ta fito parlonsu rike da warmer din abinci take tsaye jikin wani flower taki tafiya, kiris ya rage ta fashe Inda take tsaye, daga nisa ta hango Mujaheed yana tahowa waya kare kunnensa, labewa tayi ta koma bayan flower din ta tsaya da sauri, sai da ya d'an wuce inda take ta fito tayi wani kara a bayansa, still yyi na few seconds, ta fashe da dariya ya juya yana kallonta, ya wani hade rai yace "Kee" Ta wara manyan idonta tace "Toh ai baka ji tsoron ba ma" Wani kallo ya dinga mata, ta turo baki ta wuce sa, sai da ya ga tayi nisa sannan ya bi bayan ta, tsaye ya ganta tana lekan parlon inna don kofar ba duka aka rufe ba, ya cire takalmansa outside the balcony yayi tiptoeing har bayan ta, fingers dinsa ya kai gefen cikinta yayi tingling dinta, ihu ta fasa ta sake abincin hannunta, tuni ya janyeta wajen don gaba daya tuwo da miyar dake warmer din ya tarwatse a kasa, ta xaro ido a rikice tace "Innalillahi yaya ka xubar" daga cikin parlor inna ta dinga cewa "Me aka 6arar??" Ummi ta bude kofar, Imaan dai sai kallon abincin take kamar xata yi kuka, Inna ta mike ta taho wajen tace "Meye hakan?" Kamar xata yi kuka tace "Yaya ne ya xubar da abincin da na kawo maki" Inna tace "Toh sai ki kwashe ki mayar mata ta canxa min wani ba ruwana" Imaan ta shige parlon ta xauna ta rungume hannu tace "Salon Ammi ta doke ni ba ga abinci nan Ummi ta kawo maki ba" Inna tace "Aa wllh kinga ina cin wani abu banda tuwo, Ummi maxa kwashe ki kai ma Aisha kice yar ta ta xubar ta xubo min wani" Ummi tace "Mu ma fa tuwo muka yi" A fusace Inna tace "To ni ina ruwana da tuwon ku? Ku tuwon ku har wani dadi garesa miya kamar an wanke kai, ki min abinda nace kada ran kowa ya baci a gidan nan" Ummi ta mike a fusace ta kwashe tuwon ta mayar cikin warmer din, Imaan tace "Dama kice yaya ne ya xubar na ni ba" Inna tace "Haba dai, dama ina xa ki iya xubar da wannan abincin ai sai dai shi" Tsallake miyar Mujaheed yyi ya shiga parlon ya xauna, Ummi ta tafi da abincin da ta kwashe part din su Imaan, gyaran wajen inna ta dinga yi duk suna xaune, bata gama ba Ummi ta dawo da wani abincin ta ajiye ma inna tace "Imaan Ammin ki tace xa ki dawo ki sameta" Inna tace "Sai me xai faruwa idan ta sameta, bakin cikin kara min abinci take komai, ina laifin ma tace xata gamu da Mujaheed din, Imaan ce ta wani san xubar da abincin mutane, bata ta6a ba tunda take, lafiya take kawo min abinci ta koma to yau da yake ta hadu da wnn mutumi a hanya" tana kai wa nan ta shiga parlon tana kallon Ummi tace "Don Allah ki rufa min asiri ki taimakeni ki karasa goge wajen baki ji bayana ba kamar xae cire" Ummi tace "Toh su da suka xubar...." Kallon da Mujaheed ke mata yasa tayi shiru ta mike rai ba dadi ta fita ta ci gaba da gyaran wajen. Inna ta shiga daki sai ga ta ta fito da bowl na dambun nama, tace "Tun ranan litinin nake ta ajiya amma ban gan ku ba na nace to ko lafiya, na ba kowa nasa...." Mujaheed ya amsa yace "Na waye wannan din?" Tace "Na kai da takwara ta" Ya saci kallon Imaan, da sauri Imaan tace "Inna ni dai ki raba mana da kanki" Mujaheed yace "Toh samo leda sai ki raba mana" komawa daki Inna ta yi, Mujaheed ya mike kafin Imaan ta ankara har ya fice parlon, kwalo ma inna kira ta yi, ya saka takalminsa ya kara gaba, inna ta leko parlon tace "Lafiya!" Imaan ta fara kuka tace "Ya tafi da naman gaba daya" inna tace "Maxa tashi ki bisa in ya kama ki je parlon Ahmadu ki tafi" Imaan ta mike ta fita parlon, bata son gudu saboda laluranta, hakan yasa kafin ta iske sa har ya shige part din su, ta goge hawayen da ya cika idonta a ranta tace "Allah ya isa" daga haka ta wuce apartment dinsu kawai, Sai da ta tsaya Ammi ta gama fadanta na xubar da abinci da tayi sannan ta shiga bedroom dinta. Bayan isha tana saka kayan baccinta wayar ta ya fara ring, duk tunaninta Sadeeq ne don kullum sai ya kira ta da daddare sun gaisa duk da basa waya mai tsawo iyaka gaisuwa shikenan amma har wani murna take idan ya kirata, Daddy ta ga ke kiranta, ta daga a hankali tace "Ina yini daddy" yace "Lafiya lau Mamana, ya gida?" Tace "Alhmdlh ya aiki?" Yace "Da godiya, kina karatu sosai dai koh?" Tace "Ehh ina yi" yace "Maa sha Allah, daxu kafin magrib inna ta kirani wai sati daya kenan baki je gaisheta ba, why is that?" Imaan tace "Daddy na fa je yau" Daddy yace "All those days me ya hanaki xuwa?" Tace "Cewa tayi kar mu sake xuwa ni da yaya fa" yace "That's because kuna mata rashin kunya ke da shi, wato warning da na maki kafin in tafi went in vain koh?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Toh kar ki sake skipping one day baki je gaisheta ba, idan Ammin ki ce don ta maki fada xa ki k'i xuwa gaisheta, she is my mother Imaan you have to respect her much, shi ma Mujaheed na kirasa ban samesa ba ki kai masa waya yanxu" Kamar xata yi kuka tace "Toh" daga haka ya katse wayarsa, Hijab ta sa har kasa ta fita, Ammi dake parlor tana kallo ta bi ta da ido, Imaan tace "Daddy yace in kai ma yaya waya" Ammi tace "Shi me ya samu wayarsa?" Bude hannu tayi alamar bata sani ba, Ammi ta ci gaba da kallonta, hakan yasa ta nufi kofa ta fita. Babu kowa babban parlon nasu don hatta kayan kallo ma a kashe suke, ta haura sama ta na kallon direction din dakinsa don har ta manta rabon da ta je wajen, takawa tayi har bakin kofar sannan ta bude tana lekan cikin bedroom din, wani sanyayyen kamshi me hade da sanyi ya doki hancinta da fuskarta, shiga dakin tayi ta kulle kofar, ko ina fes har kan gadon dake dauke da farin bedsheet, Ko ba a fada mata ba tasan wanka yake jin saukan ruwa da kamshin sabulu da ya hadu da kamshin dakin, xaro ido tayi tana kallon sketches dinta dake bangon dakin kusan gudu hudu, tun tana Jss3 tayi drawing din mai kyau coz she is more than perfect a zane, turo baki tayi ta dau kujeran dake gaban mirror ta kai jikin bangon ta hau ta dinga cire hard carbon paper din a hankali kar ya yage. Bude kofar bathroom Mujaheed yyi ya fito da short yana goge gashin kansa da karamin towel, xaro ido yyi yana kallonta da mamaki, ta juya jin an bude kofa suna hada ido ta turo baki tace "Yaya daddyna yace in kawo maka waya" Tana magana wayarta da ta ajiye kan gado ya fara ring, sakkowa tayi da sauri ta dau wayar tace "Ga shi nan ya kara kira" daga haka ta nufesa ta daga kiran ta kai kunne tace "Daddy ga shi nan" mika masa wayar tayi ya amsa ya kai kunne hade da sallama, Kamar ance ta juya taga bowl din dambun naman da ya dauke ajiye a gaban mirror dinsa, yana magana da daddy amma duk hankalinsa na kanta kuma yana lura da ita, ganin ta nufi gun mirror din ya fixgota, xaro ido tayi xata yi magana ya rufe bakin, sai ce ma daddy yake toh don ya kagu ya katse wayar, kamar kuwa daddy ya shiga ransa yace "Shikenan we will talk tomorrow sae da safe" da sauri yace "Allah ya tashe mu lafiya Abba, mun gode, sae da safe" daga haka ya katse wayar ya juyota yana mata wani irin kallo yace "Drawings din da kika cire nake so ki hau kujeran ki maida su yanxu kafin ki fada min sanda na fara wasa da ke da xaki shigo min daki kai tsaye" ta 6ata fuska tace "Toh ba waya na kawo maka ba" Jan kunnenta yayi yace "Baxa kiyi knocking idan kinji ba a amsa ba kiyi wucewar ki" muryar Umma suka ji a corridor tana ma Maimoon masifa wai ta share datti ta kai bakin kofarta lkci daya kuma tana tambayarta ko Mujaheed na dakinsa, Maimoon da ta hade rai tace "Yana ciki" Mujaheed ya xaro ido ya ja Imaan ya bude kofar bathroom dinsa suka shiga ya kulle kofar, dai dai nan kuma Umma ta shigo dakin tana kiran sunansa, Irin tsoratan da imaan tayi ba a cewa komai, Mujaheed ya dukar da ita kasan bayin murya can kasa yace "Kee you better relax now kar in mare ki, ance maki xata shigo nan ne" kai kawai take gyada masa numfashinta na sama, ya cire Hijab din jikinta yace "Nace maki ba fa shigowa xata yi ba, breath in and out gently now" jingina take son yi da bango ya jawota jikinsa ya rungumeta yana shafa bayan ta a hankali to calm her down, tuni Umma ta fice dakin ganin Mujaheed bai ciki, bayan kusan minti biyar jin tana fitar da numfashin a hankali kuma a nutse ya dago kanta yana kallonta, hawaye ne makale idonta, ya daure fuska yace "What?" A hankali ta nuna masa kirjinta, ya mike ya fita bathroom din ya sa makulli kofar dakin sannan ya dawo ya fito da ita dakin, wajen da yake ajiye drugs da allura ya bude yana dube dube, can kasa ya hango inhaler dinta da take bari a dakinsa a da idan ta xo, ya juya ya kalleta ya ga kwanciya tayi kan gadonsa ta takure waje daya, ya mayar da inhaler din ya mike, ya dau gogaggen jallabiyarsa ya saka don tuni jikinsa ya bushe, ya feshe jikin sa da turare, ya dau drawings da ta ciro ya fara maidawa jikin Bangon, Imaan ta mike xaune tana turo baki xata ce masa don me idonta ya kara sauka kan dambun dake gaban mirror, tashi tayi a hankali har sannan hannunta na kirjinta ta isa gaban mirror din ta dau bowl din, karan bude kofar da yaji ya sa ya juya, xata fita da gudu ya bi bayanta da sauri yana cewa "ke har kin manta abinda ya same ki a bathroom ynxu koh, ba ruwana fa idan...." Tuni ta fara sauka stairs, sai da ya tabbatar ba kowa corridor sannan ya bi bayan ta da sauri, amma har ta fita gidan, can ya hangota a durkushe kusa da apartment dinsu, karasawa yyi kusa da ita a hanxarce, ya durkusa kusa da ita yace "Ba nace kar kiyi gudu ba..." Dagata yyi ganin Asthman ne ya tashi ya amshi bowl din, ya wuce da ita cikin apartment dinsu, Ammi ta tabe baki ta mike ta dauko inhaler ta jefa masu, sai da ya ga numfashinta ya dawo dai dai sannan ya mike ya dau bowl din naman ya ajiye a kafarta yana mata wani kallo ya fita parlon, a hankali take sauke numfashi ta bude bowl din ta fara cin naman.

 

 

*The book Imaan is not free, it's for sale, you read for free ur cup of coffee*🤷🏻‍♀️

 

It's 300 via Fcmb 3276052019

Hauwa Bello Jiddah

 

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.

 

16.....

 

Ranan Friday Imaan suka gama exams din first term ss2, suna tsaye tare da Mariya a bakin gate din makarantar tasu ko wannensu na jiran driver, Ummi da Rahma ko fitowa cikin schl din ma basu yi ba, Maimoon dai na tare da wata Kawarta a waje ita ma, Mariya na ganin motar Sadeeq tace "Lahh ya Sadeeq ne ma ashe shi sa ya bata mana lokaci" Imaan dai bata ce komai ba, tunda yayi parking idonsa ke kan Imaan, suna had a ido gabanta ya fadi, siblings din sa duk suka shiga motar, Mariya bata taba sanin Yayan nata na interacting da Imaan ba don Imaan din bata gaya mata ba, Mariya tace "Mu je ku gaisa da shi, shine ya ta6a ajiye ki gida ko baki gane sa ba" Imaan ta d'an yi murmushi kawai, Mariya ta kama hannunta suka nufi gun motar, Mariya tace "Ya Sadeeq frnd dita da ka taba ajiyewa a gida..." Ya cire glass din idonsa Yace "Yea na gane ta" Imaan ta sauke idonta kasa tace "Ina yini?" yace lafiya lau, fatan an gama exams lafiya" tace "Alhmdllh" yace "Toh Allah bada result mai kyau" ta daga kai tana kallonsa tace "Ameen" lallausan murmushi ya sakar mata ta dauke kai da sauri gabanta na faduwa, yace "Let drop u mana" ta girgixa kai tace "Aa yanxu driver din mu xai xo" Yace "Ohk then" ta saci kallonsa ya kashe mata ido daya, ta daga ma Mariya hannu ta juya da sauri ta tafi gun Maimoon, Sadeeq ya tada motar ya bar wajen, Ya Yusuf ne ya xo daukansu bayan tafiyar su Sadeeq da kusan minti bakwai, Maimoon na turo baki tace "Ya Yusuf driver din fa?" Yusuf yace "Ya kai su Umma kasuwa, M.A aka ce ya dauko ku tun daxu ya ki, ni kuma ynxu na dawo aiki" Maimoon ta kyabe baki tace "Da dai Anty Farida aka ce yaje ya dauko, jiya fa da yamma har Hayin d'an bushiya muka je daukota taje gidan aunt dinta, baka ga uwar wahalan da muka sha ba ga hold up sai kusan shidda da rabi muka dawo gida" Yusuf yace "Au suna tare har yanxu kenan?" Maimoon tace "Tab, sosai ma, gobe xata koma schl sai kaga tulin shopping da yayi mata" Yusuf ya sake baki yana kallonta, Maimoon ta kyalkyale da dariya tace "Amma fa wllh ya Yusuf kar ka ce masa komai, dama yace kar in fadawa kowa" Yusuf yace "Ae ko kin fada ma kowa tunda kika fada gaban Imaan da Ummi" Imaan ta hade rai tana kallonsa ta madubi tace "Ya Yousuf kamar ya?" Ya wara ido yace "Ke sai ki kwasa ki kai ma inna, Ummi kuma ta gaya ma Umma, saukin abun dai idan magana ya fita an san it's either Imaan or Ummi sae M.A ya ji dadin jibgarku da kyau" Imaan ta xumburo baki tace "Naji dai" Ummi kuwa yi tayi kamar bata ji sa ba dama, suna isa gida Maimoon tace "Dama ya Yusuf ka ja masu kunne ba ruwana idan suka fada ma kowa" wani kallo Imaan ta watsa mata ta fice daga cikin motar tana turo baki ta kara gaba. Satin da aka shiga banda shirye shiryen bikin Seeyamah babu abinda ake a gidan, tun ranan lahadi yan uwa suka fara xuwa daga nesa gida ya fara cika da jama'a, kowa ya xama busy a gidan barin Umma da Anty, Ammi kam baya baya ta dinga yi, tun a ranan lahadin dama ta kai nata gudunmawarta na tsadaddun manyan bedsheets biyu, da set din food warmer shi ma biyu masu kyau sosai, a walakance Umma ta dubi kayan aka bar su a nan parlorn. Ranan laraba Abba ya ba su Maimoon kudin gyaran gashi da lalli a kai su Saloon, Har xa su fita ya dakatar da su ya ciro wani dubu biyar din yace "Na mance ban bada na mamana ba, gashi nan ta shirya ita ma ta je" Fita suka yi su hudu Ummi na cewa su yi wucewansu kawai don Imaan ba xuwa xata yi ba, Maimoon tace "Ba ruwana Abba cewa yyi mu je mu kira ta" A balcony suka tadda Anty tana magana da wa enda xa su yi girkin biki a biya su, Mujaheed ma na xaune balcony din sai Yusuf dake tsaye, Anty tace "Saloon din xa ku yanxu" Maimoon tace "Anty Abba yace mu je da imaan" Anty tayi wani dariya tace "Wace Imaan din tab, amma ku je dai ku ji abinda xata ce" Imaan na dakinta Maimoon ta shigo parlor, nan ta sanar ma Ammi abinda Abba yace Ammi ta kira Imaan, tana fitowa Ammi tace "sai ki dau Hijab ku wuce saloon" sosai gabanta ya fadi ta marairaice tace "Saloon kuma Ammi, aa ni dai xan wanke gashina da kai na" Ammi tace "Kee! dau Hijab ki fice min parlona, dama idan baki gyara gashin nan ba yau kar ki dawo min gidan nan" Imaan fa fashe da matsanancin kuka tana kallon uwar tata, ganin Ammi ta mike ta shiga daki da sauri ta dau Hijab dinta ta fita, Maimoon ta bi bayan ta tana dariya kasa kasa, Anty na ganinta tace "Subhanallahi me ya faru Imaan" cikin kuka tace "Anty ni fa gashina bashi da wani datti kawai combing dinsa ne bana yi" Anty tace "Toh mu ga gashin" tana shesshekar kuka ta cire Hijab din ta cire hulan kanta,  Yusuf ya dauke kai bai son dariya ta fara wani sabon kukan, ga dai gashi har gashi amma duk an cukuikuye shi waje daya, Anty tace "When last kika wanke gashin" a hankali tace "Ranan nan" Anty tayi murmushi kafin ta ce komai Mujaheed ya mike fuska daure yace "Mu je in kai ku saloon din" Ta fashe da sabon kuka xata koma bayan Anty ya ja ta sai gun motarsa, Yusuf yayi murmushi  yace "Da yake Umma bata nan ba" Su Maimoon duk suka shiga motar bayan ya tura Imaan ciki, Suna isa saloon din Imaan ta hadiye kukan da take barin da taga yan mata kala kala cikin saloon din, Ita Mujaheed yasa a fara gyara ma gashin, da ruwa mai dumi sosai yace a wanke mata gashin nata bayan an sa mai, banda turo baki bbu abinda take tana runtse ido don ba daman kuka ga yan mata kar su mata dariya, lkci daya gashinta ya dawo sak na Indians sai sheki yake, ganin an kusa gama mata ya kalli kannin nasa yace "Sai ku samu napep da xai maida ku gida, coz I am a driver to none of you" daga haka ya fice saloon din, duk suka bi sa da kallo. Sai bayan magrib suka shigo gidan don har da lalle suka yi, dama Imaan direct part din inna ta nufa tun daga bakin kofa ta cire Hijab din jikinta ta shiga tana murmushi tace "Inna..." Inna tayi mitsi mitsi da ido tana kallon gashin nata tace "Ikon Allah kin ganki kin fito sak mace ko?" Imaan ta xaro ido tace "Toh da ni na miji ne?" Inna tace "Idan ba kallon isuhu nake maki wani lkcn ba shegiya nake" Imaan ta fashe da dariya har da kwanciya kan kujera, Inna ta kalli Mujaheed dake cin abinci tace "Ko kai baka gani ba Mujaheed?" Imaan ta hararesa ta gefen ido ta mike xata shiga daki Inna tace "Dawo nan ana ma yar uwar ki gyaran jiki tunda can bangarensu ya dawo kamar wajen cin kasuwar laraba" Imaan tace "Anty Seeyama" Inna tace "Ehh kema da dai Allah ya fiddo maki da mijin nan kiyi aurenki da wuri ki haifi kanninki da uwarki taki haifo maki" Imaan ta hade rai tace "Yar karama da ni xaki ce min aure?" Inna ta kalli Mujaheed tace "Don Allah Mujaheed Imaan bata isa aure ba yarinyar da ke al'ada? Ga kirjinta cike da dukiyar fulani" Murmushi Mujaheed yyi kansa a kasa yana cin abincinsa, Imaan ta harari Inna ta juya ta nufi kofa inna tace "Ke kika sani, ni ba ruwana wllh, Allah na tuba lalurorin ki na duniya ma ai tsaye yake da kafafuwansa gun d'a na, ba gwara kiyi auren ko Bukar xai huta da kashe kashen kudi kije can kuma mijin shi ma ya d'an dana ukubar" Washegari alhamis Imaan ta tashi da ciwon ciki ga bak'i a part dinsu balle tayi raki yanda ranta ke so, duk magungunan da ta sha ba wanda taji ya mata, ta lallaba da kyar ta tafi bangaren inna, ita din ma dai parlon nata duk tsofaffin kawayenta ne a xaune, imaan ta gaishesu da kyar ta shige bedroom dinta ta kwanta, lkcn Azahar nayi dama inna ta lallabo ta shigo dakin ta sa ma bandakinta makulli don ba wanda xai shiga balle ya mata kazanta duk me son yin alwala ga pampo can ta bude, idan kuwa xai kama ruwa ne to yaje sashin masu biki, ganin juye juyen da Imaan take duk ta hada xufa duk da iskan fankan dake dakin ta wani xaro ido tace "Ke lafiya meye hakan, ni fa ba ruwana idan baki da lafiya ne ki tafi bangarenku kada a gigitani a nan, meye wani juye juye kamar macijiya a kan gado na" Imaan ta fashe mata da kuka tace "Wayyo cikina ke min ciwo" Inna tace "Auzubillahi, to rufa min asiri ki sakko ki tafi gun uwarki ba ruwana" Cikin kuka tace "Akwai mutane a can" a fusace Inna tace "Mutanen banxa ina ruwanki da su, idan wani abu ya sameki maganin me mutanen xa su yi banda su cika mu da surutu, dama ba komai ya kawo su ba sai kwadayin d'an shinkafar da xa a raba a kwano da kaji banda haka wani ma anyi shekara goma ba a gansa ba, ki tashi ki tafi tasan yanda xata yi dake idan ma asibiti ne ta kai ki, idan ko ba haka ba idan ban sa an dage bikin ba ace bani ba, biki ya fi rai ne" da kyar Imaan tace "Ni fa marana ke min ciwo" Inna tace "Wai jini?" Imaan ta gyada mata kai, Inna tace "Toh shi kuma wanda kika yi ko sati ba ayi ba fa?" Tace "Ba shi bane kawai alama ne" Inna ta xabga tagumi tace "Ke kam kina ganin jarabawa iri iri a rayuwa na lalura, banda haka jinin ma idan xakiyi sai kin ta fama, anya kuwa ba a sa maki hannu ba imaan?" Imaan ta xamo daga kan gadon tace "Wayyo ni dai ki kira min yaya " Inna tace "Waye kuma yaya?" Hawaye na sakko mata tace "Ni dai ki kirasa" Inna tace "Toh su wa encan tsofaffin duk tsami sun cika min parlor kamar ni xan aurar da 'ya sun ki tafiya, ni dai na gaji wllh ana damuna, wata ma ni nafi shekara talatin ban gan ta ba, ni dai gaskiya sun isheni suje can bangaren da ake biki kuma sun ki, duk parlona ya gauraye da warin tsofaffi, wannan fitina da mai yayi kama" Imaan na son yi dariya amma ciwo yaki barin ta tayi, Inna ta fita fuska daure ta kashe TV da ke aiki tace "Kada TV ya buga in ja ma Ahmadu asara gwara a bar shi haka nan ya huta" daga haka ta dau wayarta ta fita don neman me kira mata Mujaheed, wata ta samu a tsakar gida ta nufeta tana kallon mata yan gayu xaune tsakar gidan, tace "Toh dai gida ba na bitilman bane duk wanda ya xubda ko kwayar shinkafa yyi hakuri ya share fisabillahi, kar a tafi a bar mu cikin wari cuta ta kama mu" mika ma matar wayar tayi tace "Gashi Idan kin iya karatu ki duba lambobi xa ki ga ansa Dakta, lambar Mujaheed ne shi ya sa mun shi a haka, sai ki kira min idan kuma baki iya ba don Allah kar ki rikita min wayar in shiga uku" murmushi matar tayi ta nemo number tayi dialing ta mika ma inna, ta amsa ta kai kunne, sai da yayi ringing sau uku sannan Mujaheed ya daga, inna tace "Mujaheed??" Mujaheed yace "Ina ji, ya aka yi?" Inna tace "Toh ga yar uwar ka nan dai rai a hannun Allah, duk inda kake ka rufa mana asiri ka juyo ka dawo, ni sae in iya cewa a daga bikin ma wllh don idan ta mutu ni nayi asara...." Da mamaki yace "Wacece?" Inna tace "Wacece banda Imaan, tun safe Ashe tana dakina babu inda bata mirgina ba don ciwo, tun daga kan gadon har kasan tass, wai yanxu na shiga dakin don kulle bandakina saboda marasu hankali masu shiga bayin mutum suyi kaca kaca da shi kawai naga yarinya duk ta hada xufa a kan gado kai kana ganin ta kasan...." Mujaheed ya katse ta yace "Ina hanya" daga haka ya katse wayar, Inna tace "Atoh haka kawai, bikin banxa bikin hofi..." Daga haka ta nufi part dinta, tana durkushe bakin kofa tana watsi da takalman jama'a can gefe ganin duk ya cika mata bakin kofar ta ji muryar Mujaheed a bayan ta ta mike, tace "Wannan uban sauri haka kamar wanda ya biyo jirgi, to ka shiga tana can ciki ban san isilinta ba" Shiga parlon yayi ganin mutane ya sunkuyar da kansa ya gaishe su ya wuce dakin Inna, karasawa kan gadon yayi yana kallonta yace "Me ya faru?" Ta fashe da kuka sosai tace "Yaya cikina" hannu ya kai cikin yace "Tun yaushe?" Ta cire hannunsa tace "Ni ba cikin bane ke min ciwo, period ne" ya daure fuska yace "Toh me xan maki, ba kin sha magani ba" da kyar tace "Bai yi ba, doctor Habib allura yake min" yace "Toh me ya hanaki kiransa?" Tace "Yana Lagos" yace "Toh bani da allura a nan sai na koma asibiti" ta kamo hannunsa cikin rawar murya tace "Toh ka tafi da ni asibitin plss" tana fadin haka ta fara kokarin sauka kan gadon, bude baki yyi ganin yanda tayi ma inna stain din kan gado, bai san lkcn da ya dauke kai yana murmushi ba don har ya hango inna, ita ma xaro ido tayi tace "Na shiga uku yaya" yace "Aa sai ta gani xaki ki shiga ukun ai, yanxu kina daya ne" ji tayi gaba daya ba ciwon ta sauko kasa da sauri jikinta na rawa tace "Wayyo yaya ya xan yi" Tana fadin haka ta nufi bathroom ta murda ta ji a rufe, tsayawa kallonsa tayi kamar xata yi kuka tace "Yaya ta sa makulli" parlor ya koma gun inna yace "Inna xata shiga bayi ina makullin" inna ta mike da sauri tace "Auzubillahi, wani bayin? Aa ta fito ta tafi nasu idan ma baxata iya tafiya ba ka goyata, haka kawai bayina fess ta shiga ta sa min k'arnin jini" Kunya ma yasa Mujaheed ya kasa cewa komai don mutanen dake parlon sun kai shidda, ganin inna xata shiga dakin ya rigata shiga da sauri, ya dau dankwalinta ya rufe saman gadon da shi, Imaan ta marairaice tana kallon inna da ta shigo tace "Don Allah ki ban makulli wllh xan wanke maki bayin" Inna tace "Ai uwata bata ce min je ki kya gani ba, don haka ba bayina xa a shiga a min kazanta da jini ba, ki daure ki tafi can bangaren ku idan ma tafiyar ne baxa ki iya ba sai Mujaheed ya goya ki" Kuka Imaan ta fara yi tace "Na fa ce xan wanke maki wllh" a fusace Inna tace "Kai ku fita ma ku bar min dakina kuje can bangaren ku karata, da na bar ki ma kika kwanta min saman gado duk da ban san al'ada kike ba" Mujaheed yace "Toh ki bata xan wanke maki bayin da kai na" Inna kamar xata rushe masu da kuka tace "Yau naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, wai ana dole ne, hypo uku na xuba bayin nan daxu da safe da nake wankewa, a kan wani dalilin xa aje a bata min da karni...." Ya katse ta yace "Ni kuma xan xuba maki hypo biyar" da kyar da kyar da sidin goshi inna ta bada makullin shi ma sai da aka yi yarjejeniyar baxa a bude mata drum din ruwa ba kada a xuba kazanta, Mujaheed ya dau buckets biyu ya fita debo ruwa a waje, Ita dai imaan na tsaye sai satan kallon saman gado take, Mujaheed na ajiye ruwan a bayin ta bi sa ciki tace "Wayyo yaya pant da pad da xan canxa fa?" Ya kalleta da mamaki yace "Ni ma kike tambaya?" Ta marairaice tace "Plss ko xaka je dakina...." Ya jefa mata wani kallo yace "You are stupid" fitowa bayin tayi ta bude gun kayanta a wardrobe din inna, ai ko taga panties dinta na nan, tace "Yaya toh saura pad"  Yace "Bari in xama pad din ki sa" Bata ce komai ba ta turo baki ta shiga bandakin ta rufe, juyawa yayi ya fita, ya tafi gun mai kiosk dake layin ya amso always daya ya dawo, inna dai na xaune ta daura kafa daya kan daya tace "Allah ni dai ya dubeni ya rabani da k'arni, komin xuba hypo da xa ayi a bandakin nan" Mujaheed bai ko kalleta ba ya shiga dakin, yana ta tsaye har Imaan ta fito daure da towel din inna, ya jefa mata pad din kan gado, ta turo baki tace "Thank you" komawa bandakin tayi ba a dau lkci ba ta fito, yace "Sai ki cire xanin gadon ki wanke" ta xaro ido tace "Yaya ya min nauyi fa" bude baki yyi yace "Toh ki bar shi haka nan" kamar xata yi kuka ta isa kan gadon ta shiga cire xanin gadon bayan ya dauke pillows din kai, Muryar inna suka ji tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, jinin ta xuba min a kan gado ni Asabe????" Inna ta fashe da kuka tace "Me na maki xaki saka min da haka Imaan" Mujaheed ya dauke kai yana kokarin danne dariyarsa, imaan duk ta gigice, inna tace "Toh sai ki Kwashi xanin gadon don ubanki ki Bukar kai ma Aisha ta wanke min, kai kuma ka fitar min da katifar waje ka sa min shi a setin rana, Allah ubangiji ya saka min, daga taimako sai ta xuba min al'adarta a xanin gado k'arni ya kashe ni" Inna ta kara rushewa da matsanancin kuka tace "Sannan d'an walakanci tana yoyon xata dau tawul dina ta daura salon ta goga min gaibu, ni dai na shiga uku da wannan 'ya ta Bukar, tana cutata a gidan nan" Imaan ta wani hade rai kamar xata yi kuka, Mujaheed ya cire xanin gadon ya wuce bathroom da shi, Inna na matsar kwalla ta daga hannu biyu sama tace "Allah kaga xuciya daya nake xaune da kowa gidan nan, duk mai nufina da sharri ka min iyaka da shi" Tana fadin haka ta share idonta ta fita tace "Bari xanje inji ko Aishar ce ta sa ki xo ki cuce ni yau" Imaan ta murguda baki ta fiddo kayanta a press ta saka, bude kofar bathroom din tayi ta ga Mujaheed yana aikin wanke xanin gadon.

Post a Comment for "IMAAN 15-16"