IMAAN 13-14
13.🌟⭐imaan⭐🌟
A hankali Imaan tace "Abba nasan idan muka fita kilan xai min fada a hanya" Mujaheed ya kalleta bai ce komai ba Abba yace "Toh ya maki fadan mu ga" Murmushi kawai Mujaheed yayi ya fita parlon, Abba yace "Maxa ku tafi kar kiyi latti mamana" Imaan ta bi bayan Mujaheed tana share idonta, tunda Mujaheed ya fito parlon Abba gabansa ya dinga faduwa, xaune ya ga Umma a main parlor fuskar nan nata a tamke, Mujaheed ya karasa inda take, ita ko bata fasa kallonsa ba, kofar fita Imaan ta nufa, Mujaheed yyi kasa da murya yace "Umma dama Abba...." Katse sa tayi tace "Bana son jin komai, Ban baka izinin fita parlon nan ba in har ni na haife ka Mujaheed, ko da kuwa me xai faru yau" Kallonta Mujaheed ya tsaya yi ba tare da yace komai ba, Anty ta fito kitchen da breakfast a hannunta tayi wani dariya tace "Su haihuwa manya...." Umma ta kalleta ta dakatar da ita da sauri tace "Ke in kina cin k'asa ki kiyayi ta shuri, ki daina min
shisshigi a lamari na, ki yi mai fissheki kawai a gidan nan" Anty ta tabe baki tace "Anya akwai wanda ya kai me shiga lamarin d'a da ubansa shisshigi kuwa, kuma naga duk wanda xai ce d'a kada ya bi umarnin mahaifinsa shine mai babban shisshigi a rayuwa kuma bai dauko abinda xai fishshesa ba" Umma ta mike rai bace tace "D'an ki ko nawa? tunda ba wata shegiya ce ta haifa min d'an ba sai kiyi ta kanki ki, ki kuma cire min ido kan d'a na" Anty tace "Na wuce in tsaya ina xance irin na yara da ke, amma bari in baki shawara, domin kin haifi Muhammad ba yana nufin ke kadai ke da iko da shi ba duk ki bi ki takura ma yaro sai abinda kike so xai yi a gidan nan, kina amfani da advantage din ganin yana maki biyayya dari bisa dari...." Cikin tsawa Umma tace "Da ke da shawarar taki Allah kwashe maku albarka..." Dai dai nan Abba ya fito parlon jin hayaniya, ya kalli Mujaheed dake tsaye, ya kalli Yusuf dake tsaye stairs yana kallon su shi ma sannan ya kalli su Umma yace "Me ke faruwa nan?" Rai bace Umma tace "Ka ja ma matar ka kunne Alhaji ta fita harkata kada abu ya bace tsakanin ni da ita a gidan nan, ta cire ido kan d'a na, ta kuma yi ta kanta..." Abba ya dakatar da ita yace "I asked what happened kina min warning madam" Anty ta tabe baki tace "D'an ta da ka aika yanxu... ta hana shi xuwa saboda isa da gadara, to ni kuma bana gani inyi shiru...." Abba ya kalli Mujaheed da ya kasa dagowa ya mika masa hannu yace "Bani makullin motar...." Da kyar Mujaheed ya dago yana kallonsa sannan ya kalli Umma, ta watsa masa wani kallo alamar ya basa, a hankali Mujaheed yace "Abba ai bance fa baxan je ba" yace "Eh baka ce ba, amma ba ni" Mika masa makullin Mujaheed yayi, Abba ya kalli Yusuf yace "Here, ka tafi ka ajiye Imaan a makaranta" Yusuf ya karasa saukowa stairs da yake tsaye ya amshi makullin sannan ya nufi kofa ya fita, Juyawa Abba yyi ya koma parlonsa, Mujaheed ya wuce sama a sanyaye, Anty ta tabe baki ta wuce saman ita ma, wani ajiyar xuciya Umma ta sauke ta koma ta xauna ranta fess. Sai bayan da suka bar gidan Imaan ta kalli Yusuf tace "Ya Yusuf Umma ce tace yaya kar ya kai ni koh?" Yusuf na driving yyi murmushi yace "Toh dama ya xa ayi ta bari ya kai ki?? salon ku je ya d'an rankwashe ki ki dawo kina mana ihu kina kuka" xaro ido Imaan tayi tana kallonsa, Ya ki kallonta sai murmushi yake, ta hade rai tace "Toh an doki mutum kuma baxai yi kuka ba" Yusuf yace "A'a xai yi kuka abunsa" Turo baki tayi bata ce komai ba, shi ma bai kuma cewa komai ba har ya iso islamiyyarsu ya tsaya bakin gate, ya kalleta yace "Kin fa yi latti sosai" tace "Ae xa su ga idona kuma cewa xanyi bani da lafiya, dama ban da lafiyan" daga haka ta bude motar ta fita, D'aga masa hannu tayi, yayi mata murmushi ta shiga cikin makarantar. Imaan na dawowa islamiyya karfe sha biyu kashegari lahadi ta fara shirin tafiya gidan gwaggonta wato Mahaifiyar Ammi dake unguwar rimi, Tun da ta fito daki Ammi dake xaune parlor ke kallonta, tsadadden atamfa ne jikinta sai dan kunnenta na gwal, babu abinda ke fuskarta banda eye pencil da chappete da ta goga a lips, sosai tayi kyau duk da haka, da mamaki Ammi tace "Ina xa ki?" Imaan ta xauna kusa da ita tace "Gidan Gwaggwo mana Ammi" Ammi ta mata wani kallo tace "Kin gaya ma Daddy ne?" Ta marairaice tace "Daddy baxai hanani ba fa na sani" Ammi tace "Baxa fa ki fita gidan nan ba sai da saninsa don ba ruwana" tashi Imaan tayi kamar xata yi kuka ta shiga dakinta kiran Abba, wayarta da bata damuwa da ta dauko ta yi dialing number sa, bayan wani lkci ya dauka, ta amsa sallamarsa sannan ta gaishesa, yace "Ya kike Imaan" tace "Lafiya Daddy ya aiki?" Yace "Alhmdllh, har kun dawo islamiyyar?" Tace "Ehh daddy dama gidan gwaggwo nake son in je in gaisheta shine Ammi tace sai na gaya maka" yace "Ae kina da islamiyya da yamma mamana" kamar xata yi kuka tace "Ae kafin karfe hudu xan dawo" yayi shiru kafin yace "Toh waye xai kai ki?" Tace "Ni kadai Daddy ai ina xuwa ni kadai" yace "Kai ma Ammin ta ki waya" fita dakin tayi ta kai ma Ammi waya, Ammi ta amsa ta kai kunne, daddy yace "Why not drop her plss bana son tana fita ita kadai" Ammi tace "Sai kace wata yar shekara goma yallabai, she do go out her self...." Daddy yace "Toh minti nawa ne kin ajiyeta ki dawo" Ammi tace "I told u for the past two month ban shiga motar nan ba, sai dai ta bari next week mu je tare idan Allah ya yarda, ina da aikin da xan yi yanxu, ko jiya fa naje gidan gobe ma xan je, yau kuma sai na kai Imaan?" Daddy yace "Bata wayar" Ammi ta mika mata, daddy yace "Mamana ki bari next week ku je da Ammin ki idan Allah ya kai mu" imaan ta fashe da kuka tace "Bayan na shirya daddy, na fa san hanya ba yau xan fara xuwa ni kadai ba" Daddy ya dan yi shiru kafin yace "Shikenan to kije, but go with ur nose mask, and inhaler, Allah ya kiyaye hanya" tana goge idonta a hankali tace "Toh daddy na gode" Ammi ta shiga kitchen ta dauko dambun naman da tayi ma mahaifiyarta tace "Ki kai ma gwagggo ina gaisheta sai na xo goben" Imaan ta amsa tace "Toh" dubu Biyu Ammi ta bata ta bar gidan bayan tasa gogaggen Hijab dinta har kasa, a dai daita Imaan ta samu da xai kai ta har gidan, bayan sun isa ta sauka ta basa kudinsa sannan ta shiga gate din gidan, babban gida ne sosai da su Ammi suka siya ma mahaifiyar tasu, Ammi ce ta biyu gun gwaggwo bayan babban yayansu Umar, sai maxa biyu da mace daya Anty Murja, duk sun yi aure da 'ya yansu, yar Anty Murja ta biyu Halima ce ke gaban gwaggwo kuma ita xa ayi aurenta kwanan nan, Sosai Gwaggwo tayi murnar ganin Imaan, duk cikin jikokinta ko da bata nunawa ta fi jin Imaan har ranta, Imaan ta rungumeta cike da jin dadin ganinta ita ma, Gwaggwo tace "Kin guje ni Fatima" Imaan tace "Toh Gwaggwo kinga idan naje boko da safe da yamma muna dawowa xan wuce islamiyya, ranan asabar kuma islamiyya safe da yamma, yau ma kawai dai na taho ne kuma da wuri xan koma saboda islamiyya" Gwaggwo tace "Toh Allah ya maki albarka ya baki sa'a a karatun ki, ya Ammin ki fa?" Imaan tace "Tana gaishe ku, tace in kawo maku wannan" Gwaggwo tace "Toh nagode Allah mata albarka, fatan mutan gidanku duk suna lafiya" Imaan tace "Duk lafiya lau" Ammi tace "Mujaheed ya daina xuwa min kwata kwata yanxu yana kasar kuwa?" Imaan tace "Yana nan" Gwaggwo tace "Ikon Allah, shi kuma d'an farin fa, duk da shi baya ma gaida mutane dama" Imaan tayi dariya tace "Shi ma yana nan" Gwaggwo tace "Toh Allah maku albarka, in ji kakarku tana lafiya" Imaan ta turo baki tace "Ehh" Gwaggwo tace "Toh Allah ya kara mana lafiya, ki dauko lemo fridge ki sha" Imaan ta gyara xamanta tace "Anty Halima bata nan ne?" Gwaggwo tace "Taje kai anko" Imaan tace "Toh ni ba a ban ankon ba" Gwaggwo tace "Xa ta kai maki naki har gida tace" Imaan ta washe baki tace "Toh" mikewa tayi ta dauko malt daya ta dawo ta xauna ta fara sha tana cin dambun naman da ta kawo, Gwaggwo tace "Inji yanxu ciwon ki yana sauki sosai kamar yanda mahaifiyar ki ke gaya min idan na tambaya" Imaan tace "Ehh da sauki" Da damuwa Gwaggwo tace "Allah ubangiji ya yaye maki wannan cutar Fatima, in sha Allah xaki samu lafiya gaba daya muna nan muna gaya ma Allah" Yar dariya Imaan tayi tace "Gwaggo ya Salim yana xuwa?" Gwaggwo tace "Yauwa kwanaki yayanki Muhsin ya kawo min karar ki wai baki gaida mutane" Imaan ta hade rai ta daina cin naman da take tace "Ni kullum sai yace bana gaishesa, to ma a ina nake ganinsa balle in gaishesa" Gwaggwo tace "A'a Fatima ga wannan dai waya da ta kawo komai da sauki, ko shi kika dauka ai xa ki kirasa ku gaisa" Imaan ta turo baki tace "Toh shi ma fa ba kulani yake ba wllh" cike da damuwa Gwaggwo tace "Ni dai ku rike xumunci don Allah, ba kya ganin yanda iyayenku ke yi ne, ubansa ya sha nono ya bar ma uwarki, wllh baki da yan uwan da ya wuce su don mutan gidanku ba son ke da uwar ki suke ba duk an sa maku ido, ga kakarku fitinanna, kiyi ma kanki fada ki rike xumunci da yan uwanki na nan, duk suka xo gaisheni sai sun tambayeni ke ba Usman ba, ba Muhsin din ba, ba Salim ba ga matan su ma gaba daya, ke sai kiyi shekara baki xo nan ba baki je gidajen nasu ba shi sa bakwa hadu duk da ba laifin ki bane laifin uwar ki ce don ita ya kamata ta sa ki a hanya ta kuma sa maki ido" Imaan dai sai cin namanta take tana shan malt, sallama aka yi bakin kofa Gwaggwo ta amsa Muhsin ya shigo tare da abokinsa, Gwaggwo tace "Sannun ku da xuwa, yanxu nake xancen ka Muhsin" Muhsin yayi murmushi yana kallon Imaan da ta ki kallonsa yace "Wannan fitsararriyar ce ta xo ashe" Gwaggwo tayi dariya tana kallon abokinsa tace "Sannu da xuwa Sadeeq kwana biyu ka gujeni" murmushi yyi ya cire glass din idonsa ya karaso Inda take ya durkusa yana kallon Imaan da taki dago kai sai cin namanta take yace "Sannu Kaka ina yini" Imaan ta daga kai don muryar sounds soo familiar, Gwaggwo tace "Lafiya lau Sadeeq ya mutan gidanku? Ya kuma aiki da kujuba kujuban rayuwa" ya sauke kansa kasa yace "Alhmdllh mun gode Allah Kaka" Gwaggwo tace "Toh Allah yayi maku albarka ya kare ku sharrin makiya, ya tsare ku da tsarewarsa" a hankali yace "Ameen" ya kai idonsa kan Imaan that was so uncomfortable, Muhsin yace "Ina yini Anty Imaan" boye fuskarta tayi da kujera yace "Ke yanxu kin girma kin daina kula kowa kin mance lkcn da kike kuka sai an goya ki, kiyi ta bamu wahala muna goya ki a anguwa koh" kamar xata yi kuka tace "Ya Muhsin bana so ni yaushe nake kuka a goya ni" yayi dariya yace "Tunda kin girma kin manta ai shikenan, gashi nan ma kin daina gaida kowa" kamar xata yi kuka tace "Ya Muhsin kai ma fa ba magana kake min ba, ni da bani da lafiya ka tambayi Ammi ma, kuma ni ina dadewa ban hau whatsapp ba, wayar ma ba amfani nake son yi da shi ba" yace "Yaushe ne baki da lafiya?" Gwaggwo tace "Kai ma dai Muhsin sai kace baka san dawan garin ba, sai kayi mata addua da fatan samun lafiya" Muhsin yace "Toh Allah ya sauwake Imaan amma ai kina shan magani koh?" Ta gyada masa kai ba tare da ta dago ba, yace "Sannu lil sis" ta turo baki a hankali ba tare da ta dago ba still tace "Ina yini" ya xaro ido yace "Toh boye fuskar ta meye, Kunyata kika fara ji ko na abokina" ya fadi haka yana muna sadeeq dake kallonta, kin dagowa tayi ta kuma ki cewa komai, shi dai Sadeeq sai kallonta yake, Gwaggwo tayi dariya tace "Fatima kenan, to tashi ki shiga ciki" kamar jira take ta mike ta wuce dakin Gwaggwo da sauri, Muhsin yayi murmushi yace "Imaan Daru" mikewa Gwaggwo tayi ta dauko ma Sadeeq ruwa da lemo yace "Da kin bar shi Gwaggwo daga gida mu ke ai" Gwaggwo tace "A'a idan baka son inyi fushi to ka sha, ga dambun nama yanxu Imaan ta kawo min" murmushi yyi ya dau bottle wata daya ya bude, Muhsin yace "Wai ban ga Amaryar gidan nan ba?" Gwaggwo tace "Taje kai anko, nasan tana hanyar dawowa yanxu" Muhsin yace "Da alama dai duk Halima ta kagu ta bar ki" Gwaggwo tace "Don bata nan shine xaka mata wannan sharrin, to bari dai ta dawo" Muhsin yyi dariya yace "A'a ni dai ba ruwana rufa min asiri Gwaggwo" Sadeeq dai sai murmushi yake yana danna wayarsa, hira suka dinga yi gaba daya a parlon har kusan Asr, Muhsin yace "Gwaggwo bari mu je masallaci mu dawo yanxu" Gwaggwo tace "Toh Allah maku albarka" Muhsin ya mike tare da Sadeeq suka nufi kofa, tashi Gwaggwo tayi tana kiran Imaan da bacci ya dauke tun daxu a dakin. Suna fita compound Sadeeq na kallon Muhsin yace "Wacece yarinyar nan Muhsin?" Muhsin ya wara ido yace "Ko dai kana ciki ne Abubakir?" Sadeeq yace "Na santa ne shi sa nake tambayarka" Da mamaki Muhsin yace "Haba, amma ban ga ta nuna alamar ta san ka ba" Murmushi Sadeeq yyi yana shafa sajensa yace "Ni na nuna alamar na santa banda yanxu da na fito?" Muhsin yace "Toh ina ka santa?" Sadeeq yace "Baka fada min relation dinka da ita ba" Muhsin yace "Cousin dita ce, mum dinta ita ce immediate sister din Abbana" da mamaki Sadeeq ke kallon sa yace "You mean you two are this close?" Muhsin yace "Sure" Sadeeq yace "That's Amazing, she is Mariya's school friend kaga dalilin da ya sa na santa" Muhsin yace "Maa sha Allah, amma bata gane ka ba ko?" Murmushi Sadeeq yayi yana maida glass dinsa yace "Ta gane ni sarai, that was why she was uncomfortable" Muhsin yyi dariya yace "Ohh I see, there is something a kasa kenan" Sadeeq yace "Let not miss jam'i plss" daga haka suka shiga masallacin don yin alwala. Imaan na idar da sllh tace ma Gwaggwo xata wuce don xata islamiyya, Gwaggwo tace "Baxa ki ci abincin ba kenan, shinkafa ce da miya fa" Imaan tace "Bana jin yunwa fa Gwaggwo" Gwaggwo tace "Toh shikenan ki duba siff a daki xaki ga wani sabon hijab da na dinka maki da takalmi ki dauka," Imaan tace "In ji me hannu ne Hijab din?" Gwaggwo tace "Ae nasan me hannu kike sawa, shi nayi maki" Bude kofar parlon aka yi Muhsin ya shigo tare da Sadeeq, Muhsin yace "Har kin fito kenan yan matan Ammi" Imaan tayi murmushi tace "Ehh wucewa xan yi saboda islamiyya" Muhsin yace "Mu ma yanxu xa mu wuce ai" Gwaggwo tace "Toh sai ku ajiye min ita don Allah a gida kar ta kara bin k'uran nan ta koma a samu matsala" Dariya Muhsin yayi yace "Wa yaga imaan baturiya" Imaan ta boye fuskarta, dubu biyar Sadeeq ya ajiye ma Gwaggwo yace "To kaka xa mu koma sai wani lkcn kuma, ba yawa wannan ki siya goro" Gwaggwo tace "A'a gaskiya ka dau kayan ka Sadeeq, matsalata da kai kenan idan ka xo gidan nan kai baka gajiya ne" murmushi kawai yayi, Muhsin yace "Shikenan dama ban fito da kudi ba ya fanshe ni, sai ki raba, nawa da nasa" Gwaggwo tayi dariya tace "Allah sarki, Toh Allah dai ya maku albarka ya ba ku mata na gari kuyi aure ku bar xaman nan da ku ke" Muhsin yace "Toh Ameen Gwaggwo" Tare Imaan suka fita da Muhsin don Sadeeq har ya fita, ta bude back seat ta xauna, Sadeeq ne xaune driver seat din Muhsin ya shiga front seat suka bar anguwar. Hira suka ta yi a motar, ita dai danna wayarta kawai take, amma da ta daga kai xa su hada ido da Sdeeq ta madubi, sai tayi maxa ta sauke kanta, bayan tafiyar kusan minti sha biyar ta ji Muhsin yace "Ajiye ni nan man" parking Sadeeq yyi, Muhsin ya fita yana kallonta yace "Toh anmata sai mun yi waya ki gaida Ammi, abokina xai ajiye ki gida" ta xaro ido tace "Ya Muhsin nima nan fa sauka xan yi dama" Muhsin yace "Inaaa... bayan amana Gwaggwo ta ba mu mu kai ki gida kada kura ya taba ki, nima akwai abinda xan yi anguwar nan ne amma da tare xa mu tafi" Imaan ta dinga kallon sa kamar xata yi kuka, ya daga mata hannu yana danne dariyarsa yace "Sadeeq drive her carefully plss sai mun yi waya" daga haka Sadeeq ya ja motar suka hau saman titi, Imaan dai sai wasa take da fingers dinta, bayan wani lkci ta dago a hankali tana kallon gaba suka hada ido ta madubi, da sauri ta sunkuyar da kanta, yayi murmushi yace "Kina tsoron kada in sace ki ko?" Kin cewa komai tayi, bayan kusan minti biyu taji cikin cool voice dinsa yace "I am Abubakar Sadeeq Ahmad, was born and bred up here in Kaduna, first son of the family, my primary and secondary education all in Kaduna, before I proceed to UK where I had my degree and msc, I am a medical practitioner....." Kallon sa kawai Imaan take ta madubi, yyi murmushi yace "Mariya is my step sis, I have six siblings altogether, ranan kinje gidanmu amma part din stepmum dita, namu part din yana cikin gidan though very far away, soo you've known almost all about me... Yes I am still single and searching..." daga haka yyi shiru ya kalleta yana murmushi yace "Do you mind telling me about ur self" shiru tayi da farko, can a hankali tace "Sunana Fatima Abubakar amma ana kirana Imaan" ta kallesa don a hankali yake driving din kasancewar bbu motoci sosai titin, ya gyada mata kai alamar yana ji, yana murmushi, murya can kasa tace "I am the only child of my parent" Da mamaki ya dinga kallonta, ta sunkuyar da kanta tace "I am In the same class with Mariya both School and Islamiyya, muna xaune tare da Daddy na da Ammi, with my paternal grandmum, and my Uncle with his family, i mean my father's senior brother" Sadeeq ya gyada kai a hankali yace "That's nyc, Allah maki albarka ya sa ki xamo the Apple of ur parent eyes" Murmushi tayi murya can kasa tace "Ameen" ganin sai tafiya yake ta bude manyan idonta tace "To ai baka san inda xaka kai ni ba" ya kalleta ta madubi yace "Kin manta ranan da Antynmu ta sa na ajiye ki gida kenan?" Ta wara ido tace "ohh na tuna" ya d'an yi murmushi, suna kusa layin yace "Toh baki fada min samarin ki nawa ba?" Ta xaro ido tace "Samari kuma?" Yace "Yeah" tace "Tabb, ni bani da Samari" yace "Sai dai frnds kenan" ta turo baki, yayi murmushi yana kallonta, tace "A school bani da male frnds, a islamiyya ma haka, a gida ne kawai" yace "Toh su waye?" Tace "Cousins dina" yace "Really?" Ta gyada masa kai, yace "Can I know them" murmushi tayi tace "Ya Yusuf ne sai yaya.. Ohh yaya yusuf ne ma kadai, mun daina shiri da yaya yanxu" yace "Can I know the Yusuf?" Tace "Yea he is my cousin, an engineer yana aiki a nan yana yi a Kano yana yi a zaria" yana parking kofar gidan su yace "Shi dayan fa?" Tace "Yaya?" Ya gyada mata kai tace "Shi wani lkcn yana Abuja wani lkcn yana nan, yanxu yana nan" Sadeeq yace "Maa sha Allah, to me yasa bakwa shiri?" Tace "Yanxu ya fiye mugunta baya kuma kulani kamar da" tana magana ta bude kofar motar tace "Nagode" ba karamin daure ransa yyi ba yace "Wait ara min fone naki pls, I want to confirm ko Muhsin ya tafi da nawa cos I can't find it here" komawa tayi ta xauna ta basa wayarta ya amsa ya gama danne dannensa sai ga ring din wayarsa, ya mayar mata yace "ohhh thanks yana nan ashe" ta fita motar tace "Thanks" yayi murmushin da ya bayana dimples dinsa yace "You are welcm" Xaune ta ga Mujaheed gun mai kiosk a kofar gidan yana kallonta, duk da yanda gabanta ya fadi ta dauke kai da sauri ta wuce cikin gida ta rufe gate.
*I want to use this
medium to bring this to the notice of my Fans, akwai wani namiji mai amfani da
information dina gaba daya both Facebook and WhatsApp, a lot suna chatting da
shi a tunaninsu ni ce, to bani bace ba wllh, masu nemana Facebook idan sun yi
searching xa su ga account biyu iri daya, to ni nawa account din daga followers
kadai ma mutum xai gane it's real me bcos the followers are much, idan mutum ya
duba post na timeline dina ma xai gane account dina ne, duk da ko wani update
nayi shi ma sai ya sata yayi, ga lambarsa kamar haka masu chatting da shi ta
WhatsApp 09031263639.... Billah namiji ne kuyi ta kanku, har card wasu na tura
masa da sunan xa su siya littafin Imaan to bani bace, da yawa na cewa sun biya
Noor Hayat ban sa su group ba ban basu littafi ba to shi suka ba kudinsu ba ni
ba. Beware fans katon namiji ne yake claiming khaleesat Haiydar kuma ni na bar
sa da fitowar rana da faduwarsa, duk da ban ma yarda shi din Muslmi bane, Allah
ya Isar min, a yanda ya fara a gantale haka xai kare a gantale*
Littafin Imaan is 300
via... Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Show ur evidence of
payment through my WhatsApp digit... 07087865788, subscribe and read happily
without feeling any guilt.
_Su ma masu editing min
novel su sa abinda ban yi niyyar sawa ba, bayan fitar da shi da suke ban yi
complain ba... we shall meet in the hereafter in sha Allah_ 😇
14. Imaan
Mikewa Mujaheed yyi ya
bi bayanta, tunda Imaan ta shiga gidan daman take waigen kar ya biyo ta, ido
hudu suka yi da Umma da ta fito tare da wata bakuwa, ta dauke kai ta ci gaba da
tafiyarta da sauri, Mujaheed na ganin Umma dama ya canxa direction dinsa, Umma
na kallon sa tace "Daga ina kake?" Yace "Ina xaune a waje, xan
wuce wajen aiki ne yanxu" Umma ta bi Imaan da kallo sannan ta kara kallon
sa, ya d'an buda ido yace "Umma ni ban gane kallon nan ba, ki tambayi mai
kiosk din can tun daxu nake wajen a xaune wllh" Kawar Umma tace "Yi
wucewan ka kaji Muhammad" Murmushi Mujaheed yyi ya wuce ciki, tafiya suka
ci gaba da yi Umma tace "Gani nayi kamar tare suke da warcan mai laluran
da ta wuce yanxu" Hajiya Saude tace "A'a da xan shigo daxu fa na
gansa xaune inda yace maki, to minti na nawa a ciki ko minti sha biyar fa ban
yi ba" Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Da kin san irin k'i da
tsanar da nake ma uwar yarinyar nan har cikin raina ko Hajiya Balaraba, wllh
abun ba kyau, xan iya komai a duniya don ganin na walakantata, yanda nake jin
tsanarta a rai ko kishiyata Amina ban jin ta haka, sai in ki cutar Amina amma
ita xan iya cutar ta, sai ga tsanar har ya shafi wannan figaggiya irin ciwon da
ta haifo duniya, duk na tsane su kamar yanda na tsani mutuwata, bayan na dawo
gidan nan da kyar fa na raba Mujaheed da yarinyar, sai da na tashi tsaye
kyamm" Hajiya Balaraba tace "Ikon Allah to sonta yake shi din?"
Umma tace "Auzubillahi kaji wata magana wai so, ni na haifi Mujaheed na
san halinsa, wllh ba so bane kawai shakuwa ce tsantsa da shisshige masu da
yake, sannan yarinyar ta yi mugun sabo da shi, kuma a da kafin in dawo shi ke
tsaye kan bata magunguna da dai abubuwa da ya shafi lalurorinta, kin san
sickler ce sosai...." Hajiya Balaraba tayi dariya tace "Ba fa a
shaidar d'an yau Hajiya, ke kin shiga xuciyarsa ne kika ga ba sonta yake
ba?" Umma tayi wani murmushi tace "Kin san akwai wani abokinsa
Ibrahim iyayensa hamshakan masu kudi ne, shi ma yaron ya jike jagab da naira,
da ban yi da gaske ba wllh ita Imaan din ya so hadawa da yaron wai ya nemeta,
ga yaron mai hankali da nutsuwa, wllh sai da na masa jan ido sosai, don in dai
ina raye abun arxiki baxai taba xuwa inda Aisha da 'yar ta suke ba, baxan bari
ba in sha Allah ina nan ina sa ido in ga wanda xai jajibe yarinyar da gwara
babu da ita, kullum fa ana hanyar asibiti kamar 'yar da aka sama ta mugun
hanya, to fa da nayi da gaske da Mujaheed shine ya hada yaron da kanwarsa Ummi,
yanxu ana gama bikin Seeyama xa a fara xancen na Ummin, Uban yaron fa abokin
gwamnan garin nan ne na kut da kut" Hajiya Balaraba tace "Toh Allah
dai ya kyauta" Umma tace "Sannan shi Mujaheed din akwai wata yar talakawa
da yake mutuwar so wai farida, ni a bincike na ma cewa aka yi idan ban tashi
tsaye ba wllh sai ya aureta don yayi mugun kwallafa rai a kanta, baki ga
hidimar da yake mata da iyayenta ba, duk ya talike a kansu har haya na samu
labarin yana biya masu don nasa mutane su sa masa ido a anguwar, in sha Allah
na kusa cire masa yarinyar a ransa gaba daya sai dai idan ba ni ce na haifesa
ba, sa'anninsa na neman 'ya yan masu kudi shi ya buge da neman talauci salon su
mallake min shi su tsiyace shi, iyayen fa matsiyata ne na gaske wllh"
Hajiya Balaraba tace "Toh shi ina ya samota?" Umma tace "Wllh
wai ya dawo daga Abuja ranan, kin san wani lkcn jirgin kasa yake biyowa ta a
nan anguwar ya ganta dai dai layinsu wai xata Unguwar sanusi, shine fa ya rage
mata hanya daga nan kuma ta makale masa ina jin, ni dai ina nan ina kokarin
cireta a ransa gaba daya" Hajiya Balaraba tace "Gaskiya kam, Allah
dai ya mana tsari" Umma tace "Ameen" sallama suka yi Umma ta
koma ciki. Bude kofa Imaan tayi ta fito misalin karfe tara na dare don kwashe
socks da kananun kayan da Ammi ta wanke mata a cloth line, da kyar take tafiya
don ji take kamar xaxxabi xai rufeta ga ciwon kai, tun bayan Isha Mujaheed ke
xaune kan farin kujera ta wajen parking space dinsu, yana jin fitowarta kuwa ya
mike ya tsaya kusa da wani flower dake opposite cloth line din, bbu wuta gaba
daya a wajen hakan ya ba Imaan mamaki sai tayi tunanin mutuwa bulb din yayi,
nan ko shi ya cire bayan ya dawo masallaci, sai da ya jira ta fara kwashe kayan
nata sannan ya cafkota ta baya, yasan next action dinta hakan yasa ya rufe
bakinta da sauri, tayi mugun tsorata wanda hakan yasa ta fara numfashi da
sauri, yayi freeing bakinta yana kallonta don gaba daya ya ma mance da laluran
nata, ya dukar da ita da sauri yace "Ke relax now, nine fa, stay still and
relax" kasa yin hakan tayi babu bata lkci kuma Asthma dinta ya tashi a
wajen, daga ta yayi ya shiga apartment dinsu da ita, Ammi ta mike tana
kallonsu, ya xaunar da ita kasa, Ammi ta wuce dakinta ta dauko inhaler dinta ta
mika masa ya amsa ya bude cap din ya kai mata baki, sai da Ammi ta ga
numfashinta ya fara dawowa steady sannan ta juya ta wuce bedroom dinta.
Kwanciya Imaan ke son yi ya dagota yana kallonta yace "Ina ke maki
ciwo" Hawaye cike idonta ta nuna masa kafarta, yace "Kin sha
magani?" Ta girgixa masa kai, yace "Ina magungunan?" Ta nuna
masa bedroom dinta, dagata yayi suka wuce dakin nata, ya dau magungunan ya bude
su sannan ya fita xuwa kitchen ya dauko ruwan gora da glass cup ya koma dakin,
bata maganin yayi ta karba ta sha, ya mike ya dauko na tube da take shafawa a
kafanta da bayanta, dawowa yayi kan gadon ya durkusa kusa da ita ya daga rigar
baccin jikinta xuwa thigh dinta, ta bude ido tana kallonsa, duk ta wani
langwabe tana sauke numfashi a hankali, shafa mata man xafin ya shiga yi, kamar
xata yi kuka murya can kasa tace "Wayyo Yaya yana min ciwo" hararanta
yyi bai dai ce komai ba, ta runtse ido ta kama hannunsa tace "Ni wllh ciwo
yake min ka min a hankali" Buge mata hannun yyi ta janye da sauri, haka ta
dinga yarfe hannu har ya shafe mata maganin daga thigh har fararen toes dinta,
gaba daya jikinta ya dau xafi wanda at anytime xaxxabi zae iya rufeta, a
hankali tace "Yaya saura bayan" yana kulle tube din yace "Baxan
yi ba" da kyar ta mike xaune ta sauke rigan jikinta xuwa waist dinta ta
koma tayi rub da ciki, yace "Ki shafa da kanki baxan shafa ba" a
hankali tace "Baxan iya ba ae, don Allah ka shafa min" da kamar baxai
shafa ba sai kuma ya bude tube din ya matso methylated cream din ya fara shafa
mata a bayan a hankali, lumshe ido tayi cikin sanyin murya tace "Yaya kai
na ciwo yake min sosai, kamar xaxxabi xan yi" ya hade rai yace "Ina
kika tafi daxu?" Ta bude ido da sauri tace "Gidan Gwaggwo naje"
yace "Waye ya ajiye ki a mota?" Ta xaro ido sai kuma ta turo baki
bata san duk yana kallonta ba, yace "Ba tambayar ki nake ba" kamar
xata yi kuka murya can ciki tace "Ya Muhsin ne fa" mintsilinta yyi a
bayanta yace "Ni xa ki ma karya?" Ta yi wani kara ta mike xaune da
sauri tana shafa wajen, ganin kallon da yake mata ta xaro ido tayi wani karan
ta koma tayi rub da ciki tace "Wayyo bana so yaya" yace "Nace wa
ya ajiye ki daxu?" Ta rufe idonta tace "Ya Muhsin" yace
"You are still lying koh? Wannan yayi kama da motar Muhsin?" Ta turo
baki tace "Ya canxa mota" yace "Ohk, idan kika bari na fita
dakin nan baki gaya min ko waye ba, this case will pend har ki gama langwabe
langwaben ki kuma I promise i will deal with you" kamar xata yi kuka tace
"Yaya abokin ya Muhsin ne fa, tare muke da shi sai ya sauka a wani anguwa
xai yi wani abu shine abokin ya ajiye ni shi, ka kira ya Muhsin din ma ka
tambayesa wllh" yana gyada kai yace "ke yanxu kin girma baki da aiki
sai shiga motar karti suna ajiye ki kofar gida koh?" kallonsa take kamar
xata fashe da kuka ya mike ya ajiye tube din xai fita, a hankali tace
"Yaya baka gama shafawa ba" wani shegen kallo ya mata ya fice dakin.
A stairs ya hadu da Umma xata sauko parlor, ya jira ta wuce tana kallonsa tace
"Mura kake nake jin kamshin aboniki?" Ya wara ido yace "Oh, eh
daxu naji kamar xan yi muran shine fa na shafa a kirji" Umma tace
"Toh Allah ya sauwake" daga haka ta wuce shi ma ya wuce sama ya shiga
dakinsa, gun injections dinsa ya nufa ya dau pcm da syringe yasa a aljihunsa
sannan ya sakko parlor, Umma tace "Ga fa abincin ka can ka bari yana
galallawa a dinning" Mujaheed yace "Ohk xan ci Umma" tace
"Yanxu ina xa ka?" Yace "Card xan amso waje" daga haka ya
fita, sanin halin Ummar tasa, hakan yasa ya fita gidan gaba daya, bayan kusan
minti bakwai ya dawo ciki ya nufi part din su Imaan, Ammi na kitchen tana wanke
wanke jin an bude kofar parlor ta leko suna hada ido yace "Allura na dauka
na pcm naga tana xaxxabi" yana magana yana ciro alluran a aljihu Ammi bata
tanka sa ba ta koma kitchen Bedroom dinta ya bude ya shiga ya sameta yanda ya
bar ta har ta fara bacci, ya isa kusa da ita ya xauna bakin gadon ya fara hada
alluran yana gamawa ya juya yana kallonta yace "Kee" tayi nisa baccin
dama gata mai nauyin bacci, sanin haka ya ja hancinta yace "Imaan"
bude ido tayi da kyar xata kara rufe idon yace "Baxa ki tashi ba?" A
hankali tace "Yaya me xan yi kuma" Ta bude ido sosai ganin abinda ke
hannunsa ta mike xaune da sauri tana jan rigar ta xuwa chest dinta tace
"Yaya wa xaka ma alluran?" Yace "Gado" kamar xata yi kuka
tace "Ka mance na sha magani ne" yace "Kar ki bata min lkci my
frnd" ta fashe da kuka tace "Na shiga uku Ammi ni ban ce a min allura
ba" Tana fadin haka xata mike ya fixgota ya kwantar da ita ya daga rigar
jikinta ya mata alluran ya mike ya fice daga dakin, sai da Ammi ta shigo dakin
tana mata mugun kallo sannan ta hakura da kukan ta koma ta kwanta nan da nan
kuma bacci ya dauketa. Imaan na dawowa schl ranan litinin taga calls har biyu
da ta yi missing, bayan ta idar da sllh tana xaune kan darduman ta dau wayar
tayi dialing number din, har ya katse ba a dauka ba, few seconds later sai ga
call din ya shigo wayarta, dagawa tayi ta kai kunne, sallama aka yi daga daya
bangaren cikin cool voice, tayi shiru da farko, can kuma tace "Waye
ne?" Yace "Baki amsa sallama ne?" Tace "Not a must in amsa
a fili, who are you" yayi murmushi yace "Ohk then, how are you?"
Tace "I asked who are you first?" Yace "Tsoro kike ji?"
Tace "Sorry i think it's a wrong call" yace "Why do you say
so?" Tace "Because without any doubt I know it's only my dad, mum....
and very few dat have my contact" yace "Ohk... Muhsin ya
sa in kira in ji ko kin shiga gida lafiya" ta d'an bude ido da mamaki amma
ta kasa cewa komai, yyi murmushi a hankali yace "How are you Imaan?"
Murya can kasa tace "Alhmdllh" yace "I guess yanxu kika dawo
schl?" Tace "Sure" yace "Alryt, sai islamiyya ko?"
Tace "Eh" yace "Ohk then Allah ya kiyaye hanya, amma tare xa ku
yi sauka da su Mariya?" Tace "In sha Allah" yace "Saura
wata nawa?" Tace "Two months" yace "Maa sha Allah, we will
talk later kar kiyi latti" tace "Sai anjima" daga haka ta katse
wayar ta mike ta fara shirin Islamiyya. Bayan Magrib Mujaheed na xaune parlon
Abbansa da duk yan gidan, Yusuf ma dake xaune wayarsa kawai yake ta dannawa a
parlon, Anty duk ta fiddo ankon bikin Seeyama suna nuna ma Abba, Umma dai na xaune
ta hade rai don gani take kamar Anty shishshigi kawai take mata, Anty tace
"Toh Abba ga kaya nan, gaba daya kala uku ne" Mujaheed yace "Toh
duka kala ukun xa su yi?" Anty tace "Ehh ko kana da damuwa da
hakan??" murmushi yyi bai ce komai ba, Yusuf ya daga kai yace "Amma
fa Anty yayi yawa sai kace su ne..." Mugun kallon da mahaifiyar tasa tayi
masa yasa yyi shiru ya ci gaba da danna wayarsa, Abba yace "Kice expenses
ne ba na wasa ba, to da wanne ku ke son mutum ya ji, ina laifin ma kala biyu?"
Umma tace "Haba Alhaji, abu dai na rana daya lkci daya, ni fa da cewa ma
nayi kala hudu hudu Amina tace a bar shi a kala uku kawai" Abba ya gyada
kai bai dai ce komai ba, Anty tace "Idan ma baxa ka siya masu ba ga
yayyinsu sai su masu" Umma tace "Atoh dai" Yusuf yace "Mu
dai sai dai muyi masu kala bibbiyu" Anty tace "Toh ka rike kudin
ka" Dariya yayi yace "Shikenan ni sai in ma Rahma da Ummi M.A yayi
maku sannan yayi ma Maimoon" Umma tace "Sai kayi ma Kakarku ko kala
biyu ne ita ma, shikenan it's settled" Yusuf ya dinga kallon Umma bai ce
komai ba, Abba yace "Toh mamana fa?" Anty ta buda ido tace "Ai
kuwa Imaan... kaga na ma mance wllh, shikenan sai Mujaheed yayi mata kaga hakan
ma is settled" Abba yace "Ehh sai Mujaheed yayi mata" Umma ta yi
ma Anty wani kallo tace "Wani Mujaheed din, shi Yusuf me ya hanasa yi
mata?" Anty tace "Saboda kince yayi ma Kakarsu, kinga Mujaheed sai
yayi ma Imaan" A fusace Umma tace "Toh an ruguje wannan tsarin kowa
tayi ma 'yar ta, Inna kuma Alhaji ko baban ita Imaan din su yi mata" Abba
yace "Ba tsarin da ya ruguje Hajiya, Mujaheed yayi ma ke, Amina... da
maimoon sai Imaan, Yusuf kuma yayi ma Ummi, Rahma da Inna, kuma a cire ma imaan
nata a kai mata yanxun nan" Anty ta cire ma Imaan kala uku, Abba ya kalli
Mujaheed yace "Dauka ka kai mata" Mujaheed ya kalli Umma da ranta
idan yayi dubu a lkcn ya baci, Anty tace "A'a jira, yi min transfer din
kudin Imaan din yanxu tukun, sauran ko daga baya ne sai ka yi" Mujaheed ya
kasa cewa komai, Anty tace "Malam ka min shiru ina maka magana m" ya
dau wayarsa gabansa na faduwa sai dai bai yadda ya kalli Umma da ko
ba a fada masa ba yasan kallonsa take, ya gama danne dannensa yace "Anty
ina jin ba network...." Ta mike ta isa kusa da shi ta amshi wayar tace
"Baxa ka raina min hankali ba" sanin Gtb yake amfani da lkci daya ta
danna transfer code dinsu tayi komai ta sa har account number dinta bayan ta sa
amount sannan ta mika masa tace "Sa min pin" Karba yyi ya sa pin din
ta amshe wayar, duk ya kasa kallon Umma, sai da Anty ta ga transfer din yayi sannan
ta basa wayarsa ta koma ta xauna, lkci daya aka turo masa debit ya bude ya ga
30k ta yi transfer, Abba yace "Toh ka dau kayan ka kai mata sai kace mata
kai ka siya mata" Kasa tashi yayi, Abba ya hade rai yace "Are you
stupid ina maka magana kana xaune, wato abinda kake nufi shine baka jin maganar
kowa gidan nan sai na uwar ka koh, ina fa lura da kai kuma nake sharewa"
Tashi Mujaheed yayi ya dau ledan kayan ya nufi kofa, Umma ta mike fuu ta wuce
sama, Anty tayi wani murmushi a ranta tace "da sauki ai tunda ba bin sa xa
ki yi ba" A hankali Mujaheed ya murda kofar apartment dinsu Imaan ya shiga
da sallama murya can kasa, Imaan ce durkushe parlon da yar ves sai skirt iya
cinya, nose mask na hancinta tana goge gogen kayan da ke daukan k'ura a parlon,
ta mike ta cire abun bakinta tana kallonsa, Ammi ta fito parlor jin an shigo,
yyi kasa da kai ya ajiye ledan hannunsa kan kujera yace "Abba yace a kawo
mata" daga haka ya juya ya fita ya kulle kofar, Imaan xata bude ledan Ammi
ta mata tsawa, dakatawa tayi da sauri, fuska daure Ammi tace "Kina ganin
ya shigo amma kika ki wucewa daki da wannan shegun kayan jikin ki koh, tun daxu
nake maki magana ki nemi kayan arxiki ki sa ko don saboda ciwon ki sannan kada
wani ya fado amma kin maida ni mahaukaciya, ke kam wace irin yarinya ce Allah
ya bani, in ji hankalin ki ya kwanta da ya shigo ya ganki a haka?" Imaan
sai kallonta take da mamaki tace "Ammi yaya ne fa" Bude baki Ammi
tayi tana kallonta, can tace "Sai aka yi ya don shi ne?" Tace
"Toh Ammi shi ne fa ba wani ba ya shigo, dama dai ya Yusuf ne kin san
baxan tsaya haka ba" Ammi ta kasa daina mata kallon mamaki tace "Shi
yayan muharramin ki ne Imaan?" Imaan ta xaro ido tace "Ammi yaya fa
har wanka ya taba min ina karama, kuma da ba shi ke sa min kaya ba ma idan ban
sa ba, ni dai bana jin kunyarsa wllh, dama dai yaya Yusuf ne shi ko dankwali
bana tsaya kusa da shi ban sa ba, shi kuma yaya ni xan ma iya cire kaya a
gabansa, toh har yau ba yana shafa min magani a kafana da bayana ba, ko wajen
inna idan yana nan ina....." Ammi taga bude baki fa ba nata bane ta dau
daya daga pillows na kujera ta jefa mata a mugun fusace tace "Ban taba
sanin ke shahararriyar mahaukaciya bace sai yau, wato iskanci yasa kike cewa ya
shafa maki maganin xafi koh, to in sake gani sai na ci uban ku ke da shi, kuma
kar ki fasa cire kaya gabansa tunda ke shashasha ce, sai kace warce bata taba
shiga ajin islamiyya ba wai kina cire kaya gaban namiji da ba muharramin ki
ba" Imaan ta nufi daki kamar xata yi kuka tace "Ni fa ba yanxu nake
cewa ba Ammi, da da nake nufi, kuma naga ai yayana ne shi tunda ba ni da wani
yayan" ganin Ammi ta yo kanta ta shige dakinta da gudu ta sa makulli tana
turo baki kamar xata fashe da kuka.
Post a Comment for "IMAAN 13-14"