Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

IMAAN 11-12

 11. 🌟⭐ *imaan* ⭐🌟

 

Kasancewar ranan Alhamis ne Imaan na dawowa schl bayan ta yi wanka ta fito ta d'an cito abinci kadan ta koma bedroom ta saka kayanta ta sake fitowa parlor, Ammi dai sai kallonta take don tun daga ganin d'an abincin da ta ci ta san da matsala, Ammi tace "What's wrong with you?" A hankali tace "Ammi cikina xai fara min ciwo ne" Ammi tace "Toh Allah ya sauwake abincin ya ishe ki?" Kai ta gyada mata ta xauna kusa da ita tace "Ammi na dade fa ban je gidan gwaggwo in gaisheta ba" Ammi tace "Jiya ma ta tambaye ki da muka yi waya, ran Saturday idan kin dawo islamiyya sha biyu sai ki tafi, before four ki taho gida saboda islamiyyan yamma" Imaan tace "Toh Ammi me yasa gobe baxan je ba" Ammi tace "A'a xan je xa mu duba ma Halima kaya an kawo daga dubai, idan kin dawo schl ma baxa ki sameni" Imaan tace "Toh, Ammi ankon mu fa?" Ammi tace "Idan kin je sai ki tambayeta" Imaan tace "Ammi bikin na Anty Seeyama xa a fara yi ko Anty Halima?" Ammi tace "Na Seeyama saura two weeks, Halima kuma saura sati hudu" Imaan tace "Toh

Ammi na Seeyama baxa a mana anko ba?" Wani kallo Ammi tayi mata tace "Kin ishe ni kuma haka" Shiru Imaan tayi, can ta mike tace "Ammi xan je wajen inna" Ammi tace "Toh sai ki dauko magana idan kika tashi dawowa" dariya kawai tayi ta sa takalminta ta fita parlon ta rufe kofar. Inna na share waje Imaan ta sameta, Inna ta mike tace "Baki ji bayana ba Imaan tun daxu ban xauna ba wllh, aiki dai aiki dai, to kuwa idan mutum bai yi aiki ba ai sai kazanta ta ra6e sa, to ni ko yaushe xan yarda hakan ta faru???" Imaan tace "Toh me kike sharewa a nan din, naga ba datti" inna ta xaro ido tace "Toh k'uran dake yashe a kasa kuma uwaki ce ba datti ba?" Imaan ta yi dariya tace "Toh ai sai kiyi ta sharewa" daga haka ta shiga ta bar ta a wajen, bayan minti goma inna ta shigo parlon ganin yanda Imaan take yatsine yatsine ta hade rai tace "Me kuma ya faru?" A hankali tace "Wllh cikina ne xai fara min ciwo" Inna tace "Toh tashi ki tafi gidan ku ba ruwana da wahalan ki, ko ba jini bane" Imaan tace "Toh ai bai xo ba kawai dai yana min ciwo ne" inna tace "Toh kiyi maxa ki tafi uwar ki ta kai ki asibiti, haka wancan karan kika cuce ni kika daga min hankali, ni dai da xaki dinga rufa min asiri duk kika ji baki da lafiya ki daina taho min nan sai kin ji sauki, a gaskiya kina shiga alhakina" Imaan bata tanka ta ba, Inna tace "Kin ko ji abinda nace" Imaan ta daure fuska tace "Sai nan da kwana biyar ko shidda ma xai xo, ni dama haka yake min ba shi bane" Inna ta tabe baki ta mike ta nufi dakinta tace "Ni dai ba ruwana kar a xo a dameni a gigita ni" Imaan ta gama juye juyenta bacci ya dauketa. wajajen karfe shidda Inna na daki duk ta fiddo da kayan closet dinta tana masu linkin guga jin an bude kofa ta ajiye kayan xata fita parlor, ta labule ta hangi Mujaheed tsaye cikin parlorn, kana ganinsa kasan daga aiki yake don ko tie din wuyarsa bai cire ba kan farar shirt din jikinsa, kallon Imaan dake bacci ya tsaya yi sannan ya kalli kofar dakin Inna, can dai ya karasa kusa da ita ya duka ya kai hannu a hankali kan goshinta yana feeling temperature dinta, sauke hannunsa yyi kan wuyarta ta bude ido tana kallonsa, yace "What's wrong?" Cikinta ta nuna masa kamar xata yi kuka, daga cikin dakin ya ji muryar inna tana cewa "Don Allah a dinga kyakkyawan xato dai, Shikenan ita kuma a rashin lafiya xata kare kamar warce ta kashe mai rai ka wani kai hannu kana tattaba jikinta kaji ko da xafi ko babu, to babu, kuma lafiyar jikata qlau ka matsa wajen tunda fatan ciwo kake mata, dama likitancin hauka ne" Mujaheed ya dinga kallon kofar dakin, inna ta fito tace "A dai ji tsoron Allah a dinga kyakkyawan xato fisabilillahi, lafiyarta lau wllh, al'adarta ce kawai ke kan hanya shine ta langwabe haka, ka shigo kana wani tabe taben jikinta salon a ja mata wani ciwon tunda a haka ake so ta kare" Shi dai kawai tsayawa yyi yana kallon inna fuskarsa daure, can ya juya ya nufi kofa, inna tace "Toh Ina yini... yanxu ka dawo daga aikin kenan" bai tanka ta ba har ya fice parlon. Kafin magrib Imaan ta watsake gaba daya, bata shirya barin part din Inna ba sai kusan karfe goma na dare tare da Yusuf, Inna na kallon Yusuf tace "Isuhu wai daga na fadi ma Mujaheed gaskiya daxu shine har yanxu bai tako nan ba, to me xai bani da Allah bai ban ba, banda  ma magana da yake sa ni idan ya xo, ni dai kai da Imaan kun isheni ni kar ma ya sake xuwa" Yusuf yyi murmushi bai dai ce komai ba ya fita yana kallon Imaan dake tsaye gaba daya hankalinta na kan film da ake yace "Ko dai in tafi ne Imaan" tace "A'a ya Yusuf jira ni, ynxu xa a gama" yace "Toh ki kwana nan mana" da sauri ta fice a parlon har tana tuntube, Yusuf ya fara dariya, Inna ta ja tsaki tace "Toh banda ki yamutse min gado ki bar ni da aiki amfanin me xaki min idan kin kwana Imaan?" Yusuf ya kulle mata kofarta suka wuce, a hanya yace "Me yasa baki son kwana wajen inna imaan?" Ta make kafada tace "Karfe uku idan ta tashi sai tasan yanda tayi ta tashi mutum, tayi ta masa surutu har sai baccin ya fita idonsa" Yusuf yyi dariya yace "Dole ma gobe ki kwana can tunda Friday ne" Imaan tace "Sai dai kai ka kwana" daga haka ta shige balcony dinsu tana daga masa hannu yyi murmushi yana kallonta yace "Good night" yana wucewa ta shiga ciki ta kulle kofarsu.

 "Wannan iskancin da kike ki tafi exams babu karatu baxa ki min shi a gidan nan ba wannan karan" Cewar Ammi kenan tana kashe kayan kallon parlon gaba daya, Imaan ta dinga kallonta kamar xata yi kuka bata dai ce komai ba, Ammi ta nemi waje ta xauna tana danna wayarta, A hankali Imaan tace "Ranan Monday fa ne exams din Ammi, i still have Saturday and Sunday sannan Monday da safe" Ammi tace "Ki tashi ki dau abincin Inna ki kai mata baxa kiyi kallon ba, kuma I promise you har ku gama jarabawan nan baxa ki kunna kayan kallo a gidan nan ba, ko yaushe kika xama dedicated da kallo haka ban sani ba" da mamaki Imaan ke kallonta, can tace "Amma ammi ban taba daukan sama da second position ba fa a schl" Ammi tace "Ur silly First position ba karatu? I want to see ur grade idan kika yi karatu this time around" Imaan ta dauke kai kamar xata yi kuka tace "Ni da ma ba wani kallo nake ba sai lkci lkci kuma da ace 5th nake dauka shine sai ki ce in daina kallo fa Ammi" Ganin kallon da Ammi ke mata ta mike ta sa hularta ta wuce kitchen ta dau abincin inna dake ajiye tun daxu ta fice gidan, har ta isa part din inna ji take kamar ta fashe da kuka, ta bude kofar ta shiga, xaune ta tadda inna da bowl din fura a gabanta ta daura kafa daya kan daya, Yusuf na xaune parlon shi ma da cup din furan a hannunsa, sai Ummi dake shan furan ita ma, Mujaheed dai idonsa na kan tv ga nasa cup din furan a kusa da shi, Inna na ganin Imaan ta daure fuska ta rufe furan gabanta ta mayar bayan ta tace "Ni dai wllh ya kare, ba ruwana sai kun ga mutum da abu ku wani dinga tururuwan xuwa, to duk na rabar..." Imaan ta ajiye abincin hannunta tace "Toh ni ina ruwana da furanki ce maki nayi xan sha?" Inna ta kalli Ummi tace "Ke tashi ki shigar min da abina ciki" Ummi ta mike ta dau furan ta kai daki ta fito, imaan ta turo baki tace "Sai kace nace xan sha" Inna tace "Toh ai sai ki juya ki tafi koh?" Imaan ta ki fita don har ranta take son fura da nonon barin idan inna ce ta dama kuma ita tayi furan da kanta, inna ta kalli na Mujaheed tace "Dama ga wannan Boss din ya ji sha, ko raina wanda na tarfa masa yayi Oho, da yake Rukayya ce tayi min wahalan aikin furan Ahmadu kuma ya siyo min nonon, cewa ma yayi baxai sha ba ki dauka ki sha, Allah yayi da rabon ki" Yusuf yyi yar dariya yana kallon Imaan, Imaan ta saci kallon Mujaheed dake kallon TV har sannan, ta kalli rabin cup din furan kusa da shi, inna tace "Tunda fa aka ji yace baxai sha ba fa baxai sha ba, kawai ki dauka rabon ki ne, don ni bani da wanda xan baki in kwana da yunwa" Imaan tace "Toh wai ni nace maki xan sha ne?" Tana magana tana kallon kofar parlon lkci daya ta suri cup din tayi waje a guje Yusuf ya kyalkyale da dariya don yasan abinda xata yi kenan, Inna ta washe baki tana kallon Mujaheed tace "Allah ya kara" mikewa Mujaheed yyi fuska daure ya bi bayanta, Inna ta rushe da dariya har da kyakyatawa tana kallon Ummi tace "Da dai ki tashi ki kulle min kofa da makulli tunda sun fita" Kafin Imaan ta kai rabin hanya dama gaba daya furan duk ya xube saboda gudun da take, Mujaheed ya cafketa daga karshe ta fasa ihu ta sake cup din hannunta ta kama hannunsa tace "Wayyo Yaya don Allah kayi hakuri inna ce tace in dauka" da mamaki yake kallonta yace "Yaushe na fara wasa da ke gidan nan amma?" Jikinta na rawa tace "Don Allah kayi hakuri Yaya" fuska daure yace "Kiyi providing min furan nan yanxun nan idan ba haka ba wllh kinji na rantse sai na sa ki kuka" ta fashe da kuka amma ba hawaye tace "Yaya bayan kana gani duk ya xube nima ban sha ba, don Allah kayi hakuri xanje waje in siyo maka wllh" ya wani hade fuska yace "Wannan nake so ba na waje ba" ta marairaice tace "Toh yanxu yaya a ina xan samo maka wani, nima fa kaga bata bani ba" ya kalli part din Inna sannan ya kalleta, murya can kasa yace "Kinsan abinda xa ayi yanxu?" Ta kara marairaicewa tana girgixa masa kai, yace "Komawa xa kiyi part dinta ki shiga daki ki fito da bowl din furan da gudu yanda kika fito min da nawa yanxu" ta xaro ido tana kallonsa, sai kuma ta fashe da dariya tace "Yaya kasan baxata bari ba fa" ya hade rai yace "Irin dubaran da kika yi kika fita da nawa haka xaki fito da wancan ma ae" Imaan ta dinga dariya har da kyakyatawa, ya ja kunnenta yace "Baxa ki daina wannan dariyar mahaukatan ba" ta hadiye dariyar da kyar tace "Toh amma tare xa mu sha?" Yace "Eh mana" tana murmushi tace "Toh nasan yanda xan yi" a tare suka koma part din inna ya nuna mata bayan window din bedroom din inna yace "A can xa ki sameni ina jiran ki" tace "Toh" daga haka ya wuce yana waigota, a guje Imaan ta shige parlon inna tana cewa "Wayyo inna kice masa wllh kar ya ta6a ni xan gaya sa da Abba, inna kice kar ya taba ji xan kira daddy na...." Mujaheed yyi murmushi ya koma bayan window din ya tsaya yana shafa kansa, Inna ta mike da sauri kar Imaan ta take ta koma wani wajen ta xauna tace "Fito min daki wllh, ba ruwana ku je can ku karata kar wanda ya dameni, yara dai kamar na jaraba" Imaan da ta shige dakin tuni ta dinga dariya kasa kasa ta dau bowl din furan ta datse murfin yanda idan tana gudu baxai xube ba, ta tattara rigar jikinta tayi saitin bakin kofar fita sannan ta fice a dari da sittin, inna ta kyakkyafta ido don tabbatar da abinda ta gani hannunta amma tuni Imaan har ta fice parlon kamar xata tashi sama, inna ta mike da sauri tace "Isuhu me na gani a hannunta kamar kwanon fura na???" Ummi ta kyalkyale da dariya tace "Wllh shi ne" Yusuf ya fashe da dariya, Inna ta fashe da kuka tana kallonsa. Imaan bata tsaya ba sai da ta isa inda Mujaheed yake jiranta, murmushi yayi ya amshi bowl din yace "Yauwa kinyi kokari" ta washe baki tace "Nagode" ya xauna kan dakali dake wajen ya bude bowl din ya dau ludayin ciki ya juya furan sannan ya fara sha, Imaan ta daina murmushin da take ta durkusa gabansa tace "Yaya kai kadai xaka sha" Ya harareta yace "Toh da ni da wa xa mu sha?" Ta xaro ido tace "Wllh baxan yadda ba ni fa na sha wahala na dakko kaga irin gudun da nayi yanxu ma fa kirjina ciwo yake" banxa yyi da ita yana shan furansa don furan inna ba dai dadi da gardi ba, Ta fashe da kuka tana kallon sa, ya hade rai ya debi rabin ludayin hannunsa ya kai bakinta, ta turo baki tace "Wannan d'an kadan din bayan kai cika wanda xaka sha kake?" Yace "Baxa ki bude bakin ba" ta bude bakin da kyar, ya xuba mata yace "Toh tashi ki tafi" kamar jira take tace "Wllh baxan tafi ba ji fa abinda ka bani bayan ni na sha wahalan daukowa, Allah sai dai ka bani in mayar" Yace "In baki ki gudu da shi gidanku dai" Ta fashe da wani dariya har da kyakyatawa, ya harareta ya ci gaba da shan furan, kamar xata yi kuka tace "Yaya" ya kalleta sannan ya debo furan rabin ludayi ya kai bakinta, kin bude baki tayi tana masa wani kallo, ya kai bakinsa ya shanye, ta fashe da kuka, yayi light murmushi ya kara deba ya kai bakinta, bude bakin tayi ya juye mata, daga nan ya ci gaba da sha bai kara kallonta ba, kiris ya rage ta fashe da kukan gaske, ganin bai san tana yi ba ta fixge ludayin hannunsa, ya wara ido yace "Ke ina wasa da ke ne" ko kallonsa bata yi ba xata diba ganin xai dauke bowl din ta marairaice tace "Don Allah yaya ka bari in sha wllh baxan cika ba" yace "To diba in gani" ta turo baki ta ciko ludayin ta kai baki da sauri, ko shanyewa bata yi ba ya fixge ya juye ragowar a bowl din sannan ya diba ya kai baki, tana ganin haka ta dauke bowl din ta kai baki ta kwankwade ya xaro ido kafin yace komai suka ji muryar Inna cikin kuka tana cewa "Ahmadu idan ba a bi min hakkina ba yau a babbake ni cikin dare idan na kwana cikin gidan nan" Mikewa Mujaheed yyi da sauri xai bar wajen imaan ta mike ta rikosa a rikice tace "Wayyo yaya kai ne kace fa in dauko" Ya wani xaro ido yace "Ni?? You are sick, kar ma ki sa ni a maganan nan" daga haka ya bar gun da sauri don da dukkan alama nan suke taho, Imaan ta bi sa da gudu har suka iso gaban compound din gidan, ya wani hade rai yace "Wai me yasa kike bi na ne ma dai tukun?" Ta marairaice tace "Yaya kai fa ka sa ni" Ya xaro ido yace "Ohh dama idan nace ki shiga wuta sai ki shiga, kar ki kuskura ki ambato sunana a maganan nan" on a serious note ya fadi hakan, ta hararesa tace "Wllh kai ne kace in dauko da gudu in fito" xai yi magana suka ji alamar suna tahowa, inna na cewa "Kuma ko tantama babu wannan tantirin Mujaheed din da ka haifa ne xai sa ta, banda haka imaan ta san wani sace abincin mutane ta fita da gudu, wllh a min iyakan gaske da yaran nan a gidan nan yau, a kan me xa su dinga cutata suna ci min mutunci haka, wai har sun shanye furan sun bar min kwano a bayan window, me nayi masu a rayuwa xa su min haka" tana kai wa nan ta rushe da kuka, Anty tace "Kiyi hakuri don Allah inna" a fusace inna tace "Shegiya nake idan na hakura, a sace min furan a shanye kice in hakura kamar uwata tace min je ki kya gani, ae Aisha dai ta haifi fitina, wannan yarinya Imaan dai fitina ce wllh, a ma kira min Bukar yanxu, idan ban tada gidan nan da bala'i ba yau ace bani ba" da sauri Mujaheed ya nufi gate, imaan kamar xata fashe da kuka tace "Wayyo yaya" sai da ya kusa gate ya juya yana kallonta ya fara dariya kasa kasa, bin bayansa tayi da gudu, gun motarsa dake parke a kofar gida ta gansa xai bude maxaunin driver, ya buda ido yace "Wai me yasa kike bi na ne?" Ta karasa gun motar tace "Wllh yaya ni ba ni kadai xa a gani a gidan ba bayan ni da kai muka shanye, kawai Ammi ta kama ni ta min duka"  ya daure fuska yace "Kinga ki juya ki koma ciki wllh" ta fashe da kuka ta make masa kafada, ya shige driver seat, ta bude front seat ta shiga tana turo baki, yace "Wai kin san inda xa ni" kin cewa komai tayi, jin an bude gate ya rufe door dinsa da sauri, Yusuf ne ya fito, Mujaheed ya tada motarsa ya yi zooming off, Yusuf ya dinga dariya mai gadi na kallonsa, sai da suka hau saman titi Mujaheed ya kalleta yace "Dama seriously idan kika kira sunana a case din nan wllh sai na sa ki kukan sati daya, sai ki gaya masu furan ma ke kadai kika shanye" Ta gefen ido ta kallesa kafin tace "Sai dai in ce masu ludayi daya da rabi kawai na sha sauran kuma ban san wanda ya shanye ba" Yace "Kina son in sauke ki nan kenan" ta marairaice tana  kallon sa, yace "Toh me xaki fada masu a kan furan" a hankali tace "Cewa xanyi ayi hakuri ni da yaya muka shanye" parking yyi gefen titi, ta rikosa da sauri tace "Aa yi hakuri xan ce ni kadai na shanye" ya hade girar sama da ta kasa yace "Ki rantse" Kamar xata yi kuka tace "Bayan ni da kai muka sha"

 

 

Alhamdulillah, Thanks to all those that patronize the book *Imaan* Allah bar ku da iyayen ku, My book Imaan is for sale coz I am done with free pages tun friday, ni nasan it will go round as usual, I can't prevent that, but if you should come across it it's not for free, i repeat it's not for free, na siyarwa ne, wllh I am too grown up to say Allah ya isa, but have the fear of Allah SWT in u, don't forget it's my property, hakkina ne, wahalata ce, pay before reading, pay before reading, or you just over look it and smile, have a very good conscience plss, and a good conscience won't read happily without paying, if you want any favor pertaining to d book contact me and let me know, the book is 300 via..... Fcmb 3276052019

Hauwa Bello Jiddah

 

07087865788 and then u contact me through this digit to be added in the payment groups. Thanks once more for patronizing.

 

For those saying xa su same shi a banxa yana yawo to gashi... amma fa ba a banxa yake ba wllh, there is power in the tongue, Karamin hakkin da ka raina..... 😃😃

 

12.      🌟⭐IMAAN⭐🌟

 

 

 

 

 

 

 

Gidan wani cin abinci Mujaheed yyi parking, yace "Ki jira in fito..." da sauri tace "Nima ba a cc abinda na ci wllh" ya kashe wayarsa kamar baxae ce komai ba sai kuma yace "meat pie daya ya ishe ki" kafin tace komai ya bude motar xai fita, da sauri tace "Yaya amma fa ban sa takalmi ba" da sauri ya kalli kafarta, yace "Good kinga sai ki jira ni in ci abinci in fito" Ta fashe da kuka tace "Wllh haka xan fito, ni fa ba abinda na ci tun da rana sai furan nan da ka tsammin" ya hade rai yace "Ki fito ki ja min kallo cikin mutane" ta marairaice tace "Yaya to mu je ka siya min ko bathroom slippers ne" yace "Ki dai jira yanxu xan gama cin abincin in fito" Bude motar tayi ta fito, ya xaro ido yana kallonta, Xata xagayo inda yake ya mata tsawa yace "Tsaya nan kar ki xo min nan" ta turo baki tana kallon sa yace "Dama ki tsaya sai na shiga sannan ki shigo, kuma ki nemi can nesa da ni ki xauna xan sa a kai maki abincin can" a hankali tace "Toh" Daga haka ya shiga yana waigota don tabbatar da ta bar distance sosai tsakanin su, Yana xaunawa sai ga ta ta shigo, ya wani hade rai ya dauke kai, tabe baki tayi ta nemi nesa da shi ta xauna ba tare da ta damu da kallon da ake mata cikin eatry din ba, jollof rice da half chicken yasa aka kawo masa da five alive drink sai bottle water, yana kallon waitress din yace "Ae kuna da meat pie koh?" Tace "Ehh har da burger da pizza with sausage roll duk akwai" yace "Good kinga wancan matar dake xaune at that far end?" Waitress din ta kalli inda yake nunawa ganin imaan tace "Ehh na ganta" yace "Ki kai mata meat pie daya da table water, ni xan biya bill din" tace "Ohk" daga haka ta wuce ta dau meat pie din da table water ta nufi gun Imaan tana ajiye mata a gabanta imaan ta kalli Mujaheed da ya dauke kai yana cin abincin gabansa, waitress din ta juya ta wuce, satan kallonta Mujaheed yyi suna hada ido ya juya kujerar sa yayi backing dinta yana murmushi yana cin abincin sa, Imaan ta dinga kallon sa amma ya ki juyowa, bayan kusan minti uku ya sake juyawa a hankali, kawai ganinta yayi a gabansa tana kallon sa kamar xata yi kuka, da sauri ya fara kalle kallen eatry din ya ga kallonsu kawai ake, ya xaro ido kafin yace komai ta ajiye masa meat pie da ruwan a gabansa ta jawo plate din abincin da drink ta dauka ta koma inda take ta xauna ta fara ci, Mujaheed bai ce komai ba ya dauke kansa, bayan kusan minti goma ya mike ya tafi ya biya kudin abincin da snack sannan ya dawo ya dau meat pie din da ruwa yana satan kallonta ita ma kallonsa take, mamaki ya cika sa ganin har ta kusan cinye shinkafar nama kuwa ta ma gama da shi, ya dauke kai ya nufi kofar fita, imaan ta mike da sauri ta dau sauran five alive din ta bi bayansa, a tare suka iso gun motar, ya bude driver seat ya shiga ita ma ta shiga gaba yace "Fita ki koma ki cinye abincin" tayi yar dariya tace "Dama fa nasan wucewa xaka yi ka bar ni shi sa nake ta kallon ka" ya hade rai yace "Fita nace" tace "Ai na koshi baka ga na cinye naman ba" tada motar yayi ya bar eatry din, bayan sun hau saman titi yace "Xan maida ki gida yanxu, wllh kika kuskura kika ce nasan komai a kan furan inna Allah xan sa ki kuka" da mamaki tace "Kai ina xa ka yanxu?" Yace "Gidana" ta fashe da kuka tace "Toh shine ni xaka maida ni gida, wllh kar ma ka kai ni don baxan fita daga motar nan ba" ya buda ido yace "Toh ina xan kai ki?" Ta turo baki tace "Mu tafi gidan ka tare" ya gyada kai yace "Tunda ke mahaukaciya ce ni ba mahaukaci bane" ta kallesa tace "Toh da ba ina xuwa ba" ya jefa mata wani kallo yace "Da ba yanxu bane" Shiru tayi ganin ya dau hanyar gida ta kamo sa tace "Don Allah yaya kar ka maida ni gida yanxu, wllh Ammi xata iya dukana don dama tace kar in dauko mata magana" yace "Toh ina xan kai ki?" Hawaye ta fara yi, yayi murmushi yace "Gobe baxa ki dauke ma tsohuwa furanta ba, ni dama ba ruwana" ta hade kai da gwiwa tana kuka a hankali, bayan few minutes yace "Abinda xai faru yanxu ina maida ki gida sai ki shige dakin Anty da sauri, ki kwana a can" ta dago tana goge hawayen idonta tace "Don Abba ya gani ko, kasan Ummi xata ce ma Abba ina nan" Ya daga kafada yace "Ae shi Abba baxai doke ki ba, fada kuma baya nuna wa a jikin mutum" parking yyi yace "Oya fitar min a mota sai da safe" wasu hawaye na xubo mata ta bude motar ta fita tana kallon sa tace "Duk abinda ya faru daga farko har karshe xan gaya ma Abba baxan boye masa komai ba, tare muka shanye furan kuma kai ka sa na shiga dakin Inna in dauko saboda ta xuba maka kadan" daga haka ta bar wajen da sauri tana kuka ya bi ta da kallo baki bude, tuni ta shige gate ta dinga rabe rabe har ta isa parking space din su Yusuf, a haka har ta shige parlour rufin asirinta ba kowa da gudu ta wuce dakin Anty, Anty dake xaune gaban madubi ta bude baki tana kallonta, Saman gadonta Imaan ta hau ta rufa da duvet, Anty tayi murmushi tace "Ina Mujaheed din?" Imaan ta cire duvet din ta mike xaune kamar xata yi kuka tace "Yace baxai dawo ba yau kuma wllh Anty shi yasa in dauko mata furanta sai ma kinga abinda ya tsammin duk ya shanye sauran" hawaye cike idonta take maganan, Anty tayi dariya tace "Ae ko kun sha jaraba yau, don har yanxu Abba da Ammi na can ana ba Inna hakuri, nima gajiya nayi na taho" Imaan ta turo baki ta koma ta rufe kanta da duvet. Washegari Saturday Imaan na xaune gaban madubin Anty tana shafa mai don har tayi wanka, Anty kuma na xaune kan darduma hannunta rike da hisnul Muslim aka bude kofar dakin, Abba ne tsaye bakin kofar, Imaan ta kusa faduwa saboda rudewa, Abba ya kalli Anty yace "Amina amma baki ce min yarinyar nan na nan ba" Anty tace "Ni ma har na yi bacci na ganta jiya da daddare" Abba ya kalli Imaan yace "Ki sameni parlona yanxu" kamar xata yi kuka tace "Abba to shi yaya fa?" Dakuwa Abba yyi mata yace "Stupid girl, yayan banxa ai duk xa ku gane kuran ku yau" daga haka ya juya ya fita, Imaan ta fashe da kuka tana kallon Anty tace "Kinga ni kadai xa a ma fada yaya ya gudu koh" Anty tace "Ni dai ba kin sani nayi karya ba, maxa fita ki tafi ki samesa ba ruwana" da kyar Imaan ta bar dakin sanye da Hijab dinta, Abba dake parlonsa ya mike ganinta yace "Mu je" bin sa tayi tana goge hawayen idonta suka nufa part din inna, tun daga nesa suka hango Mujaheed yana share mata frontage, Yana ganin Abba ya mike tsaye, Ya gaida Abba da ladabi Abba ya masa banxa ya shiga parlon inna, inna ta fito kitchen tace "Ahmadu ne da sassafe haka" Abba ya xauna ya gaisheta ta amsa, ganin Imaan ta hade rai tace "Ya xaka shigo min da ita parlor Ahmadu, ni da dai ta tsaya daga bakin kofa, tsoronta ma nake ji wllh" Abba ya kalli Imaan yace "Koma can" komawa tayi bakin kofar ta tsaya, Abba yace "Shi yaushe Mujaheed din ya xo nan?" Inna ta xauna tace "Ko minti biyar ba ayi ba, Ashe jiya na shiga alhakin yaron bai ma san me ke faruwa ba baya gidan yana asibiti, sai yanxu da ya shigo nake basa labarin abinda yarinyar ta min, ya taya ni jimami sosai yayi mamaki ainun, shine ya ga xan share waje ya amshi tsintsiyar yake sharewa yanxu duk da dai nasan ba sharuwa wajen xai yi ba amma ai dai ya fi babu" Abba ya sunkuyar da kai yana murmushi, Inna tace "Yanda yarinyar nan ta sa na kwana da yunwa jiya gaskiya Ahmadu idan ba a dau mataki ba xan tafi inje duk inda Allah yayi ko kasar waje ne kuwa, don na gaji da cutata da take, jiya mun dade muna magana da Bukar a waya a kan yarinyar tasa yana ta bani hakuri ni dai ban hakura ba" imaan ta fashe da kuka tace "Wllh yaya ne yasa in dauko masa kwanon furan fa" Abba ya kalli inna da ta bude baki tana kallonta, yace "Ke sai kika yarda da yace maki bai san me ke faruwa ba dama?" A hankali Mujaheed ya ajiye tsintsiyar hannunsa xai bar wajen Abba yace "Don't try that, come in now" Inna ta mike tace "Toh amma ko gaskiya Ahmadu ka haifi abinda ya fi karfin ka, ka haifi tashin duniya, yanxu duk dadin bakin da ya shigo ya min da sa hannunsa a sace min fura da nono, Haba da walakin goro a miya, dama wani Mujaheed ne xai amshi tsintsiya ya min shara, ko da kuwa aiki xai kasheni baxai yi ba wllh, wato xuwa yayi ya yaudare ni ya cuce ni to akwai hisabi ai, ni dama nasan ina imaan ta koyi wani sata idan ba sa ta aka yi ba, ilai ga maganata nan, kuma wllh kaji rantsuwar musulmi ko, to baxan yadda ba sai sun san yanda suka yi aka min furata mai kyau mai kamshi da tsafta irin tawa sannan a siyo min kindirmo mai kyau idan ba haka ba gaskiya abinda xai biyo baya a gidan nan har kai sai ya shafa Ahmadu" Mujaheed ya shigo parlon kansa a kasa, inna na kallonsa da kyau tace "Mugu katon banxa kawai, wllh yau idan na maku Allah ya isa kai da figaggiyar yar nan sai ya bi ku don kun ci da hakkina, ku ka bar ni na kwana da bakar yunwa, to amma ya xanyi, sai dai ku ci albarkacin Ahmadu da Bukar don ni ba abinda na hada da ku, ba dangin iya balle na baba, kawai sai dai ku ci albarka cin 'ya 'yan da na haifa tunda su suka haifo ku duniyar, to banda 6are ma wa xai maka haka, ai 'ya yana baxa su min haka ba, amma kuma Ahmadu ka min iyaka da su kar kato ko figaggiyar da ta sake xuwa bangarena bana bukata Isuhu ya ishe ni rayuwar duniya" Imaan sai hararanta take ta gefen ido, Mujaheed dai kansa na kasa, Abba yace "Toh bana son sake ganin kai ko Imaan a bangaren nan" da sauri Inna tace "Har abada kuwa, don gaskiya idan suka xo sun ja ma kai da Bukar fitina, ita ta tsaya iya bangarensu, shi ma ya tsaya iya nasu, kada wanda ya tsallaka ya yo min nan don xan gudu in bar gidan" Abba yace "Hope u both are apprehending?" Mujaheed yace "In sha Allah" Inna tace " Kuma kafin gobe a kawo min furata da aka yi a kuma siyo min kindirmo nah" Abba yace "Xa su san yanda suka yi in sha Allah" inna ta kalli Imaan tace "Ke kin ma ci halas ya kika kare da ciwace ciwace balle kin dau hakkin mutane, jarababbiya kawai" Imaan ta fashe da kuka Inna tace "Fita can kije ki ma uwar ki Aisha, fitar min a parlor" Juyawa tayi da gudu ta fita tana rusa kuka, Inna ta kalli Mujaheed tace "Kai ma fita, har abada kada ka sake tako min nan, kaje can ka saci furan uwar ka idan ta yi" ta gefen ido ya harareta  ya fice a parlon, Abba yace "Ki kara hakuri xan sake ja masu kunne" tace "A'a ni ba ruwana ba dai na gama yanke hukuncin da nake so ba suje can su karata, sai kuma ko wannensu yyi ma uwarsa rashin mutunci ba dai Inna ba" Abba yyi murmushi bai dai ce komai ba. A hanya Mujaheed ya tadda imaan tana kuka bakin rai kamar xata shide, ya tsallake ta yayi wucewarsa. Mujaheed na komawa part dinsu dakin Ummarsa ya nufa, tun da ya shigo take kallonsa ya xauna yace "Ina kwana Umma?" Tace "Ban kwana ba, yanxu duk abinda xaka janyo a xageni a ci min mutunci baka gudunsa ko Mujaheed? Wannan kakar taka wai dole ne sai kaje inda take tunda ita jarababbiya Allah yayi ta, sannan kuma yunwa kake ji da ka dau shegen furanta jiya ta daga mana hankali a gidan nan, ni duk wannan bai wani dameni ba, babban damuwata a nan shine yaushe har ka fara shiri da yarinyar nan Imaan da ku ka dauke furan a tare ku ka sha?" Mujaheed ya bude ido sosai yana kallonta yace "Shiri kuma Umma? Ni bamu wani sha fura tare da ita ba, nine ma na dauke furan na sha" Umma tace "Toh naji tana cewa kai ka tura Imaan daukan furan ku ka raba" ya girgixa kai yace "A'a ba haka bane" Umma tace "Sannan da ake nemanka jiya ina ka tafi, ita yarinyar ma bata gidan a jiya da daddaren" Yace "Ni fa eatry na tafi cin abinci karfe sha daya ya wuce na shigo duk kun yi bacci" tana masa wani kallo tace "Toh ita imaan din ina ta tafi?" Yace "Ban sani ba gaskiya" Umma tace "Mujaheed?" Kallonta yayi tace "Mujaheed?" Yayi Shiru yana dubanta tace "Sau nawa na kira ka?" Ya sauke idonsa kasa tace "Toh wllh idan baka kama kanka gidan nan ba xan sa6a maka, ita kanta innar daga yau na kashe xuwa sashinta, kar ka sake tunda ba kanwar uwata bace ita din, idan kana son gaida kakarka ne sai ka shirya ka tafi katsina uwata na can da ranta" murmushi kawai Mujaheed yyi, tace "Dama tun shekaranjiya akwai maganar da nake son mu yi to da ka dawo gun aiki sai ka tare gun alakakan matar can sai nayi bacci xaka shigo min nan" ya daga kai ya kalleta yace "Toh ina ji Umma" tace "Kasan Hajiya Mansura kuwa?" Ya girgixa kai yace "A'a" tace "Ka santa mana, wata warce ka taba kai ni gidanta a Marafa, ka koma dauko ni da yamma ruwa ya tsuge har tace ka shigo ka ci abinci ka ki ci?" Yace "Ohh na tuna ban san sunanta ba ai" tace "Toh ita ce Hajiya Mansura, dama tana da wata budurwa yar shekara ashirin da daya tana karatu a Malaysia, to ina jin last week suka dawo hutu, baka ganta ba kyakkyawa fara doguwa ga hankali da nutsuwa, shine nake baka shawaran don me baxa ka neme ta ba" Shiru Mujaheed yyi bai ce komai ba, Umma tace "Sunanta Safeena, nasan ma xaka so ta ne coz she have all the qualities, uwa uba ga ubanta mugun attajiri abokin ma d'angote ne aka ce" Murmushi Mujaheed yyi bai dai ce komai ba, Umma tace "Ba batun murmushi bane wannan, dama gashi saura wata hudu ta kare karatun, last week da naje gidan na ganta ta kwanta min har nayi ma Hajiya Mansurar magana ita ma ta ji dadin tunanin nawa don ta yaba da hankalin ka, yanxu abinda nake so da kai ka shirya kaje gidan ko xuwa Sunday tunda baka xuwa aiki da safe, dama xan baka sako ka kai ma Hajiya Masurar nasan xaka ga Safeenar" Murya can kasa Mujaheed yace "Toh, Allah ya kai mu" Umma tace "Ameen son, Allah maka albarka" yace "Ameen, xan je in yi breakfast Umma" tace "Toh shikenan" mikewa yayi ya fita dakin ya kulle mata kofar. Karfe takwas Mujaheed ya fito xai fita kofar gida yaga imaan tsaye jikin mota tana jiran fitowarsu Maimoon su wuce islamiyya, idonta ya kumbura kana ganinta kasan ba karamin kuka ta ci ba, tunda ya fito take kallonsa ta wani cika kiris ya rage ta fashe, Mujaheed ya saci kallonta suna hada ido ya dauke kai, ta fashe da wani matsanancin kuka, da sauri ya kalleta kafin yace komai ta shige gidan da gudu, direct parlon Abba ta nufa, ta samesa kuwa yana kallon news shi kadai, ta xube nan tsakiyar parlon ta dinga rusa kuka kamar xata shide, ya mike da sauri yace "Subhanallah, me ya faru mamana?" Tana kuka sosai tace "Abba Yaya ne ke min dariya, Wayyo Abba" da mamaki yake kallonta, yace "Dariyar me yake maki" ta kara fashewa da kuka tace "Nima ban sani ba wllh Abba" komawa yayi ya xauna yace "Xo nan" mikewa tayi ta koma kusa da shi tana kuka sosai, yayi murmushi ya rungumeta yace "Ya isa haka mamana kiyi hakuri kinji" ta kasa cewa komai yace "To baxa ki daina kukan ba?" Da kyar tace "Xan daina" Ya dau handkerchief ya mika mata yace "Toh goge idon ki kiyi Shiru" tana sauke ajiyar xuciya ta amsa tana goge idonta wasu hawayen na sakkowa, Umma ce ta shigo parlon rike da mug din ruwan Lipton yana turiri, tun da ta shigo take kallon Imaan dake rungume jikin Abba har sannan ta dinga kallonta da wani expression a fuskarta, Umma ta dai ajiye mug din hannunta xata xauna Abba yace "Nemo min Muhammad" Umma tace "Muhammad kuma, lafiya? Ina jin dai ya fita uxurin gabansa ba gwanda a kai ta asibiti ba idan ma ciwon nata ne ya tashi" Abba ya dau wayarsa yayi dialing number Mujaheed, Mujaheed dake xaune gun mai kiosk dake 2 houses away bayan ya siya card ya dinga kallon screen din wayarsa ganin Abba ke kira, ya daga ya kai kunnen kafin yace komai Abba yace "Muhammad ka sameni parlona yanxu" Daga haka ya katse wayar, Umma ta tsaya kallon Abba fuska daure, ba a dau lkci ba Mujaheed ya shigo parlon da sallama, sosai gabansa ya fadi ganin Imaan kusa da Abba ga Umma ma tsaye a parlon, ya sunkuyar da kai ya duka kasa a hankali yace "Abba gani" Abba na kallon Imaan yace "Me kika ce ya maki mamana" cikin rawar murya tace "Dariya ya min ban san ko ya san Ammi ta doke ni bane" Abba yace "Subhanallah ta doke ki kuma, me kika mata" ta fara kuka tace "Wai na sha ma inna fura shine ta mareni ta kuma dokeni a bayana" Abba yace "Aa bata kyauta ba xan je In sameta yanxu kuwa, kai kuma Mujaheed dariyar Uwarka kake mata" Umma ta dinga ma Abba wani irin kallo, Mujaheed ya girgixa kai yace "Abba ni ban fa ganta ba balle in mata dariya" Imaan tace "Wllh ya gan ni ya dinga kallona a sace" tana fadin haka ta fara share hawayen dake sakko mata, Mujaheed yace "To tayi hakuri tunda tace na mata dariya amma ni ban mata ba" Imaan ta turo baki ta dauke kai, Abba yace "Ai kin hakura koh" kin cewa komai tayi Abba yace "Toh kiyi hakuri mamana Aisha kuma zan je in sameta yanxu, maxa tashi ki tafi makarantar kar ki makara" Umma ta fice parlon rai a bace, a hankali Imaan tace "Abba nasan su Maimoon sun tafi yanxu" Abba yace "To mu je in ajiye ki" yana fadin haka ya mike ya dau makullin mota, Mujaheed ya mike yace "Bari in ajiyeta Abba" Abba ya dau dubu biyu ya bata yace "Toh ga kudin lunch din ki" ta rusuna ta amsa.

 

Alhamdulillah, Thanks to all those that patronize the book *Imaan* Allah bar ku da iyayen ku, My book Imaan is for sale coz I am done with free pages tun friday, ni nasan it will go round as usual, I can't prevent that, but if you should come across it it's not for free, i repeat it's not for free, na siyarwa ne, wllh I am too grown up to say Allah ya isa, but have the fear of Allah SWT in u, don't forget it's my property, hakkina ne, wahalata ce, pay before reading, pay before reading, or you just over look it and smile, have a very good conscience plss, and a good conscience won't read happily without paying, if you want any favor pertaining to d book contact me and let me know, the book is 300 via..... Fcmb 3276052019

Hauwa Bello Jiddah

 

07087865788 and then u contact me through this digit to be added in the payment groups. Thanks once more for patronizing.

 

For those saying xa su same shi a banxa yana yawo to gashi... amma fa ba a banxa yake ba wllh, there is power in the tongue, Karamin hakkin da ka raina..... 😃😃

Post a Comment for "IMAAN 11-12"