KWAI CIKIN KAYA BOOK 2 PAGE 58
ƘWAI CIKIN ƘAYA
BILYN ABDULL
*_FARIN WATA SHA KALLO🤓
ZAFAFANKU SUN DAWO GAREKU A 2021😋😋😋😋🚴🏼
*_ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥🔥🔥
*_SABUWAR SHEKARA_*
*_TAREDA SABON SALO_*👍
✔️ *_A DUNIYAR RUBUTUN HAUSA SU NA DABAN NE,_*
✔️ *_A DUNIYAR NISHADANTUWA DA KARATUN HAUSA SU DIN NA MUSAMMAN NE,_*
✔️ *_A DUNIYAR FADAKARWA DA
QAYATARWA NA KARATU SU DIN NA FARKO NE,_*✔️ *_A 'BANGAREN NISHADANTUWA DA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA MAI SHIGA RAI DA SANYA SHAUQI DA NUTSUWA TO SU DIN ZA'BABBINE,_*
✔️ *_A 'BANGAREN SANYA NISHADI DA BARKWANCI TO SU DIN QWARARRINE,_*
*_Shin ko kunsan su ake kira da zafafa biyar masu tashe?_*
_*Idan kin/ka san kai maabocin karatun littafan HAUSA ne to tabbas karku Bari ayi Babu ku*_
*_domin kuwa wannan karon sun dawo muku da wani sabon salon Wanda babusa a DUNIYAR karatu,_*
*_cikinsu Babu wadda bataga jiyaba bataga yauba a fagen nishadantarwa._*
*_ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥
_*YANKAN BAYA*_💚
_BILLYN ABDUL_
( _kwai cikin qaya_ )
( _raina kama_)
( _wutsiyar raqumi_ )
*_SIRADIN RAYUWA_*💛
_SAFIYYA HUGUMA_
( _alqawarin Allah_ )
( _daurin boye_ )
( _Dangantakar zuci_ )
💙
_*KIBIYAR AJALI..*_💜
_MISS XOXO_
(Sulke baya tsare ta sai ta wuce)
( _Igiyar zato_)
( _Kaimin halacci_ )
( _Naufal_ )
*_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡
_HAFSAT RANO_
( _ruhi daya_ )
( _Sauyin qaddara_ )
( _Daurin goro_ )
*_MIN QALB_*❤️
_MAMUHGEE_
( _buri daya_ )
( _tarayya_ )
( _eznah_ )
Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,
Guda hudu 4 Kuma 500,
Guda uku 3 Kuma 450,
Guda biyu 2 Kuma 400,
Guda daya akan 300.
Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*09044191709*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
*09033181070*
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
Page 58
.................Muna tsaitsaye a inda aka bamu iznin tsayawa, Rose na mana bayani akan abinda zamu tunkara. Cikin takunsa na zaratan jami'ai da sukasan aikinsu ya fito Hafiz biye da shi da bullet proof jacket a hannunsa da alama ta boss ɗince, A boss ɗinsa dana fara sani yake yau, kura ga tsoro gaban tsoro, zakin da babu abinda ya sani face farauta a lokacin da yunwa ta ciyo cikinsa, gwarzon da baya alfarma ga dukkan wanda baima kansa alfarmarba, ɗaya tamkar da dubu abin buƙatar kowacce ƙasa, kowanne yanki, ko wacce zuri'a. Cike da izzarsa mai cike da tsantsar damuwa da ɓacin rai yazo gabanmu ya tsaya yana ƙare mana kallo ɗaya bayan ɗaya. Ya furzar da wani zazzafan huci daga bakinsa yana nunamu da yatsansa manuniya. “Kusa a ranku aiki zaku fita bakin rai bakin fama, sakacinku na nufin sakaci da ƙasarku, sakaci da yankinku, sakaci da garinku, sakaci da familys naku, idan kuka zama jajirtattu kun fido da martabar ƙasarku ne, yankunan ku, garinku da familys naku dama rayukanmu baki ɗaya da hukumarmu. Aikine mai cike da haɗari, ka kashe ko a kasheka wannan duk hukuncin ALLAH ne, shawarar kawai itace addu'a, ina fatan kuna faimta ta”.
“Yes Sir!!!” muka faɗa cikin haɗa bakuna tare da buga ƙafa ƙasa mukai salute nashi. Juyawa yay ga Rose yay mata maganar da bamaji kafin ya kalli oga Hafiz shima. Shima maganar sukai suka bar wajen kuma zuwa inda su Sir Ahmad ke tsaitsaye tare da manyan jami'anmu da sojoji kusan goma sha biyar.
Mudai muna nan tsaitsaye muna jiran umarni, a haka oga Jabeer ya zo wajen ya bamu damar zuwa mu shiga jirage masu saukar angulu (Helicopters) da za'ai tafiyar dasu. Mu matan an haɗamu ne a guda ɗaya, drivern mu ma ta kasance mace ce yarinya ƙarama da bazamu gaza sa'anni gudaba, sai baba ƙaura kaɗai daya kasance namiji a cikinmu wanda ya wuce muce masa uba kawai sai dai kakanmu. A yau babu zancen fira mu dasu Ummie, kowa addu'a ce ɗauke da bakinsa da fatan nasara, a can ƙarƙashin zuciya kuma tsorone da kowa ke ƙoƙarin dannewa. Sai da muka hangi tashin wasu jiragen kafin namu ya tashi, kusan duk sai da muka lumshe idanu kowa shi kaɗai yasan abinda ke a cikin ransa.
Kamar a wancan karon tafiyace mukai da hasashe bazai iya ƙididdigar iyakartaba, sai dai kawai muka tsinkayi saukar jirginmu a tsakkiyar jeji mai cike da surƙuƙi da haɗarin gaske. Mun firfito kowa na ƙoƙarin kare ƙurar da fankokin jirgin suka tayar da hannunsa domin samun damar ganin hanya da ƙyau, wasunmu da basa son ƙura har ƴan ƙananun tari sukeyi da atishawa. Su boss suma duk sun firfito a nasu. Sir Ahmad na ƙoƙarin buɗe taswurar jajenin da ya amsa a hannun oga Aliyu baba ƙaura ya dakatar dashi. “Ranka ya daɗe bama buƙatar wata taswura, insha ALLAHU komai zai kasance yanda muke fatansa, babu wani lungu ko kogo da zai layancemin a wannan jajenin kaf ɗinsa, inda muke buƙatar zuwan zamu dosa kai tsaye babu ko gargada a ciki”.
Sosai naga al'ajabi a saman fuskokin jami'anmu, muko da muka san wanene baba ƙaura hakan bai zame mana sabon abuba, fatanmu kawai samun kariyar UBANGIJI da nasara.
Tafiya muka farayi a cikin jejin, su oga Aliyu da boss da wasu a cikin sojojin da baba ƙaura ne a gaba, sai su Sir Ahmad a bayanmu. Munyi tafiya mai nisa kafin mu isa wani ƙyaƙyƙyawan tsuburi dake da ƙaramar ƙorama a gefensa, sai tsuntsaye jefi-jefi dake shan ruwa. Da hannu boss ya tsayar damu kafin mu ƙarasa ga ƙoramar, Oga Jabeer ya matsa kusa da boss, bullet proof jacket ɗin dake a hannunsa ya shiga ƙoƙarin saka masa suna magana, nidai ina satar kallonsune da faɗin ‘Ɗan gata rigarma sai an saka masa’. Ya juyo saitin da muke yana bama Jabeer bayansa danya gyara masa can, ido muka haɗa nai azamar janye nawa, a bazata naji yace, “Miemaa!”. Abinda ya tsargamin nai saurin haɗiyewa, yayi masifar iya ambatar sunannan fiye da zaton mai tunani, kallonsa nayi na amsa da “Na'am”. Ya ɗauke idanunsa daga kaina yana faɗin, “Ki gyara wannan jacket ɗin taki bata zauna da ƙyauba”. Gaba ɗayansu suka zubamin ido banda su Sir Ahmad da hankalinsu ba wajanmu yakeba. Kaina na jinjina masa ina haɗiye yawu da ƙyar dan yanda duk suka zubomin ido sai naji na takura. Nazifa dake bayanace ta taimakamin na gyara, idonsa har yanzu a kaina yace, “Matan nan ku kasance kusa da wani komai rintsi, sannan banda harbi a kai, ciki, ƙirji, duk harbin da zakuyi karya wuce ƙafa ko hannu da inda baza'a mutuba”. Kai muka jinjina masa da faɗin, “Okey Sir!!”.
Rose ta taɓe baki tana harar Bilkisu ta gefen ido, duk da tasan abinda Jawaad ya faɗa musu dokace kasancewar a harbin da duk su bilkisu zasuyi babu kisa sai ankai maƙurar da babu mafita taji zafi a ranta, dan a ganinta Jay ya faɗama bilkisu ne ita kaɗai kawai cikin tsantsar nuna kulawa, tunda harda cewa ta gyara jacket ɗinta. ‘Mtsossw’ taja ƙaramin tsaki a ƙasan maƙoshi da matsawa gaba.
Da ga inda muke tsaye muna hango gini maiban mamaki da tu'ajibi, dajine sosai fa. amma sai ga gida a tsakkiyarsa, gida ginanne daya amsa sunansa gida da ko a cikin gari ya cancanci kallo bawai sakaran gini ba ne. Babu wanda al'ajabi bai sakashi kallon baba kaura ba. Cikin dattakonsa yay murmushi shima batare da ya kalli kowa a cikinmuba. “Wannan gini ginine da ya ɗauki kusan shekaru ashirin da bakwai a cikin jejin nan, magina aka kawo suka ginashi kamar yanda ake gina kowanne irin gida, duk shekarar duniya kuma sai an sabunta masa fenti da abubuwan ƙawa. Mabanbanta mutanene ke zuwa cikinsa ziyara, abinda suke aikatawa a cikinsa kuma, sai munje idanunku zasu gane muku komai a yanzun, domin yau ranace da suka ware ta musamman domin shaiɗancinsu, shiyyasama muke anan tsaye bisa ƙafafunmu batare da sun farga da zuwan namu ba”. Kawuna kawai muke iya jijjigawa kamar wasu ƙadangaru, shine yay mana nuni damu ƙarasa.
Ararrabe muka fara dosar ginin muna zagayesa kamar yanda commander'n (boss) tafiyar ya bada umarni, ɗai-ɗai muka ringa shiga cikin dabara na salon aiki, ina niyyar bin bayansu nima aka riƙo hannuna, waigowa nai da sauri dan bansan waye da aikinba. Ya harareni damin alamar na dawo bayansa da idanu. Bani da zaɓin da ya wuce bin umarninsa, na dawo ta bayansa yana gaba, duk da gani a baya sai ya raba hankalinsa wajen kallon bayansa da gabansa, da haka muka shiga ciki muma kamar yanda oga hafiz da Aliyu, Jabeer sukayi, sauran kuma suna daga waje su da su sir Ahmad. Tafiya muke a sannu-sannu, babu wanda yay harbi dai a cikinmu kamar yanda har yanzu nidai banji motsi na alamar akwai mutum a gidanba.
Cikin matuƙar zafin nama da ALLAH ya bama boss ya fisgoni tare da duƙar da ni saboda tahowar wuƙa da aka wulwulo a bazata wadda sam hankalina baya wajen, bakuma musan dga inda take ba, jikinsa na faɗa, shi kuma ya cafe wuƙar a hannunsa. ɗagowa nai ƙoƙarin yi idanuna suka sauka akan ƙafa dake ta wani ɗan lingu, komawa nai na duƙe har yanzun hannun hagguna na cikin na boss. Handkherchief ɗin aljihunsa nasa hannu na ɗauka, tsayawa yay yana kallona yaga mizanyi, na zare hannuna daga nasa na ƙarasa takawa inda ƙafar take cikin sanɗa, sai da naje gab sannan na miƙe sosai cikin zafin nama na ratayo handkherchief ɗin a wuyan wanda ke tsayen, kafin yay wani yunkuri na ɗaure masa wuya da ƙarfi yanda ko ƙara zaiyi babu maiji. Sukur-sukur ɗin da mutumin keyine na neman ƙwatar kai ya saka boss kallona, fuskarsa ɗauke da murmushin dana jima ban ganiba yaymin jinjina👍🏻. Nima sai nayi murmushin dan ya bani dariya a salon da yay da idanu da murmushin harma da jinjinar. Zagayawa yay ta ƴar ƙofar daya gani wajen wanda har yanzu nake ɗaure da wuyansa harya suma, yaymin nuni dana cire handky ɗin, ya kamasa ya kwantar ƙasa nima na zagaya.
Jinjina ya sake min, cikin magana raɗa-raɗa yace, “Aikinki yayi ƙyau Babie”. Ɗan murmushi nai masa sannan muka shige ta ƙofar da muka gani cikin sanɗa. Saurin dakatawa yay yaɗan ja baya kaɗan muka koma jikin bango da ɗauke numfashi. Baƙin mutumin da sam babu imani tattare da shi yazo ya wuce ta kusa da mu sai dai bai kawo inda muke ba, har yay ɗan nisa sai kuma ya dawo baya yana waige-waige. Yana zuwa gab damu boss ya jawo masa riga ta baya, cikin wani irin zafin nama ya juyo sai kawai ya buga masa kansa yay baya, oga Hafiz daya ƙaraso wajen ya taresa da saurin ɗora masa handkherchief ɗin hannunsa a hanci, da alama wani abun ya shaƙa masa, dan a take jikinsa ya saki. Ƙasa ya kwantar da shi yana ɗagowa, ya matso kusa damu sosai cikin magana raɗa yace, “Boss kuzo gasu tanan”. Binsa mukai cikin sanɗa ta hanyar daya biyo boss nata faman murza goshinsa da yayma mutum can gware alamar yana masa zafi wajen har yanzun.
Tsaye muka tadda su Jabeer cikin matsanancin ruɗani, ni da boss muka ƙarasa jikin glass ɗin wajen da akayisa domin kwalliya kawai muka leƙa. A take tsigar jikina ta tashi, ƙirjina yay wata irin dokawa nai saurin yo baya ina ambaton ‘Wa'iyazubillah’. Boss kam tsaye yake kyam akan ƙafafunsa ya dasama wajen ido baya ko ƙyaftawa, sai dai jikinsa shi kansa tsuma yake, gashin duk sun mimmiƙe alamar shima tsigar jikinsa tashi take. Duk mai imani dolene ganin wannan shaiɗancin ya tada hankalinsa.
Shirka ƙuru-ƙuru ga waɗanan shaiɗanun mutane da a zahiri suke ambaton kayinsu musulmai harsu shiga masallaci suyi salla cikin jam'i ma. Gaba ɗayansu zindir suke sai wani ƙyale ja da suka ɗaura a ƙugu ɗan guntu da iya al'aurarsu kawai ya rufe, sai wani ɗaure a kansu, durƙushe suke gaba ɗayansu sunyi Sujuda, tsakkiyarsu ƙaton kaskon tukunyar ƙasa ne da aka kunna wuta a ciki tana ci, sai babban shiɗaniyar tasu da kasancewarta tsirara yasa muka gane mace ce zaune bisa kujera kanta a duƙe itama riƙe da sandar da maybe itama ta tsafin nasu ce. Hawaye na gani suna sakkowa a kumatun boss, jin damshi a tawa fuskar ya tabbatar da nima hawayen nakeyi ashe. Ganin zasu miƙe boss yay saurin maidoni baya muka koma jikin bango, muna kallonsu ta haka. duk suka miƙe tsaye suna wani yare da su kaɗai sukasan mi suke faɗa, da fuskar Alhajin da naje gidansa na ɗakko tukunyar nan na fara cin karo, ganinsa da nai a hoto a gidansa yasa ananma na shaidashi, sai wanda ke a kusa da shi daya kasance shima mutum mai tarin faɗa aji a ƙasar nan, zuciyata wani irin luguden daka take kamar zata faso ƙirjina ta fito nakai dubana gana uku, shidai ban sanshiba kam, sai na huɗu shima ban sanshi ba, a na biyarne kam ƙafafuna suka nemi gaza ɗaukata, dan kuwa ba kowa bane face Uncle Nasir, bankai ga fita a ruɗanin dana shigaba na ganin Uncle Nasir idanuna suka sake sauka akan Dadyn Zuhrah, sai yayan Dadyn su Ummie dana taɓa gani a ranar bikin yayemu daga Jami'a. A haka na cigaba da binsu da kallo, wasu na riga da na sansu a tv, wasu kuma ɗai-ɗaiku a zahiri, wasu ko ban taɓa ganinsuba sai anan, nabi wanda ya juya mana baya riƙe da ƙoƙo da kallon sani, sai dai bana ganin fuskarsa, amma hakan bai hanani jin zuciyata raunana ba matuƙa akansa, so nake naga wanene amma ya juya baya.
Durƙusawa yay yayi sujuda (Wa'iyazubillah😭) ga wannan la'ananniyar tsohuwar mata dake a kan kujera kamar basarakiya, sai kuma ya miƙe da ƙoƙon hannunsa yaje gabanta kansa a rissine ya miƙa ƙoƙon. Ƙyalƙyalewa tai da wata irin mummunar dariya da sam muryar tata bata kama data mata, sai kuma ta haɗe fuska tana faɗin, “Jariri!! Kai mutum ne mai daraja a wannan Bakandamiyar tamu, kaine farkon fara nasara ga dukkan matakai da tsare-tsarenmu da ƙa'idoji, kowane aikinka ka gudanar da shi babu kuskure ko sau ɗaya, sai a na ƙarshe da ya zama cikamakin ayyukanka ya gagareka?, ta dalilin yarinya ƙarama a cikamakin ayyukanka mun fuskanci asarori masu yawa. Hhhhhhhh Mun baka dama tun a watan jiya Jariri amma ka kasa damawa, munce ka nemo mana asalin yarinyar kace asalinta na farko daka kawo shine asalinta, sai dai mu bamu amince da hakanba. Lallai Jariri wannan yarinya bincikenmu ya gano mana akwai sirri mai nasaba da mafarkin mu na watan jiya dangane da ita. Jariri wannan itace dama ta ƙarshe da zamu baka akan wannan yarinya, Bakandamiyar mu na buƙatar jininta tunda budurcinta ya gagara, Jariri, idan ka gaza hakan daga nan zuwa kwanaki biyu zaka fuskanci mummunan hukunci daga Bakandamiya, zakuma mu saukeka daga shugabancin da kake kai. Sannan Jariri a yau ɗinnan ka tabbatar an sake ɗaura igiyar aure tsakanin gudalliyarka da yaron nan, inba hakaba bazamu yafe makaba a wannan karon dolene ka bamu jinin gudalliyarka........”
“Tuba nake uwargijiyarmu, tuba nake uwa maba da mama, tuba nake mai share kukanmu, ina sake roƙon alfarmar a barni da gudalliyata dan itace zuciya ta, zan iya yarda na rasa abubuwa da yawa amma banda gudalliyata ya shugata, nayi rantsuwa da shugaban shaiɗanu a yau sai igiyar aure ta ƙullu tsakanin gudalliyata da halattaccen jinin Bakandamiya. Ina mai sake rantsuwa da a gobe saina kawo jinin wannan yarinya wa Bakandamiya shine zai zama abin kalacin mabiya Bakandamiya yake abar bautarmu”. (wa'iyazubillah😭🙏🏻)
“Bakandamiya ta amsa maka, ta kuma baka damar ƙarshe ta dawowa da martabarka tare da dukkan muhimman abubuwan ƙungiya dake a hannun yarancan da jininsu ya halatta ga Bakandamiya. Kurakuranka zasu goge a dutsen rubuta laifuka bayan ka cika alƙawuranka da jinin babban ɗanka Jariri kamar yanda yake a rubuce a sharuɗan Bakandamiya”.
“Naji na karɓa yake mai biya mana dukan buƙatunmu”.
“Hhhhhhhhhhhhhhhhh!!!!!!!!!!!!!!” ta kece da wata mahaukaciyar dariyar da ta saka duk saida muka toshe kunnuwanmu saboda yanda dajin gaba ɗaya yake amsawa bama gidan kawai ba, tanayi tana tsiyaya masa wani abu mai kama da jini a cikin ƙoƙon hannunsa. Da baya baya ya baro gabanta yana wasu surkulle da shi kaɗai yasan abinda yake faɗi, sauran na amsa masa.
Mamaki, tsoro, al'ajab da ruɗani duk suka saukarmin lokaci guda ganin Dad a inda tunanina ko tsammani bai taɓa raya minba, saurin ɗaura hannuna nai na rufe bakinna jin kuka na neman kufce min. “D... Da...Daddy!!”. na faɗa cikin rawar murya dana jiki ina mai matsawa jikin boss dake tsaye abinsa yana kallonsu Dad ɗin shi da su Oga Hafiz.
Cikin matsanancin furgici Dad ya saki ƙoƙon hannunsa da kai dubansa inda yaji muryar da bai zatoba ta ambaci sunansa. Ido huɗu sukai da bilkisu da jikinta ke wani irin matsanancin tsuma.
A take Dad ya zazzaro idanu waje cikin tsananin firgici da ruɗani, jikinsa sai wata iriyar tsuma ya keyi domin ganin wadda bai taɓa zato ko tsammani ba. duk da glashi ya raba tsakaninsu, bai gaza gane bilkisu da Jawaad ba harma da jin furucinta raɗam a kunnuwansa, dan basu da wani shamaki wajen iya jiyo maganar juna duk da akwai hilashin daya rabasu.
Bansan sanda wani ƙarfi da zafin nama yazomin cikin jini da jiki ba na bigi gilashin wajen da ƙafa jikina karkarwa saboda wata irin mummunar tsanar sa ce ta saukarmin lokaci guda da ƙyamarsa.
Sauran abokan shaiɗancin nasa da tuni suma sun mike suna kallonmu a cikin matsanancin firgici na alamun bazata a fuskokinsu suka shiga ƙoƙarin motsawa cikin rawar jiki dan neman kariya.
Kafin suyi wani yunƙuri su Jabeer sun afko suma tare da su Ummie dake jiran umarni a waje. Zagayesu akai da bindugu, hakan ya tabbatar musu basu da wata dama kuma saina miƙa wuya........
“Ƙassaaa!!!!” Boss ya faɗa a iya ƙololuwar hasala jijiyoyin jikinsa na sake mimmiƙewa. Durƙushewa sukai bisa gwiwoyinsu suna aza hannayensu bisa kawunansu alamar yin surrender.
Ban samu dawowa hayyacina ba daga kallon al'ajabi da ruɗanin da nakema Dad sai da Wani irin ihu shaiɗaniyar matarnan da tayi ya shiga dodon kunnena. miƙewa tsaye tai da buga sandar hannunta ƙasa, a take ɗakin ya fara turniƙewa da hayaƙi, sake bugawa tayi, sai jikinta ya fara canja launi harda su Dad ɗin suma. ta ɗaga zata buga na uku nai wani wawan tsale na dire a gabanta na riƙe sandar. Bazan iya fassara muku mawuyacin halin dana shiga ba a wannan lokacin, domin tsafi gaskiyar maishi ne, abinda kawai nake iya jiyowa harmutsewar wajen da ƙarar harbe-harbe ta waje alamar musayar wuta ta ɓarke tsakanin wasu a cikin jami'anmu da suke a waje da yaransu masu tsaron gidan.......
Jawaad yay azamar nufar inda Bilkisu da matar nan ke riƙe da sandarnan, jikin bilkisu wani irin rawa yake da karkarwa ga zufa, amma dan taurin zuciya taƙi yarda ta sakar matar sandar. ta gama fuskantar buga sandar nan da take sonyi zai iya zama kuskure ko halaka a garesu wajen baki ɗaya, kokuma wani siddabarun nasu zasuyi don son ƙuɓuta.
Cikin tsawa Baba ƙaura ya dakatar da Jay da ya kai hannu domin bama bilkisu taimakon. “Karka taɓata, barta da ita!!”. Ya faɗa a kausashe yana nufosu, Hankalin Jay a tashe ya juyo yana kallon Baba ƙaura da girgiza kai, “Bazan iyaba bab....” kafin ya gama rufe baki baba ƙaura ya riƙo hannunsa, hakan yayi dai-dai da hankaɗa bilkisu baya da matar tayi, ta ɗaga sandar zata buga a ƙirjin bilkisun.
Da sauri nai wani irin juyi sandar ta caki ƙasa, nasa ƙafa na taɗo tata ƙafar itama, baya tai, na bigi sandar da ƙafa itama tai sama na cafe cikin hannuna daga kwancen da nake.
Wani irin mummunar amsa kuwwa ce ta karaɗe jejin lokaci guda, hakan ne ya saka ruɗani gasu Jay kowa ya shiga ƙoƙarin toshe kunnensa banda baba ƙaura da yasa ƙafa ya hankaɗa tukunyar kaskon wutar nan dake ci har yanzu ya kife a kujerar da matarnan take zaune ɗazun. Tamkar an tsaida ihun sai dajin yay cak lokaci guda kuma. Waige-waige su Jabeer suka fara dan su Dad gaba ɗaya basu a wajen sai matar kawai dake a kwance ƙasa inda bilkisu ta zubar da ita, saboda take mata ƙafa da Baba ƙaura yayi.
Hankalinsu duk tashi yayi suka shiga leƙe-leƙen lungu da saƙo na cikin gidan hankulansu a tashe, sai dai abin mamaki babu ko ɗaya a cikinsu sai mutane da aka ringa zaƙulowa a cikin ɗakunan cikin hardasu Alhaji Babba da ke a cikin mawuyacin hali.
Baba ƙaura ya cire jikkarsa ta fatar damisa ya ajiye ƙasa, da hannunsa ɗaya ya buɗeta ya ɗakko wani wani irin kibiya ta ƙarfe sai sheƙi take da walwali ya shaƙo wuyan matarnan ya miƙar da ita tsaye, watsa mata wani mugun kallo yay yana huci, a take ta ƙwalla kururuwa jikinta na rawa. “Barde kaga zan dawo dasu kaimin rai karka kassarani mai babban suna, na tuba nabika”. “Bana buƙatar tubanki shaiɗaniya, ai dama na faɗa miki nine ajalinki kokin manta na tuna mikii!!!!”. “Cikin rawar jiki take girgiza masa kanta, ya fincike manyan layun dake a wuyanta ya watsar ƙasa, a take ta zube a wajen tana fashewa da kuka. Cikin ƙwarewa da sararafa hannunsa guda ɗaya da dungulmin ɗayan ya ɗana kibiyar nan ta ƙarfe a kanta. Da sauri ta buga ƙasa da hannunta har sau uku sai gasu Dad dake can gefe rufe da wani jan ƙyalle sun bayyana.
‘Innalillahi wa'ina ilaihirraji'un yau muna ganin tsantsar tashin hankali da shaiɗanci, da a labaran tatsuniyoyi da fina-finai kawai muke jinsu. Koda ake cewa akwai matsafa a duniya da yankunanmu ban taɓa yardaba, a nawa zaton labarine kawai na ƴan shafawa labari shuni, ashe gaskene, ashe zan gani da idanuna, ashema harda jinina a cikinsu wanda na ɗauka uwa uba ma. Hawaye nake masu zafi da ƙunar zuciya, kaina juyamin yake gaba ɗaya dama duniyar kanta, tun ina fahimtar abinda ke faruwa har jina da ganina suka ɓace ɓat daga duniyar mutane, daga haka ban sake sanin abinda ke faruwaba kuma.
Cikin zafin nama Ada ta tare Bilkisu da juwa ta ɗiba, a tsorace take kiran sunanta tana girgizata ganin batama numfashi gaba ɗaya. Aliyu ne yayo kansu yana tambayar lafiya, dan Jay tunda aka fiddo su Alhaji Babba yabar nan zuwa garesu.
Ba Bilkisu ce kaɗai ta sumaba, Zuhrah tun cin karo da idanunta sukai da Abbanta ta sume, hakama Ummie ganin yayan mahaifinta tuni ta suma, sai cikin mutanen da aka iske a wajen da yawansu basa cikin hayyacinsu harda su Alhaji babba da basu wuci awanni da kawosu wajenba, dama ga tsufa kuma. Wasu daga cikin yaran su Dad an harbesu, harma da waɗanda aka kashe.
Jejin ya hargitse sosai, bakajin komai sai ƙarar helicopters na sojoji dake shigowa cikin jejin saboda wayoyi da su Sir Ahmad suketa faman yi da amsawa. Dandanan sojoji da masu bada taimakon gaggawa harma da ƴan jarida dake cikin jami'an tsaron da su Qaseem duk suma suka iso. Cikin ƙanƙanin lokaci jejin ya sake harmutsewa da motsin mutane dana ababen hawa.
Su Dad na durƙushe cikin ƙasƙanci daga su sai jajayen ƙyallayen kawunansu dana ƙugu da sukaɗan rufe jikinsu kaɗan, sai da jami'an tsaron da suka iso suka sauka sannan bisa alfarmar da General ya buƙata aka basu mayafai suka rufa, amma da Jawaad yace a haka za a fita jejin dasu har cikin gari domin sauran al'umma su gansu.
Dajin fa kamar wasa sai gashi ya tara jama'a masu yawa kama daga manya-manyan jami'an tsaro, zuwa shugabannin ƴan siyasa da ƴan jaridu, dan babu abinda ke kai kawo sai helicopters da ƙananun jirage na yaƙi. Mutanen dake a cikin gari kansu sun fahimci ƙasar babu lafiya yau, dan kai kawon da helicopters keyi kawai ya isa amsa. yayinda kuma ƴan Jaridu suka fara nuna komai ta gidajen tv'n su live. Duk ta yanda manyan ƙasar sukaso kar hakan ta kasance basuci nasaraba, dan kuwa ƴan jarida sunada ƙarfin iko da ƴancinsu suma, balle kuma akan wannan al'amari mai tsananin saka ruɗani da al'ajabi ga duk mai sauraro bama kallo kawai ba.
An shiga kwasar su bilkisu da suke a halin suma aka fara barin jejin dasu domin miƙasu ga likitoci su samu taimakon gaggawa, sai waɗanda suka sami harbi da gawawwaki da mutanen da aka samu an kawo harma da gawarwakin mutane da aka iske a wani ɗaki cikin freezer irin wadda ake saka gawarwaki a asibiti, dan gidan suna amfani da babban janareto dake basu wuta 24hours, duk wani abun more rayuwa kuma akwaisa a gidan hatta da ruwa.
Su Jay ne keta kai kawo haɗa rahotanni har aka kammala kwashe mutane da gawarwaki da wasu kayan sirrika da ke a cikin gidan tas, basu baro jejinba sai bayan sallar la'asar, zuwa lokacin labari ya gama karaɗe lungu da saƙo na ƙasar harma da ƙasashen ƙetare, to abinka da manyan mutane da ake ganin mutuncinsu acikin manyan riguna da kuɗi suka saya musu.
__________________________
Su Ummah basu farga da rashin su Jawaad a gidanba sai da su Nabeelah sukai kusan mintuna talatin da baro kitchen. Cikin ƙaguwa Umm-Anum ta kalli ƙannen nata cikin hausarta da bata fita da ƙyau yanzun tana faɗin, “Mariya wai ina ɗanku ya shige da matarsa ne? Nifa na ƙagu naga ubana, gara yazo ya kaimu ala bashshi sai su ɗakko su Abbun Anuwar ɗin daga can idan sun iso”. Murmushi Ummah babba tayi, ta kalli Nabeelah da suke kallon hotuna a wayarta da Anum. “K Nabeelah kiramin yayanku”. Cikin ƴar ruɗewa Nabeelah tace, “N...n.....na'am Ummah mi kika ce?”. “Ƙaniyarki nace dan gidanku” ta faɗa tana mata daƙƙuwa. “Kai Ummah ALLAH nifa banji bane ba”. “ALLAH ya shiryeki to, canai kije ki kiramin yayanku”. Jimmm tai na tunanin abinda zata faɗa, sai kuma dai ta miƙe ta fita, a babban falo ta tsaya tanata kaikawo, tarasa wacce amsa zata koma ta bama Ummah ne, tsoro faɗar gaskiya take kodan gargaɗin da Jay yay mata akan hakan”. Anuwar da ya shigo falon ya lallaɓo ta bayanta yaja jelar gashinta. A firgice ta juya zata ƙwalla ƙara na tsorata yay azamar rufe mata baki yana kallon sashen Bilkisu cikin ɗan zaro idanu. Sai da ya tabbatar ta nutsu sannan ya saketa yana sauke ajiyar zuciya da murmushi kan fuskarsa, “beauty ke matsoraciya ce gaskiya”. Cike da shagwaɓar data saba ta tura masa baki, “Yoni tsoro naji ALLAH, nazata Yayanmu ne”. Murmushi Anuwar yayi dake sake bayyana kamaninsa da Jawaad sosai yana ƙara narkar da idanunsa a kanta, “Kiyi haƙuri tam, halan laifi kikaima Yayan kike tsoron ku haɗu?”. “A'a ba laifi namasa ba, sai dai Ummah nason tajamin nayi masa yanzu”. ta ɗan wawwaiga kamar mai tsoron Jay ɗin ya ganta sannan ta juyo ga Anuwar da shima ke tayata waigen, ƙasa tai da murya cikin raɗa ta faɗa masa gargaɗin Jawaad. Sosai abin yaso bashi dariya, shifa tun a bikin su Jay ya fahimci Nabeelah akwai wautan autanci tattare da ita, “To ai kin kuma faɗamin yanzu, kenan bakiji gargaɗin nashi ba?”. Idanu ta waro waje sosai tana ɗaura hannunta biyu aka zata fashe da kuka”. “Kinga wasa nake miki” Anuwar ya faɗa da sauri ganin zata saka masa kuka. “To faɗamin mi zan cema su Ummah?”. Kafin ya bata amsa Aunty Batool ta shigo, ganin ta wucesu tana kuka sukai saurin bin bayanta.
Hankalin su Umm-Anum a matuƙar tashe suka tari Batool, kowa tambaya yake jeho mata akan miya sameta?. Yanda duk suka rikice sai suka bata matuƙar tausayi, bata ɓoye musu komaiba ta labarta musu halin da ake ciki har zuwan su Jawaad da tafiyarsu office akan case ɗin.
Faɗuwar Umm-Anum kawai sukaji batare da kowa yaga sanda tai yunƙurin faɗuwarba, hankalinsu a take ya sake tashi, basu wani tsaya maida yanda akayiba suka kwasheta zuwa asibiti, dole Batool ce tai driving ɗin, dan Anuwar baisan hanyaba.
Anum da Nabeelah nata kuka su Ummah na rarrashinsu. Saboda ta samu kulawar gaggawa sai Batool ta nufi asibitin Dr Tayyeb da su, ai ko babu ɓata lokaci aka karɓesu da bama Umm-Anum taimako akan lokaci..........
__________________________
A ɓangaren su Mom kuwa sun gama yanke hukuncin sake ƙulla auren Jawaad da Shahudah batare da neman yardarsa ba, dan haka babu wani ɓata lokaci mama Atika ta saka aka tattara mata su Uncle Sulaiman, sai dai kuma babu Uncle Nasir, acewar matarsa yayi tafiya tun daren jiya.
Mom ta kira wayar Dad shima a kashe, hakan bai dameta ba, dan tasan shima burinsa kenan ai, dan haka sukace Uncle Uwaisu ya wakilci Dad ɗin, Uncle Sulaiman kuma Jawaad.
Duk yanda Uncle Sulaiman yaso fahimtar dasu kuskuren yin hakan sam Mama Atika taƙi fahimta, saima rufesa da tayi da masifa tamkar zata cinyesa ɗanye. Haƙuri ya bata, a take aka tattara samarin gidan da maƙwafta kasancewar weekend ne aka sake ƙulla auren Jawaad Abdul-Aziz yusif da Sabeera Aliyu Fillo akan sadaki naira dubu ɗari da Uncle Sulaiman ya biya.
Zo kuga farin ciki wajen Shahudah amarya dasu Mom da Mama Atika, dan a wannan karon sun ɗauki alwashin babu abinda zai dakatar dasu daga cika burinsu akan abinda suka jima sunama ƙwaɗayi. Ana cikin wannan murnarne ɗiyar Uncle Sulaiman tazo sashen mama Atika da gudu tana kuka da faɗa musu cewar suzo mama Badiyya na wani abu mara daɗin gani.
Gaba ɗayansu suka kwasa Uncle Sulaiman har gudu yake da tuntuɓe dan mahaifiya tafi gaban wasa. Sosai hankalinsu ya tashi, murnar ɗaurin auren da sukeyi ta gushe tabar fuskokinsu baki ɗaya. Cikin gaggawa aka ɗauki Mama Badiyya zuwa asibiti, kasancewar kowa yasan matsalolin asibiticinmu na gwamnati sai Mom ta bada shawarar a nufi asibitin Dr Tayyeb zatafi samun kulawar gaggawa. Da wannan shawarar sukai amfani suka nufi can, sauranma suka shiga motoci suka dafa musu baya.
Da gaggawa aka amsheta, itama sauran likitoci suka rufu kanta dan Dr Tayyeb yana wajen Umm-Anum a lokacin, sai da yaga numfashinta ya dawo jikinta, ma'ana ta farfaɗo sannan ya saka mata ruwa ya fito dan amsa kiran da Mom keta masa a waya. Sai a lokacinne shi yakejin cewar mama Badiyya suka kawo, bai tsaya bama su Ummah gamsashshiyar amsar da suke buƙatar jiba ya basu haƙuri akan su jirashi ya nufi ɗakin da aka kai Mama Badiyya..............✍
Hummmm koya zata kaya a asibiti kuma tsakanin waɗan nan familys guda biyu? Ga tashin hankalin dake faruwa daga su Jawaad wanda duk ya shafi waɗanan ahali, kumuje zuwa dan jin yanda zata kaya masoya, dan aski yazo gaban goshi insha ALLAHU, kuma da gaske bily ta DAWO GARE KU🤗😍😍😘.
ALLAH Ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
Post a Comment for "KWAI CIKIN KAYA BOOK 2 PAGE 58"