IMAAN 1-2
*Imaan*
_By Khaleesat Haiydar_
*All thanks to Allah SWT
for giving me the chance, privilege and ability to start this book, my special
greetings goes to my lovely mum Hajiya Hajara and my sweet aunties (Small mums)
my siblings aren't excluded also... I love them all, Ban mance ki ba Mama dutse
ina gaisuwa da fatan anyi sllh lafiya Allah ya amshi ibadunmu, Hajiya Asabe
kema ina gaida ki sosai da maki fatan alkhairi Allah ya raya xuri'a, Hafsat Oum
Ilham I greet you too with respect, and My Sophiee I know you won't see this
but get this.. jiddo Love's you
dear, Lovely fans ina maku fatan alkhairi da fatan gamawa da iyaye lafiya*
1.....
Babban compound ne sosai
dake dauke da shuke shuke da bishiyoyi masu daukar hankali, kai kana ganin tsakar
gidan kasan naira ta xauna, makeken tsakar gidan na dauke da sassa har uku masu
fenti iri daya, ko wani sassa kuma akwai tazara mai tsayi tsakaninsa da wani
sassan, sashin farko wanda shi xaka ci karo da bayan shigowar ka gate din
xamanin dake babban gidan ba dai girma ba don sashin duk ya fi sauran girma,
duplex ne babban gaske sai parking space gari guda dake gefe. Durkushe a bakin
tap dake babban sashin farko wata farar budurwa ce da baxata wuce shekaru sha
takwas ba, duk da a duke take hakan baxai sa aki gane doguwa ce ita din ba,
ruwan tap din na ta xuba bucket din da ta tara don ya cika, sai shafa socks din
hannunta take kamar mai tausayinsa, daga ves, huluna sai socks kala uku sune
kayan da take wankewa a wajen amma ta kusa awa daya, kofar entrance da ta ji an
bude ya sa ta kamewa daga inda take durkushe lkci daya ta xaro ido gabanta ya
fadi don ita dai a iya saninta babu kowa sashin banda ita da ke wanki tun daxu,
occupant din bangaren duk sun tafi biki ta kuma ga fitarsu, wanda da ace suna
nan tasan ko hauka take baxata fara xuwa bangaren su tayi wanki ba, a hankali
ta juya don ganin wanda ya fito, wani matashi ne dogo sosai wanda baxai haura
shekaru talatin da uku ba tsaye dai dai entrance din shiga gidan sanye da
jallabiya milk color, Ta dauke kai tana ci gaba da daurayenta, ya rungume
hannuwan sa calmly yace "Keee" kamar xata yi kuka ta juya ta kallesa,
yace "Me ya kawo ki wanki nan?" Ta buda manyan idanuwanta tace
"Tap din mu fa ne ya lalace jiya kuma....." Ya katse ta yace
"Tashi ki bar wajen" Tace "To ai na kusa gamawa fa"
strictly yana d'an daga murya yace "Kwashe kayan ki ki bar nan kar ki
yarda in iso inda kike" ta dauke kai hade da turo baki ta mike ta xubda
ruwan gaba daya ta hade buckets din bayan ta xuba yan kayan da ta wanke ciki ta
kwashesu gaba daya ta bar wajen kamar xata tashi sama ba tare da ta sake kallon
inda yake ba, ta murguda baki bayan tayi nisa, murya can kasa tace "Allah
ya isa" Dai dai part na biyu da ya kasance wani babban hadadden Bungalow
ta tsaya, shi ma kuma bangaren na da nasa parking lot din da xai dau motoci
uku, ta dinga kallon sauran kayan da bata gama wankewa ba kamar xata yi kuka,
to ita yanxu ya xata yi da su, Ammi na ganin bata gama ba sai ta fara mata fada
yanxu tace tun daxu me take, kallon hanyar da xata bi xuwa part din karshe
tayi, ta tabe baki sanin ba lallai ma mai sashin ta bar ta ta ta6a mata tap ba,
tana ta tsaye can kuma dai ta wuce can bangaren karshen, shi ma sashin bungalow
ne sai dai bai kai nasu ba, tsarin ma ba iri daya bane, a hankali ta ajiye
buckets din hannunta dai dai tap din dake opposite entrance din shiga parlor
tana yi tana satan kallon kofar, cikin dubara ta bude tap din yanda xuban ruwan
bazai yi kara ba, ta tara bucket din a karkace kar ma aji xuban ruwa ta ci gaba
da daurayenta, sosai gabanta ya fadi jin taku duk a tunaninta mai bangaren ce,
mutumin daxu ne ke tahowa bata yarda sun hada ido ba ta ci gaba da wankinta, ko
kallon inda take shi ma bai yi ba, bai kuma kai ga shiga parlon ba suka ji
muryar wata tsohuwa tana cewa "Ni wai ya nake jin kamar ana taba min pampo
a wajen nan ne" da sauri ta kashe tap din ruwan xata kwashi kayanta ta
gudu sai ga tsohuwar ta fito, Sake baki tayi tana kallon ta kafin tace
"Waye kuma wannan, meye kike min kusa da pampo?" Budurwar ta turo
baki tace "To inna namu ya lalace..." Inna ta katse ta da sauri tace
"Da ya lalace ni na lalata maku?" Budurwar tace "To wai ma ba
daxu kika ce in xo in debo maki ruwa in kai maki bayi ba, shine fa na zo xuba
maki" Inna na mata wani kallo tace "Ke din? Ke din da na sani ce xaki
kai min ruwa bayi munafuka? bayan ba Aisha sunana ba, to wllh ki kiyaye ni a
gidan nan ruwana ba na banxa bane kar ki sake xuwa min nan, kin lalata naku
nima ki xo ki lalata min nawa saboda mugunta koh, to uwar ki ce xata debo mun
ruwan idan na tankin ya kare, haka kawai ki bar ni da diddigin pampo duk tsutsa
cuta ta kama ni in bar 'ya yana da wahala, ke dai wannan yarinya ta Bukar
muguwa ce wllh, shegen barnar ki ta fi karfin ki, to wane 6era ma" ita dai
Budurwar sai kallon ta take kamar xata yi kuka, inna na xaro ido tace
"Maxa dau min ruwana ki tafi ki juye min a bandaki, ni dai a gidan nan duk
wanda ya diba da hakkina gaskiya ban yafe ba tunda abun haka ne, don kowa sai
da aka dasa masa pamponsa amma don mugunta sai ku wani kwaso shegun bokitan ku
duk datti kuna kwashe min ruwa mugayen yara" Ita dai tana tsaye wannan
karan ta daure fuska sai kallon ta take, A fusace inna tace "Baxa ki je ki
juye min a bandaki ba ko sai nasa an kira min Bukar ya taho duk inda yake
yanxu?" Daukan ruwan Budurwar tayi fuuuu ta wuce ciki, inna ta shiga
parlor ta dauko wani karamin kwado ta kulle tap din ta wuce cikin parlor tana
cewa "Gwara in ta tsayawa ba ruwan nima da a xo ana ta debe min a cuce
ni" Tana shiga parlor ta kalli matashin dake xaune kan kujera yana danna
wayarsa, ta hade rai ta dau kyallen da take goge goge ta ta fi gun kayan kallo
ta ci gaba da gogenta tana cewa "Ka sake dawowa karasa sauran fitsarar da
ka mance baka yi ba kenan, wato duk wanda kayi jiya bai isheka ba, to ni dai a
fita a bar min parlor ba ruwana, ba katon banxan da zan kula yau ta kaina nake,
kaje can kayi ma uwar ka" shi dai bai tanka ta ba sai danna wayarsa yake,
Bayan wani lkci ya mike yace "Dama Abba ne yace in xo in baki hakuri"
daga haka ya nufi kofa fuska daure, da karfi Inna tace "Imaan tunda
mutumin nan ya shigo kinji ya ce min wani abu?? To ni dai ba ni ka ba hakuri ba
wllh, idan kuma ba ka yi hankali ba sae in iya fitar har ofis in sami Ahmadu
ynxu" Imaan ta rufe babban roban da ta jawo daga karkashin gado tana kokarin
daure alkakin da ta cika a leda jin inna ta sake kiranta tace "Gani nan
xuwa" window ta bude a hankali ta jefar da ledan ta shiga bayi ta wanke
hannunta da sauri ta fito ta shiga parlor fuska daure tace "Meye kike
kirana" Inna na nuna sa tace "Ke tunda kika shigo kin ji muryar bawan
Allahn can?" Imaan ta tabe baki tace "Wai wa?" Inna tace
"Mujaheed" Imaan tace "To ni na sani? Ni da nake cikin
daki" daga haka ta bi ta gefensa ta fice a parlon, sauran kayan wankinta
ta dauka ta xaga baya da sauri ta dau ledan alkakinta ta wuce part dinsu, a
hankali ta bude kofar parlon tana lekan ciki ganin Ammi bata ciki ta wuce
bedroom din ta da gudu ta kulle ta ajiye buckets din a bayi. Da yamma Ammi ta
shigo dakin ta sameta kwance tana bacci, Ammi tace "Imaan" bude ido
tayi a hankali, Ammi tace "Ki tashi daga baccin nan haka, yamma yayi, kin
kwaso socks din naki da kika wanke" tana murxa ido tace "Xan
kwaso" Ammi tace "Ga hijabs din ki da na wanke can clothe line din su
Anty ki tafi ki kwaso su ma sun bushe, don kawai yan gidan basa nan sai ki k'i
tafiya makaranta ko?" Ita dai bata ce komai ba, Ammi ta juya ta fita, xaro
ido imaan tayi ta mike da sauri ta shiga bathroom din ta ta matse socks din da
hula da inner wears ta xuba su a dryer na washing machine ta kunna sannan ta
fita, Tana kwashe hijabs din ta a clothe line da Ammi ta ce mai gadi ya bude
gate, wani rantsatsen mota ya shigo gidan direct parking space dake babban part
din ya taho, sai ga wata motar ta biyo bayansa xuwa parking space din, Mutumin
daxu da safe ne ya fito driver seat sanye da kananun kaya daga cikin motar
farko, wata yarinya da baxata wuce Imaan ba ta fito front seat din motar,
sannan wata mata da baxata haura hamsin da hudu ba ta fito back seat tare da
wata yarinya mai shekara ashirin, kana ganinsu kaga yan daki daya, Imaan ta
dauke kai tana ci gaba da abinda take, Bude dayar motar aka yi, wani mai kama
da Mujaheed Sak ya fito sai dai shi ya fi sa haske, Shima dogo ne kuma Mujaheed
ya girme sa da 4 years, mahaifiyarsa ce ta fito bayan motar da kanninsa duk mata
hudu su ma, murmushi mahaifiyar tasa tayi ganin Imaan tace "A'ah wanki aka
yi yan mata" Imaan tayi murmushi tana boye fuskarta tace "Sannu da
dawowa Anty" Anty tace "Sannu Imaan, ya Ammi fa" Imaan tace
"Tana gida" Kallon matashin da ke tsaye kusa da Anty yana kallon ta
tayi tace "Ina yini ya Yusuf" yace "Lafiya lau, Imaan din daddy,
sai dai nasan ba ke kika yi wankin nan ba" ta xaro ido tace "Ni nayi
fa" Anty ce "Toh shi xai maki idan baki yi ba banda tsokana, share sa
kin ji" tuni Mujaheed ya nufi entrance din shiga part din su mahaifiyarsa
Umma dake satan kallon Imaan da ta ki kallon ta ta bi bayansa, Anty ma ta wuce
Yusuf na biye da ita yana waigo Imaan yace "In ji yau baki je tsokanan
inna ba ta hada ki da daddy" Imaan tayi dariya tace "Ni ina ruwana da
ita ai na daina xuwa part din ta" Daga haka ta juya ta wuce bangarensu. Da
daddare Imaan na kokarin saka kayan baccinta ta kwanta Ammi ta shigo dakin,
tana kallon ta tace "Ki je Abba na kiran ki" xaro ido tayi tace
"Abba kuma Ammi?" Juyawa Ammi tayi ta fita, kamar xata yi kuka ta
saka hijab din ta ta fita tana tunanin kiran me Abba ke mata da daddaren nan. A
hankali ta bude kofar parlon Abba ta shiga bayan ta cire takalmin kafarta, Abba
na xaune a 3 seater cikin parlon Mujaheed na xaune shi ma kan lallausan carpet
din dake malale kasa, sai Umma dake xaune kan one seater, Anty ma haka, Imaan
ta karasa kanta a kasa ta xauna kasa kusa da Anty, murya can kasa ta gaida
Abba, Abba ya amsa yace "Ya karatu" tace "Alhmdllh" yace
"Imaan discipline din ki kenan rashin gaida na gaba da ke?" Imaan ta
daga kai tana kallon sa, ya daure fuska yace "Ita Hajiya sa'ar ki ce da ba
kya gaisheta a gidan nan?" Shiru tayi bata ce komai ba, ya hade rai yace
"I am talking to Imaan, kuma ki bar kallona my friend" A hankali ta
fara 6ata fuska tana jan yatsunta, lkci daya ta fashe da kuka, Abba ya mata
tsawa yace "Daman kuka kika samu don ban xane ki ba yanxu" kuka take
yi sosai kamar warce aka duka, Mujaheed ya mike ya mata wani raxanannen tsawa
ta mike da gudu ta nufi kofa, xai bi ta Abba ya dakatar da shi yace "Rabu
da ita M.A, Allah ya shiryeta" Umma ta tabe baki tace "yaran yanxu da
ba a sangarta su ba ma ya aka kare ballantana wannan?" Anty ta mike ta
fita parlon, Abba dai bai ce komai ba, imaan bata xarce ko ina ba sai sashin
inna, tana shiga parlon ta xube kan kujera ta rushe da kuka, inna ta fito daki
da sauri, Yusuf ma dake kwance kan 3 seater ya mike xaune da mamaki yace
"Me ya faru Imaan" jikin inna na rawa tace "Me ya samu
Aishar?" Imaan ta ki cewa komai sai kuka, tuni inna ta nufi kofa, cikin
kuka Imaan tace "Ni ba abinda ya samu Ammina" inna ta dawo tace
"Ke dai ki dinga jin tsoron Allah, da yanxu xuciyata ta buga ya kike son
'ya yana su yi, ya zaki shigo da kuka ki janyo min wata fitinar ina xaune"
Cikin rawar murya tace "Ko ba Umma bace" inna tace "Wacece
haka?" Imaan bata ce komai ba sai kuka, Inna tace "Warcan mata mai
kama da zabiya kike nufi wai, ko ba uwarsu fitsararren yaron nan Mujaheed
ba?" Imaan ta hadiye abu da kyar tace "Ita" Inna ta share wani
xufa tace "Toh xata ga barbadin rashin mutunci yau kuwa, me ta maki?"
A hankali Imaan tace "Shine taje ta gaya ma Abba wai ni bana gaisheta
alhalin fa ko na gaisheta bata amsawa, shine Abba ya kirani...." Sai kawai
ta fashe da kuka, inna tayi wani murmushi tana gyada kai tace "Biri yyi
shige da mutum, Sai aka yi ya da ya kira ki" imaan ta kalleta cikin
shesshekar kuka tace "Yana min fada....." Tuni Inna ta fice parlon,
Imaan ta saci kallon Yusuf da yyi tagumi yana kallon ta ta mike tana turo baki
ta fita. Inna na isa bangarensu Yusuf kai tsaye parlon Abba ta wuce, har sannan
Abba na xaune da Umma a parlon sae Mujaheed, gaba daya daga kai suka yi suna
kallon ta, inna ta tsaya tsakiyar parlon tana kallon Abba tace "Yanxu yaro
tun da sauran numfashin Bukar a duniya zaka sa ma 'yar sa ido? Yanxu a kan
wannan matar zaka ci mutuncin yarinyar da lafiya ma bai isheta ba sai dai
godiyar Allah? Yanxu Ahmadu duk son da d'an uwanka ke maka xaka rufe ido a hadu
da kai a ci mutuncin yar sa kwaya daya tal..." Kunce ha6ar xaninta tayi
tana matsar kwalla tace "Naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba..."
Abba kasa cewa komai yyi da farko, can yace "Haba inna, wannan wace irin
magana kike...." A fusace tace "Ohh yare nake maka da xaka tambayeni
wani irin magana nake, to wllh bari ka ji, a kan Fatima a gidan nan ina iya
sa6a ma ko wani mahaluki, kuma baxata gaida matar taka ba, ita katuwar gaida
mutane take?" Mikewa Mujaheed yyi ya nufi kofa kamar xai tashi sama inna
ta bi sa da wani shegen kallo, sannan ta ja tsaki ta maida dubanta kan Abba
dake ta kallonta ta daure fuska tace "Ahmadu yaushe rabon ita matar taka
ta kai kafafuwanta bangarena gaisheni? Lallai... ni a su wa xata je gaidawa? Ni
din banxa xata gaidar?? To hirrrr wllh, kada wanda ya kara sa ma jikata baki a
gidan nan idan ba haka ba sai in sa Bukar ya koma daya gidansa dama shi ya nace
xama waje daya da kai, tunda yar sa xa a takura gwara kawai ya bar gidan...Dubi
fa Mujaheed haushi ya ji yanxu don na ambaci uwarsa, kana gani saura kiris ya
bangaje ni in fadi duk cikin bacin rai, to uwa ta fi uwa ne?? don me kai ma
baxa ka tattala ni haka ba, duk ka bi ka daure mata kugu bata gani na da gashi
a gidan nan, to mu xuba da ita xan ga ko ita ta haifo min kai duniyar, wannan
ai raini ne wllh, wai taji haushi Imaan bata gaisheta ba to baxata gaidata din
ba, kar ta kuskura ta sake sa min jika a baki tayi ta kanta kawai a gidan
nan" shi dai Abba shiru yyi kansa a kasa, Umma ta rungume hannunta daga
xaune tana kallon wani direction din, Abba ya dago yana duban mahaifiyar tasa
yace "Kiyi hakuri Inna" ta maka masa wani kallo tace "Sai dai ka
ba matar ka hakuri tunda na 6ata mata rai" Tana kai wa nan ta fice. Imaan
har ta kusa part dinsu taga shukanta na wake da tayi a babban gwangwani a
madadin assignment da aka basu a Agricultural science, a yashe duk root din ya
fita daga cikin gwangwanin, ta xaro ido ta ta fi wajen da sauri, lkci daya
hawaye ya kawo idonta tace "Wllh nasan Rahma ce xata kwabar min da shuka
na" sai kuma ta fashe da kuka na takaici ta durkushe wajen, ba ta lura ba
har Mujaheed ya iso wajen, ta juya hawaye sha6e sha6e idonta tana kallon sa ta
sake rushewa da kuka, ya daure fuska yana kallon kafarta yace "Me ya
faru?" Ta mike cikin rawar murya tace "Yaya kalli fa abinda Rahma
tayi ma assignment dina kuma ten marks ne, xa muyi submitting ranan Friday,
kalli fa har ya girma, don nawa duk yafi nasu sai ta kwabar min" ganin sai
hararanta yake ta juya ta wuce tana ci gaba da kuka, fixgota yyi yana mata wani
kallo yace "Shi Abban kika tafi kika yi reporting gun Inna?" Lkci
daya ta tsaida kukan da take bayan ta gane biyota yyi, ta fizge hannunta ta
kwasa a guje, kiris ya rage ya kamata ta shige parlonsu ta banko kofar tasa
key, Ammi dake xaune parlon tana kallo ta mike tace "Meye haka
Imaan?" Dariya ta fashe da ta wuce daki da sauri tace "Sauri nake in
xo in kwanta fa Ammi" tana shiga bedroom din ta ta sa makulli. Har Imaan
ta fara bacci wajajen karfe goma Ammi ta bude kofar dakinta, bude ido tayi Ammi
ta hade rai tace "Uban me kika debo ma inna a dakinta?" Ta mike xaune
da sauri tace "Na debo mata abu kuma? Haka ta ce?" Ammi tace
"Kinga na raba ki da xuwa sashinta ki dauko min magana ba ki ji ko? To ki
fito mata da duk ma abinda kika daukan mata gata can bakin kofa" Imaan ta
turo baki ta sauko daga saman gadon ta bi bayan Ammi da ta fita, ido hudu suka
yi da inna da ke tsaye bakin kofa ta tsuke fuska, Imaan ta hade rai tace
"Ni me na dibar maki xaki biyo ni cikin daren nan" Inna tace
"Duk cikin jikokina babu mai ta6a min kaya ban basa ba sai ke, duk kece
mai mugun halin nan don haka maxa ki fito min da alkaki na, don ba a rame na
bar sa ba ina sane da abinda nake ba fara haukacewa nayi ba" Ammi dai ta
nemi waje ta xauna, Imaan ta 6ata fuska kamar zata yi kuka tace "Wai
yaushe naje da har xan dibar maki kayan ki ni da ba ci ma nake sosai ba, to ma
ba xaki gansa hannuna da xan fita ba" Wani tsawa Ammi ta yi mata tace
"Kin tafi kin dauko abinda kika diba ko sai na mare ki" Imaan ta
harari inna ta wuce kitchen sai ga ta ta fito da ledan alkakin, Inna ta saki
baki ta warce ledan tace "Naga Ikon Allah ni Asabe, da yake Aisha ce ta
xauna ta min tuyar bayan ta kwa6a dole ki kwaso ki kawo maku ku ci, to ni kar
in sake ganin kafafuwanki a bangarena don halin ki abun tsoro ne, wannan ai ba
tarbiya aka maki ba ki shiga har karkashin gadon mutane ki jawo kwalla ki debe
min kayana, yanxu banda jinin ka jininka ne kin xata idan na ja Allah ya isa
baxai bi ki ba, ni wllh darajar d'a na kike ci a gidan nan gaskiya, kar in sake
ganin ki a parlona ni dai dama baki tsinanamin komai sai dai ki malale kan
kujera kina mik'a, duk kin ru6ar min da kujeru" tana kai wa nan ta juya ta
wuce, Imaan bata yarda ta kalli Ammi ba ta wuce daki ta rufe kofa tayi
kwanciyarta tana turo baki.
Maa sha Allah, I am back by Allah's grace... daily update in sha Allah, but if schl shud resume anytime soon xan dakata da posting for some weeks coz I will be having exams in sha Allah. Hope you guys will love the *book*, though I know I never disappoint my fans when it comes to writing in sha Allah....
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
2......
Washegari da safe Imaan
ta fito parlor shirye cikin well ironed uniform dinta da beret dake kanta,
kitchen ta shiga gun Ammi, Ammi dake juye ruwan shayi flask tace "Yau ma
baki yi combing gashin ba koh" ta jingina da kofa cike da shagwaba tace "Wllh
Ammi xafi, baxan iya ba" Ammi bata ce komai ba ta gama xuba ruwan a flask
ta xuba mata nata a cup dinta ta hada mata shayin sannan ta mika mata, Karba
Imaan tayi ta fita xuwa dinning, Ammi ta kai mata dankali da kwan da ta soya
mata ta ajiye tana kallon agogo tace "Kiyi sauri kar su jira ki don
Allah" Imaan ta xaro ido tace "Ammi kullum fa ni ke jiransu"
Ammi tace "Toh kar kiyi saurin" daga haka ta wuce kitchen don yin
wanke wanke, imaan na gamawa ta kai plate din da cup kitchen, ta dauko jakarta,
Ammi tace "Ki duba gaban dressing mirror a daki na akwai duba daya ki
dauka, dakin ta shiga ta dauko sannan ta fito tace " Ammi sai na
dawo" Ammi tace "Ohk Allah ya tsare kiyi addu'a kafin ki fita, and
you make sure baki mance ko wani book ba tunda hankali bai ishe ki ba"
dariya kawai tayi ta fita gidan bayan tayi addu'a, Can parking space din su
Yusuf ta tafi ta tsaya don nan take jiransu, yawanci Yusuf ke kai su wani lkcin
kuma Anty ta ajiye su tunda tsohon driver dinsu ya tafi, Tana ta tsaye jikin
mota ta hango plant din su Ummi, Rahma da Maimoon don duk ajinsu daya wato ss2,
kamar xata yi kuka ta dinga kallon waken nasu da duk ya fito da ganye, ga nata
can an lalata mata, kallon entrance din gidan tayi lkci daya ta nufi wajen da
plant din suke da kafa ta haure gaba daya biyun banda na maimoon don kowa ya sa
sunansa, sai da ta tabbatar roots din sun fita sannan ta koma jikin mota da
sauri, Ummi ce ta fara fito sanye cikin uniform irin na jikin Imaan sannan
Rahma sai Maimoon, Babu wanda ya kalleta cikin su banda Maimoon da tace
"Imaan kin gama maths assignment din ki" Imaan tace "Ehh na
gama" Maimoon tace "Toh idan mun shiga mota xan kwafa plss ban yi
ba" Imaan tace "Ohk" Mujaheed ne ya fito rike da makullin mota
fuska kamar hadari, Imaan ta xaro ido tana kallon Maimoon murya can kasa tace
"Shi xai kai mu?" Maimoon tace "Ehh ya Yusuf baya nan ya tafi
Zaria daxu, shine Anty tace ya Mujaheed ya ajiye mu, shine yake fushi"
Imaan ta turo baki bata ce komai ba yana bude motar ta shiga back seat tare da
Maimoon da Rahma, Ummi ta shiga gaba, har suka bar gidan babu wanda yace komai
cikin su, Imaan ta bude jakarta ta ciro assignment din ta ba Maimoon, tafiyar
minti ashirin ke kai su makarantar su, amma saboda gudun da yyi cikin few
minutes suka iso, yyi parking dai dai makarantar yana kallonsu da kyau yace
"Dama kuna tashi ku fara trekking din dawowa gida don baxan xo daukan kowa
ba" a hankali Ummi tace "Ya M.A ai soon Abba xai dau mana wani driver
fa" yace "Sauka malama" bude motar tayi ta fita, tuni Imaan da
Maimoon ma suka fita suka shige cikin makarantar. Anty ce ta xo daukan su bayan
sun tashi ranan, Anty na kallon Imaan dake ta yamutse fuska tace "Me ya
faru Imaan" a hankali ta nuna mata kanta, Anty tace "Toh idan kin
koma gida kin ci abinci sai ki sha magani ki kwanta ki huta" to kawai
imaan tace, ko da suka isa gida har bacci ya dauketa Maimoon ta tasheta ta bude
ido, Anty tace "Toh shiga gida imaan" kai kawai ta gyada mata ta fita
ta nufi part dinsu tana dingishi. Ruwan xafi Ammi ta hada mata ta shiga tayi
wanka sannan ta ci abinci, Ammi ta bata magani tace "Sai ki daure kiyi
shirin tafiya islamiyya it's too early ki fara fashi this week, today is
Monday" Imaan bata ce komai ba, Ammi na fita ta koma kan gado ta kwanta
kamar xata yi kuka, hudu da minti biyar Ammi ta shigo dakin jin shiru bata fito
ba, ganin har bacci ya dauketa ta kai hannu jikinta taji da dumi, girgixa kai
tayi ta juya ta fita, Maimoon ne ta shigo parlorn sanye da uniform din
islamiyya, Ta gaida Ammi sannan tace "Ammi imaan muke jira" Ammi tace
"Bata jin dadi ku tafi Maimoon" a hankali Maimoon tace "Allah ya
sauwake" sannan ta fita, Ammi na girkin dinner a kitchen wajen karfe biyar
Imaan ta fito daki, wani internal heat kawai ta ke ji, kuma tana kunna Ac tasan
sauran ta dinga lekan kitchen kamar xata yi kuka, a hankali ta nufi kofar fita
ta bude kofar yanda baxa aji kara ba sannan ta fice xuwa part din inna don ta
je ta kunna Ac, Inna na wanke gun tap dinta da take sa ma kwado ta daga kai
tana kallon Imaan tace "Baki tafi islamiyyar bane yau" Imaan ta turo
baki tace "Ehh" daga haka ta shige parlon, kunna Ac tayi ta kwanta
kan kujera dake kallon Ac din ta lumshe ido, inna na gun tap din har sannan sai
ga Mujaheed, ta mike tana kallon sa tace "Baka ji bayana ba Mujaheed kamar
xai balle, ko kai baka ga yanda wajen pampon yayi haske ba tun daxu nake ta
gurza gashi sai kyalli yake, ai kazanta bata da kyau, yanxu kaga ko tuwo aka
xuba a wajen mutum xai iya xaunawa ya ci" Mujaheed dai bai tanka ta ba ya
shige parlorn bin bayansa tayi, ya ajiye ledan hannunsa yace "Gashi Abba
yace a kawo maki" tace "Toh Allah yayi masa albarka... Dama raina na
son kayan marmarin" xai fita Inna tace "Mujaheed kaga yarinya nan
abinda ya kawota kenan ta xo ta kunna Ac wata cutar ta kamata ace ai a parlorn
inna ne, to ni dai ba ruwana ka kashe min kayana taje can ai su ma suna da shi,
duk yanda aka yi kuma uwar hanata kunnawa tayi shine ta taho ta kunna nawa
salon ace parlorn inna to Allah ya fi ki babu me sa ni a bakin duniya"
Mujaheed ya kalli Imaan da tayi rub da ciki kan 3 seater din ya tabe baki xai
fita Inna tace "kai ya ina maka magana xaka fita, idan uwar ka Rukayya ce
xaka mata haka Mujaheed?" Fuska daure ya juyo ya xauna yana kallon ta da
kyau yace "Wllh idan kina sa mahaifiyata a baki Hajiya xa mu kwashi yan
kallo dake a gidan nan, komai sai kice uwata" Inna ta saki baki tace
"Kai ni kake daga ma murya" yace "Toh ki daina sako mahaifiyata
a xancen ki idan baki son a daga maki murya, ke kwata kwata rayuwarki baki son
xaman lafiya daga kice wannan yayi maki sai ki ce wannan yayi maki...." Inna
ta gyada kai tace "To ka tara kuma ka samu, xaka san ni ka fada ma bakar
magana" Tana fadin haka ta kashe Ac dinta, Imaan ta mike xaune kamar xata
yi kuka tace "Meye xa ki kashe min inna" Inna tace "Bukar yasa
na kashe, na ku lalacewa yayi xaki taho min nan, ni dai a daina xuwa ana sa ni
magana ana min rashin kunya gaskiya" imaan ta marairaice tace "Don
Allah inna ki kunna xafi nake ji a cikin jikina" Inna tace "Toh baxa
ki ji xafi a jikin ki ba ga magani nan an kawo maki tun daga Nijar kin ki amsa
sai yawo kike min da hankali kamar ni xai amfana, duk tashi fadin da nake a
kanki ba ki gani, mutum bai san inda xai dace ba, idan an baki magani sai kiyi
biyayya ki amsa ki sha sai kiga Allah ya yaye maki wannan ciwace ciwacen da ba
a san kansa ba" Imaan tace "Wa yace maki ba a san kansa ba, to ai da
shi aka haifeni kuma ba warkewa...." Inna tace "Oh oh Allah, Mujaheed
kaji irin fitinar da take ja ma kanta da bakinta ko, kai wannan 'ya ta Bukar
anyi doluwa wllh, ke fata kike kar ki warke d'a na yayi ta cacan kudi, duk
cikin jikokina babu mara tunani dama irin ki" Imaan ta hade rai tace
"Ehh na ji, ki kyaleni da ciwo na Babu ruwanki, baxan kuma sha maganin ba
don ina da na asibiti da nake sha, ni bance ki dinga amso min magani ba dama
ai" inna tace "Kada Allah ya sa ki sha, to ni Allah na tuba a haka ma
wa xai yi sha'awar aurem ki yau ciwo gobe lafiya duk tattalin arxikinsa ya kare
a asibiti, tun kina mitsitsiyar ki nake wahala da ke kan maganan magani shi sa
ma kika yi kyan gani, ke da kike kamar kwarangwal da taimakon Allah da taimkona
da magungunan da nake amsar maki gun malamai shine kika marmaro, in dan ta uwar
nan taki ce ai sai dai ki mutu tana kunshe daki ba fita xata yi ta nemo maki
magani ba tana jiran na asibiti, Toh wllh daga yau na fita harkan ku ki ji da
ciwon ki nima inyi ta kai na" Imaan ta fashe da kuka tace "Ehh naji,
ki kyaleni tunda ba dole bane shan maganin ki" daga haka ta fice daga
parlorn da gudu, Inna tace "Duk xa ku yi bayani bari iyayen naku su
dawo" Mujaheed ya tabe baki ya mike ya fice mata a parlorn shi ma. Imaan
na kwance kan kujera bayan isha Ummi ta bude kofar parlorn tana tsaye daga
bakin kofa tace "Abba na kiran ki a bangaren Inna Imaan" daga haka ta
fita, Ammi dake cin abinci xaune parlorn ta kalli Imaan da ta wani juya bata
dai ce komai ba, bayan kusan minti biyar Ammi tace "Amma dai kin ji abinda
tace Imaan" Ta juyo kamar xata yi kuka tace "Wllh Ammi kafana ciwo
yake min ban san ko xan iya tashi ba" Ammi ta galla mata wani harara tace
"Sai ki rarrafa ai tunda baxa ki iya tashi ba" hawaye cike idonta ta
mike ta sa Hijab ta fita tana taka kafar da kyar. A hankali ta bude kofar
parlorn Inna ta shiga da sallama, Abba ne xaune parlorn sai Inna da Anty, Imaan
ta sunkuyar da kanta ta karasa kusa da Anty ta xauna kanta a kasa ta gaida su,
Abba da Anty kadai suka amsa, inna ta wani tsuke fuska, Imaan dai bata ko
kalleta ba, Inna tace "Wato shi Mujaheed din jira yake kaje ka ciccibo sa
da kanka koh?" Abba ya kalli Imaan yace "Tashi ki tafi can bangaren
ki kira min Yayanku" Imaan ta mike ta d'an harari inna ta gefen ido ta
fice a parlorn, tana isa part din su Mujaheed ganin bbu kowa parlor sama ta
haura ta tsaya corridor tana kallon door din dakinsa har ta mance rabon da ta
je kusa da kofar, bude kofar Umma aka yi sai ga shi ya fito, ta matsa da sauri
don kusa da kofar dama take tsaye tace "Abba yace in kira ka" ko
kallon ta bai yi ba ya fara sauka stairs, ta murguda masa baki ta bi bayansa,
har suka isa part din Inna bai juya ba, ya bude kofar ya shiga da sallama, kusa
da Anty Mujaheed ya durkusa kansa a kasa, Abba sai kallon sa yake yana girgixa
kafa, Imaan ta shigo parlorn ganin inda ya durkusa tace "Waje na ne
nan" Murmushi Anty tayi, shi kam ko kallon ta bai yi ba balle ya motsa,
Inna tace "Ahmadu na fa gaji da xama nan kamar warce xa a ma gafara, aji
da ni in tashi in shiga ciki in kwanta" Abba ya kalli imaan yace
"Samu wani wajen my friend" ta harari Mujaheed ta koma wani wajen ta
xauna, Abba na kallon Mujaheed yace "Muhammad ita innar ka mayar abar
wasar ka a gidan nan?" Inna ta tabe baki tana jijjiga kafa, Mujaheed bai
dago ba kuma bai ce komai ba, Abba yace "Am I not talking to
Mujaheed" ya dago a hankali yace "Abba kayi hakuri don Allah"
Abba yace "Stupid, ni ma kake ba hakuri?" Ya kalli inna yace "Kiyi
hakuri inna" dakatar da shi tace "A'a malam a gaban ubanka xaka ce
min inna kenan, wllh Ahmadu daxu yana nuna ni da yatsa a can bakin kofar kamar
xai make ni Hajiya yace min, ni na ma xata duka xai kai min bayan ya gama
kashedin, to gaskiya da sake, sam yaranka basu da d'a'a basu da kunya Ahmadu,
isuhu ne kadai dama mai gudun bacin raina duk da shi ma ko aiki xai kashe ni
baya taimakona, to ynxu Mujaheed da wani ne da ya xo ya gan ni durkushe ina
faman gurje gun pampo ba amsa xai yi ba ya taya ni, to wllh bai amsa ba sai
xagina ma ni da yayi daga karshe, a xo har sashina a dinga ci min mutunci, to
hirrr don duk ranan da aka isheni tattara kayana xan yi in bar gidan nan kuma
sai anyi shekara duba ana nemana" Mujaheed ya d'an daga kai ya kalleta ta
gefen ido ya maida kansa kasa, Abba dai bai iya yace komai ba, Anty tace
"Kiyi hakuri inna, a yafe masu" Inna tayi kasa da murya tace
"Wllh Amina daga nace kai kuwa Mujaheed haka kake ma Mamarka a gida ina ma
magana xaka wuce, kuma fa cikin lallami nayi tambayar kawai ba sai ya sakar min
aradu a kai ba, ita kuma wancan lankwasasshiyar mai kama da yar tsana bbu
abinda ta mance bata gaya min ba daga nace Imaan ga maganin da na amso maki
saboda ciwon ki da ba a san kansa ba ba a san dalilinsa ba, wllh Ahmadu sae
kaga wanke ni da yarinyar tayi tasss har da ce min ba ruwana da ciwonta kuma
ciwon ba me warkewa bane" Imaan ta fashe da kuka har da shessheka, Abba
yyi mata tsawa cikin rawar murya tace "Abba xagina fa ta ke yi
wai...." Abba ya dakatar da ita yace "Keep shut" ta hadiye
abinda xata ce tana hawaye, Mujaheed yace "Kiyi hakuri Inna" Inna
tace "Atoh ya xan yi idan ban hakura ba, dama wanda aka cuta ake ba
hakuri, amma daga kai har ita kar in sake ganin kafufuwanku a bangarena, tunda
kun raina ni, Isuhu da Maimuna sun ishe ni" Fada sosai Abba ya dinga ma
Mujaheed da kansa ke kasa, inna sai matsar kwalla take ita a dole an 6ata mata
rai, hakuri Mujaheed ya kara bata, Anty ta sa Imaan ma ta bata hakuri, mikewa
Imaan tayi da sauri ta fice parlorn tana kuka, Inna tace "Sai ubansa na
magana yayi ta sinne kai kamar na kirki alhalin crooo kenan ku ke gani, kar ka
sake xuwa min sashi ni dai na gama magana" Mujaheed bai kalleta ba balle
ya tanka ta ya mike ya fice parlorn, can kusa da wani flower ya ga Imaan
durkushe tana kuka, ya dinga hararanta har ya isa wajen da take, ta mike cikin
rawar murya tace "Yaya don Allah kai kaji na xage ta daxu?" Ba tare
da ya tsaya ba yana ci gaba da tafiya yace "Ke ma ai ba dukan ki naga aka
yi ba" Ta bi shi da kallo tana shessheka.
Post a Comment for "IMAAN 1-2"