IMAAN 5-6
_By khaleesat Haiydar_✍🏻
5.....
Gaba daya Mujaheed ya daburce ya rasa abin cewa, Abba yace "Ko in kai ta asibitin kawai" da sauri yace "Noo Abba, naga bani da kayan aiki a gida ne, sai dai in kai ta asibitin in duba ta a can" Abba yace "Toh hakan na da kyau" Magana yake amma gaba daya rabin attention dinsa na kan window din dakin Umma duk da baya hango komai, amma fatansa yanxu ace bata tashi bacci ba duk da yasan da wuya, Ya sunkuyar da kansa yace "Toh xan dauko makullin mota a ciki" Daddy ya mika masa nasa makullin motar yace "You use my car, duk yanda ake ciki you let me know" Mujaheed ya risina ya amsa makullin motar yace "Toh Abba" daddy yayi ma yayan nasa sallama ya wuce ba tare da ya kalli imaan da ta cika saura kiris ta
fashe ba, bayan ya tafi Abba ya kalleta yace "Sannu Mamana" Ganin hawaye idonta yace "Baki son bin Muhammad din kenan?" Da sauri ta gyada masa kai hawayen na sakkowa idonta, yace "Kuma baki son daddyn naki ya huta koh, am sure kila xuwa anjima ko gobe xai koma bakin aiki, shi Mujaheed din ba yayanki bane?" Ta fashe da kuka tace "Abba ihu xai ta min a hanya fa" Abba yyi murmushi mai sauti sai dai bai ce komai ba, Mujaheed dai sai kallonta yake ta gefen ido, Back seat Abba ya bude mata yace "Shiga" a hankali ta shiga ta jinginar da kanta jikin motar, Abba na kallon Mujaheed yace "You take very good care of her, ko kallon banxa ban yarda kayi mata ba" Ya sauke idonsa yace "Toh Abba" Abba ya daga mata hannu ta mayar masa tana goge idonta, ya juya ya wuce ciki, Mujaheed ya gama warming motar yayi horn ana bude masa gate ya fita gidan, sai da suka hau saman titi yace "Saboda baki son xuwa schl shine kika fake da ciwon karya salon ki ba mutane wahala koh?" Jin bata ce komai ba ya kalleta ta madubin motar, murguda masa baki take, suna hada ido ta turo bakin kamar xata yi kuka sai dai bata ce komai ba, ya gyada kai yace "Xaki gwammace schl kika yi tafiyar ki yau" ta fashe da kuka tace "Dama dai Abba yace duk abinda ka min in gaya masa" Bai tanka ta ba har suka iso asibitin da yake aiki, yana gama parking ya bude motar ya fita ita ma ta fita, ya rufe motarsa ya dau hanyar entrance din shiga hospital din, a sauri ta bi bayansa, tsaye ta gansa reception suna gaisawa da nurses dake wajen da fara'a, Wata nurse tace "Doctor I heard an sake transferring dinka xuwa nan, kuma shiru ba mu ganka ba" Yace "Sure da yau xan yi resuming, but due to some reasons sai Wednesday in sha Allah" duk nurses din suka amsa masa da Allah ya kai mu, juyawa yyi yaga Imaan ta nemi kujera tayi xamanta, wata nurse tace "Dr sister dinka ce?" Yace "Sure bata da lafiya ne" daga haka ya wuce sama, duk sai da ya shiga office din doctors dake duty safiyar, Dr Mukhtar na ganinsa ya mike yace "Kaga mara kirki dama yau xaka yi resuming shine babu sanarwa" Mujaheed ya karasa yana murmushi suka gaisa yace "Sai Wednesday in sha Allah, na kawo sister na ne bata da lafiya" Mukhtar yace "Subhanallah Ummi ko Rahma?" Yace "None, cousin dita ce wannan" Dr Mukhtar ya koma ya xauna yace "Ohk tana ina" Yace "Tana reception" Dr Mukhtar ya buga waya downstairs ba a dau lkci ba wata nurse ta shigo office dinsa, gaida Mujaheed tayi da fara'a ya amsa yace "Ya aikin Zainab" tace "Alhmdllh Dr" Dr Mukhtar yace "Ki taho da patient dake reception" tace "Wanne they are almost 7 patients downstairs" Mujaheed yace "Imaan sunanta" tace "Ohk" daga haka ta fita, tare suka dawo da Imaan da ta wani yi laushi da kyar take jan kafar, Dr Mukhtar ya nuna mata kujeran dake kallon wanda Mujaheed ya xauna, ta xauna xata kwantar da kanta kan table Mujaheed ya mata wani kallo yace "Tashi" kamar xata yi kuka ta dago kanta, likitan yace "Sannu Imaan, ya kike jin jikinki, like ina ke maki ciwo?" A hankali tace "Jiya da daddare bayana ya dinga min ciwo har da kai na kuma ina jin sanyi, ban ma yi bacci ba" likitan yyi murmushi yace "Yau da safe fa" Ta kallesa murya can kasa tace "Kafafuwana suka fara min ciwo da na tashi, anjima kuma duk jikina ya fara min ciwo" Ya langwabar da kai yace "Ikon Allah, suna maki haka ne?" Kai ta gyada masa, yace "Toh kina shan wasu magunguna ne?" Kai ta gyada masa, yace "Kin san sunan su?" Ta gyada masa kai, yace "Can you write them down for me now?" Tace "Sure" farar takarda ya ajiye mata da pen, nan ta rubuta masa gaba daya drugs dinta har da na shafawa ta mika masa takardan ya amsa yana dubawa, bayan few seconds ya daga kai yana kallon Mujaheed dake kallonsa shi ma, kafin yace komai Mujaheed yace "Rubuta mata injections taje ayi mata" Likitan yyi yanda Mujaheed yace, Mujaheed ya amshi takardan yana kallon alluran da ya rubuta mata sannan ya mika ma Imaan da ta kife kanta da table yace "Karba kije nurses su maki alluran" ta dago da sauri tace "Yaya allura kuma, ni doctor na baya min allura magani kawai yake ban" ya jefa mata wani kallo yace "Sai ki jira ya dawo ya ci gaba da baki maganin, nan kam allura xa a maki, get up my friend" a d'an tsawace ya karasa maganan, Ta amsa lkci daya hawaye ya cika idonta ta juya ta fita office din, a hankali Dr Mukhtar yace "Is she a sickled cell patient Mujaheed?" Mujaheed ya girgixa kai yace "Not at all, She is only carrying the trait, a carrier" da mamaki Likitan yace "But it's almost mimicking the disease" Mujaheed ya buda hannu yace "Mu ma haka muka gani" Dr Mukhtar yace "Subhanallah, this is kind of rare, Allah ya bata lafiya" Mujaheed yace "Ameen" Dr Mukhtar yace "Kasan alluran are strong, ta ci abinci kuwa?" Mujaheed ya mike da sauri yace "I don't know, bari in tambayeta, kafin in dawo plss kayi prescribing drugs in addition to hers" daga haka ya fita, injection room ya shiga bayan nurses din sun sanar masa suna ciki xa a mata alluran, tsaye take tana hawaye nurse din ma na tsaye rike da alluran sai kallonta take, tana ganin Mujaheed tace "Yauwa Dr ta ki fa" Mujaheed ya hade rai yace "Are you a baby? Waye kike son ba wahala, xan maida ki gida da ciwon ki ne idan baki yi respecting kan ki ba" ta fashe da kuka bata ce komai ba, Yace "Kin ci abinci?" Cikin rawar murya tace "Na sha shayi kadan amma yunwa nake ji" wani kallo ya dinga mata, can ya kalli nurse din yace "Nurse let me get her something to take plss" nurse din tace "Ba damuwa Dr" daga haka ya fita, nurse din ta nuna mata kujera ta xauna. Rike da malt Mujaheed ya dawo injection room din, ya bude sannan ya mika mata, Kadan ta sha xata ajiye yace "Wa za ki ajiye ma" ta hadiye na bakinta da kyar tace "Xan sha idan an gama min" nurse din tace "Aa ki kara kadan" da kyar Imaan ta kara malt din sannan nurse din tasa ta tashi, ta mike ta fashe da kuka tana kallon Mujaheed tace "Wllh tsoro nake ji xai min xafi" nurse din tace "Baxai maki ba kuwa" Mujaheed yace "Xan fa tafi in bar ki a asibitin nan kina bata min lkci" tace "Don Allah kai ka min plsss" yace "Baxan yi ba, kin tsaya ko inyi tafiyata" da kyar ta isa kusa da nurse din, ta kallesa ta mika masa hannu jikin rawar murya tace "Don Allah ka rike min hannu Yaya" bai san lkcn da yyi murmushi ba ya karasa inda suke, ta kama hannunsa ta runtse ido, nurse din tace "Me yasa baki sa under skirt ba?" Ta turo baki tace "Ni bana so" nurse din tayi murmushi, ta daga mata abayar jikinta, rungume Mujaheed tayi ta kwantar da kanta kirjinsa, cikin rawar murya tace "Wayyo Yaya don Allah kace ta min a hankali, kar ta min da xafi" Mujaheed ya amshi alluran hannun nurse din yayi mata, xaro ido tayi tana cewa "Yaya ta sa alluran? Don Allah tayi a hankali, tuni ya amshi dayan alluran yyi mata shi ma, sae da ya cire syringe din ta sakar masu ihu duk tunaninta lkcn xa ayi alluran, ya turata daga jikinsa, ta dinga xaro ido, nurse din tayi dariya tace "Toh ba gashi har an gama ba" Imaan ta zaro ido tace "Da gaske? To ban ji sanda aka cire ba" Mujaheed dai ko kallonta bai yi ba yyi disposing syringe din ya nufi kofa, nurse din tace "Ki fa danna wajen sosai idan kun koma gida" Imaan ta gyada mata kai tana goge idonta har sannan tana mamakin wai har an mata allura don bata ji zafin da take ta jira ba, ta dau sauran malt dinta ta fita, xaunawa tayi reception ganin bata gansa ba, bayan kusan minti goma sai gashi ya sakko, yana kallonta ya nufi kofa, da kyar ta mike tace "Yaya na fara jin jiri" yace "Toh ko in bar ki a nan" da sauri ta girgixa masa kai ta isa gunsa, saura kadan ta fadi gun fita, ya kalleta sau daya yyi gaba, back seat ta shiga ta kwanta tana maida numfashi, ya shiga motar ya tada suka bar asibitin, wani pharmacy ya tsaya xai fita tace "Yaya wllh idona juya min yake" nan ma dai bai tanka ta ba, drugs dinta da sabbin da Dr Mukhtar yyi prescribing ya siya mata sae lucozade boost babba biyu, duk ya ajiye bayan motar, har suka isa gida yyi parking a parking lot din daddy bacci Imaan take, daga cikin motar ya dinga lekan apartment dinsu gabansa na faduwa, ya juya ya kalleta, sannan ya fito daga motar, ya bude back seat yace "kee" bude ido tayi da sauri, yace "Sakko" ba musu ta fito daga motar da kyar, ya dau magungunan da drinks din ya rufe motar, da sauri ya juya ganin kiris ya rage ta fadi ya kara kallon apartment dinsu, kamo hannunta yyi ta jingina jikinsa. Har suka isa bangarensu, ya bude kofar ya shiga parlon hade sallama, Imaan ta kwanta saman kujera ya ajiye drugs din hannunsa da lucozade boost ya kalleta kafin yace komai daddy ya fito parlon, yace "Har kun dawo kenan?" Mujaheed yayi kasa da kai yace "Eh mun dawo Abba" dukawa yyi ya dau ledan maganin ya fiddo gaba daya, ya bude wanda xata sha a lkcn yana kallonta yace "Tashi ki sha magani" Daddy ya tafi kitchen don dauko table water da cup, Mujaheed daure fuska kamar tana ganinsa yace "Baxa ki tashi ba?" A hankali ta bude ido ta mike xaune kamar xata yi kuka, daddy ya iso parlon ya ajiye ruwan da glass cup yace "So how much is the bill doctor" kallonsa Mujaheed yyi, sai kuma yyi murmushi yace "Bill kuma Abba" Daddy yace "Eh ba asibiti ku ka je ba, ga kuma drugs ka siyo" ya girgixa kai yace "A'a Abba, I have settled everything, Allah ya bata lafiya" daddy yace "Toh madalla, Allah ya yi albarka" Mujaheed ya debi ruwan ya mika mata tare da drugs din ta amsa, tana runtse ido ta kai baki sannan ta sha ruwan, mikewa Mujaheed yyi yace "Xan koma daddy Allah ya bata lafiya" Daddy yace "Ameen thanks Son" daga haka ya fita parlon, daddy na kallonta yace "Toh tashi ki shiga ciki ki kwanta" ba musu ta mike ta wuce bedroom dinta. Mujaheed na shiga parlonsu ya kalli mahaifiyarsa dake sakkowa downstairs, kai kana ganin shirin da tayi kasan fita xata yi, Anty dake parlor tana kokarin sa turaren wuta a burner ta kalli Mujaheed tace "Har kun dawo kenan, ya jikin nata?" Gabansa ya fadi sosai, ya hadiye abu da kyar yace "Eh na dawo" Anty tace "Daxu Abban ku ke gaya min ka kai Imaan asibiti, da naga breakfast dinka baka yi ba" kasa cewa komai Mujaheed yyi, ya d'an saci kallon Umma da ta tsaya stairs tana kallonsa baki bude, Anty tace "Ji walakanci ba da Mujaheed nake magana ba" Da kyar yace "Anty ba fa ni na kai ta ba, Abbanta ne ya kai ta" Shiru Anty tayi ganin yanayinsa, can ta saci kallon inda yake kallo, d'an tabe baki tayi ta duka ta ci gaba da abinda take, Umma ta juya ta koma sama, da kyar Mujaheed ya ja kafarsa xuwa dinning, har Anty ta gama abinda take Mujaheed na xaune bai taba komai a dinning table din ba, tace "Idan baka ci ka kai min su kitchen a ba almajirai" ya marairaice yace "Anty da baki yi magana a gaban Hajiya ba" Anty ta maka masa wani kallo tace "tunda uwata ce ita ba" Bai ce komai ba, bayan wani lkci ya mike ya fita parlon ko a mafarki bai ma son haduwarsa da Umma, to me ma xai ce mata ta yadda, part din Inna ya nufa, ya sameta xaune kan tabarma rike da cazbi tana ta xuba gyangyadi, kwanciya yyi kan kujera ya lumshe ido, inna ta yi gyangyadin ta mai isarta sannan ta bude ido, a tsorace ta koma baya ganin sa tace "Meye wannan?" Shi dai bai tanka ta ba bai kuma bude ido ba, tace "Wannan dai ba yi bane ina Lazimi kato ya fado min parlor ba sallama" Ba tare da ya bude ido ba yace "Kina gyangyadi dai" rai bace tace "Ya xaka ce ina gyangyadi ga carbi hannuna, ai asararre ne xai yi gyangyadi a wannan lokacin walha fa na gama ina lazimi ka shigo sadaf sadaf ban sani ba" Mikewa xaune yyi yace "Akwai ruwan shayi?" Tace "Eh akwai wanda uwarka ta kawo min" ya kalleta bai ce komai ba, tace "Can din hanaka ruwan shayin suka yi?" Komawa yyi ya kwanta, tace "Sai dai in sa Aisha ta dafa maka don baxan iya ba, baka ji bayana ba tun safe nake aiki, ko kai baka ga ko ina fess ba, leka dakina ma kaga yanda yake talli" shi dai bai ce mata komai ba, tace "Duk na tattara ma yarinyar nan me shigo min daki ta kwanta ta bar min tsummokaran dankwalayenta idan ta tashi tafiya, suna can baranda na ajiye mata, sai kaga hasken da dakin yyi wllh, ni dai da xata taimaka ta daina shigar min daki don Allah, ni tsoron da nake jiye mata idan tayi aure, ko ina fa ta samu barin kayanta take kamar mahaukaciya, Bukar dai ya haifo abinda ya fi karfinsa" mikewa Mujaheed ya sake yi ya shiga kitchen, ba a dau lkci ba ya fito rike da cup din ruwan xafi yace "Ina kayan shayin?" Makulli ta kunce a habar xaninta ta mika masa tace "Saboda ire iren su Imaan nake adana kayana, ba ruwana" Ya tabe baki ya amshi makullin ya shiga dakinta, closet dinta ya bude yaga gwangwanin madara manya har biyu da milo biyu sai kwalin sugar uku, da kwalin lipton girgixa kai yyi ya sauke madaran da Milo, muryarta yaji a bayansa tace "Da dai ka bari in xuba maka Mujaheed kada ka min barna" Wani kallo ya mata, ya debi cokalin Madara har uku ya xuba, ta bude baki cikin tsawa tace "Kai ubanka ne ya siyo min xaka diba haka, Bukar ne dai mai siyo min kayan shayi, shi Ahmadu sai dai ya jibge min kayan abinci kamar mayunwaciya, kudin nan fa da wahala ake samun su" shi dai bai tanka ta ba har ya gama hada shayin sa ya fita, tayi kwafa ta kwashe kayanta ta maida closet din ta kulle da makullin tana cewa "Ae dai gobe rana ce" Daga haka ta fito parlor. Har kusan azahar Mujaheed na bangaren Inna, har ya gaji da jin muryarta gashi bai taho da earpiece balle ya toshe kunnensa ba. Yana kokarin tashi ya je yyi alwala jin an kira sllh aka bude kofar parlon ya kalli kofar da sauri, Imaan ta shigo parlon rike da warmer, har ta rame ciwon kwana daya sai manyan idanuwa, Inna ta saki baki tace "Wacece wannan kuma?" Imaan bata ko kalleta ba ta ajiye warmer din hannunta, inna ta rike ha6a tace "Ni dai naga abinda ya isheni bai ishi ubangijina ba, yanxu fa sai ace jikinta ne ya tashi, fisabillah dubi yanda yarinya ta zabge ta koma fiyot kamar kyanwa Mujaheed, anya iyayenki na son ki kuwa yar nan, haka xasu xuba ido suyi ta kallonki kina wahala ga magani kasadan na wani malami a Maiduguri ance min babu ciwon da baya warkarwa, dubu hamsin aka ce xa a basa Bukar ya maida ni ban san abinda nake ba kamar shi ya haifeni, ta rasulu kawata xata cuce ni ne ake tunani? ce min fa tayi xata min hanyar samun maganin don can bayan tsauni mutumin yake, kuma babu kalan iskan da bai warkarwa da ciwace ciwacen da ba na Allah da annabi ba irin na yarinyar nan, amma iyayenta sun ba tsinannun turawa karfi sun amince masu dari bisa dari ba saurarana xa su yi ba, dubi don Allah yanda ta fige, lafiya muka rabu jiya amma ga iskan har ya tashi tunda gashi bata je makaranta ba" Mujaheed yace "ina kika ce mai maganin yake" Inna ta gyara xama tayi kasa da murya tace "Wllh a bayan tsauni ta rasulu tace yake, sannan aikinsa yanda kasan yankan wuka, sha ynxu maganin ynxu, duk xata fitsare ciwon da iskan inji ta rasulu" yyi murmushi yace "Ikon Allah, boka ne kenan?" Buda baki tayi tace "Kaji salu6a66e ko, ni dai ka rufa min asiri kar ka ja min kasa Ahmadu ya kafa min sabon babin wa'axi, kai ynxu fata kake inje wajen boka d'an nan" yace "Atoh, mutumin kirki dai baxai je bayan tsauni ya xauna ba" tace "Yo ai ni ce gantalalliya ma da nake xancen nan da kai na mance ashe d'an aiken turawan ne kai ma, Allah wadaran naka ya lalace, ba damuwa ni da ya xame ma dole xanje samo mata magani kuma kada wani shege ya min maganan banxa, Allah kuma ya tsine ma turawan nan dai" Imaan dake tsaye bakin kofa har sannan ta tabe baki tace "Kar ma ki amso ni baxan sha ba, daddy yace min in daina hada na asibiti da gargajiya" a fusace Inna tace "Kya tsufa a gida ina kallonki kina kallona don wllh babu namijin da xai auri ciwo da kudinsa ki karar masa da tattalin arxiki a asibiti, wllh baxan bari a cucesa ba duk sai na xayyane masa lalurorin ki don ni ba yar cin amana bace, ni yar gaskiya ce, ke ce ciwon kafa, kece ciwon baya, ke ce ciwon kai, ke ce ciwon mara, kece sanyin k'ashi, kece xaxxabi, kece ciwon jiki, ga shegen son jiki sannan in rufe masa da cewa duk iska ne da ba a san kansa ba, ba ruwana wllh" murmushi Mujaheed yyi ya mike ya fita don yin alwala, Imaan ta mata wani kallo bata son magana saboda daddy ta juya kawai ta fice mata daga parlonta tana murguda baki.
I am soo grateful for
the birthday wishes from families, friends, fans, and love ones, Allah bar
xumunci ya kara mana shekaru masu albarka.
[6/11, 12:34 PM] +234
703 570 1601: 🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟
_By khaleesat Haiydar_✍🏻
6.....
Hatta islamiyya Imaan
bata iya taje ba ranan banda bacci babu abinda take, xuwa lkcn jikin ya mata
sauki sai dai rashin kwari, Daddy dake parlor a study area dinsa ya kalli Ammi
dake parlon ita ma yace "It's almost six madam baxa ki tada Imaan
ba?" Ta kallesa tace "Kafin magrib xan tasheta" yace "Amma
jikin ba xafi koh?" Tace "Ehh ba xafi but she's weak" yace
"Allah ya bata lafiya" a hankali Ammi tace "Ameen" bayan
wani lkci ta kallesa tace "Am really disturbed with Imaans health
ailment... She have suffered a lot but always claiming strong, and...."
Sai kuma tayi shiru, a hankali ta ci gaba "I don't want to loose her"
Daddy na kallonta yace "Allah plans best, ke dai ki ci gaba da yi mata
addu'a a ko da yaushe wataran sai labari, Allah xai yaye mata" Ammi tace
"In sha Allah" Bayan magrib Ammi na kitchen taji muryar inna a
parlor, fitowa tayi ta gaida ta da ladabi tace "Sannu da xuwa inna"
inna tace "Ina mijin naki?" Ammi tace "Ya fita masallaci"
Inna tace "Daxu Imaan ta xo duk tayi wani fayau fayau da ita, jikin ne ya
matsa mata koh?" Ammi tace "Ehh wllh, amma taji sauki ma yanxu, tana
daki xata yi sllh" Inna tayi kasa da murya tace "Yanxu 'yar nan idan
shi mijin nan naki boko ya gama cutarsa ya ratsa sa ta ko ina ke baxa ki maida
hankali ki tashi tsaye kiyi ta kanki da 'yar ki ba? Fisabillilah meye laifin
maganin gargajiya Aisha, komai sai ace sai asibiti ga na gargajiya
kasadan?" Ammi tace "Gaskiya ne inna" Inna tace "Wllh
malamin a bayan tsauni yake" Ammi ta d'an bude ido tana kallonta, tace
"Ga aikinsa kamar yankar wuka, duk xata fitsare jaraban ta dawo kamar
mutane, amma ni tsoron magana nake Bukar da Ahmadu ba kirki ne da su ba sai su
karee min rashin mutunci suce boka ne alhalin ba boka bane kawai Allah ne yyi
xamansa a bayan tsauni, ta rasulu ta sha xuwa can kuma ana kwana daya da rabi a
hanya kafin a kai, tunda kika ji haka ai kinsan akwai kamshin nasara, tafiyar
kwana daya har da rabi ai kuwa akwai nasara....." Shigowar Daddy ya sa
tayi shiru, daddy ya gaida ta da ladabi ta amsa masa sama sama tana kallon Ammi
tace "Kina ji 'yar nan bari in koma na bar kofa bude kada yaran gidan nan
su min aika aika ga dambun nama ta can daki, dama Mujaheed sai xarya yake min
tun safe, ko shi ya isa ya kwashe, yanxu dai yaushe mijin naki xai koma?"
Ammi tace "Xuwa gobe in sha Allah" Ammi tace "Toh idan ya tafi
ki taho sashina ki same ni mu karasa maganar a can don sirri ne" daga haka
ta nufi kofa daddy na mata sai anjima ko tanka sa bata yi ba. Bangarensu
Mujaheed inna ta nufa tana cewa "Ita kuma Amina bara inje inji ko lafiya
ban ganta yau ba" Mujaheed ne xaune parlor sai Yusuf, Hajiya na dinning
tana jera abinci Rahma na taya ta, gaba daya Mujaheed bai yarda sun hadu ranan
ba sai yanxu da ta riskesa a parlor ta fito kitchen, Inna na kallon Yusuf tace
"Kai ina uwar ka, lafiyarta yau bata xo gaisheni ba" Yusuf yace
"Yanxu da daddaren nan xaki kamo hanyan xuwa nan inna" Hajiya ta
karaso parlon tayi kasa da kai tana daga tsaye tace "An yini lafiya
Inna" Inna tace "Rukayya idan Hadiza ce xa ki gaida ta a tsaye
sandandan haka?" Juyawa Umma tayi ta koma ta ci gaba da abinda take ba
tare da ta bata amsa ba, inna ta kara da cewa "Sannan kiyi min rai ki rufa
min asiri ki daina gaisheni kwata kwata a gidan nan idan kin gan ni, don Allah
bana bukata, wnn ae kanki kike munafurta, kuma Allah ya tsine ma gaisuwar"
Wani kallo Mujaheed ke ma inna fuskarsa daure, inna tayi kwafa tace "Mu
xuba dai, xamu ga mai kwashewa, ae kema ga naki d'an ya isa aure ba don ya
tsaya shashanci ba xaki ji ko da dadi ko babu" mikewa Mujaheed yyi yace
"Ke dai ba dai alkhairi ya kawo ki nan ba sai fitina da complaint, haba
don Allah, gaba daya ba a ta6a maki dai dai...." Inna ta bude baki tace
"Ni kake xagi Mujaheed?" A fusace yace "Mu bar sa a hakan"
daga haka ya wuce ta kamar xai tashi sama, Yusuf ya bi sa da wani kallo, tuni
Umma ta shige kitchen ranta fari fat duk da haushinsa da take ji, Yusuf ya mike
yace "Yi hakuri muje in raka ki" Inna ta fara matsar kwalla tace "Isuhu
kaga abinda Mujaheed ya min ko? Da ina kusa da shi babu mai hanasa make ni....
Ina mahaifin ku yake" Yusuf yace "Ke dai mu je, Abba bai dawo
ba" Da kyar Yusuf ya lallabata suka fita parlon tace "Wllh in har
Mujaheed zae ci gaba da xaman gidan nan sai dai ni in tafi" Yusuf ya danne
dariyarsa suna isa part din su Imaan ta bude kofa, daddy dake xaune yana duba
laptop ya mike ganinta tace "Bukar babu abinda Mujaheed ya mance bai gaya
min ba yanxun nan daga nayi ma uwarsa gyara, sai ku xaba ko ni ko shi a gidan
nan" daga haka ta rufe kofar. Yusuf dai tuni yyi gaba, suna isa part dinta
ta rushe da kuka tace "Sai yanxu abun ke min ciwo isuhu, kai kaga wahalar
da nayi da Mujaheed kare baxae ci ba wllh" Yusuf yace "Sai kiyi
hakuri, Mujaheed din ki ne fa" a fusace tace "Mujaheed dinsu dai,
bari dai mahaifin ku ya dawo xai gaya min ko shi ke koya masa ya min rashin
arxiki" kiran Isha da ake yasa Yusuf ya bar part din inna, tare Daddy ya
je gun Inna da Imaan bayan isha, Inna ta fito daga daki ta shimfida tabarma ta
xauna tace "Wllh Bukar daga nace ma Rukayya ta daina gaisheni a gidan nan
don na munafurci ne, shi kenan Mujaheed ya hayayyako min yana huci..."
Daddy yace "Kiyi hakuri Inna, ina fita xan je in samesa yanxu" a
fusace tace "Oh oh babu xancen samunsa, kawai ni ba na son ganinsa gidan
ne ko kuma ni in tafi ai dama ya isa aure sai yyi ya koma gidansa baxan xauna
tare da shi wataran ya mareni ba, wai ku me yasa baku san ciwon uwar ku ba,
uwarsa fa na yi ma fada shine ya min rashin arxiki haka, kai ko ga ka xaune
sandandan gabana kana bani hakuri, ya fi karfin ka ne mujaheed din ko kuma
uwarsa ta fi naka ne, Ahmadu dai bai ba yaron tarbiyar da ya ratsa jikinsa ba
wllh" Daddy ya mike yace "Xan dawo anjima inna" daga haka ya
nufi kofa tace "Yauwa, ka titsiye sa sai ya gaya maka ko ni sa'arsa ce
kafin ya bar gidan" shi dai bai ce mata komai ba har ya fita, Inna tayi
kwafa tace "Xai san ya ta6a uwar su yau" Imaan dai na kwance kan
kujera tana kallonta, Inna tace "Ni na ma fara tsoronsa tunda abinda ya
zama kenan yanxu" Imaan tace "Toh ke me ya kai ki bangarensu"
inna tace "Ya za ki ce min haka 'yar nan, ni da gidan d'a na kuma kice me
ya kai ni?" Imaan dai bata ce komai ba, Inna tayi kwafa tace "Ke kin
ga wahalar da nayi da Mujaheed?" Imaan tayi dariya tace "Ae ke dama
kullum sai kice kin yi wahala da kowa" Inna tace "Kee na Mujaheed
k'are baxai ci ba, ni nasan me nake cewa, ina fa tsaye bakin kofar dakin
haihuwa daga safe har dare sannan aka haifesa, sai kin ga wahalar da ya ba uwar
d'an banxan, ai ko aka haifosa lafcece ya kusa biyun wani jaririn, duk ya cika
asibiti da kuka nyaaa ke kina gani kinsan sadauki aka haifo, gashi jajir da shi
fari hulll, gashin kansa kuwa ga bak'i ga cika yanda kika san d'an balarabe, ke
ki bari kawai, nan dai muka koma gida na wanke sa tass, baki ga uwarsa ba lkcn
yar siririya kamar xata karye ba yanxu da ta ci kudin d'a na iya ci ba ta koma
kamar buhun masara, kullum zanyi wanka da sassafe daga gidana in tafi gidan
Ahmadu yi ma fitsararren yaron nan wanka, don babu abinda uwar ta iya wai
tsoron jaririn ma take don bala'i, a haka har yayi wata uku ya koma yanda kika
san bredi wato ya xama wani lukeke, ga kyau tsantsa, ba sai uwar tayi ta cika
masa nono yayi ta tumbudi ba duk k'arni??" Imaan ta fashe da dariya har da
kyakyatawa tace "Shi yayan?" Inna tace "Wllh shi, to ni ko ina
xan iya kazanta da k'arni, oh oh nan na taka mata burki, ga uwar kazama dn har
sannan tana tashen kuruciya ni fa ko abincin gidan bana iya ci da, ana haka har
Mujaheed ya kai shekara biyu, ba sai naga ana neman hallaka yaron ba, ba shi da
aiki sai kukan banxa, fitsari a tsaye kashi a tsaye, ga uban shan yogurt, to da
yake ba yanda na raini ubansa ba kenan bakina a leko na daukesa, kin ji mafarin
komawansa waje na kenan, kuma Mujaheed bai bar gu na ba sai da uban ya biya
masa kudin karatun likita a kasashen turai bayan ya gama sakandari, to ace
banyi wahala da d'an banxan yaron ba kuwa, tsakaninsa da iyayensa fa sai dai
bayan kwana biyu yaje ya gaishesu ya dawo, ko k'uda bana yarda ya ta6a min shi
balle shegun kishiyoyina da duk suka mace yanxu, Allah dai ya ji kansu amma
shari'ar mu da su sai a lahira...." Imaan tace "Ni lokacin ma ba a
haifeni ba koh?" Da mamaki Inna tace "Oh oh kaji wata magana kamar na
ta6a66u, wa ke ta ke, ke da aka haifa jiya jiya, a hannuna fa kika fado, ai
wannan labarin da nake baki a lkcn mu duk mun dauka uwar ki juya ce...."
Imaan ta mike xaune ta hade rai tana kallon inna, inna ta gyara xama tace
"An auro uwar Mujaheed da shekara uku fa Ubanki Bukar ya auri bafillatanar
uwar ki tana tallan nono a lkcn, a gidan sa fa tayi wnn karatun da take takama
da shi" Imaan ta daure fuska tana kallonta, inna tace "Bayan an auri
Uwar ki Aisha da yan watanni na tursasa Ahmadu ya sake aure shine fa ya auro
Uwarsu isuhu, don a lkcn Rukayya na tashen rashin kunya duk an hure mata kunne,
ga kazanta duk ta bi ta ru6ar min da gidan d'a na, To ita kuma uwar isuhu lkcn
kawar Mamarki ce, kin ji musabbabin rashin shirin Rukayya da mamanki har yau,
Rukayya ta dinga jin haushin Aisha tunda kawarta ta aure mata miji, Uwar su
isuhu na shigowa da wata goma sai gashi ta haifo wannan d'an albarkan isuhu shi
ma dai a gabana aka haifesa ina tsaye, ke ko uwar ki shiru kamar malam ya ci
shirwa, ke in takaice maki har bayan shekaru aru aru sai dai uwar ki ta ci ta
sha tayi kashi duk tayi bake bake a gida babu haihuwa babu dalilinsa, babu
yanda banyi da Bukar ya karo mata ba amma yaron nan ya bijire min to duk ta
shanye min shi ta rarraba min sunansa inda bai kamata ba, ke kinga bafillatani?
To wllh kiji tsoronsa mugwaye ne na kin karawa, ni dai na dage rokon Allah ba
dare ba rana don Allah ya warware abinda tayi ma d'a na, to wllh karshe sai da
Ahmadu yayi 'ya ya shidda sannan uwar ki ta haifo ki, murna gun mahaifinki kuwa
ba a cewa komai, duk lkcn fa ba mu san ba lafiyayya bace ke din, nayi ta xuba
idon xuwan kanninki amma shiru, astagfirullah wa ya sani ma ko sai a lahira
idan ana haihuwar tunda gashi yanxu kin doshi ashirin, kuma tun da kika fara
wayo Bukar ya kulla adashin da ba kwasa da asibiti, shine ake nan har yanxu
jiya e yau, ni yanxu mai kwasan ki ma nake tausayi wllh kada ya kasa rike ki,
wannan idan talaka kika aura ae sai dai mu xo wataran mu dau gawarki muna koke
koke, to banda haka sata xai yi ya kai ki asibiti? abinda Bukar yace min a
kalla magungunan ki suna yin kusan dubu hamsin duk wata, wa xai iya wannan idan
ba mai kudi ba irinsu yaran d'an tata, mu dai Allah ga mu gare ka, ka yaye ma
jikata wannan iska da ya sa ta gaba yake cutan ta, ita kenan gun d'a na"
Imaan na hararanta tace "Daga labarin yaya kin wani dawo bada labarina kamar
an tambayeki, har na gaji da jin labarin nan a gidan nan" inna tace
"Toh wa ke ta wani yaya da barin gidan xai yi gaba daya, ai yau sai ya san
ya ta6a uwar masu gida" Da sallama Abba ya shigo parlon, Inna ta daure
fuska, Daddy ma ya shigo parlon Mujaheed na biye da shi a baya, inna na ganin
Mujaheed tace "Ni dai n shiga uku, mutumin nan ya fitar min a parlo don ba
ruwana" Mujaheed ya durkusa d'an nesa da ita ya sunkuyar da kansa yace
"Kiyi hakuri inna" inna tace "Oh oh Allah, ni dai wllh sai naga
kamar tsoron yaron nan ku ke Ahmadu, ni cewa nayi ku taso sa ya bani hakuri? Me
xanyi da hakurinsa, idan da amana Mujaheed zae dinga fifita uwarsa a kai na
kuwa? Ni da na ci fitsarinsa na ci kashinsa ba irin wahalar da ban yi da shi
ba, wannan wani irin fitina ne, me yasa Isuhu baya min haka?" Shi dai
Mujaheed bai dago ba, inna tace "Toh ni dai a bar min parlo na" Daddy
yyi murmushi bai dai ce komai ba, Abba yace "Mu dai sai dai mu ce kiyi
hakuri, shi kuma nasan maganinsa" inna ta wani tsuke fuska bata ce komai,
Imaan dai na kwance sai murmushi take, Abba na kallon Mujaheed yace "On a
serious note Mujaheed be careful... you had better respect yourself in this
house, and mind you no matter how she does her things, how she behaves, how
annoying she might be, she is still my motherr, yes she is my mother I can't
change her from who she is, and you have got to respect her to the fullest, you
keep that grandma and grandchild play aside since she doesn't cherish that, she
have got all right to complain of ur mother, let her be entitled to her
opinion, today shud be the last that she will complain of ur attitude toward
her Muhammad am I clear" Mujaheed bai iya ya dago kansa ba yace "in
sha Allah Abba" Daddy yace "Maa sha Allah" inna da sai tabe baki
take tace "Oho dai duk a banxa tunda baxa ku iya koransa a gidan ba"
Mujaheed yyi kasa da murya yace "Kiyi hakuri" tace "Tashi ka
bani waje, ba dai aure xaka yi ba wataran, wllh duk sai matar ta rama min
abinda uwarka tayi min a duniyar nan, takanas xan tattara kayana wllh in koma
gidanka da xama duk ni xan dinga koya ma yarinyar, nan Rukayya xata ji ko da
dadi ko babu" Mujaheed dai bai ce komai ba, Abba yace "Leave
now" mikewa yyi yana hararanta ta gefen ido ya fice daga parlon, Imaan ta
fara dariya kasa kasa. Ranan juma'ah da daddare Inna na xaune parlonta Imaan
kuma na kwance kan kujera gaba daya ta gaji da labarin da inna ke bata, tana
son tashi ta wuce amma ciwon da kafarta ke mata yasa ta kasa tashi, tun magrib
take wajen bayan ta kawo mata abinci har wajen tara da rabi yanxu, Inna tace
"To kin ji abinda ya raba ni da uwar d'an gwate kenan, kuma fa lkcn
kakanku bai san ina xuwa ba, kai jama'a na xuba farin jini gun masu kudi
wllh" Imaan dai bata tanka ta ba, bude kofar parlon aka yi Mujaheed ya
shigo da sallama, Inna tace "Dama shi kadai ne me shigo min da sallama
banda su oh oh" Ta gefen ido Imaan ta kalleta, ya ajiye ledan hannunsa
yace "Gashi" ta jawo ledan tana budewa tace "Lahh kaza ce kamar
yasan ina marmari wllh " Imaan ta mike xaune, inna ta hade rai ta rufe
ledan, mikewa Mujaheed yyi ya dauko plate ya ajiye gabanta, ta mayar gefe tace
"Ni dai wllh kuna takura ni gidan nan kai da Imaan ba haka isuhu da su
maimoona ke min ba, su basu da sa ido" ta hade rai ta bude ledan ta dau
cinya daya ta dungura masa a plate din, dariya yyi ya dauka yace "Ni fa na
siya maki kazar ba Abba ba" Inna tace "Auuu" kara bude ledan
tayi ta fiddo tsoka daya ta manna masa kan plate din, Ta kalli Imaan tace
"Naga kina son albasa da kabeji dauko kwanon can da kika ci abinci in kwashe
maki in hada maki da tsoka daya" Imaan tace "Ni nace maki
xan ci kaza?" Inna tace "Toh na sani? Gani nayi kin xabura kin tashi
kamar Bukar ya siyo min" Daga haka ta kai cinya baki tana ci tace
"Allah maka albarka Mujaheed duk cikin jikokina kafi jin k'aina wllh, shi
sa ma kana aure zan tattara yanawa yanawa in koma gidan ka na rantse" ya
xaro ido yace "Gidan wa?" Ta kallesa tana washe baki tace "Gidan
ka" yace "A'a wllh ga yar gaban goshin ki nan kice kuma gidana"
tace "Waye yar gaban goshi na?" Yace "Gata nan xaune" inna
tace "Oh oh ni gidan ka xan xauna xai fi min kwanciyar hankali, idan matar
ka xata rainani nasan xajka taka mata burki kai da baka son abinda xai ta6a ni,
wannan salubabbiyar kuma ai yunwa ma kadai ya isa ya koro ni, ni fa ban jin
imaan ta iya girki tunda take ko tafasasshen ruwan xafinta ban taba d'andanawa
ba" dariya Mujaheed yyi, Imaan ta wani hade rai tana kallon inna, Mujaheed
yace "Kinga idan tayi aure xaki d'an dana idan kin koma gidan ta da
xama" Inna tace "Ni fa baxan xauna gidan imaan ba gidan ka xan xauna
wllh" yace "Wllh baxa ki xaunar min gida ba sai dai nata" Inna
tace "Toh me yayi xafi haka, wannan satin idan nayi gidan ka wani satin
sai inyi a gidan ta duk da nasan a rame dai xan dawo daga gidan nata amma dole
naka naka ne, idan na koma gidan ka sai in murmure" Mujaheed yyi dariya
yace "Inaaa ba wannan xancen gidan mijinta ko gidan Yusuf xai fi maki
kwanciyar hankali amma gida na kam sai dai ki hangesa daga nisa shi ma kuma a
photo, Kinga duk sanda mijin nata ya gaji sai ya koro ki da ita" Inna tace
"Wai tsaya Mujaheed da kake wannan xancen da kudin asibiti mijin xai ji ko
da nawa dawainiyar ka fa san irin cimar da nake ci bana banxa bane, gwara dai a
bar sa ya ji da jinyarta, ni kuma in xauna gidan ka ko Yusuf koh Maimoon, amma
ina ni ina xaman gidan imaan ga yunwa dai kiri kiri tunda ba girki take ba sai
a wani fake da ciwon numfashi kamar yanda uwarta ke cewa" fuu imaan ta
mike xata fita cikin rashin sani plate din da ta ci abinci ta bari wajen ya
xamar da ita sai ga ta rijib a kasa, wani ihu ta fasa da karfi tana cewa wayyo
kafarta, Inna ta xaro ido ta mike da sauri ta bude kofa tace "Ni dai na
shiga uku da jaraba, yi maxa fita da ita Mujaheed, fitar min da ita kar ma ace
a parlo na ta fadi" Mikewa Mujaheed yayi yana mata wani kallo yace
"Baxa ki tashi ba" cikin kuka tace "Wayyo yaya kafana ya rike
baxan iya tashi ba" Inna ta gwalo ido tace "Ka ji ko? Mujaheed ka
fitar min da ita kada a sani a bakin duniya" Ganin da gaske ta kasa tashi
Mujaheed ya daga ta, ta zaro ido tana yarfe hannu tana cewa wayyo kafarta, inna
duk ta rude tana ce ma Mujaheed ya fitar da ita, ko fita basu gama yi ba ta
tura su gaba daya, ta kulle kofarta tasa makulli tace "Dama kada a kuskura
ace a parlo na ta fadi wllh don ba ruwana" Mujaheed ya xabga ma imaan
harara yace "Baxa ki tsaya da kyau ba" cikin kuka tace "Wllh ba
karya nake ba yaya kafar ya rike min" kalle kallen wajen ya fara yi, can
yayi tsaki ya dauketa kamar yar baby ya nufi bangarensu da ita, gam ta rikesa
tana rera kuka.🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟
Post a Comment for "IMAAN 5-6"