Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

IMAAN 3-4

 

_By Khaleesat Haiydar_🏻

3......

Imaan ce xaune kitchen sai faman xuba surutu take ma Ammi dake girkin dinner a kitchen, yar  skirt ne jikinta sai ves da yake ranan alhamis ne babu islamiyya, Ammi dake ta saurarenta ta tabe baki daga karshe tace "Aikin kenan sai dai ki cika mutum da surutu ba taimakon fari balle na bak'i" shiru Imaan tayi tana kallon Ammi, Ammi ta kalleta ganin yanda mood dinta ya canxa tayi murmushi tace "Toh ci gaba ina jin ki" sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, Ammi ta karasa kusa da ita tace "I was joking sweetheart, tafi ciki let me fry some onion and pepper" mikewa Imaan tayi a hankali xata wuce Ammi ta bi ta da kallo har ta fita, Ammi ta jingina da cabinet din kitchen din ta sauke ajiyar xuciya, can ta nufi kofa ta fita don bata son tayi bacci coz shine next abinda xata yi in har ta shiga daki, dakinta Ammi ta shiga ta sameta har ta kwanta, Ammi tace "Baxa kiyi bacci ba yanxu yamma yayi, je dakina xa ki ga leda da atamfa a ciki kan dressing chair ki kai ma su Anty kice ankon bikin Halima" Imaan ta mike xaune tace "Ammi to na mu fa" Ammi tace "Sai ki kirata ki tambayeta ban san ko an fidda naku ba" Imaan tace "Toh,

Anty kawai xan nuna ma?" Ammi tace "Ehh sai ki ce mata ta nuna ma Hajiya, na dai fita ai" daga haka Ammi ta fita dakin, imaan ta sa hijab har kasa kan kayana jikinta ta fita ta dau ledan ankon a dakin Ammi, tun da ta shiga parlonsu Anty take yamutse fuska ta dalilin yaji dake tashi sosai daga kitchen, lkci daya ta rike numfashinta, har xata juya ta fita sai ta nufi stairs da gudu don ta shiga dakin Anty, tsarkewa tayi sbda rike numfashin da tayi ga kuma gudun da take, lkci daya ta fara tari sosai breathing dinta na sama, dai dai corridor ta fadi tana kokarin jan numfashi, Maimoon ta fito dakin Anty ganinta ta durkusa gabanta da sauri tace "Subhanallahi me ya faru Imaan" sound din faduwarta yasa Mujaheed ya fito daga bedroom din sa, ganinta a kasa ya kalli kofar Ummarsa kafin ya karasa da sauri ya dagata yana kallon Maimoon da ta rikice yace "Tafi ki karbo inhaler dinta da sauri" da gudu ta sauka xuwa part din su Imaan, Mujaheed ya bude kofar dakin Anty ya shigar da ita ya xaunar da ita kasa ya jinginar da ita da gado ya cire Hijab din jikinta, dai dai nan Anty ta fito daga bandaki, a rude tace "Subhanallahi, Asthman ne, garin Yaya? Ko in amso inhaler dinta" yace "Maimoon taje amsowa" sosai imaan xata baka tausayi saboda ynda take struggling da numfashinta, Mujaheed ya mike ya fita don bin bayan Maimoon suka kusa cin karo bakin kofa, fixge inhaler din yyi ya juya ya koma dakin ya durkusa gabanta ya kai mata baki, dafe hannunsa tayi tana inhaling, Anty dai na tsaye sai kallonta take cike da tausayinta, bayan wani lkci numfashin nata ya fara fita a hankali yana kokarin dawowa normal, Anty ta xauna gefen gado tayi tagumi tana kallonta, Ummi da Rahma na tsaye bakin kofar suna kallonta su ma, Har sannan Mujaheed na duke gabanta idonsa a kanta, muryar Umma suka ji tana cewa "Lafiya me ya faru ku ka tsaya cirko cirko bakin kofa?" Rahma tace "Asthma ne ya tashi wai" Umma ta leko dakin ganin Mujaheed ta wani xaro ido tace "Me Mujaheed yake a nan?" Mikewa yyi da sauri, ta wani hade rai tace "Tambayar ka nake, me ka shigo yi, ko kayi kama da likitan ta ne?" Ya girgixa kai yace "No na xo wucewa ne...." Dakatar da shi tayi tana masa wani shegen kallo tace "Sai ka tsaya aikin da ba lada koh? To ka shiga hankalin ka, Ka guji bacin raina, basu da number likitan ta ne ko kuma neman suna kake?" Shiru yyi bai ce komai ba, Cikin tsawa tace "Xo ka fita malam bana son shishshigi da kwala kai a faranti, kanwar uwar ka ko ta ubanka?" Bai ce komai ba ya kalli Imaan da Anty ke kokarin kwantarwa kan gado ya juya ya nufi kofa xai fita, Anty ta tabe baki tace "Ciwo dai bai wuce kan kowa ba, ita ma ba ita ta doro ma kanta ba....." Umma ta katse ta da sauri tace "Allah yayi mana tsari da irin wannan ciwo nata, ya tsari jikokinmu da tatta6a kunne, a rayuwar nan ta ynxu wa enda ba sickler ba ma ya suka kare, ae irinsu ne ke tsiyata namiji a sintirin asibiti...." Tsaye Mujaheed yyi bakin kofa yana kallon Umma, Anty ta wani hade rai tace "Kinga ki daina kiranta da sickler ita din ba sickler bace, Allah kuma yyi mata tsari da shi" Umma ta wani tabe baki hade da dariya tace "Kwa dinga boye ma wanda ku ka raina ma wayo, Allah dai ya ba kowa lafiya...." A hankali Mujaheed yace "Umma ba fa sickler bace, she is just a carrier...." Umma ta maka masa wani kallo tace "Meye maraban dambe da fada? And did you have any problem with her being a sickler or not da har kake karyata ni Mujaheed?" Bude kofar yayi ya fita dakin bai ce komai ba, ta ja tsaki ta fice ita ma. Anty ta girgixa kai ta zauna kusa da Imaan da ta lumshe ido numfashinta na sauka a hankali tana mata sannu, sai da ta ga alamar tayi bacci sannan ta mike ta fita, Imaan bata dau lkci tana bacci ba ta tashi ta dalilin ciwo da kirjinta ke mata, ta dinga juye juye kan gadon hawaye na xuba idonta, bude kofar dakin aka yi Mujaheed ya shigo, ya karasa kan gadon yana kallonta, daure fuska yyi yace "Me ya faru kuma?" Kirjinta ta nuna masa ta fashe da kuka, yace "Toh kukan ne xai sa ya daina ciwo, tashi xaune" mikewa tayi ta xauna da kyar, sai ga Anty ta shigo dakin, da sauri ta isa gadon tace "Me kuma ya faru Imaan, are you feeling pain anywhere?" Ta gyada kai tana nuna kirjinta, Anty ta dau Hijab ta nufi kofa tana cewa "Bari in je in kwaso magungunanta dai" Xaunawa Mujaheed yyi gefen gadon, ta koma xata kwanta yace "Kar ki kwanta" ta jingina da gadon tana goge idonta, ba a dau lkci ba Anty ta dawo da ledan maganin gaba daya, Mujaheed ya amsa yana duba maganin ya cire mata wanda xata sha, still yyi jin an bude dakin Umma, sai kuma ya ji muryarta tana tambayar inda yake, tashi yyi da sauri ya tafi bayan kofa ya tsaya, Anty ta tabe baki ta balli maganin ta dau table water ta mika ma Imaan, bude dakin aka yi Umma ta kare ma dakin kallo kafin ta tabe baki ta kulle, Shi dai yana tsaye bayan kofar, Anty ta sa Imaan ta kwanta bayan ta sha maganin sannan ta kallesa tace "Don Allah ka fita min a daki malam, tunda aikin xumuncin ma ba so ake kayi ba, kai ma kuma tsoron yi kake, yau ko da ace baka san Imaan ba a matsayin ka na likita ka ganta a wannan hali ai baxa ka ki taimaka mata ba balle tana yar uwarka halak malak, Allah dai ya shiryi mahaifiyar ka" shi dai bai ce komai ba, bayan karin mintuna uku ya bude dakin ya fita. Anty na xaune kan darduma bayan ta idar da magrib Imaan ta tashi daga baccin da ya kara dauketa, Anty tace "Sannu ya jikin Imaan" a hankali tace "Na ji sauki" Anty tace "Toh shiga bayi kiyi alwala ki xo kiyi sllh" ba musu ta mike ta shiga bandakin ta dauro alwala ta fito Anty ta mike kan darduman ta fita, Imaan ta sa Hijab dinta ta hau kai ta tada sllh, tana ta xaune kan darduman bayan ta idar sai ga Anty ta shigo da plate din abinci dakin. Imaan na gama ci ta mike rike da plate din tace "Anty sae da safe" Anty tace "Au baxa ki kwana nan ba" murmushi tayi ta make kafada ta nufi kofa, Anty tace "Toh baki fada min ko na meye atamfar ba" Ta juyo da sauri tace "Lahh, Ammi ce tace in kawo maku ankon bikin Anty Halima" Anty tace "Ashe abu ya xo dai, toh ki ce mata xan shigo gobe" Imaan tace "Toh" Anty tace "Allah ya sauwake Imaan" murmushi tayi a hankali tace "Ameen" daga haka ta fita, tun da ta sakko downstairs umma ke mata kallon tsana tana tabe baki, Imaan dai bata ko kalleta ba ta nufi kitchen rike da plate din, Rahma ce kitchen din ta gama wanke wanke, sai Mujaheed dake tsaye yana xuba ruwan Lipton daga teapot a cikin mug, Imaan xata ajiye plate din, Rahma tace "Kinga plate mai datti a wajen ne malama" turo baki tayi ta dau morning fresh ta bude xata wanke plate din, Rahma tace "Ya M.A in debar maka abincin ne xan fita?" Ya harareta yace "Abincin da ku ka cika yaji ko wanda ba yaji?" Yar dariya tayi tace "Ya Mujaheed yajin fa ba yawa" tsaki yyi yace "Ance maki ban yi tasting abincin bne ku dinga cika ma mutane ya ji a abinci kamar mayyu" Tace "Toh in maka cous cous?" Yace "I will take tea" Imaan ta gama wanke plate din ta juya ta fita kitchen din. Kallonta Ammi ta dinga yi bayan ta shigo tace "Ya jikin Imaan" tayi murmushi tace "Na ji sauki Ammi" daga haka ta nufi dakinta Ammi ta bi ta da kallo. Karfe sha daya saura Ammi ta shiga dakin Imaan, ganin tayi bacci ta tasheta tana mika mata wayar hannunta tace "Me ya sa kika kashe wayar ki" Imaan na murxa ido tace "Kila mutuwa yyi ba charge" Ammi tace "Toh idan kin gama ki maido min wayata daki" Imaan tace "Toh" sannan ta kai wayar kunne tace "Daddy ina yini" Daga daya bangaren ya amsa yace "Why is ur phone switched off" ta langwabar da kai tace "Daddy ban sa a charge ba tun jiya" yace "Toh kiyi kokari ki sa ya jikin?" Tace "Naji sauki, daddy ina missing dinka yaushe xaka dawo?" Yace "Weekend in sha Allah" ta wara ido cike da jin ddi tace "Plss daddy ka dawo week end din kar ka daga, wllh ina son in ganka" kamar xata yi kuka ta kare, yyi murmushi yace "Sure dear, plss ki daina wasa da shan drugs din ki kinji" tace "Ina sha Allah daddy, har yanxu Dr ma bai xo ba" yace "Ehh mun yi waya daxu yace bai dawo ba" Imaan tace "Toh" yace "Sleep tight dear, banda kunna Ac" yar dariya tayi tace "Toh daddy byeee" katse wayar tayi ta mike ta kai ma Ammi daki sannan ta dawo dakinta ta shige duvet. Yau Friday Imaan na dawowa schl bayan tayi wanka tana kokarin saka kayanta taji k'aurin abincin da Ammi ta bar mata a kitchen kan gas don tana shigowa gidan Ammi ta fita kasuwa yin cefane, da gudu ta fita daure da towel don kashe gas din don dama sae da Ammi tayi mata kashedi kan cewar kada ta yarda abincin ta ya kone, muryar inna ta ji a balcony tana cewa "Aa kawai ni dai naga kwana biyu bata shigo bane shine nace in xo in duba ko jikin ne, tunda haka Allah yyi ta mai laulayi, ni jiya ma ko abinci basu kawo min ba wllh, in ma ba ta da lafiya ita Aishar baxata iya takowa ta kawo min abincin ba tunda ba uwarta Habiba bace, abu dai gashi ba tsari da ni fitinanniyar tsohuwa ce ba Bukar xan kira ince matarsa ta bar ni da yunwa ba?" muryar Yusuf imaan taji yana dariya yace "Toh ae an kai maki daga gidanmu naga" da sauri Imaan ta shige daki ta dau Hijab dinta ta fito ta shige kitchen ta kashe gas din sannan ta bude kofar kitchen din ta fice tana murguda baki ta sa Hijab dinta da iyakarsa gwiwa, ko takalmi bbu kafarta ta dinga tafiya har ta zagayo front din gidan, Mujaheed ne xaune kan farin kujera yana waya, ta turo baki ta wuce sa da sauri, ko minti biyar ba ayi da wucewarta ba shi ma ya ji muryar inna tana tahowa, mikewa yyi da sauri tun kan ya bar wajen ta gansa, da karfi ta kwalo masa kira tana murmushi, ya ki juyowa har ya sha corner, Yusuf sai danne dariyarsa yake, Inna ta bude baki tace "Wato ni Mujaheed xai walakanta ina kiransa ya min banxa kai shaida ne ko Isuhu" tana magana tana kunce ha6ar xanin xata goge kwalla, Yusuf ya kasa daurewa ya fara dariya yace "Ke fa kika ce kar ya sake xuwa bangaren ki..." A fusace tace "To shi mahaukaci ne bai san bacin rai ba" Karo Mujaheed ya kusa yi da Imaan dake kokarin lekowa taga ko inna ta taho bangaren, ya hade rai yace "Baki gani ne?" Tana shafa Inda ya bugeta tace "Ko ba inna bace, ta wani biyoni gidanmu anjima tace ina mata rashin kunya" tafiyarsa yyi ya bar ta wajen tsaye, ta turo baki ta bi bayansa, jin tafiyarta a bayansa ya tsaya ya juyo yace "Wai me yasa kike bi na ne" Tace "Ni ba bin ka nake ba tafiyata kawai nake" Tsayawa yyi ya daure fuska yace "To yi tafiyar ki, bana son ganin ki kusa da ni" ba ta ce komai ba ta fara tafiya kamar mai counting steps dinta, yana ta tsaye yana jiran tayi nisa ganin ynda take tafiyar ya girgixa kai ya wuce ta cikin lokaci kankani, sai a sannan ta kara saurinta har ta jera da shi, d'an murmushi yyi bai dai ce komai ba bai kuma kalleta ba, sai da suka kusa entrance din kitchen din part dinsu tace "Yaya ka mance promise da ka taba min 2 years back koh?" Kallonta yayi kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Na me?" Ta wara manyan idanuwanta tace "Idan nayi saukan al-quran, gashi mun kusa in few months time" tabe baki yyi xai bude kofar kitchen din yace "I can't recall...." Ta xaro ido ta rikosa da sauri tace "Wllh nasan baka mance ba" Buge hannunta yyi yana mata wani kallo yace "Keee" Ta turo baki tana kallonsa, yace "Sakeni kar in mare ki" sake sa tayi ya bude kofar kitchen din ya shiga ya kulle, tana ta tsaye wajen bayan few minutes ta murguda baki ta wuce, ta kitchen dinsu ta bi ta kulle kofar sannan ta wuce dakinta ta sa kayanta. Yau tunda Imaan ta tashi take ta murna, gaba daya farin cikin ta ya kasa boyuwa, Kitchen ta shiga tace "Ammi da yaushe daddy xai iso?" Bude baki Ammi tayi tace "Kina kallon agogo kuwa Imaan?" Imaan tace "Ammi wai yau ma da daddyna xai dawo sai naje islamiyya?" Ammi ta mata wani mugun kallo tace "Uwar me xa ki xauna ki min ko yace maki da safe xai taso, common kin 6ace min a nan kin je kin shirya ko sai na 6ata maki rai" a hankali Imaan ta juya a sanyaye ta koma bedroom dinta ta fiddo uniform dinta ta shiga sa wa, sai da Ammi tayi mata jan ido ta amince da yin breakfast da ta hada mata, tana xaune dinning tana shan shayin da kyar Maimoon ta shigo parlon sanye da uniform, Ammi dake goge goge a parlorn tace "Maimoon ku yi wucewar ku kar ta bata maku lkci ko da kafa ne sai ta je" dariya kawai Maimoon tayi ta fita, Imaan ta mike don kanta ganin takwas ya wuce ta dau jakarta ta fita tana matsar kwalla ko ta kan kudin makarantar bata bi, Ammi dai ko kallonta bata yi ba, Tsaye taga Mujaheed jikin motar banda masifa babu abinda yake ma kannin nasa, duk kallonsa kawai suke babu wanda yace komai, "Don samun waje nan nan da islamiyyar ma sai an kai ku a mota ku ga yan gayu ko, to wllh ni ba driver din kowa bane a cikin ku da xa a dinga cewa in ajiye ku a makaranta, Yusuf da ya ga xai iya sai yyi, I won't tolerate that shittt" A hankali Ummi tace "Amma ya Mujaheed kawai don kana nan ne yasa xaka kai mu ai ba kai ke kai mu ba dama, kuma Abba yace kila Monday xa mu samu sabon driver...." wani kallo ya dinga mata fuska daure, ta sunkuyar da kanta, Imaan da isowanta kenan ta bude motar xata shiga ya dakatar da ita yace "Kee, do I look like drivern gidanku da xaki ajiye ni for the past 15 mins a nan, to ke daga yanxu ma xa ki fara naki trekking din" yana fadin haka ya nuna mata makeken gate din gidan yace "Bi can ki kama hanyar makarantar" ta wani gwalo ido tana kallonsa, lkci daya ta juya kamar xata yi kuka xata koma part dinsu tace "Ni dai ban ta6a tafiya da kafa ba...." Wani tsawa yyi mata yace "Wllh ki ka yarda na takowa har Inda kike sai na sa ki kuka" tsayawa tayi tana hawaye don bata mance last abinda ya mata ba, ya nuna mata gate on a serious note yace "Bi  can" Gate din ta nufa tana kuka ya jira ya ga fitar ta sannan ya shiga motar ya bar gidan har ya wuce ta. Tsaye tayi bakin titi ta rufe fuskarta da Hijab tana kuka, ta kusa minti sha biyar tsaye a haka taji cikin cool voice ance "Are you okay" xame hannunta tayi a hankali daga fuskarta tana lekan ko waye ta cikin hijab dinta, wani dogon matashi ne da baxai wuce thirty two ba, yana sanye cikin kananun kaya idonsa sanye da bakar spec, dogo ne shi din sosai, sannan shi ba baki ba kuma baxa a sa shi a jerin farare ba, kuka ya kara taho mata ta dinga rerawa, yace "Subhanallah, wani abu ya faru da ke ne? Talk to me plss" Cikin rawar murya tace "Yaya ne ya ce baxan shiga mota ba trekking xanyi kuma islamiyyar mu da nisa wllh" kallonta ya dinga yi da mamaki, ta sake lekosa ta cikin Hijab suka hada ido ta yi saurin rufe fuskar tana shessheka, ya d'an yi murmushi yace "Kin masa laifi kenan" girgixa masa kai tayi, yace "Toh mu je in ajiye ki ga ride dina can, while going inside the filling station na gan ki tsaye bayan nayi refilling tank na fito I still saw u the way you were so I decided to check if you are alright" shiru tayi bata ce komai ba yace "Mu je to" tace "A'a" yace "Ohk in samar maki adai daita?" Kai ta gyada masa, ya tsayar da adai daitan ta shiga ya basa kudin, a hankali tace "Nagode" ya mata murmushi kawai mai adai daitan ya ja suka bar wajen, Yusuf ne ya dauko su daga islamiyyar bayan sun tashi karfe sha biyu, tun a mota ya dinga tambayar Imaan me ya faru ganin yanda take yamutse fuska, da kyar tace "Kafana ke min ciwo" yace "Toh sannu, idan muka isa gida sai ki shafa maganin" a hankali tace "Toh" suna isa gidan da kyar ta fito motar, Yusuf ya kama hannunta ya rakata har sashin nasu sannan ya bude mata kofa ta shiga ciki, wanka kawai tayi ta saka doguwar riga Ammi ta shafa mata methylated lotion din da take shafawa a kafafuwanta sannan ta sa ta kwanta nan da nan kuma bacci ya dauketa, dab da la'asar Ammi ta tasheta, Ammi bata mata xancen islamiyya ba Imaan ta wara ido ganin irin girke girken da Ammi tayi tace "Ammi is all this for daddy?" Ammi tace "No it's for Imaan" murmushi Imaan tayi ta rungumeta ta baya tace "Thanks sweet mum" Ammi tace "Ki tafi kiyi sllh ko baki ga lokacin hr ya gota ba" da sauri ta koma daki, tana idar wa ta fito, Ammi tace "Daddy ya kira yana gate, ki fita ki shigo masa da kaya" da sauri Imaan ta nufi kofa Ammi na kiranta ta xo ta sa hajib don rigar jikinta karamin hannun garesa amma tuni ta fice, dai dai nan mai gadi ya bude gate sai ga motar Daddynta, da gudu ta nufi parking space ta tsaya cike da murna, Mujaheed dake kokarin bude motarsa suka yi ido hudu da daddy da ya fito Imaan ta rungumesa, Daddy ya sakar masa murmushi, hakan yasa ya nufe sa kamar mai kirgan steps dinsa, daddy na shafa kan Imaan yace "Ba kya girma koh Mamata" ta kara kankamesa tace "Don Allah daddy ka daina dadewa haka wllh ina Missing dinka" yyi murmushi yace "To xan daina mamana" Mujaheed ya risina yace "Sannu da hanya Abba" Wani hade rai Imaan tayi tana hararansa ta gefen ido, Daddy na murmushi yace "Thanks Son, ka bar mu a birnin tarayya ynxu koh" murmushi Mujaheed yyi yace "Ae kam daddy" daddy yace "Toh Allah yayi jagora, ya aikin fa?" Yace "Ae ban fara ba sai Monday Abba" Daddy yace "Allah ya kai mu" Daddy ya mika ma Imaan da ta turo baki ledan apples dinta da chocolates don a ko da yaushe tsaraban ta kenan, Mujaheed dai ko kallonta bai yi ba ya dau jakar laptop din daddy da wasu files ya nufi part dinsu, Murguda baki Imaan tayi ta jera da daddynta tana ci gaba da gaya masa yanda tayi kewarsa, Mujaheed ya sunkuyar da kai ya gaida Ammi bayan ya ajiye jakar hannunsa da files, ta amsa ta dau jakar ta wuce daki, Daddy ya xauna yace "Barrister bai dawo ba ko Mujaheed?" Mujaheed yace "Ehh bai dawo ba" Daddy yace "Ohk mun yi magana daxu ma" Mujaheed ya dukar da kai yace "Toh Allah ya huta gajiya Abba" daddy yace "Madalla nagode son" har ya fara tafiya Daddy ya kalli ledan apples da chocolates da Imaan ta sa gaba tana dubawa yace "Son baxa ka Debi apples ba" Da sauri Imaan ta jawo ledan jikinta tana kallon daddy, Mujaheed da har xai ce A'a don he isn't a fan of Apple ganin abinda tayi yayi kasa da kai yana shafa gashinsa yace "Toh Abba" daga haka ya nufeta, bude baki tayi tana kallon daddy lkci daya hawaye ya kawo fararen idonta, Mujaheed ya jawo ledan yana kallonta da kyau ya cire spare leda ya debi apples har hudu a cikin guda takwas da Daddy ya siya ya xuba a wani ledan yana kallonta har sannan, ya kara bude ledan chocolates din ma ya debi mai yawa ya xuba a ledan hannunsa, har ya mike ya sake dawowa ya dau Apple daya ya sa ka a ledan, daddy ya dauke kai yana murmushi, Mujaheed bai yarda ya kallesa ba yace "Nagode Abba" daga haka ya fice parlon.

[6/11, 12:34 PM] +234 703 570 1601: 🌟⭐ *Imaan*⭐🌟

 

 

 

 

 

_By Khaleesat Haiydar_🏻

 

 

 

 

 

4.....

 

Daddy ya kalli Imaan dake goge hawayen idonta yace "Don yayanki ya debi apples kike kuka Imaan?" Ta marairaice tace "Toh daddy ai ba shi ka siyo ma ba gashi ya kwashe min gaba daya kuma wllh baya cin apple" Daddy yyi murmushi yace "Shi yace maki bai ci" cikin rawar murya tace "Ae nasan baya ci tun da can" Daddy yace "Toh anjima idan na fita xan karo maki" a hankali tace "Toh nagode" yace "Wai amma me ya hada ku da yayan naki all of a sudden Imaan" Ammi da ta fito parlon tace "I am still wondering also, lkci daya aka yi parting" Daddy yace "Ko kin masa wani abun ne dai" ta turo baki ta dawo kusa da daddy tace "Kawai dai naga ya xama mugu ne shi sa na daina kulasa" Dariya kawai daddy yayi, Ammi tace "Har nan ma ai baya shigowa yanxu" Daddy yace "Toh Allah ya kyauta" Imaan tace "Daddy ni dai ka daukan min personal driver dina plss" daddy yace "Ba Abbanku xai daukar maku driver ba, ai mun yi magana da shi bayan tsohon drivern ya wuce" Tace "A'a daddy ni dai nawa daban nake so, kilan ba yanxu driver din ma xai xo ba, yau fa Yaya bai bari na shiga motar ba don na bata masu lkci da kafata na tafi islamiyya shi sa tun da na dawo duk jikina ke ciwo sai da Ammi ta shafa min magani na kwanta da na tashi shine naji sauki"' Murmushi kawai Daddy yayi ya mike yace " Bari in yi wanka daughter " daga haka ya wuce bedroom dinsa, Ammi tace "Sai ki tashi ki kai ma Inna abinci ko yau ma baxa ki ba" Ta kalli Ammi da sauri tace "Ammi ca tayi bata son sake ganin kafata a part dinta fa, kuma in je yanxu ta gaya ma daddy" Ammi tace "Tashi ki dauki abinci ki kai mata nace" Daga haka Ammi ta bar parlon, mikewa Imaan tayi ba don ta so ba ta shiga kitchen, kusan duk abinda Ammi tayi ma daddy sai da ta dibar ma inna duk ta ajiye a basket, Imaan ta dau basket din me dauke da abincin ta fita, har ta isa part din Inna fuskarta a daure yake irin ko kulata din nan baxata yi ba, ta dinga kallon takalman dake bakin kofa kafin ta bude kofar ta shiga, Mujaheed na xaune yana kallon inna dake bada labari tayi mitsi mitsi da ido, banda murmushi babu abinda yake don da wuya yake dariya, su Maimoon da Rahma kuwa dariya har da kyakyatawa, Inna ta saita hannu sama tace "Ji kawai muka yi ratatatata.... Ba sai kakan ku ya shige karkashin gado ya bar ni da halina da 'ya yana ba, lkcn Bukar na bayana sai tsala ihu yake, Ahmadu kuwa fitsari ya dinga saki yayi sau uku a wando...." Ganin Imaan Inna tayi shiru ta jawo daya daga apples biyar dake cikin leda a gabanta ta kai baki, Har sannan su Maimoon dariya kawai suke, imaan ta ajiye basket din hannunta tana kallo   chocolates din da Daddy ya kawo mata a hannunsu Maimoon, ta saci kallon Mujaheed ta juya xata fita Inna ta tabe baki tace "Ga dambun naman ki can a daki ni dai na ajiye maki bana bi ta halin ki ba" ba tare da ta juyo ba tace "Bana ci" inna na ci gaba da cin apple dinta tace "To wa yayi asara?" Mujaheed yace "Yana ina a dakin?" Da sauri Imaan ta juyo ta shige dakin, Inna tace "Ya xaka ce yana ina bayan ka ci rabon ka da wanda ma ka dauka ban baka ba" yace "Haba" tayi tsaki tace "Yana nan cikin roba xa ki gansa a rufe, duk naki ma ya fi yawa" Imaan ta fito rike da uban dambun naman da inna ta ajiye mata a bowl mai murfi ta nufi kofa, inna tace "Wannan liyafar hala Bukar ne ya dawo?" Imaan tace "Bai dawo ba" daga haka ta fita, Inna tace "Duk ta ma fige kamar bata cin abinci" Rahma tace "Mu dai ci gaba da ba mu labarin da kike yi don Allah inna" inna ta gyara xama xata ci gaba, mikewa Mujaheed yyi ya fita parlon. Imaan na komawa bangarensu ta tadda Yusuf ya shigo gaida Daddy, Ya bi ta da kallo ta boye bowl din hannunta tana wara masa manyan idanuwanta tace "Nasan ka ci naka dai" fitowar Daddy parlon yasa Yusuf bai ce mata komai ba, daddy yace "Engnr ashe kana gari" Yayi murmushi yace "Ina nan daddy, da fatan kun iso lafiya" yace "Alhmdllh My son, ya aikin fa" Yace "Mun gode Allah Daddy" daddy ya xauna kujera yace "Madalla, kowa dai lafiya koh?" Yusuf yace "Duk lafiya" Yusuf bai wani dade ba ya mike yace xai wuce, daddy yace "Baxa ka tsaya mu ci abinci ba" Yace "Alhmdllh daddy na ci abinci" Ammi dake dinning tana jera abincin tace "Anya Yaya Yusuf" dariya yayi yace "Ammi wllh na koshi" tace "Toh shikenan" sallama yyi ma daddy ya fita. Bayan magrib daddy xai je gaida inna babu yanda bai yi da Imaan su je ba ta ki, har hakan ya basa mamaki ya tafi shi kadai, inna na goge tiles din parlonta daddy ya shiga da sallama, ta mike tace "Amma dai gaskiya Bukar ka dinga kwa6a ma yar ka ta daina karya, ce min fa tayi baka dawo ba" Ya xauna yana murmushi yace "Sannu inna, ina yini" ta shimfida tabarma ta xauna tace "Lafiya lau, amma ai karya ba shi da amfani kuma a gaskiya Imaan ta iya karya" Shi dai bai ce komai ba, tace "Toh ya hanyan?" Yace "Alhmdllh mun baro hanya" tace "Wannan karan kuma kamar baxa ka sake dawowa ba" yace "Aiki ne yyi yawa Inna" tace "Toh Allah ya bada sa'a ya tsare mana ku a duk Inda kuke, ya maka albarka" yace "Ameeen inna" Tace "Toh ya xa ayi, Allah ya kaddara a can abincin ka yake, banda haka na tabbata da kana gidan nan da ka dinga share min hawaye daga bakin cikin da nake fuskanta" Daddy na kallonta da mamaki yace "Bakin ciki kuma Inna?" Inna tace "Yo bakin ciki mana Habu... Kaga yayanka baxai fito daga masallaci ya tako nan tun asuban ba ya gaisheni sai ina jin wajen karfe tara xai taho da safe ya duka can bakin kofar ya gaida ni a gurguje ya kara gaba, bana sake ganinsa Bukar sai ina kokarin kulle kofa ta da daddare shi ma Allah yasa ya yi minti biyu xaka ga yace sai da safe daga haka ya wuce, Kaga matar nan tasa Rukayya take ko wa? Uwarsu Mujaheed dai wllh kaji rantsuwar musulmi tafi wata biyu ina ga bata tako ta xo nan ta gaisheni ba sai ta gan ni a tsakar gida ko a can bangaren, ita kuma dayar mai kama da fulanin Bararoji wato Amina da suke ce ma Anty sai ta bushi iskarta xata kwaso kafafuwa ta xo gaisheni, ita wnn farar wa take da suna? Uwar wannan yarinya Imaan d'an wankin da take min da duk ta watsar sun xugeta, in kuwa wannan 'ya taka Imaan borinta ya tashi ta ki kawo min abinci to ranan fa da yunwa xan kwanta a gidan nan, Aisha ta fi karfin ta taso takanas ta kawo min da kanta, to me yafi wannan bakin ciki Yaro? Gashi gaba daya 'ya yanku sun rainani sun maida ni ba bakin komai ba, sun maida ni kakarsu tun ma ba wannan katon Mujaheed ba da ramammiyar 'yar ka, sai wannan kazamar Ummi, ni nasan da sun ga ido wllh taka ni xasu dinga yi suna wucewa, isuhu kadai ke raga min a gidan nan sai wannan yarinya Seeyama, Imaan idan ta fara balbale ni wlh shiru nake, haka ma Mujaheed yaron da aka haifa a gabana, to ina dalili ina da gata na ta ko ina don dai d'an abincin da ake yarfa min a kwano sai a maida ni bola" Daddy dake ta saurarenta ya dago kansa a karo na farko yace "Kiyi hakuri don Allah inna" a fusace tace "Na gaji da jin wnn axxalumin kalman, ayi ta baka hakuri ana cutan ka, ni dai a fita harkata, don idan tsiyata ta debeni wllh sai an fita har kasashen waje ana nemana" Daddy yace "Xa a gyara Inna, duk ki yafe masu, ita Imaan xan sameta yanxu, shi ma Mujaheed din xan gamu da shi" Tace "Atoh, sai ka xaunar da su ka tambayesu kaji ko xaman gidan ne basa son inyi, ka tambayesu dalilin da yasa basa fitsaran su a waje sai a cikin gida cikin gidan ma a kan uwarka, kayi masu jan ido ka nuna masu bacin ranka Yaro" Daddy yana murmushi yace "In sha Allah" nan suka ta6a hira amma kusan hiran gaba daya na complain ne daga karshe daddy yace mata xai wuce masallaci don an kira isha. Daddy na dawowa masallaci ya dinga kallon Imaan dake xaune parlor tana cin abinci, ya xauna yace "Imaan yanxu ita innar kika mayar abar wasar ki a gidan nan?" Kallonsa ta dinga yi kamar zata yi kuka, ya hade rai yace "would you take ur eyes off me silly girl, haka kike ma uwar ki? I warned you the last time a kan haka shine kika sake repeating foolishness din yanxu ko?" Ta sunkuyar da kanta, ya gyada kai yace "Nasan maganin ki, tashi ki bar min parlor" tashi tayi da sauri ba tare da ta bi ta kan abincin ba ta shige bedroom dinta ta kulle, ita dai Ammi bata ce komai ba, Daddy yace "I don't like this nonsense character of her, ita innar abokiyar wasanta ce, ke kuma Aisha baki taka mata burki, a kan me xata dinga rainata, I don't like that, and I am going to teach her manners soon" Ammi ta tabe baki ta mike ta dauke abincin da ta bari ta kai kitchen ta rufe, ta tsaya kitchen din tana wanke plates da ke sink. Washegari wajen karfe bakwai da rabi Imaan ta fito sanye da uniform din islamiyya, kanta a kasa ta gaida Ammi dake jera breakfast a dinning, Ammi dake kallonta tace "Wato ke ba isa a maki fada ba shine kika kwana kuka ido ya kumbura koh?" Ta fashe da kuka tace "Ni Ammi don Allah kar ki sake ce min in kai mata abinci kullum sai tayi ta ma mutum sharri alhalin ba abinda nayi mata" Ammi tace "Ko ban baki abinci kin kai ba ma da kanki naga kike kwasan kafafuwanki kije can din ko da kuwa koranki tayi" Imaan ta hade rai tace "Yesterday was the last day da xan je part dinta, har abada baxan sake xuwa ba" Ammi tace "Toh bari dai ya ji ki gashi can ya fito, ni ba ruwana" shiru Imaan tayi tana juya shayin da Ammi ta hada mata, Daddy dake tsaye parlon yace "Madam me yasa ba a kai ma Inna breakfast ne wai?" Ammi tace "Breakfast kuma?" Yace "Ehh ai ya kama ta ne" tace "A'a don Allah yallabai kar ka hada ni da ita, kullum sai Abba ya tura mata bread, tana da kayan shayi kuma tana da heater ta iya amfani da shi, meye breakfast din dama idan ba shayi da bread ba sai kwai wani lkcn, lunch da kanta tace bata so a daina kai mata wai jagwalgwalon yara ne" Tuni Daddy ya xauna ya sa news channel, Ammi ta shiga kitchen ta ci gaba da abinda take, Imaan ta gama breakfast din ta mike ta iso cikin parlor ta durkusa ta gaida Daddyn nata, sau daya ya kalleta ya amsa ya ci gaba da kallonsa, ta mike ta tafi kitchen ta amshi kudin makarantar ta gun Ammi ta fito ta dau jakarta bayan ta sa takalmi da safa tayi ma daddy sallama ba tare da ta kallesa ba ta fice daga parlon, kiranta daddy yyi ta juyo ta dawo ta sunkuyar da kanta tace "Ga ni" room freshener har biyu ya nuna mata dake ajiye yace "Dauka ki kai ma Inna kafin ku wuce" shiru tayi tana kallonsa kamar xata yi kuka, bata dai ce komai ba ta durkusa ta dauka sannan ta fita xuwa part din inna, Inna na ta goge goge bayan ta gama share ko ina fesss, banda kamshin turaren wuta babu abinda ke tashi a parlon, imaan bata kalleta ba ta ajiye abun hannunta fuska daure tace "Ina kwana" xata fita inna tace "Me ya sami idonki ni Asabe? An umaki wani abun ne" Imaan da har ta kai kofa ta juyo lkci daya ta fara kuka tace "Kawai sai kije kice ma daddy ina maki rashin kunya yaushe rabon da in xo nan...." Tana fadin haka ta fashe da matsanancin kuka, Inna da ta saki baki tace "Shine ya maki me?" Cikin kuka tace "Fada ya dinga min mana yace zai yi magani na" Inna ta dau dankwalinta ta fita parlon imaan ta bi ta da kallo tana share idonta, Ko sallama babu inna ta bude kofar parlon, daga daddy har Ammi suka daga kai suna kallonta, tace "Bukar dama yaro ba lallabasa ake yi ba a rayuwar nan, daga mun yi magana tsakanina da kai sai ka taho ka far ma yarinya da bala'i, to ae gwara ita sau dubu a kan sauran, Imaan bar ta da son jikinta amma wllh wllh bata da matsala, haka kawai ka ja mata wani cutan dama gata mai cuta iri iri kamar ta kashe d'an mutum, yanxu da kasa ta kwana tana kuka idan wani abun ya sameta me xa ka gaya ma Allah, kai dai wllh ka cika bala'i, ba haka yayanka Ahmadu yake ba, ba ruwansa da irin wannan hali, to wai ma me ta min da xafi haka da xaka sa ta kuka haka, ga abun duka can Mujaheed me nuna ni da yatsa, mai ce min Hajiya, ni tunda nake wllh xan iya kirga sau nawa Imaan ta mayar min magana shima kuma duk laifina ne....." Ammi dai tuni ta shige kitchen, Daddy kuma ya kasa cewa komai, Inna ta juya ta nufi kofa tana cewa "Wannan dai ba yi bane, kamar ba kai ka haifeta, yar gata daga ita sai ita amma kuma ka takurata, da wanne xata ji da rashin karo mata kanni da ba ayi ba har yau ko kuma da fitinar mahaifinta, kuma ka tashi ka kawo min turaren bature da ko kamshi babu wai in fesa a daki, to uwata bata ce min je ki kya gani ba turaren wuta tsadadde mai kamshi nake nufi, sai ka ba matarka mai kumewa a daki kamar matar liman ta fita kasuwa ta siyo min" daga haka ta fice ta kulle masu kofa. Dama imaan direct gun mota ta nufa bata yarda ta ma bi ta part dinsu ba. Yusuf ne ya ajiye su islamiyyar, karfe sha biyu Anty ta dauko su, A hankali Imaan ta bude kofar parlonsu tana lekan ciki, babu kowa hakan yasa ta shiga ta rufe kofar ta nufi bedroom dinta da sauri, tana kokarin cire Uniform dinta Ammi ta bude kofar, Imaan ta gaisheta kanta a kasa, Ammi tace "Amso min card waje kafin ki cire uniform din" Imaan ta amsa tana kallonta tace "Ammi daddy fa?" Ammi tace "Yana daki" Imaan ta marairaice tace "Ni fa ban gaya ma inna ya min fada ba, kawai taga idona ne haka" Ammi tace "Wannan ya rage naku ke da shi, ni kiyi sauri ki amso min card din" imaan ta maida Hijab dinta ta fita, kiosk din is just a house from theirs, ta amso card din ta juyo ta shigo gida, Umma ta gani tsaye parking space alamar xata fita, Mujaheed ya iso wajen ya bude mata back seat, sannan ya shiga driver seat,  Imaan na hada ido da Umma dama ta dauke kai tayi wucewarta, Mujaheed ya bi ta da kallo ta madubi, Umma ta shiga cikin motar tace "Wllh duk ranan da ka gaida uwar yarinyar nn ko da mistake a gidan nan ban yafe maka ba Mujaheed, duk kanninka ma na karanta masu haka nasan kuma sun dauka...." Yana kallonta ta madubi yace "Haba Umma kema kin san....." Ta karasa masa da sauri tace "Baxa ka iya ba ko? tunda ga ta kanwar Ahmad ko kanwata, Mara tunani kawai da bai san ciwon uwarsa ba, to mu xuba da kai wllh, ba dai makiyana su ne mutanen arxikin ka ba a gidan nan, ka ci gaba, a ta dalilin munafukar uwar yarinyar nan na bar gidan ubanka for good 5 years, ta hade kai da kishiyata suka yi ta kulla min makirci har ubanka ya sakeni, da yake akwai sauran xamana a gidan na dawo few years back na tarar baka da masoya da ya wuce makiyana, ka maida Aisha uwarka, ka nuna duk gidan nan baka da kanwa da ya wuce yarinyar Aisha, yarinyar da bata gaisheni a ynxu ko idona xai makale a nata saboda uwar ta hanata, da kyar da siddin goshi da rokan Allah na rabaka da su, ni da ba a kan idona na haifeka ba kuma ina haihuwar ka aka ajiye min kai a gefe na da wllh bbu abinda zai sa baxan ce canjen ka aka min a asibiti ba, sam baka san mutunci na ba, ace makiyana su ne masoyan ka Mujaheed? Anya kana son gamawa lfya kuwa?" Shi dai ya kasa cewa komai, ta gyada kai ta bude motar ta fice tana cewa "Ga ka ga su ai, daga ynxu ma ka tatttara yanaka yanaka ka koma bangaren nasu" a hankali yace "Umma I have avoid a lot of things a gidan nan kema kin sani, wllh ko kadan bani son abinda xai bata maki rai, don Allah kiyi hakuri...." Ko saurarensa bata yi ba ta fice daga compound din ya sauka ya bi bayanta da sauri. Washegari har Ammi ta gama hada breakfast ta fito daga kitchen imaan bata fito daki ba, ta kalli agogo ganin bakwai da quarter ta nufi dakin ta bude ta shiga, kwance ta ganta ta dukunkune cikin bargo, Ammi ta karasa da sauri ta cire bargon tace "Are you okay Imaan?" Ta bude ido kamar xata yi kuka, Ammi ta dinga kallonta don jikinta ya dau xafi sosai, a hankali tace "Ina ke maki ciwo kuma?" Kafafuwanta ta nuna mata da kai, hawaye cike idonta tace "Ammi duka jikina ciwo, jiya ban yi bacci ba" Ammi ta kamo hannunta cikin sanyin murya tace "Ba ki sha magani ba jiya da daddare ko daughter" ta nuna ma Ammi magungunanta a side drawer tace "Na sha Ammi" saketa Ammi tayi ta mike ta shiga bathroom ta hada mata ruwan wanka ta fito tace "Toh shiga kiyi wanka sai ki kara shan maganin" da taimakon Ammi ta sauka kan gadon, Ammi na rike da ita suka shiga bathroom, bayan ta wanke baki Ammi ta taimaketa tayi wanka ta fito, barin ta tayi ta sa kaya ta tafi hado mata shayi, Daddy na xaune parlor yana dube dube a laptop, ta tsaya bayan kujerar tace "Yallabai jikin imaan fa kar ya rikice mana ko xa aje asibiti tunda likitan ma baya nan" daddy ya mike yace "Bata jin dadi ne" Ammi tace "Nima yanxu na shiga ganin bata fito ba, her temperature is high tace bata yi bacci ba" daddy ya d'an yi shiru, Ammi tace "Kwanakin baya ciwon ya lafa sosai, as from some weeks ago yanxu duk sai ya tasar mata ga xaxxabi da ciwon kai kuma tana shan drugs dinta" Daddy yace "Toh ta shirya mu tafi asibiti" Ammi tace "Toh" komawa yayi ya xauna, ita kuma ta wuce dinning don hada mata shayi. Kwance ta sameta bayan ta sa abayar da ta fiddo mata, da kyar Imaan ta sha shayin, Ammi ta fesa mata turarrukan ta ta bata veil din abayar sannan suka fito parlor, kwanciya tayi kan kujera tana gaida daddy dake rike da makullin mota yana jiransu, ya amsa yace "Sannu mamana, tashi mu je to" mikewa tayi ya kama hannunta suka nufi kofa Ammi na masu Allah ya kiyaye hanya, A hanya daddy ya hadu da Abba ya taho daga part din Inna, gaisawa suka yi, Imaan ma ta gaishesa a hankali, Abba yace "Jikin ne ya tasar mata?" Daddy yace "Wllh kuwa, xa mu je asibiti ne yanxu" Abba yace "Subhanallah tana shan magunguna kuwa" Daddy yace "I think so" Abba yace "Toh likitan ta fa?" Daddy yace "Yayi tafiya ne" Abba yace "Toh tunda Muhammad na nan ba sai ya dinga dubata ba kafin likitan nata ya dawo, ko gwara a tafi asibitin?" Daddy yace "Noo in xai dubata shikenan, dama don likitan baya nan ne xa mu je asibitin" Abba yace "Let me give him a call, na barsa sashin inna, idan ma asibitin xa a sai ya kai ta kawai" Yana kokarin kiran Mujaheed suka hangosa yana tahowa, Abba ya maida wayarsa, har Mujaheed ya isa parking space da suke tsaye kallonsu kawai yake, Ya risina ya gaida Daddy, ya amsa masa da fara'a, Abba yace "Imaan xaka duba Mujaheed, bata jin dadi" Sosai gabansa ya fadi ya kalli Imaan dake jingine da mota duk ta wani langwabe.

 

I appreciate my fan's love always, ina yinku fisabilillah😘😍

Post a Comment for "IMAAN 3-4"