KWAI CIKIN KAYA BOOK 2 PAGE 55
Page 55
.................“Baba bazan iya barin anguwarnan ba sai da ita”. “Bazai yuwuba Jawaad, kaje itama insha ALLAH lafiya zata fito, dana koma yanzu zan fiddotane itama”. “Baba kaima fa bazai yuwu ka zaunaba, dan zamanka akwai haɗari Sadiq zaizo ya ɗaukeku tare, kaje ka haɗa duk wani abunka mai muhimmanci”. “To shikenan ɗana, ALLAH yay maka albarka sai ya zo”.
CIKIN JIRGI
Tun ɗaga gadon farko da Bilkisu tayi jikin Alhaji kokino ya bashi, to amma yasan akwai mai tsaron wajen koma waye tsautsayi ya kaisa sai dai gawarsa. Sai dai kuma ƙarfin gwiwarsa ta sare lokacin da yaga zoben dake a hannunsa yana canja kala zuwa baƙi, gabansa yay matuƙar faɗuwa, gashi babu damar kiran waya, a take komai nasa ya fara kwancewa lokacin da zobe tsafinsu ya shiga hasko masa abinda bilkisu keyi, sai dai ALLAH ya hanashi ganin fuskarta sam sai duhun inuwarta kawai yake gani harta ɗauki tukunyar data ɗauki tsawon shekaru a jiye babu wani mahaluki da ko yatsansa ya taɓa taɓata, sai maman yara da idanunta suka gani itama kuma saida ya sakata tai nadamar hakan, tanama can cikin nadamar ma (Masu karatu Alhaji kokino fa baisan yanzu maman yara bata wajen yaransa ba, dan randa ƴarsa ta saka masa maganin barci koda ya farka a washe gari har an maida masa wayoyinsa, babu wata kuma alama da Jawaad ya bari dazai iya zarga, shikuma da yasan babu wani mahaluki da zai iya masa makamancin haka sai bai kawo komai a ransaba, a washe garin ya bar ƙasar batare da yayi waya da yaransa akan komaiba. ALLAH kuma ya hana shaiɗanun dake taimaka musu fahimtar komai balle shugaban nasu na dodon tsafi damar sanar masa.
Gaba ɗaya ya jiƙe da uwar zufa sharkaf kamar ana masa wanka da ruwan zafi, jiyake tamkar ya rikito jirgin ƙasa dan tsabagen tashin hankalin da yake a ciki, gashi sauransu kusan awa ɗaya da rabi kafin ma su sauka. Lallai wannan ko wanene a cikin gidansa sai ya ƙarar da dukan ahalinsa bama shi kaɗaiba.
Jawaad kam kai tsaye gidan Alhaji babba ya nufa, sun fito masallaci kenan sai ganin Jawaad ɗin yayi ya fito a mota, sai dai yanayinsa yay masifar ɗaga hankalinsa. Tambayoyi ya shiga jera masa, Jay dai bai amsa masa ko gudaba a ciki ba, “Baba wannan ba lokacin amsa tambayoyi bane”. Ya faɗa yana nufar cikin gidan da tukunyar a hannunsa dan da duk a wajen gate suke inda Jawaad ɗin ya faka motarsa. Alhaji babba da ciwon ƙafa ya matsamawa a kwanakin nan ga yawan mafarke-mafarke da faɗuwar gaba da yake yawanyi yabi bayan Jawaad jiki a sanyaye, iskesa yay tsaye tacan bayan ɗakunansu ya ɗaga tukunyar zai fasa bakinsa ɗauke da addu'a. “Kai wai minene kake haka? sai kace wani matsafi?”. Jikake “Tassss!” Jawaad ya buga tukunya da ƙasa.
Fashewarta tayi dai-dai da faruwar abu uku a zahiri, biyu a ɓoye.
Na farko shine saukar jirgin da alhaji kokino ke a ciki bisa ƙasa. Na biyu mummunar faɗuwar gaba ga duk masu alaƙa da tukunyar, na uku faɗuwar Umm-Anum dake a kicin tana dafama Abbu shayi da yake a gidanta yake yau. Na baɗinin kuwa daga can fadar shaiɗancinsu ya faru.
Wasu irin mugayen layune manya-manya guda uku a ciki, sai ƙananun allurai da wasu irin abubuwan surkulle da baisan minene ba shima, sai ruwan kuwa da suke ciki na jini ne sai wani uban wari ya keyi maiban tashin hankali, Alhaji Babba ya waro idanu waje jikinsa na rawa da toshe hancinsa da hannu yace, “Muhammad minene wannan? A ina ka samoshi ni Nuhu?”. Taga-taga Jawaad yay zai faɗi idanunsa a matuƙar jazur, Alhaji babba yay saurin riƙosa. Atare suka sauke ajiyar zuciya, da sauri Jawaad ya zare hanunsa daga na Alhaji babba ya nufi cikin gidan, hankalin Alhaji babba sake tashi yayi, ya kalli tukunyar da kayan ciki ya kalli hanyar da Jawaad yabi, ya juya zai bishi sai gashi ya fito ɗauke da ashana da gallon ɗin fetur na Genretor. Akan kayan ya zuba ya ƙyasta musu wuta. A take gidan ya ɗauki wani irin mahaukacin ƙauri mara daɗin shaƙa, sai ƙananun motsi kamar ana guje-guje, suka hau waige-waige suna dafe kunnuwansu da hannu da sauri, sai kuma aka fasa kuka da wata irin murya mara daɗin saurare. Ana ƙwalla kiran sallar isha'i gidan kuma yay tsitt dan masallacin idan aka kira salla kakanji tamkar a cikin gidan akeyi tsabar kusancin da suke dashi. Jagwab Jawaad ya zauna a ɗan dakalin da aka shuka fulawoyin gidan, ya dafe kansa yana karanto hasbinallahu wani'imal wakil. Sai kuma ya miƙe zumbur saboda tunawa da bilkisu da baba, lallai duk inda Alhaji kokino yake yanzu jirginsu ya isa sauka ƙasarnan. “Baba ina zuwa ya faɗa yana nufar gate cikin zafin nama. Sake binsa da kallo Alhaji babba yayi harya fice.
Jay ya buɗe mota zai shiga saiga drivern gidan Ummah babba ya kawo Batool, baiko kallesu ba duk da ɗaga masa hannu da takeyi ya buɗe motarsa ya shiga tare da yin reverse yabar anguwar da mahaukacin gudu kamar zai tashi sama.
★★★★
Tun ina ɗaukar ciwon kai wasa har ya fara neman fin ƙarfina, dan idanuna sun fara rufewa bana ganin abu da ƙyau, innalillahi wainna'ilairraji'un naketa ambata da sauran addu'oi. A wannan halin lariya ta shigo ta sameni ɗaya daga masu akin gidan. “Larai kije inji hajiya”. Gabana ne ya faɗi, dan a tunanina kodai ta gane wani abune?.
A babban falo na iskesa tsuggune ita kuma tana daga tsaye da hijjab jikinta alamar salla tayi, “Haba dai baba, ai bai kamata ace a darennan zata wuceba, gashi bamu tanadar mata komai ba, kacema wanda yazo ɗaukar nata yayi haƙuri sai da safe sai ya dawo su tafi”. Baba da gabansa ke faɗuwa yace, “To hajiya banƙi ta takiba, amma da anyi haƙuri sun tafin dai babu damuwa, idan ta gama kwanakinta a can ɗin saita dawo nan ta ƙara miki kwana ɗaya daga nan saita wuce”. Shiru tai kamar bazata amsaba, sai kuma tace, “To shikenan na amince da wannan shawarar taka, bara na basu ko kuɗin motane, amma dan ALLAH fa kartaƙi dawowa”. “Insha ALLAHU zata dawo Hajiya”. Kallona tai da ɗan murmushi, “To larai kije ki ɗakko kayanki anzo ɗaukarkine”. Kaina na ɗaga kamar banason tafiyar jikina a sanyaye, ta nufi sashenta ni kuma na nufi ɗakin da aka saukeni na ƴan aiki, ƴar bakko ɗin kayana na ɗakko na fito bayan nama sauran sallama, kaina ne kemin ciwo sosai, dauriya kawai nakeyi.
Dubu biyar hajiya ta bani, nai mata godiya da cewar ai zan dawo na sake mata kwana biyu kafin na tafi, da haka mukai sallama. Muna fitowa daga cikin gidan ana yin horn a ƙofar gate. Wani irin Masifaffen faɗuwa gabana yay, shi kansa baba mai gadi a take ya diririce, saurin nunamin ɗakinsa yay yace na shiga ciki, shi kuma yaje ya buɗe gate ɗin.
Drivern Alhaji kokino ya danno kan motar da sauri, kamar yanda baba ya saba duk sanda ya shigo gidan zaije su gaisa kafin ya shige, yanzunma hakan yayi, sai dai sama-sama Alhaji kokino ya amsama baba maigadi, yay ciki da masifar sauri tamkar zai tashi sama. Drivern ya kalli Alhajin ya kalli baba maigadi yana faɗin, “Anya kuwa lafiya gidan nan yake yau? Tunfa a filin jirgi yake azalzalata kamar wanda akace gidansa naci da wuta”. Baba maigadi yace “kadai bisa da jikkar ka dawo”. Yana ganin drivern shima ya shige yay saurin nufar ɗakinsa, jikkarsa daya gama haɗawa Bilkisu ta haɗo da tata ta fiddo, ƙofa ya buɗe mata ta fice da sauri shima ya rufa mata baya, suna fitowa Jay na isowa wajen, da sauri bily ta buɗe gaba ta shiga baba kuma ya shiga baya, jan motar yay da gudu yabar anguwar.
Da gani har baba muka sauke wata nannauyar ajiyar zuciya. Sai kuma naji hawaye na gangaromin a fuska a hankali, kife kaina nayi saman jakunkunanmu dana shigo dasu kawai na cigaba da kukana, babu wanda yay magana a cikin motar har muka iso, sai sheshshekar kukana kawai.
___________________________________
Ɓangaren Alhaji kokino kam koda ya shigo falon sama yay cikin sassarfa, sam bayama jin sannu da zuwan da ƴaƴansa suke masa harda ma matar tasa. Kaɗan ya rage babbar rigarsa ta taɗesa ya faɗi a step na bakwai, yay azamar riƙe ƙarfen ALLAH ya soshi bai faɗinba.
Matarsa da abin ya girmi kanta tuni ta take masa baya da hanzarinta, sai dai tana zuwa ƙofar ɗakin sai ta jita a datse alamar ya kulle kansa. Duk da bayau ya fara mata hakanba sai taji na yau yay mata zafi, ta shiga buga ƙofar tana ambatar sunansa amma ko tari bataji yayi ba. Tana nan tsaye hankalinta a matuƙar tashe ya buɗe ƙofar da ƙarfi ya fito, jikinsa sai ɓari yakeyi.
“Alhaji lafiya wai?”. Maimakon ya bata amsar tambayarta sai cayay, “Wanene ya shigarmin ɗaki?”. “Alhaji ban gane wannan tambayarba, wanene zai shigar maka ɗakin bayan ni?......” “K!! Bansan iskanci, uban wanene ya shigarmin ɗaki?!!”. Yanda yay maganar tamkar zai haɗiyeta da mugun hargagi kuma sai duk ta firgice, jikinta na rawa ta shiga girgiza masa kai, “Alhaji babu wanda ya shiga wlhy sai ni, sai ko jikar baba maigadi da nasa ta gyara maka saboda aiki yamin yaw.....” wani irin wawan mari ya ɗauke fuskarta dashi jikinsa na rawa. “Sau nawa zanmiki gargaɗi akan saka wani yaymin gyaran ɗaki a gidan nan?!!”. Yanda jikinsa ke karkarwa dolene ya bama mai kallo tsoro, tunda take da shi ko sanda yay auren amaryarsa yana mata wulaƙanci saboda asirin waccan bai taɓa ɗaga hannu a kantaba ko murya irin haka, gashi gaba ɗaya tama lura baya a cikin hayyacinsa, mike damun mijinta haka ne? Mi Larai ta aikata masa a ɗakin da ita bata ganiba? dan yanzu ta shiga ta gama haɗa masa ruwan wanka ta kuma ƙara Air Fresheners a ciki bayan ta shirya masa abinci a dining....
Cikin wata gigitacciyar tsawar ya kuma cewa, “Ina yarinyar take?!!!”. Share hawayenta tayi ta nufo ƙasa tana kiran larai, shima biye yake da ita yana baza idanu da babbar riga yaga ta ina larai zata ɓillo?. Sai dai tun kafin su sakko ƙasan ma ƴaƴansa da ma'aikatan gidan harsun bazu nemanta suma.
“Momy wlhy fa Larai bata gidan nan”. A rikice hajiya tace, “Ban gane bata gidan nanba, yo ina zataje?”. Kafin wani cikinsu ya bata amsa Alhaji kokino yace, “Wai ita laran ƴar gidan uban wacece? Da ga ina kuka samota?!!”. “Dady jikar baba maigadi ce” laila ta bashi amsa a tsorace.
“Maigadi?!!” ya faɗa a wani irin zazzaro idanu, kafinma wani yace wani abu tuni ya fice daga falon zuwa gate, driver kawai ya iske akan bench a zaune yana ƙoƙarin zuba abincin da aka kawo musu daga cikin gidan. “Kai Mati ina maigadi?!”. Yanda Alhaji yay maganar ne ya saka driver sakin plate ɗin abincin ƙasa a tsorace, “Alhaji lafiya kuwa?”. “Ina tambayarka maigadi kana tambayata kafiya?!”. “Ayi haƙuri Alhaji, yana bayi inaga, nima dana fito ban gansaba, nasan dai bazai wuce banɗaki ya zagaya ba”. “Ƙwanƙwasa masa maza ya fito” tashi driver yay ya nufi cikin ɗakin maigadi, sai dai yana taɓa ƙofar toilet ɗin da nufin bugawa sai kawai yaga tama buɗe da kanta, ya leƙa babu alamar mutum, kai da ganima ba'ayi amfani da ruwaba yanzun dan bayin a bushe yake ƙamas. fitowa yay da sauru yana faɗin, “Wlhy bayanan ashe”. Shaƙosa Alhaji kokino yayi yana faɗin, “Idan baya nan dan ubanka ina yaje?!” sosai hankalin kowa ya ƙara tashi, dan ya koma musu tamkar wani zararre. Jikin driver sai rawa yake dan yaji shaƙa, Alhaji kokino ya wullar dashi gefe ya shiga ɗakin da kansa. Hakan yasa Hajiya ta sake take masa baya duk da a tsorace take. Abun mamaki duk kayan baba maigadi babu su, sai abinda ba'a rasaba waɗanda sam basu da wani muhimmanci ga mai su. A yanzune hajiya ta fahimci lallai akwai abu a ƙasa kenan. A fili tace “Mi hakan ke nufi to?”. Cikin tsananin tashin hankali Alhaji kokino yace, “kezan tambaya Nafisa, shikenan kin kasheni Nafisa, taya za'ai har wani ya kawo baƙon ido gidan nan kai tsaye ki yarda da shi harki bashi damar shigarmin ɗaki?!!”. “Wlhy Alhaji ni....” hankaɗeta yay gefe batare da ya jira ta ƙarasa faɗaba, ya fice da saurinsa yabar mata ɗakin, kuka mai tsuma rai ta fashe da shi a ranta tana mamakin miyasa baba maigadi zaiyi haka? Shekaru nawa suka ɗauka tare bai taɓa cutar da suba sai a yanzun? shin minene maigadi yasa Larai ta aikata ne? Ta tuno fitarta ɗazun lokacin da take mata tambaya akan ina taje ita da aka saka aiki? Tabbas ba cikin nutsuwa larai ta bata amsa da cewar yana ta fita sharewa ba, amma da yake bata kawo komai a ranta ba sai bata zargeta ba.
SAUDIA
Hankali tashe Anum ta ƙwala kiran sunan Abbu da Anuwar dake falo suna jiran shayi, har rige-rige. isowa suke cikin kicin ɗin, ganin Umm-Anun yashe a ƙasa yay masifar ɗaga hankalinsu, Anuwar ya tallafo kanta ya aza bisa cinyarsa yana mai fashewa da kuka, Abbu ne yay ƙarfin halin komawa ya ɗakko goran ruwan zam-zam ya dawo, a hannu ya zuba ya shafa mata a fuska. Ta kawo wani irin nannauyan numfashi da gurnani, ƙara ɗiba yay ya zuba mata a fuskar, nanma tagwayen ajiyar zuciya ta sauke a jajjere. Matsawa yay sosai yana ambatar ainahin sunanta, BILKEESU! BILKEESU!!, BILK...... Da sauri ta buɗe idanunta tana amsawa da “Na'am BAB......” sai kuma tai shiru ta kasa ƙarasawa ta kafe Abbu da ido, saurin janyewa tai ta maida kan Anum, sai kuma ta kalli Anuwar da take a jikinsa. Cikin ɗan rawar baki tace, “Jawaad!”. Abbu da Anuwar suka kalli juna, sai kuma suka kalleta, zaune ta tashi tana raba idanu a kansu, sai kuma tai saurin dafe kanta tana faɗin, “Ya ALLAH”. Riƙe mata kan Abbu yayi yana faɗin, “Sannu, kinga tashi muje ɗaki”. Bata musaba ta yarda ya taimaka mata suka fita, sai faman lumshe idanu take saboda jiri.
Kwantar da ita yay a saman gado ya ɗaura kanta bisa cinyarsa, umarni ya bama Anuwar ya ɗakko masa wani magani a ɗakinsa, babu jimawa Anuwar ya dawo, cayay ya zubashi a abin turare, nan danan hayaƙi mai ƙamshi ya fara tashi a ɗakin, shi kuma ya shiga karato addu'oi yana tofa mata. Cikin mintunan da basu gaza biyarba barci yay awan gaba da ita. Duk ajiyar zuciya suka sauke, kafin Abbu ya gyara mata kwanciya suka fito falo suka barta.
Cikin ɗaurewar kai Anuwar yace, “Abbu Yah Jawaad fa ta kira”. “Naji Anuwar, amma lallai akwai wani abinda ya faru inaga, dan yanayinta yayi kama dana wadda ta dawo hayyacinta gaba ɗaya, dan a farko sunan baba zata kira ganin nine yasa tai shiru”. “Abbu to kona kira Yah Jawaad ɗin muji?” kansa ya ɗaga masa alamar eh.
★★★★★★★
Su Jawaad na zaune a falon Alhaji babba sun rufu kan bilkisu da keta juye-juye a ƙasa da kukan kanta suna mata addu'a kira ya shigo wayarsa da Numbers ɗin ƴan saudiyyane kawai a ciki, ɗagawa yay yana miƙewa, daga can Anuwar ya gaishesa, sama-sama ya amsa masa da tambayar “ina Ummuna?”.
“Gata a kwance barci ya ɗauketa, dan tana kitchen zata haɗa mana shayi kawai sai ta faɗi, ALLAH yasa Anum na tare da ita, sai dai abin mamaki ana saka mata ruwa ta kawo numfashi saita fara ambatar Baba saboda Abbu da ya kira sunanta, ni kuma tana kallona saita kirani da sunanka”. Lumshe idanu Jawaad yayi hawaye masu zafi suka ziraro masa saman fuskarsa, kafin yace wani abu yaji maganar Alhaji babba a bayansa. “Mi kuke ɓoyemani?”.
Duk da gabansa ya ɗan faɗi sai ya matsa ya rungume Alhaji babba ya saki wani irin kuka mai tsuma zuciya wanda bai taɓa sanin ya iya irinsaba. Cikin matuƙar tsorata Alhaji babba shima ya riƙesa hannu bibbiyu, “Muhammad karka rikitar dani, minene ya faru dan ALLAH? Kai ne da kuka kuma?”. “Abubuwa da yawane suka faru baba, sai dai dan ALLAH kaimin alfarmar yimaka bazata a kansu daga nan zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu”. “Namaka Jawaad, ALLAH yay maka albarka”. Ɗagowa Jay yayi yana jinjina kai, Alhaji babba ya share masa hawayen, da ƴar tsokana yace, “Yau maza sun koma mata kenan?”. Murmushin ƙarfin hali kawai Jay yay masa, amma bai iya cewa komaiba.
Ciki suka koma inda suka samu Bilkisu taɗan samu barci, tana jikin Batool da bata wuce gida ba. Kallonsu yay sannan ya kalli Bilkisun, “Baba bara mu wuce gida, shi baba zai kwana nan gidan kafin zuwa safiya idan ALLAH ya kaimu, kema Batool ki tashi kije gida dare nayi, amma dan ALLAH karki gayama su Ummah komai sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zakuji koma mike faruwa”. Kanta ta jinjina masa, tace “To ya ya za'ai da mai sunan hajiya, bai kamata a tada taba tunda yanzu ta samu barcin”. “Karki damu bara na ɗauketa kawai”.
Cak ya ɗauki bilkisu duk da yana jin nauyin su Alhaji babba, sai dai babu yanda zaiyi idan ba haka ɗinba. Sallama yay musu ya fito, Batool dake biye da shi ta buɗe masa baya ya kwantar da ita, sannan ya koma mazaunin driver ya zauna, ita kuma ta nufi inda driver ke jiranta. Kusan tare suka bar anguwar. Sai da ya isa gidane yama tuna da Sadiq da ya baro a office, hankalinsa a tashe ya ɗauka waya yay kiransa, bugu ɗaya kuwa ya ɗaga, “Sadiq badai kana nan kana jiranaba har yanzun a station?”. “Ina nan wlhy Oga, harma dasu oga Aliyu”. “Ya salam, kayi haƙuri kaji, ka tafi gida kawai dare yayi, suma kace musu ina gida karsu damu”. Daga can Sadiq yace, “To oga”.
Bayan ya ajiye wayar ya buɗe ya fito, sake ɗaukar Bilkisu yayi zuwa cikin gidan, ya shinfiɗeta a gadon ɗakinsa sannan ya koma motar ya ɗauka wayoyinsa. Kiran Anuwar ya sakeyi, ya tabbatar masa har yanzu Umm-Anum barci take, Abbu ya bama wayar sukaɗan yi magana sannan ya kashe, ya zauna a bakin gadonsa ya tsirama Bilkisu dake barci ido, gani yay harma taɗan rame masa a kwana biyun nan, wani tausayinta ya kamashi, matarsa ta isa a kirata jaruma a ko ina, shi harma baisan yanda zai musalta yaya ya keji a kanta ba, gadon ya hau ya rungumeta a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya a jajjere kamar wanda ya haɗiyi wuta.
DAREN ALKAIRI KO RUƊANI?.
Dolene mu ambaci wannan dare da sunaye masuma yawan da sukafi haka a ɓangarorin mutane masu yawa. Jawaad, Alhaji babba, baba maigadi, Maman Amina, Yaya sule, Abbu, Abu-Siddiq, Anuwar, Anum, aunty Mahfuzah, da wasu gungun mutane sun ƙare wannan dare daga farkonshi har ƙarshensa wajen miƙama UBANGIJI godiyarsu da kukansu, a tsakkiyarsa ALLAH ya bama bilkisu da Umm-Anum damar farkawa suma sukabi ayarin masu bautar ALLAH da raya wannan dare da ƙiyamul laili.
A ɓangaren Alhaji kokino kuwa da duk mai alaƙa da wannan tunkuya wannan dare ya kasance daren tashin hankali da ruɗani a garesu. Babban tashin hankalinma shine kowa ya gaza fasalta kamannin bilkisu a gidan balle ai maganar samun hotonta, sannan baba maigadi tunda suke dashi basu taɓa tambayarsa garinsu ba, abinda kawai suka sani daga ƙauye yake, wane ƙauye? Shine basu saniba, bayan kuma ya kai kusan shekara ashirin yana musu aiki, tsabar bashi bane a gabansu ba basu taɓa bibiyar komai nashi ba a rayuwa, dan shi Alhaji kokino wani irin mutum ne da abinda ke damuwarsa shine kawai mai muhimmanci a garesa. Bai taɓa takaicin wannan baƙar halayyar tasaba sai a yau ɗin nan.
Tun a daren aka baza jami'an tsaro neman baba maigadi, sai dai shiru kakeji, sudai sunce suna kan aikinsu. Daga can kuma tushen tsafinsu sam an kasa ganin inda su Bilkisu suke, abinda kawai suka gani shine an fasa tukunya.
A daren duk wani mai alaƙa da wannan ƙungiya aka sanar masa gobe akwai mitin, duk inda kake dolene ka dawo dan gagarumin mitin ne mai muhimmancin gaske.
SAUDIA
Tunda aka idar da sallar asubahi a ƙasar Abbu ya zaunar da Umm-Anum ya zayyane mata komai da ya sani game da ita dan su gwada suga ko hankalinta ya dawo jikinta sosai. Aiko a take ta shiga rairai masa kuka da roƙon Abbu akan ya kaita wajen ƴan uwanta, tanason tagasu, ita ba zata sake kwana a saudia ba sai ta dangana da ƙasar haihuwarta.
Da ƙyar suka lallasheta shi da Su Abu-Siddiq da su Anuwar. saboda gudun zuwan irin wannan ranar a bazata yasa Abbu bai taɓa sakaci da duk wani abinda zai taimakesa akan fita ƙasar ba idan Umm-Anum ta dawo hayyacinta, dan haka ya bata haƙuri akan ta kwantar da hankalinta zasu tafi a yau ɗin nan komai dare insha ALLAH.
Gari na ƙarasa wayewa suka fita shi da ɗan uwansa Abu-Siddiq, abinka da manyan mutane cikin amincin ALLAH sai gashi cikin awa uku sun kammala dukkan wani abinda ya dace, jirginsu zai tashi ƙarfe sha ɗaya na agogon ƙasar. cike da farin ciki suka kirasu a waya tunkan su ƙarasa akan su fara shirin tafiya. Ai Umm-Anum da Anum sunfi kowa ɗoki, Anuwar kam ai ba'a cewa komai, kayansa ya loda na fitar hankali, a cewarsa saiya more ƙasarsa da ƙyau, ya kuma more ƴan uwansa da bai sani ba. Sudai dariya sukaita masa kawai.
__________________________________
Da safe na tashi Alhmdllh, dan babu ciwon kan sam sai rashin jin ƙwarin jiki, ganin gidan yay ƙura naɗan tashi na fara gyarawa, amma yana shigowa sai ya hanani yace na barsa anjima Nabeelah zatazo ta gyara, yanzu muɗan sake kwanciya zuwa goma saimu fita zuwa gidan Dad zan ɗakko ɗayan wuri ɗin nan da nace na taɓa tsinta.
Haka kawai sai na samu kaina da faɗuwar gaba mai tsananin gaske, dan kuzarin dana tashi da shi ya ida kakkaɓewa gaba ɗaya. Barcin da yaso muyi sai ya ƙauracema idanuna, harma shi yayi nasa ni idona biyu inata saƙawa da kwancewa, ga mafarkin danayi a daren jiya kafin na tashi naga yana salla nima nayo alwala sai dawomin yake a cikin rai. Da tunane-tunane na cinye nawa lokacin barcin, harma goman tayi ya farka. Kallon tuhuma yayta bina da shi akan banyi barciba, na dai fuske abina bance da shi komaiba. Tare mukai wanka, hakama shiri da taimakonsa na shirya dan duk bani da wani ƙarfin zuciya balle akai gana jiki kansa. Muna gama kimtsawa mun fito sai ga Nabeelah da breakfast.
Zama mukai mukaci, koma nace yaymin ɗura, dan ko lauma ɗaya ban iya kaiwa bakina ba, sai da taimakonsa, daga ƙarshema sai na ringayin yunƙurin amai, dole ya ƙyaleni da iya abinda naɗanci muka fita muka bar Nabeelah a gidan akan bazamu jimaba zamu dawo, dan dama ai yau juma'a ce..
Tunda muka bar gidan babu mai iya ƙwaƙwƙwaran motsi, nai shiru inata kallon hanya da sauke ajiyar zuciya, shima haka yay shiru idanunsa a rufe.
Kai tsaye ya bama Sadiq umarnu akan yay horn a ƙofar gate ɗin, haka kuwa akayi, Sadiq yayi horn, sai da baba maigadi ya leƙo, ganin mune sannan ya buɗe gate ɗin.
Kasa fitowa nai sai da ya fita sannan ya zagayo ya fiddoni, jikina ya ƙarayin sanyi, ga hawaye sun cikamin ido, narasa dalilin shiga irin wannan yanayin haka?. Yah Salman da ya fito daga sashensu daga shi sai wando da singlet yay turus yana kallonmu, boss yi yay tamkar baima gansa ba, sai nice nace, “Yah Salman!”. Da ɗan rawar baki ya amsa saboda wata muguwar harara da boss ya zuba masa, kafin ya ƙara da faɗin wani abu yaja hannuna muka shige falon da sallama.
Mom na zaune tayi wujiga-wujiga da waya a hannunta, da alama magana ta gamayi a ciki, sai Aamilah a gefenta ta zabga tagumi. A tare duk suka kallemu da waro idanu na maɗaukakin mamaki da al'ajabi. Bayan boss na koma na laɓe, shiko ko'a kwalar rigarsa murmushi ma yaketa zubawa. Zama yayi ya kamo hannuna ya zaunar a gefensa.
“Mom kun tashi lafiya?”. “Kuka ta fashe da shi kawai tana nunamu da hannu, sai dai tama kasa magana gaba ɗaya. “Kinga kwantar da hankalinki Mom, ba wani abune ya kawomu ba na tashin hankali, abu matata zata ɗauka mu tafi, “Miemaa tashi muje”. Kasa tashi nai dan nima jikin nawa rawar yakeyi hawaye na gudu akan fuskata, ya finciki hannuna yay ciki dani batare da ya saurari Mom ba, Aamilah dama bata iya furta komaiba dan tsorata.
Tsaye Jawaad yay yana kallon ɗakin, dan an bala'in hargitsashi tamkar ɗan adam bai rayu a cikinsa ba. Lallai maganar baba ƙaura ta tabbata. juyawa yay ya kalli Bilkisu da itama tai kasare tana kallon ɗakin da mamaki na gaske. “Ina kika ajiye?”. Hannu ta ɗaga da ƙyar ta nuna masa jakar islamiyyarta da ita kaɗaice zaune a inada ta barta ba'ako motsata ba. Yana ɗora hannunsa akan jikkar Dad da basusan yana garinba ya shigo ɗakin tamkar an jehosa..............🤔😱✍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
Plx anty Billy ataimaka Mana da kwai cikin Kaya page 56
ReplyDeleteHlo sister billy hope dai all is well,don munji ki shiru kwai cikin kaya page 56
ReplyDelete