NOOR ALHAYAT 38
38🐈🐈🐈✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨
Aliyu ya fi minti
goma xaune cikin mota bayan ya iso gida, gaba daya ya rasa me ke masa dadi
duniyar, har ya fita kamanninsa saboda damuwa,
Mumy ta fito jin shiru shiru bai shigo ba, ganinta yasa tun kan ta karaso parking lot din yyi karfin halin bude motar ya fito kansa a kasa, kamar bai son taka kasa yake tafiya, har ya iso
inda take kallonsa Mumy take cos he looks so sick, shi kam ya kasa dagowa balle
ya kalleta, Tace "Abuturrab are you okay, ciwon kan ne har yanxu" ya
gyada mata kai a hankali yace "Na sha magani mum da sauki" daga haka
ya wuceta ta bi sa da ido, bin bayansa tayi tace "Toh bacci ka je clinic
din kake yi?" Bai juyo ba yace "Eh" da damuwa tace
"Maimakon ka tsaya gida ka huta Aliyu tunda baka da lafiya, da sai ka kira
asibitin ka bada uxurin ka, xa ma ka iya dubata yanxu ko kawai mu wuce
asibiti" tsaye yyi bakin kofa ya rasa abinda xai ce mata ya kuma kasa
juyowa duk jikinsa yyi sanyi, Cike da karfin hali yace "Xan tafi asibitin
da ita likita xa su duba ta a can" mumy tace "Toh kai ma gaskiya a
dubaka wani irin ciwon kai ne haka lkci daya tun safe, sanusi sai ya kai ku clinic
din" Bude kofa aka riga sa yi Anty khadijah dake tsaye bakin kofar tana
kallonsa da kyau tace "Me ya same ka kai kuma, baka da lafiya ne?"
Gefenta ya bi ya shiga gidan ba tare da ya bari sun hada ido ba yace "I am
better now" Anty khadijah ta kalli Mumy mamaki shimfide fuskarta tace
"Dama baya da lafiya ne Anty fati?" Mumy tace "Tun safe kafin in
fita aiki yace min yana jin ciwon kai ban san wani kalan ciwon kai bane haka
har yanxu, ni na xata ma baxa shi aikin ba ganin har na fita yana gida"
Anty khadijah ta bi bayansa da sauri ganin har ya kai stairs, ta hada har da
d'an gudunta har hakan ya ba Mumy mamaki, Tsaye Aliyu yyi bakin kofar dakin ya
kasa shiga, ta labe jikin stairs tana jiran ya shiga ita ma ta shiga, a hankali
ya murda kofar ya sa kai ya shiga, Tana ganin haka ita ma ta shige, Baby da ke
xaune gefen Khadijah da ke kwance da damuwa tace "Yayanmu Iman bata da
lafiya she is just crying, and her temperature is very high" hawaye cike
idonta take magana, khadijah na jin sunan da Baby ta kira ta bude ido da sauri
hade da yunkura ta mike xaune, Aliyu ya kasa kallon direction din, wani sabon
kuma khadijah ta saki a raunane, Anty khadijah dai na tsaye kofa tana kallonsu,
Aliyu bai iya ya kalli khadijah ba yace "Ki sa ta shirya xa mu je asibiti
yanxu" baby tace "Toh" daga haka ya juya suka yi ido hudu da
Anty khadijah, tabe baki tayi ta juya ta bar wajen tana cewa "Haka dai aka
iya, da yar uwar ka ce ba lafiya ai baxa ka bi ta kan mu ba ma" shi dai ba
ce komai ba ya fita. Hijab baby ta ba Khadijah, Khadijah taki sawa tana girgixa
mata kai cikin kuka tace "Ni bana son xuwa asibitin, idan nayi bacci I
will okay, baxan iya xuwa ba" baby tace "Nooo, ki sa mu tafi don
Allah" kin yarda Khadijah tayi hakan yasa baby ta fita sai ga ta sun shigo
tare da mumy, mumy ta karaso kusa da ita ta amshi hijab din ta sa mata tace
"Kiyi hakuri ki tashi ku je asibitin kin ji, Allah ya sauke" daga
haka Mumy ta dago ta, Aliyu dai na tsaye corridor yyi backing kofar, muryar
Mumy ya ji tana cewa "Toh ka kai ma Sanusi makullin sai yyi driving din koh"
Juyowa yyi xai yi magana amma ya kasa ganinta tsaye tare da Khadijah tana rike
da hannunta, Wani mugun tausayinta ya dinga ratsa shi ganin irin karfin halinta
cos he was thinking baxata iya fitowa ba, bai yarda sun hada ido ba kamar yanda
ita ma kanta ke a kasa, ya fara sauka stairs Mumy ta bi bayansa tana rike da
hannun Khadijah baby na biye da su a baya, Anty khadijah dake tsaye bakin kofar
dakinta ta saki baki ta bi Khadijah da ido a ranta tace wa yaga boss lady, don
kusan kalau take tafiyar ta, nan kuwa daga ita har Aliyun basu san mugun karfin
hali take ba, she is in pain all over, only trying her best to be okay, Mumy ta bude bayan motar ta shigar da ita
tasa baby ma ta xauna a baya kusa da ita, sanusi ne ya ja motar cos da gasken
Aliyu bai jin xai iya tukin, har suka isa asibitin kansa na jingine da kujera,
baby kuma na rungume da Khadijah da ta ki bude ido tana kukan xuci. Sanusi na
parking Aliyu ya bude motar ya fita, Baby ta fito tana kallon khadijah tace
"Iman ki sakko we are at the hospital" A hankali khadijah ta fito
cikin motar tana rike da hannun baby, Aliyu ya kalli baby yace "Ku koma
tare da sanusi" xaro ido tayi tace "Yaya but Mumy tace in tsaya da
ita, wa ye xai tsaya kusa da ita idan anyi hospitalising dinta, look shes very
sick fa" irin kallon da ya dade bai mata ba ya shiga yi mata a lkcn, Bata
sake cewa komai ba ta shiga motar hawaye cike idonta, Khadijah ta fashe da kuka
a hankali tace "Don Allah kar ki tafi ki bar ni" Baby na share
hawayen ta tace "He said I shud leave Iman" Aliyu ya juya ya wuce
ciki sai ga nurse ta taho ta shiga da Khadijah asibitin, sanusi ya ja motar
yana ma khadijah Allah ya sauwake ya kama hanyar gida. Nurse din na rike da
hannun Khadijah da ke ta hawaye ta wuce office din Aliyu da ita kamar yanda yyi
instructing dinta, baya office din hakan yasa ta fito ta shiga office din kusa
da nashi ta samesa xaune, ruwan xafi yasa ta fara kai ma khadijah bathroom
dinsa tayi wanka sannan ya bata magunguna da alluran da xata mata, daga haka
kuma ya bar asibitin, kulawa sosai nurse din ta bata don ta bata tausayi yanda
ta ga jikinta duk da ba ta san takamaiman abinda ke damunta ba, tana mata
alluran kuwa bacci ya dauketa nan dakin Aliyu. Aliyu na gidansa har ya samu
bacci ya daukesa.... ring din wayarsa ya tashe sa, dubawa yyi da kyar ya ga
Mumy ce, ya kai hannu ya daga a hankali ya kai kunne, da damuwa tace
"Aliyu ya jikin Khadijah, or shud I come over naji shiru shiru" yace
"Noo mum, da sauki anjima sanusi yaje can asibiti ya mai da ta gida"
Mumy tace "Kai kana ina?" Ya d'an yi shiru kafin yace "Na taho
nan gida na ne, I need sleep" da mamaki mumy tace "Kuma ka bar ta ita
kadai asibiti gashi ka ki barin Baby ta xauna da ita Abuturrab" yace
"Nurses din xa su kula da ita mum" Mumy ta d'an yi shiru kafin tace
"Toh shkkn, Allah ya sauwake, kai ya jikin naka?" Yace "Alhmdllh
am better now" tace "Ohk, amma da ka daure kai ka je ka maido ta gida
don Allah, bbu dadi hakan kamar bata da gata, idan baxa ka ba ni in je"
yace "Toh mum xan je yanxu kiyi hakuri" daga haka ta yi masa sallama
ta katse wayarta. Bayan magrib Aliyu yyi wanka bayan yyi sllh ya canxa kaya ya
bar gidan, yana isa clinic din ya kira nurse da ya bari da Khadijah a waya yace
tayi mata alluran karshe na ranan ta fito tare da ita yana waje, nurse din tayi
yanda yace sannan suka fito tare da Khadijah, bin nurse din da ke rike da
hannun ta take kamar iska xae kadeta ta fadi, duk ta rame lkci daya, yana
kallon nurse din bayan sun iso a hankali yace "Hope you did all what I
instruct you to" nurse din tace "Yes but, I don't knw why she's
finding it difficult to walk, kuma tun daxu take complaining chest pain, Dr
bashir ya bata magani dai daxu, har da shi ma cikin wa ennan" ta fadi tana
nuna masa drugs din da Khadijah xata kai gida, Khadijah dai na tsaye kanta a
kasa duk a tsorace take ga xuciyarta dake bugawa da sauri da sauri, Aliyu ya
gyada kai yace "Thanks nurse Maryam" Nurse din tayi murmushi ta sa
Khadijah ta shiga gaban motar ta rufe tana mata Allah ya kara lfya, tada motar
Aliyu yyi ya bar haraban hospital din, har suka isa gida bai ce komai ba, yana
lura da hawayen da take yi tana gogewa da Hijab dinta tun bayan da suka fito
clinic har ynxu da suke gida, ya gama parking ta bude motar a hankali ta fita,
ya bi ta da ido ganin yanda take tafiya har ta shiga gida, sae sannan shi ma ya
fito ya rufe motar ya shiga gidan. Mumy dake xaune parlor da su siyama da Anty
khadijah ta mike ganin Khadijah tace "Sannu khadijah, ya jikin"
Khadijah ta kasa dago kanta tace "Naji sauki Mumy" Anty khadijah sai
kallonta take babbu kiftawan kirki, Aliyu na shigowa parlorn ya haura sama,
Mumy ta kama hannun Khadijah ta wuce sama xuwa bedroom dinta da ita, da kyar
khadijah ta iya cin pepper soup din da mumy ta mata, duk bakin ta babu dadi, a
nan dakin bacci ya dauketa. Cikin dare misalin karfe biyu xaxxabi ya kuma rufe
ta, dakin Aliyu Mumy ta shiga ta samesa xaune kan darduma ta xauna gefen gado
ta jira ya sallame sallahn da yake da damuwa tace "Aliyu har yanxu fa
jikin Iman" yace "Xaxxabin kuma?" Mumy tace "Ehh dama"
yace "Mumy to ta kara shan drugs din..." Mumy tayi shiru bata ce
komai ba, can tace "Toh shkkn" sannan ta mike ta fita, magungunan ta
sake bata ta rufe ta da duvet sai kusan asuba bacci mai nauyi ya dauketa. Da
safe tea Khadijah ta sha bayan mumy ta tilastata da kyar, da tayi ma Aliyu maganan
alluranta da ya rage yace driver ya kai ta sai karfe goma shi xai fita aiki,
sanusin ne ya kai ta ya maido da ita, kafin yamma taji saukin jikinta sosai sai
dai ta rasa irin ciwon da take jin kirjinta ke mata, kuma hakan na faruwa ne in
dai ta tuna incident din ranan sai taji mugun faduwar gaba, har lkcn Aliyu bai
barin su hada ido a gidan kuma bai ce mata komai, idan tana wuri ma bai yrda ya
tsaya a gun, Anty khadijah dake lura da komai har wani farin ciki da nishadi na
musamman take ji a gidan, har Mumy ta dinga mamakin yar uwar tata, duk fadace
fadace da xage xagen ta rage yanxu hatta Khadijah ta daina hantara nan ko
shirin sake komawa inda taje kwanaki kamar yanda aka ce mata ta dawo idan ta
tabbatar komai ya wakana a lkcn ma xa a fara aikin, tunanin karyan da xata yi
ma Mumy kawai take ta tafi inda xata. Aliyu na bedroom dinsa da daddare baby ta
shigo, ta xauna kusa da shi tace "Yayanmu I want to ask you something
pleaseee" yana kallonta yace "What?" Ta langwabar da kai a hankali
tace "Iman tayi maka wani laifi ne, naga you no longer talk to her, ko ta
gaisheka sometimes you do pretend you didn't hear, why please, ka gaya min me
tayi maka, gashi ita ma she is always sad yanxu, I've caught her severally tana
kuka cikin dare..." Katse ta yayi yace "Na fara wasa da ke da yawa
koh?" Da sauri ta girgixa masa kai, ya hade rai yace "Toh tashi ki
tafi" mikewa tayi da sauri ta fita ya ci gaba da danne dannen laptop da
yake yi. Washegari da sassafe Anty khadijah ta shirya har da kwallarta take ce
ma Mumy xata Abuja an kirata wai Yusuf d'anta ba lafiya yana asibiti, mumy
jikinta yyi sanyi har da bata dubu goma ta hau mota, ta karba ta yi mata godiya
ta bar gidan. Karfe goma saura Mumy ta tafi aiki gidan ya rage khadijah da baby
sai Iklima don su siyama sun tafi makaranta, Aliyu ma na sama a dakinsa, tun
bayan abinda ya faru tsakanin khadijah da Aliyu ta rage xaman cikin gidan sae
Mumy na nan, always a baya xaka ganta xaune ita kadai, yau ma xaune take tayi
nisa a tunanin da take kamar ance ta juya taga Aliyu tsaye d'an nesa da ita,
mikewa tayi a tsorace tana komawa baya, ya dauke idonsa daga kallonta yace
"Iman" hawaye ya cika idonta ta kasa amsawa, karasowa yyi kusa da ita
ya tsaya tana komawa baya a hankali, yace "Za ki gane gidan step mum din
ki?" Khadijah sai kallonsa take xuciyarta na bugawa, ya hade rai yace
"Am asking" a hankali tace "Kila in gane" yace "Ohk...
Am coming back now" daga haka ya juya ya koma ciki, ba a dau lkci ba ya
dawo, envelope ne rike hannunsa ya mika mata taki amsa gabanta sai faduwa yake,
yace "Collect it" hannunta na rawa ta karba, yana gyada kai yace
"Go Iman, go back to ur step mum, I can't continue my life the way I want
living with you in the same roof, you are now a barrier to my happiness pls ki
tafi Iman go anywhere, leave our home, bana son Ina ganinki ina jin haushin kai
na cos nobody is above mistake, just go plss" A hankali ta juya masa baya
hawaye na sakko mata tace "Ohk xan tafi... thank you very much for all
what you've done to me throughout my stay in your home, Allah saka maka da
alkhairi duk hidiman da ka min, but ina neman alfarmar ko xan iya yi ma Mumy
sallama kafin in tafi, don ban mata hallaci ba idan na tafi bata sani ba"
a takaice yace "Noo, just go Iman" ta fashe da kuka sosai tace
"Ohk nagode" juyawa yyi ya nufi cikin gida... Sai kuma ya juya da
sauri yana kallonta yace "And one more thing... Forgive me plss" ta
juyo hawaye na sakkowa idonta tace "I have done that already" yace
"Thank you" daga haka ya juya ya shiga ciki ya rufe kofa. Share
hawayen idonta da ya ki tsayawa ta dinga yi, dama Hijab ne jikinta kawai ta
nufi gate ta fita gidan, da kafa ta karasa bakin titi ta samu napep tana
kallonsa a hankali tace "Tasha xaka kai ni" yace "Toh" daga
haka ta shiga napep din, har suka isa tasha bata sani ba tayi nisa a tunanin da
take, mai napep din ya dawo da ita duniyar tunanin da taje, sai a sannan ta
tuna kudin da xata basa, da sauri ta leka cikin envelope din da Aliyu ya bata
taga kudi ne me yawa a ciki ta xaro dubu daya hawaye na sakko mata ta shiga
tashar ta nufi inda taji ana kiran kano, dama mutum daya ake jira tana shiga
motar ta bada kudinta bbu bata lkci suka dau hanyar kano.Mumy ta fito jin shiru shiru bai shigo ba, ganinta yasa tun kan ta karaso parking lot din yyi karfin halin bude motar ya fito kansa a kasa, kamar bai son taka kasa yake tafiya, har ya iso
Please how can I get the complete novel?
ReplyDeleteFill the contact form with functioning email. I wll send it to you
DeleteFill the contact form with functioning email. I wll send it to you
Delete