NOOR ALHAYAT 31
Ranan Monday da asuba
Mumy ta shiga kitchen gun kyauta dake ta kokarin hada ma yan makaranta
breakfast, cike da ladabi ta gaida Mumy, mumy ta amsa tana mata sannu da aiki
sannan tace "Khadijah bata tashi ba?" Kyauta tace "Ina jin tana
can tana sallah
ne" kyauta ta dai fada haka ne amma in dai khadijah tasan
tana can tana bacci, Mumy tace "Wai boko nake son ta fara xuwa yau..."
Kyauta ta xaro ido tace "Boko Hajiya, Allah ya saka maki da alkhairi, ya
kara daukaka, Allah ya biya maki bukatun ki masu kyau Hajiya, yanda kike
taimako kema Allah ya ji k'an ki a nan duniya da ma lahira" Mumy da ke ta
kallon kyauta tayi murmushi tace "Toh Ameen" daga haka ta juya ta
wuce, kyauta ta rike ha6a baki bude murya can kasa tace "Ko ya baxawara
xata dau xancen nan idan ta dawo, Ashe ko akwai karamin yaki a gidan nan"
a stairs mumy ta hadu da Aliyu ya shirya xai fita aiki, tace "Da asuban
xaka fita aiki?" Yyi kasa da kai ya gaisheta ta amsa tare sa cewa
"How was ur nyt?" Yace "Alhmdllh" tace "Breakfast din
fa?" Yace "Xan yi a office" tace "Bawan Allah ai bbu xancen
yin sammakon fita aiki xaka kai khadijah makaranta anjima" Juyowa yyi ya
kalleta da sauri yace "A'a ni Mumy baxan iya xuwa ba, Ba ga sanusi ba da
mai aikin can su kai ta mana" kallonsa mumy ta tsaya yi, can tace
"Directly ma kake ce min baxa ka iya xuwa ba koh?" Yace "Toh
Mumy ni da xan fita aiki kuma wani makaranta xan kai ta, komai fa sanusi xai
iya yi kin sani" Mumy bata kuma saurarensa ba tayi wucewarta sama,
fuskarsa daure ya juya ya koma sama shi ma. Tun da kyauta ta tada Khadijah tayi
mata albishir din xancen da Mumy tayi mata khadijah ke ta murna har da rawanta,
can kyauta dake taya ta murnar ita ma ta hade rai tace "Wato ni ce dai
hajiya bata so a gidan nan ba arabi ba boko, sai dai in sauke in daura in yi
shara inyi wanke wanke, akwai Allah" khadijah da har xata shiga bathroom
ta dawo da sauri ta yo waje da ido tace "Anty mai girki? Katuwa da ke baki
gama school ba dama, me kika tsaya yi toh?" Kyauta ta dunguri hancinta
tace "Ai ban kai baxawara ba da take kamar buhu" Khadijah ta wara ido
tace "Ni kinsan yaushe rabon da in je school, to in gaya maki tun ina
gidanmu tare da Ummata, Allah ya sa ban girma ba da shikenan yanxu ni ma baxan
je ba" bata sake sauraren kyauta ba ta shiga bathroom da sauri ta rufe.
Kafin karfe bakwai duk yaran gidan sun shirya kyauta ta tabbatar khadijah ma ta
shirya cikin daya daga kayan da ta siyo mata a kasuwa shekaranjiya ta lafta
mata uban kwalli a ido, ta shafa mata jan powderta a fuska, Da kyar khadijah ta
yarda xata yi breakfast saboda excitement, duk ta kagu su wuce makarantar, shi
dai Aliyu na xaune parlor hannunsa rike da mug din coffee, su siyama kuma na
dinning suna breakfast, Khadijah kuma na kitchen kyauta ta shimfida mata wani
xaninta a kasan tiles din kitchen din don kar kayan jikinta yayi stain, jin
Driver na horn a waje Kyauta ta daga khadijah da sauri ta kwace bread din
hannunta ta turata waje tana cewa "Shegiya sai ta sa sun canxa ra'ayinsu
maxa tafi xa su wuce" Aliyu ya fita ya samu Driver yace "Sanusi ni
xan kai su, don't worry" Har su Siyama sun fita Sanusi ya gaya masu abinda
Aliyu yace, Siyama ta tabe baki hade da jingina da motar tace "Shine yana
ganin mun fito baxai gaya mana ba, I don't just like this Ya Aliyu
sometimes" Aneesah tace "Ni kuma ina son sa haka, ya ma fi min ya
Saleem" Siyama tace "Shi yasa nake ta addu'ar ya saleem su dawo tare
da Abba anjima" Motar Aliyu suka nufa, baby da fitowarta kenan ta bi
bayansu, Aliyu ya wuce upstairs dakin mumy ya sameta har ta shirya xata kai
khadijah makarantar da kanta, ya d'an bude ido yace "Mumy kin fa san I
didn't mean it, ko baki fada ba ai xan kai ta..." Ta katse sa tace
"Toh tunda Allah ya ban lafiyata ba gwara in fita in biya ma kai na
bukatar dake gabana ba, Saleem will Neva look into my face yace min baxa shi ba
ai, so this is just ur differences" Aliyu yayi kasa da murya yace
"Toh kiyi hakuri Mumy, ban san ran ki xai baci ba, I am very sorry"
tace "Noo ni rai na bai baci ba, kai dai da na bata ma rai xaka iya tafiya
aikin ka kayi hakuri, ni da ya xame min dole xan kai ta da kai na"
murmushi yayi yace "Don Allah mumy kiyi hakuri ni xan kai ta ba sai kin je
ba" da kyar Aliyu ya samu ya lallaba Mumy ta hakura ta bar shi ya kai
khadijah makaranta tare da Kanninsa, babu yanda bata yi ya amshi wayarta ya
masu transfer din duk fees din a can makarantar ba ya ki yace xai yi da nasa
kudin, da haka dai ta hakura ta kyalesa ya sakko parlor rike da makullin motarsa,
makale ya tadda Khadijah jikin kofar parlor da alama su siyama dai sun korota
ne, Kyauta ma na bakin kofar bayan sanusi yace mata Aliyu ne xai kai su, sai
leken su siyama take tana Allah wadaran da halin baxawara da suka yi, tana
ganin Aliyu tayi tsit, tayi kasa da kai tace "Sannu da fitowa
yallabai" yace "Yauwa" sannan ya fita, tura khadijah tayi ta
rufe kofar parlorn. Khadijah ta dinga bin Aliyu har suka isa gun motarsa, su
siyama suka yi shiru daga xancen da suke ko wacce na kallonsa, Yace
"Wacece ta korata a cikin ku?" Da sauri baby tace "Allah ya so
bani bace ba wllh yayanmu" yana kallonta yace "Toh waye?" Nuna
masa su Aneesah tayi, yace "Why did u both send her away?" Aneesah
tace "Toh yaya kawai ta xo gun mota ta tsaya mu da makaranta xa mu"
yace "Ita ma makarantar ae xata" Da sauri siyama tace "What???
Wani makarantar?" Baby tace "Na mu mana, ai Mumy ta gaya min da na yi
wanka a dakinta daxu" Siyama da ta rikice tace "Yaya kamar ya
makarantar mu, ni yaya ko xa a sa ta makaranta let it not be ours, they are a
lot of schools out there don Allah a kai ta" Har da guntun hawayenta,
Aneesah ma duk hankalinta ya tashi, ita dai khadijah na daga gefe tana
kallonsu, yace "Alryt idan na kai ta makarantar taku kada ku bari ayi
admitting dinta" daga haka yace baby ta shiga mota, baby ta shiga gaba ya
bude back seat yana kallon khadijah yace "Get in" da sauri ta shiga
motar ya rufe ya bude driver seat ya shiga yana kallonsu siyama yace "Ku
je sanusi ya kai ku coz xan iya maku abinda ke raina idan ku ka shiga motar nan,
mind u kada warce ko da wasa ta sake shiga cikin gidan can, it's either ku je
sanusi ya kai ku makaranta or you remain here till 4" daga haka yayi
warming motarsa mai gadi ya bude masa gate ya fice daga gidan, siyama ta fashe
da kukan takaici Aneesah na taya ta. Essence int'l school, abinda khadijah ke
ta nanatawa kenan a xuciyarta tun shigiwarsu cikin babban makarantar, baby ta
bude kofa ta fita, ya juya yana kallon khadijah, xaro ido yyi yana kallon nata
idon yace "Meye wnn din a idon ki?" Ta buda hannu tace "Anty mai
girki ce ta sa min kwalli" tsaki yyi ya Ciro handkerchief a aljihunsa ya
mika mata yace "Common goge wannan bakin abin da ta goga maki a ido kamar
herbalist" khadijah ta kyalkyale da dariya ta karba tace "Herbalist
kuma" bai tanka ta ba ta shiga share kwallin, jawota yyi ya fixge
handkerchief din a hannunta ya fara goge mata idon, sai bata fuska take xata yi
kuka, ya hade rai yace "What?" A hankali tace "It's
painful" yace "Good... Next time idan xata sa maki baxa ki yarda
ba" ajiye handkerchief din yyi bayan ya tabbatar bbu sauran kwallin a
idonta ya fita, ita ma ta fito ya wuce direct office din principal din
kasancewar shi ma makarantar da yyi kenan, kuma har lkcn ba a canxa principal
ba, da ladabi ya gaisa da principal din da shi ma yyi murnar ganinsa sosai, nan
Aliyu ya sanar masa ya xo enrolling khadijah ne, principal din ya tambayi
khadijah class din da take xata ce jss2 Aliyu yyi saurin cewa Jss3, xaro ido
tayi ta kallesa ya mata wani kallo ya ci gaba da yi ma principal din bayani, farkon
abinda principal din ya bukata shine transfer letter daga previous schl dinta,
Aliyu ya d'an yi jim, can yace masa xai karbo ya kawo, da yake principal din ya
san shi yasan family dinsu bai masa gardama ba, nan kuma yasa aka yi
interviewing dinta, babu bata lkci kuma aka yarda a sa jss3 din coz she is
capable, a take Aliyu yyi transfer din school fees da other fees da ake biya na
makarantar har takardu da uniforms guda uku, Principal na kallonta xai cike
mata receipt yace "What's ur name" kafin Khadijah tace komai Aliyu
yace "Khadijatul Iman" Khadijah ta xaro ido tana kallonsa, principal
din yace "Surname" sai a sannan Aliyu ya kalleta, ta langwabar da kai
a hankali tace "Muhammad" principal din ya so aliyu ya maida ta gida
gobe tayi resuming yace A'a ta fara yau din shi aiki xai wuce ba gida ba, a
tare suka fito da Khadijah office din principal din bayan yace Aliyu ya nuna
mata ajinta, Tana biye da shi a baya ya juya yana kallonta yace "Wani
makarantar kika yi primary da jss1?" Tace "Yan dutse" yace
"Kano?" Ta gyada masa kai, bai sake cewa komai ba har ya isa class
dinsu Baby ya nuna mata ta shiga tana daga masu hannu, ya juya ya tafi gun da
ya bar motarsa. Karfe hudu saura driver ya ajiye su a gida, sai da su siyama
dake ta kumburi cikin motar suka fita sannan khadijah ta fito rike da ledan
uniforms dinta da takardu, Baby ma ta fito rike da sauran takardun khadijah,
Duk sai da kyauta ta bi ta yi ma uniforms din tsirara daga ledansu tana washe
baki tace "Yarinya ta xama yar boko, toh me suka koya maku yau a
makarantar" Khadijah tayi dariya tana cire kayan jikinta tace "anty
mai girki yanxu xan yi wanka ne, idan na fito xan koya maki" daga haka ta
shiga bathroom da sauri, har daki kyauta ta kawo mata abinci bayan ta xuba ma
su siyama nasu a dinning, khadijah dake ta kallon pepper soups kala kusan uku
da ta xubo mata tace "anty mai girki, kinyi girki da yawa kenan yau?"
Kyauta tace "Ke Alhaji da kanin Aliyu xa su dawo anjima, yanxu haka suna
can cikin jirgi a sararin samaniya, ai girkin da nayi ya fi kala shidda yau tun
safe nake kitchen, na kuma ji Hajiya nacewa kila baxawara ma ta dawo yau"
Khadijah ta tallabi cin dinta tace "Waye Alhaji anty mai girki?"
Kyauta ta hade rai tace "Babansu Aliyu mana" Khadijah ta xaro ido da
mamaki tace "Dama yana da baba, ai na xata shine baban gidan" Kyauta
tayi tsaki tace "Dadina dake shegen shirme, toh an ce maki shi ya haifi
kansa, ubansa nace maki xai dawo anjima tare da kanin sa saleem" Khadijah
ta turo baki tana d'and'ana naman ragon gabanta tace "Toh naji" Baby
ce ta shigo dakin bayan Khadijah ta gama cin abinci kyauta ta fita da plates
din, baby tace "Mumyna tace in kira ki" Mikewa Khadijah tayi ta bi
bayanta suka wuce sama, tun bayan da Anty khadijah ta koreta sai ranan ta sake
hawa saman gidan, baby ta bude kofar dakin mumy ta shiga, khadijah ta tsaya
daga bakin kofa tana lekan dakin, Mumy da ta hangota tace "Shigo
khadijah" khadijah ta shiga ta xauna kasa tace "Ina yini Anty"
mumy tace "Lafiya lau, ya school din" Khadijah tayi murmushi tace
"I like it Anty" Mumy tace "Sun baki uniform?" Khadijah ta
gyada mata kai, Baby tace "Mumy same class fa muke da ita" Mumy tace
"That's good, ina books din da suka baki" mikewa Khadijah tayi da
sauri ta ce "Xan dauko" daga haka ta koma kasa ta dauko books din ta
ajiye ma Mumy, Mumy na kallon book din ganin Iman a jiki tace "Iman? Is
that ur name?" Khadijah tayi murmushi ta gyada mata kai a hankali, mumy
tace "Maa sha Allah" wani sabon jaka da bakin cover shoe da socks uku
mumy ta dauko ta mika ma khadijah tace "Gashi sai ki xuba books din
ciki" khadijah ta wara ido tace "Anty nagode, thank you" Mumy
tace "Welcm, tashi ki tafi" mikewa khadijah tayi cike da murna ta
fita, baby dake kallon mumynta tace "Mumy ni yaushe xa ki siya min sabon
jaka?" Mumy tace "Soon" har kitchen Khadijah ta kai ma kyauta
abinda mumy ta bata, kyauta ta amshe tana washe hakora tace "Allahu Akbar
barin baxawara gidan nan ya maki rana dije, Allah ya makaleta a duk inda take
har Hajiya ta gama dake ta dawo kai na nima" Shigowar Aneesah kitchen din
yasa Kyauta tayi shiru sum sum ta fita don kai kayan daki Khadijah na biye da
ita a baya. Suna shiga dakin ko minti biyar ba ayi ba aka kwankwasa kofa kyauta
ta tashi da sauri ta bude, Aliyu ne tsaye rike da wani jakar mai kyau ya mika
ma kyauta yace "Gashi ki bata" kyauta ta risina ta karba tace
"Toh ta gode, Allah saka da alkhairi" bai ce komai ba ya juya ya bar
wajen, kyauta ta bude jakar jin da nauyi ta ga takalma har biyu da safa uku a
ciki sai water bottle irin nasu baby, kyauta ta rike haba tace "Ni dai ce
ba a so a gidan nan wllh" Khadijah dake jera books dinta a jakar da mumy
ta bata ta taso da sauri tace "Anty mai girki menene" Kyauta ta
dungura mata tace "Duk kin fi ni goshi wllh" Khadijah ta kyalkyale da
dariya ta karbi jakar da a gabansa aka rubuta *Iman* ta wara ido tace
"Waowww"
Post a Comment for "NOOR ALHAYAT 31"