NOOR ALHAYAT 29
Washegari thursday Kyauta xa ta kasuwa tare da Khadijah
bayan Mumy ta fita aiki, Anty khadijah kuma ta fita anguwa, Aliyu kadai suka
bari gidan kasancewar night duty yake yanxu, da ido ya bi su har suka fita
parlorn, Driver da xai kai su kasuwar ya tada motar ganin sun fito, Daya daga
dogayen riguna Umma ta siya ma
khadijah ne jikinta sai hula da Kyauta ta sa
mata ta bata karamin mayafi ta daura a kan, Khadijah ta karbi list din abubuwan
da xa su siyo ta dinga karanta su kyauta na jifanta da hararan wa ya sa ta?
Driver Sanusi yace "Wai wannan yarinyar madam tace mu je tare da ke ayi ma
siyayya?" Kyauta tace "Ehh ita ce" Drivern yace "Kin ga shi
kenan sai ayi mata gaba daya koh? Daxu ta bani dubu ashirin da biyar kafin ta
fita" kyauta tace "Ka ji sanusi da wani xance, cefane fa xa mu je yi
ba kasuwar kaya ba" Sanusi yace "Toh shkkn, gobe sai mu je kasuwar
kayan" sai kusan karfe daya Kyauta ta gama duk siyayyar da xata yi suka
dawo gida, babu kowa gidan har Aliyu ma ya fita, nan ta daura girki a gurguje
Khadijah kuma ta tafi yin sallah kamar yanda tace mata tana idarwa taki fita
tayi kwanciyarta. Karfe Uku da rabi su Siyama suka dawo gida, kyauta ta xuba
masu abinci gaba daya ta kwashi uniform dinsu ta kai gun wanki, baby kadai ce
parlor ta sa cartoon tana kallo da plate din abincin a hannunta da yake bbu
islamiyya, su Siyama kuma suna can kan dining, khadijah ta fito daga daki
tashinta daga bacci knn ta makale jikin bango tana kallon Cartoon din da baby
ke kallo, Baby na ganinta ta kashe tvn da remote ta hade rai, shiru khadijah tayi
bata ce mata komai ba, su Siyama suka fara dariya suna kallon khadijah dake
tsaye, bude kofa aka yi duk suka juya Aliyu ya shigo parlorn Baby ta kallesa
tace "Yayanmu sannu da xuwa" ya karaso parlor ya ajiye makullin
motarsa saman table ya xauna tare da jinginar da kansa da kujera yace "Ya
school, yau ba islamiyya sai kallo koh" baby bata ce komai ba ta kai fork
dake dauke da taliya bakinta, ya kalli TV yace "Wa ya kashe television
din" Baby ta nuna masa khadijah tace "Ko ba ita bace take kallon
cartoon din da nasa, tell her to get away" kwace remote din yyi ya kunna
tvn yana hararanta, Tayi shiru bata ce komai ba, yace "Wawiya kawai"
daga haka ya mike yyi wucewarsa sama, baby ta hade kai da gwiwa xata yi kuka,
juyawa khadijah tayi ta wuce kitchen, su Siyama suka bi ta da harara. Khadijah
na ta tsaye kitchen tana kallon naman da kyauta ta daura yana ta soyuwa a cikin
mai kyauta kuma na can waje, jin an shigo kitchen din ta juya da sauri taga
Aliyu ne, cup ya dauka ba tare da ya kalleta ba yace "Have you eaten?"
Kai ta gyada masa ita ma bata kallesa ba, sai ga kyauta ta shigo kitchen din,
ganin Aliyu tayi saurin cewa "Sannu da xuwa yallabai, in kai maka
abinci" ya juya ya nufi kofa yace "A'a nagode" khadijah tayi
narai narai da ido tace "Wallahi anty mai girki ni ban kulasa ba shi ne
yyi mun magana ki tambayesa ma ki ji" da sauri kyauta ta tura kofar
kitchen din ta rufe ta daura hannu a ka tana xaro ido tace "Na shiga uku
ni kyautar Allah, yanxu 'yar nan me nace maki xaki ja min salalan tsiya?"
Khadijah tayi shiru tana kallonta, kyauta ta bude kofar kitchen din ta turata
waje tace "Tafi ki ban waje ni dai" turo baki tayi ta juyo taga Aliyu
xaune parlor da baby dake sulking har lkcn, ta wuce daki tana ci gaba da turo
baki. Da daddare khadijah ta fito wanka tana daure da xanin da kyauta ta bata
ta dinga wanka, kyautar kuma na tsaftace kitchen aka bude kofar dakin, Anty
khadijah ce ta shigo baby na biye da ita a baya, kana ganin Khadijah kasan ba
karamin tsorata tayi ba ganinta, Anty khadijah ta riko duk hannayenta biyu da
hannu daya fuskarta kamar bai taba ganin ruwan alwala ba tace "Don kaza
kazan ki kinsan matsayin yarinyar nan a gidan nan?" Ta fada hakan tana
nuna mata baby, Khadijah da ta gama tsorata gaba daya cikin rawar murya tace
"Anty kiyi hakuri" mari Anty khadijah ta sauke mata, lkci daya tayi
saurin daura hannunta a lebbenta alamar kar tayi kara, hawaye ya shiga sakko
mata ta dinga girgixa mata kai, kalle kallen dakin Anty khadijah ta dinga yi ko
xata samu wayar wuta amma bbu, hakan yasa ta kuma kai mata wani mari, Cikin
kuka khadijah tace "Anty don Allah kiyi hakuri ban mata komai ba" da
hannu Anty khadijah ta dinga dukan bare skin dinta tana mintsilinta ta ko ina
tana cewa "Toh wllh ko kallon baby kika sake yi a bisa kuskure cikin gidan
nan sai na sumar da ke shegiya balle ki mata kallon banxa, gayyar tsiya arna a
idi, kuma daga yau kika sake tsayawa cikin parlor ba kitchen ba koh cikin dakin
nan sai na kashe ki in kashe banxa" wani Marin tayi mata ta rankwasheta ta
hankadeta sannan ta kama hannun baby suka nufi kofa tana cewa "Banda Anty
fati hau ya fada mata ina ita ina dinga yi ma shegun mutane abinda take yi
yanxu, ai sai dai idan bana gidan nan amma duk sai na sa an sallameki har
tsinanniyar kyautar, ni kadai raina ma xan iya aikin gidan nan gaba daya idan
Allah ya yarda, shegu kwadayayyu yan maula" Kuka kawai khadijah take har
da shessheka rabonta da irin wannan kukan tun tana gidan kawunta, fita tayi
dakin ta wuce kitchen gun kyauta tana kuka sosai, nan taga kyauta bata kitchen
ta bude kofa ta fita can gun da kyauta ke cewa ta xauna ta xauna nan ta dinga
kuka kamar ranta xai fita, Aliyu ya mike daga xaunen da yake yana aiki a laptop
ya leka kasa, juyawa yyi ya bude kofa ya fita, tsaye yyi kanta yana kallonta,
ganinsa ta hade kai da gwiwa tana ci gaba da kukanta, ya durkusa yace
"What happened?" Dagowa tayi tana kallonsa amma ta kasa cewa komai
saboda kukan da ya ci karfinta, yyi shiru bai ce komai ba, ya kyaleta don kanta
ta daina kukan a hankali sai ajiyar xuciya da take, yace "Me aka
maki?" Cikin rawar murya ta nuna masa cikin gidan wasu hawayen na sakko
mata tace "Wannan Antyn nan ce ta min duka" shiru yyi yana kallon
tafin hannun dake kwance saman fuskarta da yyi ja, yace "Wace Anty?"
Kasa cewa komai tayi saboda wani sabon kuka da ya taho mata, yace "Don't
cry again, ki fada min wace Anty ce ta doke ki" ta buda masa hannu
muryarta na rawa tace "Ban san sunanta ba" Fiddo wayarsa yyi a aljihu
ya shiga gallery ya nuna mata hoton kusan yan gidan gaba daya yace "Wacce
a ciki?" Ta goge hawayen idonta tana kallon hoton da yake nuna mata da
kyau, a hankali tace "The one wearing blue" sake kallon hoton yyi
yaga Anty khadijah ce, yace "Me kika mata" wasu sabon hawayen suka
taho mata tace "May be wannan yarinyar ce tace mata ina kallo a
parlor....." yace "wacce yarinya?" Shiru ta yi bata ce komai ba
hawaye na taruwa idonta, Ya sake shiga gallery ya nuna mata hoton daxu ta nuna
masa baby, dauke kai yyi bai ce komai ba can ya kalleta yace "Toh ina
kayan ki?" A hankali tace "I just took my bath shine ta shigo daki"
rushewa ta kuma yi da kuka yace "Don't cry, ki jira ni a nan" daga
haka ya mike ya wuce ciki, ba a wani dau lkci ba ya dawo rike da hannun baby
dake kallonsa a tsorace, Ya iso gun khadijah da ita yana kallon khadijar yace
"stand up" mikewa tayi, ya mayar da dubansa kan kanwarsa yace
"Me ta maki kika yi reporting dinta gun Anty, kuma if you dare lie to me
you are in big trouble" kamar xata yi kuka tace "Yayanmu am
sorry" ya hade rai sosai yace "I will give u a dirty slap idan baki
yi answering question dina ba" Muryarta na rawa tace "I only told
aunt that...." Yace "That what?" Hawaye ya cika idonta tace
"Don Allah yaya kayi hakuri" kalle kallen gun ya fara yi, ta fashe da
kuka tace "Wayyooo yayana kayi hakuri" ya buge bakinta ya mata alamar
da ta yi shiru, ta toshe bakinta da hannu daya tana hawaye, ya isa gun wani
flower ya karya branch din ya dawo yace "Kawai saboda ke muguwa ce kika je
kika sa Anty ta mata duka koh" a rikice ta dinga girgixa masa kai tace
"Aa wllh, yaya kayi hakuri baxan kara ba, let me tell her sorry now
plss" hannunta ya fixgo yace "Kika kuskura kika min ihu idan na dauke
ki daga nan wllh asibiti xa mu tafi" daga haka ya shiga tsula mata bulalan
yanda yasan xai yi mugun shigarta yayi hakan kusan sau biyar tana tsalle tana
son kwace kanta amma ta kasa gashi ba daman ihu, sai da yaga hannunta yyi ja
sannan ya saketa tana tsalle hawaye na sakko mata, ya hade rai yace "Tafi
ki bata hakuri" da sauri ta isa gun khadijah dake kallonsu cikin rawar
murya tace "Don Allah kiyi hakuri" Khadijah tayi kasa da idonta tace
"ke ma kiyi hakuri" Fixgota Aliyu yyi tana kuka tace "Yaya wllh
na bata hakurin" yace "Tell her you two are now frnds from this
moment" ta kuma kallon khadijah da sauri tace "We are now frnds from
dis moment" a hankali khadijah tace "You are welcm" ya sake
kanwarsa yace "Maxa goge idonki kije tap ki wanke fuskar ki tafi ki
kwanta, if I shud hear pimm, you will spell doom, I mean idan kika kuskura kika
gaya ma kowa abinda ya faru sai na kusa cire maki kunne" da sauri ta je ta
wanke idonta ta goge fuskarta sannan ta wuce cikin gidan, ya kalli khadijah da
ta bi ta da kallo yace "Ke ma good nyt" ta kallesa ta gyada masa kai
a hankali tace "Bye" daga haka ta shiga ciki ita ma.
Post a Comment for "NOOR ALHAYAT 29"