NOOR ALHAYAT 28
Karfe hudu duk yaran gidan suka gama shirin tafiya
islamiyya, kyauta ta hada socks dinsu
gaba daya da Uniform din autar Mumy da ake kira da Baby saboda sunan Anty
khadijah gareta xata wanke, kallon khadijah dake tsaye kanta tayi tace
"Toh ni dai kin
tsaya min kamar soldier ki tafi can dinning area ki kwaso
duk plates din wajen, saura kar kiyi a hankali" khadijah tace
"Toh" sannan ta wuce ciki, bbu kowa dinning area din sai plates da
shinkafa da aka yi littering a wajen, Khadijah na ganin Anty khadijah a parlor
xaune tana gyara ma Baby Hijab tayi saurin dauke kanta ta shiga hade plates din
waje daya, muryar daya daga yan matan parlorn taji tana cewa "Anty wacece
wancan yarinyar wai?" Anty khadijah ta tabe baki tace "The new
housemaid" Baby ta xaro ido tace "Anty is kyauta going?" Anty
khadijah tace "Noo she is not" Baby ta sauke ajiyar xuciya tace
"Better... coz I don't think i like that girl, she can look for Africa as
a whole" horn da driver yake yasa Siyama da Aneesah suka mike rike da
jakar islamiyyarsu suka ma Anty khadijah sallama suka fita, Anty khadijah tace
"She's not even worth talking to, don hka bbu ruwanki da ita yar aikin
gidan ce kin ji takwara" baby tace "Sure" khadijah ta turo baki
tana kallonsu, baby ta harareta ta fice daga parlorn, khadijah ta ki daukan
komai a dinning din ta fita gun kyauta da gudu tana kumbure kumbure, kyauta
tace "Ina kwanukan?" Ta fashe da kuka tace "Anty mai girki kinga
yarinyar nan har da neman tsokanana koh, shine har da ce min I can look for
Africa where as she was the one looking at me, kuma Anty mai ihu tace mata ni
house girl ce" Kyauta ta tabe baki ta nuna mata wani dakali tace
"Tafi can ki xauna, ni dai ba ruwana idan kina kallon yan gidan nan sai su
dake ki ma su daki banxa nima ba kyaleni suka yi ba gwara babyn ma a cikinsu,
idan ba iskanci ba... Ba aikin aka kawo ki kiyi ba har xa ki ji haushi don an
ce maki house girl?" Khadijah ta turo baki bata ce komai ba, kyauta ta
gama wankin ta tafi ta kwaso plates din ta gyara dinning din, khadijah ta hada
ma kayan wanke wanken can bakin tap kar ta jika kitchen din ita kuma ta shiga
girka dinner, da ta leka sai ta ga kamar ba a wanke wanken, daga karshe fixgota
tayi bakin tap din ta turata waje daya ta shiga wanke wanken tana bala'i,
khadijah ta toshe baki kar tayi dariya jin har da kiranta lazy ass, har kusan
magrib khadijah na kusa da kyauta a kitchen komai kyauta ta sauke kan wuta sai
ta ba buda mata hannu xata d'an d'ana tun kyauta na mata da mugunta tana konata
da cokalin miya har ta gaji ta kyaleta sai ta xuba mata a d'an karamin plate,
kyauta ta samu wani roba ta xuba duk pepper soup din da tayi mai yawa a ciki
bata yi gigin ba khadijah ba tace "Tafi ki leka su waye a parlor"
khadijah ta dawo tace "Ba kowa Anty mai girki" kyauta ta fita da
sauri ta bude dakinsu ta ajiye masu bayan kofa sannan ta dawo ta jera komai kan
dinning bayan ta ba khadijah na su Usman mai gadi ta kai masu, Kyauta na gama
tsaftace kitchen suka wuce daki da Khadijah, sai a sannan ta xauna ta fixgo
khadijah tace "Ke bakya sallah ne hala?" Khadijah tace "Ina yi
amma bani da Hijab yanxu" turata bayi kyauta tayi tace "Ni ina da shi
ai" Khadijah na xaune kan dankwalin da kyauta ta shimfida mata ta yi sllh
tana ta kallon kyauta dake addu'a ta idar da sallahn ita ma, Muryar Mumy kyauta
taji ta shafe addu'ar ta mike da sauri ta fita khadijah ma ta bi bayanta da
sauri, Mumy tace "Ki xuba ma Aliyu abincin xai wuce aiki yanxu, ku kun ci
abincin?" Kyauta tayi kasa da kai tace "Xan xuba masa yanxu Hajiya,
mu kuma yanxu xa mu xuba" Mumy tace "Toh sai ki debar maku har da
farfesun" Kyauta tace "Toh mun gode Hajiya" Mumy tace "Toh
ya tana kokarin aiki kuwa ita?" Mumy ta fada tana nuna khadijah, kyauta
tace "Ehh ba laifi Hajiya" Mumy ta juya tace "Toh shkkn" A
dinning kyauta ta dibar ma Aliyu nasa abincin a plate ta xuba masa farfesun
kaji sanin bai cin sauran, sama ta tafi kai masa khadijah ta biye da ita, ta
kwankwasa masa kofa ba a dau lkci ba ya bude yana buttoning din shirt din
jikinsa, kyauta tace "Ga abinci yallabai" kallo daya yyi masu ya
karbi tray da kyauta ke mika masa yace "Nagode" khadijah tace
"Nan ne dakin ka" bai ce komai ba ya rufe kofarsa, kyauta ta ja
khadijah suka sauka ta shiga daki da ita ta hade hannayenta biyu tace "Ke
wai dan gidanku ina ruwan ki da likitan gidan nan, kin taba sanin sa ne idan ba
shisshigi ba?" A hankali tace "Kiyi hakuri" kyauta ta ja bakinta
da karfi hade da dungurinta tace "Sai na cire maki wannan mayun idon naki
wllh idan kika sake yi ma kowa magana a gidan nan" khadijah ta gyada mata
kai hawaye cike idonta, kyauta ta fita ta bar jin alamar su baby sun shigo
gidan daga makaranta. Ko kafin kyauta ta sallamesu ta dawo ciki har khadijah
tayi bacci, tashin ta ta shiga yi ta ci abinci cikin magagin bacci take cewa
Umma na koshi, kyauta ta debo ruwa ta yarfa mata a fuska, da sauri ta farka
gaba daya kyauta ta ajiye mata abincin a gabanta ta shiga bayi don yin alwala,
ko da ta fito Khadijah bata ci abincin ba ta koma bacci, hakan yasa tace
"Ke kika sani" dagata tayi ta kwantar ta xauna cin abincin ita kafin
tayi sallahn. Washegari kyauta na idar da sallah ta fita daura breakfast, ta
gama fere dankalin turawa Anty khadijah ta shigo kitchen din, kalle kalle ta
shiga yi kafin tace "ina wannan yarinyar take?" Kyauta tace "Ina
kwana Anty?" Anty khadijah tace "Lafiya, ina yarinyar nace?"
Kyauta tace "Na aiketa daki shiru shiru" fita Anty khadijah tayi ta
bude kofar dakin kyauta tana yatsine fuska, kwance ta tadda khadijah shame
shame kan gado, karasawa tayi ta maka mata duka har sau biyu a baya, khadijah
ta farka a rikice, Anty khadijah ta fixgota tace "Ko yan gidan gaba daya
ma sun tashi bare ke shegiya, a hakan xa ki iya aiki a gidan nan, a kirga har
dubu goma a bai ma iyayenki jiya ki yi ma mutane shame shame kina bacci kan
gado har yanxu?" Khadijah ta sauka kan gadon hawaye cike idonta tace
"Anty kiyi hakuri" fixota Anty khadijah tayi ta turata waje da karfi
tace "Fita kije ki kama ma kyauta aiki, ko ita din baiwar ki ce, ina ce
yanda ake biyanta haka ake biyan ki kema" khadijah ta wuce kitchen da
sauri tana hawaye, Anty khadijah ta biyota har kitchen din tace "Maxa hada
wanke wanke ki fita ki yi" da sauri ta dinga fita da plates waje hawaye na
sakko mata, ita dai kyauta bata ce komai ba har Anty khadijah ta fita kitchen
din, khadijah ta dau cups uku xata fita da su, kyauta tayi tsaki tace
"Mata ta ki xaman aure duk ta xo ta addabe mutane a gida tirrr, ke kuma ai
kinga result din bacci kamar matatcciya" khadijah dai bata ce komai ba ta
fita, Kyauta ce tayi wanke wanken bayan ta sallami yan makaranta khadijah na
mata dauraya, karfe tara da rabi mumy ta sakko xata fita aiki, bayan sun gaisa
da kyauta dake hada mata breakfast a dinning mumy tace "Ina khadijah"
Kyauta tace "Tana can tana shara Hajiya" Mumy tace "Ohk"
kyauta ta koma kitchen bayan ta gama hada ma mumy shayi sanin gimbiya na can
sama tana ta bacci yanxu haka, Kallon khadijah tayi da tasa dankali da kwai da
shayi a gabanta ta ki ci, Kyauta tace "Au baxa ki ci ba?" Khadijah ta
kalleta tace "Ina ci" sai kuma ta fara kuka, Kyauta tace "Samun
waje, wato duk da lafiyayyen abincin nan dake gaban ki har kuka kika samu daman
yi koh? Kila ma a gidan da kika baro baki samun irin haka" khadijah ta
mike tana kuka ta daga rigarta tana nuna ma kyauta bayan ta tace "Anty mai
girki har yanxu fa xafi wajen da ta dokeni yake min" kyauta ta buda baki
ganin shatin hannun Anty khadijah a bayanta, can tace "Tabdi, toh Allah ya
isan ki, kuma in sha Allahu a baxawara xata Karachi rayuwarta, ni kam ko yanxu
na bar gidan nan nasan xan samu mijin aure, ita kuwa wllh sai dai taga ana yi,
kuma ina jin ita ma ta bar 'ya yanta a wani gidan to haka xa ayi ta cin ubansu
ana gallaza masu in sha Allahu" Kyauta ta sauke rigar tace "Maganinki
kenan kema dai, gobe ba sai kin jira an tashe ki ba" daga haka kyauta ta
ci gaba da aikinta, da sauri kyauta ta fita jin mumy xata wuce gun aiki, ta
gama sauraren abinda mumy ke ce mata ta risina tace "In sha Allah Hajiya,
Allah ya tsare hanya" tsaye jikin kofa Mumy ta hango khadijah tace
"How are you" a hankali khadijah tace "Good morning maa"
mumy ta kalli kyauta tace "Anya baki cika ma yarinyar nan aiki kuwa
kyauta?" Da sauri kyauta tace "Wallahi ko daya Hajiya, ki tambayeta
bana cika ta da aiki" Mumy tace "Ohk" sannan ta mayar da dubanta
kan khadijah tace "Am off to work, hope kin yi breakfast?" Ta gyada
kai tace "Nayi Anty" Mumy tace "Good" daga haka ta nufi
kofa, kyauta ta rakata tana mata Allah ya kiyaye, Mumy na fita da motar ta
kyauta ta koma kitchen ta kwashi sauran kayan wanke wanke ta tafi wankewa a
waje, khadijah na ta tsaye bakin kofar kitchen din Aliyu ya shigo gidan, tun da
ta kallesa bata sake kallonsa ba har ya wuce sama, bayan kusan minti ashirin
sai ga shi ya sakko, har lkcn khadijah na gun da take a tsaye, ya shiga kitchen
din ya hada abinda xai hada a cup ya fito har ya wuce ya juyo ya daure fuska
yace "Baki iya gaisuwa ba koh?" Ta turo baki tace "Good
morning" daga haka ta juya ta wuce gun kyauta a waje, ya kusa second
ashirin a tsaye kafin ya juya ya wuce sama. Ruwan wanka kyauta ta hada mata
bayan sun koma daki, khadijah tace "Anty mai girki ni fa ban yi brush ba
kika bani abinci" kyauta tace "Ni na hanaki brush?" Khadijah ta
langwabar da kanta tace "Toh su fauxiyya sunyi lost din min brush dina a
gidansu" kyauta tace "Oho dai tafi kinyi wanka ga ruwa can"
khadijah na fitowa daga wanka kyauta ta bata Vaseline ta shafa sannan ta fiddo
mata da daya daga kayan ta da ta linke bayan ta kwaso mata su jiya, khadijah
tace "Anty mai girki kinsan wa ya siyo min new pants din nan" kyauta
tace "Oho" khadijah tace "My lovely Umma" kyauta bata sake
kula ta ba ta fixgota ta lafta mata uban kwalli a ido ta shafa mata farin powder
a fuska sannan tace "Wuce can baya ki xauna kar ki shigo gidan nan sai na
kira ki na gaji da surutun ki" khadijah tace "Toh" sannan ta
fita, dakalin da ta saba xama ta xauna bayan ta tsinka flowers da yawa ta dinga
yin jakar hannu da su kamar yanda aka koya masu a schl da dadewa, kamar ance ta
daga kai suka hada ido da Aliyu dake kallonta, ta dauke idonta ta ci gaba da
abinda take, bayan wani lkci ta daga kai bata sake ganinsa xaune balcony din
ba, gajiya da xama tayi ta shiga ciki ta bude kofar kyauta a hankali ta ganta
kwance tana bacci, shiga tayi ita ma ta kwanta gefenta nan da nan bacci ya
dauketa. Da yamma Mumy na xaune parlor da Anty khadijah da ita ma dawowarta
gidan kenan tun daxu da ta fita, khadijah ta fito daga daki bayan ta ajiye
kayan kyauta da ta bata, mumy ta kirata ta karasa parlorn ta durkusa tace
"Anty gani" mumy tace "Meye da meye bbu a kayan ki?"
Khadijah tayi shiru tana naxari, can ta fara lissafo su da fingers dinta tace
"I don't have toothbrush and toothpaste, I don't have towel, I only have
six pants da ummata ta siya min sauran fauxiyya ta sace min, even ves bani da
shi, kuma bani da mai da xan shafa, Anty har da na gashina" murmushi kawai
Mumy take, Anty khadijah kuwa ta hade rai kamar bata taba dariya ba, Aliyu dake
dinning yana cin abinci tabe baki kawai yyi, mumy tace "Toh in ga kan
naki" khadijah ta xame hular kanta Anty khadijah ta saci kallon dogon
gashin, mumy tace "Kai maa sha Allah ran Saturday sai ki bi su Siyama kema
a gyara maki koh" da sauri khadijah ta xauna a tsorace tace "Anty
ummata ta gyara min ai, it's just of recent ta kai ni saloon" Mumy tace
"Anjima driver xai kawo maki duk abinda baki da, kina da takalmi
koh?" Ta gyada kai tace "Amma ya kusa tsinkewa su fauxiyya suke sa
min" mumy tace "Toh tashi kije xa a siya maki" khadijah tayi
murmushi tace "Toh Anty I like you" daga haka ta wuce kitchen gun
kyauta da sauri. Mumy na kallon Anty khadijah da har lkcn ranta a bace yake
tace "Khadijah am thinking ko in sa yarinyar nan a islamiyya su dinga xuwa
tare da su baby da yamma, kowa ya ganta yasan she is from a wealthy home, it's
just condition...." Katse ta Anty khadijah tayi tace "Anty fatima ki
raba kanki, Anty Fatima ki raba kanki ki kyale mutum yanda kika gansa na sha
gaya maki times without number, su wa enda suka kawo ta gun aikin sun fa pi ki
sanin akwai islamiyya, me yasa kike son sa ma kanki matsala ne wai, tsinannun
masu aikin nan da kiris suke jira su tura wanda ya kyautata masu cikin rana,
meye hadin ki da yarinyar idan ba shisshigi ba da neman wajen xama??" Mumy
ta kalli Aliyu dake ta kallonsu tace "Abuturrab yanxu don nace ayi
enrolling din baiwar Allahn nan a islamiyya laifine don Allah?" Ya mike
yace "Noo, ba laifi bane mum, sai ma lada da xa ki samu in sha Allah"
daga haka yayi wucewarsa sama, Anty khadijah ta bi sa da wani mugun kallo, mumy
tace "Atoh, baka san yanda Allah xai yi da naka ba gobe, baka kuma san ina
reward din ka yake ba, yarinyar nan tare da ke take gaya mana ita marainiya ce,
to don me baxa a ji tausayinta ba, kika san kudin iyayenta a da, don duk wanda
yaga yarinyar nan yasan ba daga karamin gida ta fito ba, just put little baby
in her shoes... Kin dai ga sa'anni ne su din daga ganin, to da baby ce ta shiga
irin halin nan yaya xa ki ji, Allah ya rufa min asiri don dai kudin islamiyya
xan iya biya mata, toh ni ban san meye damuwarki ba khadijah" Tsaki Anty
khadijah tayi ta mike ta nufi stairs tana cewa "Muna nan da ke sai kin yi
da kin sani Anty, shi kuma Aliyu ya ci gaba da daure ma karya kugu, daga ganin
yarinya shegiya ku hakikance ku ce a sa ta a Islamiyya for what reason, shi aka
aikota yi gidan nan" Mumy tace "Aniyar ki ta bi ki khadijah, shi yasa
kike samun matsala da kowa a rayuwa ni dai baki yo halin mahaifanmu ba Allah ya
ji kansu, nima ba halin mu daya ba, tirr"
Post a Comment for "NOOR ALHAYAT 28"