NOOR ALHAYAT 27
Kyauta ta gama shanyan kayan ta dau sabulun da ya rage ta
mika ma khadijah dake ta xaune a gun da ta nuna mata tace "Kina shiga
parlor xa ki ga wani kofa, maxa ki shiga ki ajiye sabulun nan saura kuma ki min
tabe tabe nasan yanda na ajiye komai na" tashi
khadijah tayi ta karbi
sabulun ta wuce ciki, ta kusa minti daya tsaye bakin kofar kitchen tana lekan
parlorn don har lkcn Anty khadijah na nan, tun xuwanta wajen Aliyu ya ganta, da
sun hada ido sai ya dauke kansa, can dai small mum din tasa ta mike tace
"Xan tafi in kwanta Son" yace "Alright" daga haka ta wuce
sama, sai a sannan khadijah ta shigo parlorn tana taku a hankali ta shiga kofar
da kyauta ta ce mata, kare ma dakin kallo ta dinga yi, komai fes fes kamar ba
dakin mai aiki ba har da gado a dakin, khadijah ta ajiye sabulun tsakiyar dakin
sannan ta juya ta fito, gun Aliyu ta nufa ta tsaya kusa da shi tana kallon
laptop din kafarsa tace "Kasan me?" Ko kallonta bai yi ba idonsa a
kan laptop din, tace "Nima ina da laptop da Abbana ya siyo min
ah...." Shiru tayi tana kallon sama tana son tuna sunan kasar, ta
langwabar da kai tace "May be it's china! kuma na iya operating laptop din
amma kawu ya amshe min" kamar xata yi kuka ta kare maganar, ya dago kai ya
kalleta yace "Na tambaye ki?" Dariya ta yi har da rufe fuskarta tace
"A'a kawai gaya maka nake yi" yace "Toh juya ki bar nan"
Dai dai shigowar kyauta parlon, ganin Aliyun tayi kasa da kai tace "Sannu
yallabai" yace "Yauwa sannu da aiki" Kyauta ta shiga dakinta, ya
kalli khadijah yace "Wuce ki ban waje" ta buda ido tace
"Ohk" daga haka ta bi kyauta dakinta, kyauta dake kokarin ajiye
sabulun da khadijah ta yasar mata a tsakiyar dakin ta juya ganinta ta rufe
kofar dakin, sannan ta ja kunnenta tace "Ba nace ki daina ma mutan gidan
nan shisshigi ba, ke wani irin kunnen k'ashi gare ki, me ya hada ki da likitan
har xaki je ki tsaya gabansa?" Khadijah ta turo baki tace "I was just
telling him about my laptop" sake baki kyauta tayi tana kallonta, can ta
dungureta tace "Sannu baturiya, you dey tell am about ur laptop koh? Wai
ma ina iyayenki?" A hankali khadijah tace "They are late?"
Kyauta tace "Wa ya kawo ki gun aiki?" Khadijah ta langwabar da kai
tace "Wata mata ce, she is very wicked" kyauta ta rike ha6a tana
kallon khadijah, muryar Hajiya taji tana kiranta a parlor ta juya da sauri ta
bude kofar ta fita khadijah ta bi bayan ta, Hajiya dake tsaye tace "Kyauta
white rice kawai xa ki yi da miya for lunch, pepper soup din da xa ki yi kuma
na dinner ne idan kinga xaki iya yi yanxu kiyi, idan baxa ki iya ba ki bari da
yamma" kyauta ta risina tace "Toh Hajiya" Mumy ta juya ta koma
sama, Aliyu dake parlorn har lkcn yace "Mumy baxa ki aiki ba yau"
Tace "A'a sai gobe" Kyauta ta shiga kitchen Khadijah na biye da ita,
Ruwan shinkafar ta daura kan gas, duk inda ta bi a kitchen din sai khadijah ta
bi ta, gajiya da karon da suke ci Kyauta tayi ta fixgota ta nuna mata kofar
fita kitchen din tace "Tafi ki ban waje baki min ko wani amfani a nan"
da sauri khadijah ta fita kitchen din, bbu kowa parlorn haka yasa ta dau remote
da sauri ta canxa xuwa cartoon, ta rakube kasan kujera tana kallo, kafin karfe
daya Kyauta ta gama shinkafa da miyar ta fito parlor, dai dai sakkowar Anty
khadijah downstairs, tun a stairs ta bude baki tana kallon khadijah da gaba
daya hankalin ta na kan TV, kyauta na ganinta tayi kasa da kai xata koma
kitchen ta kwalo mata kira, sai a sannan khadijah ta mike da sauri, cike da isa
Anty khadijah tace "Ba ki gaya ma yarinyar nan rules din gidan nan bane
kyauta?" Kyauta tace "Ban kai ga gaya mata ba Hajiya, tun daxu ina
kitchen ne da na san nan ta xauna kallo da baxan barta ba kiyi hakuri
Hajiya" Anty khadijah ta kalli khadijah fuskarta daure tace "An ce
maki nan din gidan ubanki ne da kika taho kika hakikance a parlor kina kallo a
matsayin ki na mai aiki da aka dauka yau" khadijah tayi shiru bata ce
komai ba, a tsawace Anty khadijah tace "Ba magana nake maki kike kallona
da shegun idanuwanki ba" Kyauta tace "Kiyi hakuri Hajiya hakan baxai
kara faruwa ba idan Allah ya yarda" Anty khadijah tace "Halan baki
san ita ma aiki aka dauketa ba da xaki bar ta tana kallo ke kuma kina ta aiki a
kitchen, ina ce tare ya kamata ku yi aikin ba?" Kyauta ta risina tace
"Kiyi hakuri naga yarinya ce Hajiya" Wani kallo ta jefeta da shi tace
"Yarinya? Ai iyayen nata sun san yarinya ce suka kawo ta gidan aiki, maxa
idan akwai wani aikin ki bata ta tafi taje tayi yanxu, daga yanxu kuma bana son
sake ganin kina aiki ita tana xaune" kyauta ta juya da sauri tace
"Toh Hajiya" bin bayan ta khadijah tayi, Anty khadijah ta dakatar da
ita tace "Daga yau na sake ganin ki xaune cikin parlorn nan wllh sai na
lahira ya fi ki jin dadi gayyar tsiya kawai" A hankali khadijah tace
"Am sorry maa" daga haka ta bi bayan Kyauta da sauri. Kyauta ta
fixgota bayan sun shiga kitchen din ta ja kunnenta tace "Kin ga xaki fara
ja min matsala koh? Da nace ki wuce daga kitchen ce maki nayi kije kiyi
kallo??" Khadijah ta girgixa mata kai kamar xata yi kuka, kyauta ta nuna
mata can wani gefe tace "Tafi ki je ki xauna wawiya kawai, dole ne sai kin
yi kallo har wancan baxawarar xata dinga maki gori bata san at times condition
ke sa crayfish yyi bend ba, banda haka uban me xai kawo mu gidan nan"
khadijah tayi dariya har da kyakyatawa tace "Anty is crayfish bent?"
Hararata kyauta tayi ta juya ta ci gaba da abinda take, a dinning kyauta ta
jera lunch din duk me son ci a can xai je ya diba, ta dau wani katon roba ta
kusa cika sa da shinkafa nama yayi takwas ta fita parlor tana leke leke, dawowa
tayi da sauri ta mika ma khadijah tace "Maxa maxa tashi ki kai dakina da
sauri ki ajiye a bayan kofa ki rufo dakin" khadijah ta mike ta karba
abincin ta fita da sauri, har xata shiga daki ganin Aliyu ta tsaya, sai kuma ta
nufesa har gun stairs tana nuna masa abincin ta tabe baki tace "Kaga Anty
mai girki tace in kai mata abincin nan daki da sauri, may be she fetched all
the food kila har da kai ma baxa ka samu ba, cos there is nothing left in the
pot, I even saw when she was pouring water inside" Aliyu ya rungume hannunsa
ya hade rai yace "Where did u knw me from?" Tana rike roban abincin
da kyau saboda tiririn da yake innocently tace "In this house mana,
I...." Turata yyi baya da sauri har sai da ta kusa faduwa shi ma ya koma
baya ganin ta sake roban hannunta gaba da uban shinkafa da miyar da nama suka
tarwatse kasan tiles har kan stairs, ta xaro ido ta toshe baki kamar xata yi
kuka tace "Shikenan ka xubar... wllh bani bace ba kai ne ka xubar, ka
xubar ma Anty mai girki abinci...." Kyauta ta fito da gudu daga kitchen jikinta
na rawa jin karar faduwar roba kamewa tayi gun ganin khadijah can bakin stairs
ga tulin shinkafa a xube kasa, xata koma kitchen suka yi ido hudu da Aliyu ta
sake dawowa da gudu bakinta na rawa tace "Subhanallahi ta xubar, ban san
baxata iya ba dama nawa ne da nata da nasu Usman..." Khadijah ta daga
hannu da sauri tace "Noo Anty mai girki bani bace ba fa, shine ya turani
baya kawai abincin ya fadi a hannuna" Aliyu ya tsallake abincin ya bar
wajen, Kyauta ta koma kitchen da gudu ta dauko wani karamar roba ta dawo ta
dinga kwashe shinkafar tana xubawa a babban roban, khadijah tace "Hope u
are nt eating this any longer?" ko kallonta kyauta bata yi ba ta gama
kwashe abincin ta kai dakinta da gudu ta fito ta shiga kitchen ta fito da
sweeper, cikin yan mintuna ta gama gyaran gun ta goge, sai a sannan ta mike
tana hararan khadijah tace "Ae yau sai dai yunwa ya kashe ki gidan nan, ba
dai ni kika yi niyyar toxartawa ba? Yanxu da baxawara ce ta sakko ba bawan
Allahn nan ba ya xan yi da raina?" A hankali khadijah tace "Kiyi
hakuri" kunnenta ta ja tace "Baxan yi ba, sai kin gaya ma yan garin
ku da yunwar cikin ki yau, little brat kawai" daga haka kyauta ta koma
kitchen da sauri, khadijah ta langwabar da kai ta bi ta da kallo. Da kyar
khadijah ke cin shinkafar tana yi tana kallon shi da kyau ko xata ga dirt a
ciki, kyauta sai hararata take tana ci hankali kwance, Khadijah tace "But
Anty mai girki me yasa baki xuba mana wani ba?" Kyauta tace "Kika
sake ce min Anty mai girki sai na kalla maki mari, Anty mai girkin gidan ku,
nace idan baxa ki ci ba ki dau naman ki tashi ki ban waje ni xan iya cinyewa,
kila ma gidan da kika baki samun irin wannan xaki xo nan kina min iyayi"
Khadijah ta xaro ido tace "The woman is always cooking concoction there,
bata taba irin wannan abincin ba" Kyauta tace "Toh ki rufe min baki
ki ci abinci yanxu yaran gidan xa su dawo daga makaranta" khadijah tace
"Ohk" Jin shigowar mota kyauta ta bar ma khadijah sauran abincin ta
mike da sauri tace "Toh gasu can... Idan kin cinye ki fito da roban kika
kai kitchen" daga haka kyauta ta fita, yara uku ne suka shigo parlorn
sanye da kayan makaranta daya kamar khadijah take tana jss3, daya kuma na ss1,
babban cikinsu na ss2, khadijah ta fito rike da sauran abincin ta tsaya bakin
kofa tana kallon yaran, Gaba daya dinning suka nufa ko wacce na cewa "Yaya
ina yini?" Aliyu dake xaune gun ya amsa masu gaba daya, bbu warce ta gaida
kyauta dake ta masu sannu da xuwa duk suka wuce sama, banda yar karamar cikinsu
sa'ar khadijah, Kyauta ta washe baki tace "Yauwa sannu Anty khadijah ya
makarantar?" Yarinyar da ita ma sunanta khadijah tace "Alhmdllh,
kyauta who is that girl staring at us?" Kafin kyauta tace komai khadijah
ta turo baki tace "I am not staring at you..." daga haka khadijah ta
shige kitchen da roban hannunta, duk wannan abun Aliyu na kallonsu daga
dinning, yarinyar ta juya da sauri ta tafi gunsa tace "Ya Aliyu who is
she?" Ya kamo hannun Kanwar tasa yace "Ask mumy" yarinyar tace
"Ohk" daga haka ta wuce sama kyauta na cewa ta na cire uniform tayi
sallah ta xo ta karbi abincinta, kyauta ta bi khadijah kitchen ta jawota
fuskarta daure tace "Ke fa ba ruwanki da yaran gidan nan naga har kin fara
masu fetsara, ki tsaya a matsayin ki idan ba haka ba baxawara ta ishe ki"
Post a Comment for "NOOR ALHAYAT 27"