NOOR ALHAYAT 22
Daukar waya
Umma tayi ta shiga kiran layin step sister dinta Yakumbo amma baya shiga alamar
dai wayar a kashe yake, da safe bbu abinda ta girka ma m utan gidan a madadin
breakfast, ta dai hada ma Khadijah tea ta siyo mata bread ta bata, Karfe takwas
ta shiga bangaren mai gidan nasu ta sanar da shi xata mayar da Khadijah gida
,
ya kirgo dubu biyar ya mika mata yace "Gashi ku yi kudin mota, idan kin
dawo sai a san yanda xa ayi batun makarantar nata in ji ko nawa ake biya"
Umma ta girgixa kai tace "A'a ka bar shi mun gode Alhaji, muna da kudin
mota" Yace "Shi kenan, Allah ya tsare" mikewa tayi ta fita
dakin, a cikin wata karamar jaka Umma ta hada ma Khadijah d'an kayan da ta fara
siyo mata, suka fito parlor ta sa ma kofar kwado bayan ta rufe, khadijah dake
sanye cikin doguwar riga da karamin Hijab tace "Umma ina xa mu?" Umma
ta kasa kallonta tace "Xa mu d'an yi tafiya ne khadijah" daga haka ta
kama hannunta suka nufi kofa, tana jin su Shafah da Hasana na dariya suna cewa
"Toh a sauka lafiya, sai a kara gaba can da ita" ita dai bata tanka
su ba har ta fita. Tasha suka tafi cikin a dai dai ta, can suka samu motar
Kaduna, bayan wani lokaci motar ta cika suka yi set off xuwa Kaduna garin
gwamna... Ko barin kano basu yi ba khadijah tayi bacci jikin Ummanta, har suka
isa Kaduna bata tashi ba, suna isa kawo bayan driver yyi parking kowa ya fara
alighting daga cikin motar, Umma ta tada khadijah suka sauka su ma, sai kalle
kalle khadijah take tace "Umma where is this?" umma tace
"Kaduna" Khadijah tace "Wow I've heard of Kaduna in school"
Umma ta samar masu napep suka yi ciniki sannan suka shiga xuwa hayin rigasa
Unguwar da yakumbo take, tafiya ce mai nisa kafin su iso rigasa, da yake Umma
sunan layin kadai ta sani ba wai ta wani san gidan yakumbo bane a bakin layin
tasa mai napep din ya sauke su ta basa kudinsa tana rike da hannun khadijah
suka shiga layin umma na bin ko wani gida suka xo wucewa da kallo don ta haka
kadai xata gane gidan yayarta kasancewar ta jima bata xo wajenta ba, sun fi
minti talatin suna bulayi a layin, Khadijah sai tambayarta take "Umma where
is this, everyway is dirty, they are smelly gutters everywhere" Umma tace
"look I don't want to here ur mouth again" shiru khadijah tayi, daga
karshe dai wata mata da ta gansu suna ta yawo ce ta tambayesu gidan da suke
nema, Umma tayi shiru tana tuna sunan da aka fi sanin yakumbo da shi, can tace
"Kulu mai waina" Matar tace "Ikon Allah, yo ai ga gidan can kun
wuce" Umma ta juya tana kallon gidan da matar ke nuna mata, matar tace
"Wancan gidan mai keke a gaban sa" Umma tayi murmushi tace "Kin
ga kuwa sai yanxu na gane, gaskiya na nagode sosai" daga haka suka juya
khadijah na biye da ita a baya, tsallake gutter din dake kofar shiga gidan Umma
tayi Khadijah ma ta yi haka sannan suka shiga xauren gidan, gida ne ginin kasa
duk ya kwarabe, Khadijah ta xaro ido tana bin gidan da kallo, Yakumbo ce xaune
tsakar gida tana hura icce duk hayaki ya cika ko ina, Umma tace
"Yaya" dagowa yakumbo tayi ta xaro ido tace "Aminatu"
karasawa Umma tayi ta rungumeta tace "Rai kan ga rai yaya" cike da
farin ciki Yakumbo tace "Sannu da xuwa Amina, daga ina haka? ya mai gidan
naki?" Umma tace "Wllh daga kano Yaya, yana nan lafiya yace duk a
gaida ku" Yakumbo tace "Maa sha Allah sai dai kin rame kan lokacin
bikin, wacece wancan" Yakumbo ta fada tana nuna Khadijah, A hankali Umma
tace "Yar marigayin mijina ce Alhaji Muhammad" Yakumbo ta rike haba
tace "Ikon Allah gashi ta kusa xama budurwa, sun hakura sun baki ita
kenan?" Umma tace "uhn, labari ne me yawa yaya bari dai mu yi
sallah" Yakumbo tace "Gaskiya ne bari in kawo maku ruwa" tabarma
ta fara shimfida masu kafin ta tafi debo ruwan alwala, Umma ta xauna ta nuna ma
khadijah dake tsaye gefenta, khadijah ta karaso tana tsattsallake bololin dake
watse tsakar gidan, Umma tace "yaya ina mutan gidan?" Yakumbo tace
"Toh jikokin nawa sun fita wasa, tun safe rabona da su, yaran makwabtana
kuma duk sun tafi talla, iyayensu kuma aikatau suke na yini, Ladi ce kadai ta
shiga makwabta daxu, nima anjima xan fita suyan wara da dankali a bakin
titi" shiru Umma tayi jikinta yayi mugun sanyi, yakumbo ta kara da cewa
"Ai Allah ma yyi ban tashi a gidan nan ba kika xo, don duk mai gidan ya ba
mu notice xai rushe gidan wai, to gida ne duk ya rube" Umma ta kalleta da
sauri tace "Ina xa ku koma yaya?" Yakumbo tace "Oho dai har
yanxu ina lalube ne, kudin kama wani gidan ma ai xaune yake da kugunsa, talauci
yyi yawa ta ko ina, ko daxu na fita duba gida don sati daya ya ba mu xai watsar
mana da kaya waje" Umma tace "Ikon Allah" Yakumbo tace "Ai
ke dai kawai sai du'a'i duniyar ta xama abinda ta xama" Yakumbo ta kalli
khadijah da ta takure gu daya tace "ke yar nan tashi ki fita waje gun mai
kanti ki siyo min farin maggi" Umma tace "Yaya ai bata san ko ina
ba" Yakumbo tace "Ka ji ki, nan nan ga masu kanti kamar jampa a jos
ta ko ina a anguwar nan, tana fita duk inda ta bi akwai mai kanti" daga
haka Yakumbo ta kunce kullin xaninta ta fiddo wani naira ashirin dake a dunkule
ta jefa ma khadijah, mikewa khadijah tayi ta karasa ta duka ta dau kudin tana
kallon Yakumbo tace "How much own" yakumbo ta d'an bude ido tace
"Eh??' Umma tace " twenty naira" khadijah ta juya ta fita,
yakumbo tace "Sai na ji kamar yare tayi" Umma tayi murmushi tace
"Turanci tayi" Yakumbo tace "Au tohhh abun na manya ne
Ashe" ita dai Umma bata ce komai ba ta mike taje tayi alwala ta dawo tayi
hau kan tabarman ta tada sallah, jin shiru shiru Umma na idarwa ta bi bayan
khadijah, a bakin xaure suka kusa cin karo Umma tace "Ina magin kuma me ya
sa kika dade?" Khadijah tace "Umma I've forgotten the one she
mentioned" Umma ta hade rai tace "Bani kudin" mika mata khadijah
tayi ta umma ta koma ta dau dari a Jakarta ta fita, farin magin hamsin ta siyo
mata da maggi star saba'in sannan ta dawo gida, garau garau na dafaduka Yakumbo
ta girka masu, ta xubo a faranti. Umma kadai ce ke cin abincin a sanyaye tana
tausayin khadijah dake tsintar shinkafar, yakumbo kuwa na ta yankan warar da
xata fita soyawa kamar yanda tace suna yi suna hirar xumunci da yar uwarta,
la'asar nayi Yakumbo ta kira almajiri ya kai mata kayan bakin titi gun da take
suyar, Tana kokarin saka Hijab dinta da yyi dukun dukun tace "Toh Amina
xan fita kasuwa, idan kun ji yunwa ku kara deban abincin, sai ki d'an taimaka
ki share min daki ki fiddo kayan wanke wanken ki ajiye su bakin kwararon can ko
yarinyar nan ki sa tayi" Umma tace "Toh yaya, amma fa har yanxu yaran
basu dawo ba" Yakumbo tace "Rabu da gantalallu suna makwabta na sani,
idan yunwa ta kwakulesu xa ki ga sun dawo da daddaya da daddaya" daga haka
yakumbo ta fita rike da roban dake dauke da dankali a ruwa, Umma ta bi ta da
kallo, Khadijah ta yatsine fuska tace "Umma the food is somehow" Umma
ta hade rai tace "Haka nan xa ki ci, ko ni ma baki ga hakan na ci ba"
Khadijah bata ce komai ba, Umma ta mike ta shiga d'an karamin dakin yakumbo,
har wani wari dakin yake gashi bbu ventilation don windown dan karami ne, ga
kaya ta ko ina, plastern dakin duk ya faffashe gashi ko leda babu, jikin umma
yyi sanyi ta daga dan karamin katifar da tayi bakikirin ta shiga gyaran dakin
ta fidda duk kwanukan da har da funfuna jikinsu sannan ta fara sharan dakin. Ko
da ta fito bayan ta gama bacci ta tarda khadijah na yi, ga shinkafar ta bar sa,
Umma ta tada ta ta bata Dari biyu tace "Kije kantin da kika je daxu ki
karbo Nutri milk da biscuit din hamsin ki xo ki ci" Karba khadijah tayi ta
fita. Sai kusan karfe biyar jikokin yakumbo uku suka dawo gidan sun yi dukun
dukun da dirty, duk kanana ne yaran, Umma ta masu wanka da sabulun wankin da ta
gani, ta xuba masu abinci, Khadijah dai na xaune sai kallonsu take da wani
expression, nama Umma ta fita ta nemo a anguwar ta xuba masu kan abincin ko
khadijah xata ci, nan ta tsince naman ta bar mata shinkafar wai ta koshi, sai
dab da Isha yakumbo ta shigo gidan tare da Almajiri da ya dauko kayan suyanta,
Sannu ta dinga ma su Umma, Umma ta mike ta taya ta karban kayan.... sha dayan dare
bayan su khadijah sun yi bacci Umma ta shiga yi ma Yakumbo bayanin abinda ya
kawo ta da Khadijah, bayan yakumbo ta gama saurarenta tace "Ikon Allah,
mugunta fa yyi yawa a duniyar nn yanxu ki kuluwa" Umma tayi shiru bata ce
komai ba, Yakumbo ta kyabe baki tace "Toh ni wannan ai ba matsala bace,
don dai in rike marainiya, bakomai wllh" Dubu 30 Umma ta kirgo ta ba
yakumbo tace "Wannan sai ki siya kayan abinci da indomie ki ajiye
yaya" makaranta kuma ayi mata Register da ta gwamnati idan Allah ya hore
min sai in canxa mata, dubu ashirin ta kuma bata tayi ma khadijah siyayyar
makaranta, yakumbo ta dinga godiya kamar ita ta ba kudin, sai kusan karfe daya
suka kwanta bayan yakumbo ta gama tsine ma matan mijin Umma, da su kawu.
Washegari da safe Umma ta dau hanyar kano bayan ta rubuta ma Yakumbo lambarta
kan cewa duk inda suka koma ta sanar da ita in case xata dawo duba khadijah,
dubara aka ma khadijah aka aiketa daga nan Umma ta samu ta bar gidan duk
jikinta a sanyaye, da Khadijah ta dawo ta kyallara ido taga ba umma ta dinga
ihu tana kuka a gidan tana cewa a kai ta gun ta, Bakin yakumbo a leko ta dauko
muciya tace "Kin ga wannan abun hannu na? To wllh da shi xan fasa maki kai
idan kika ci gaba da tona min asiri a anguwa, kaji min katuwar banxa, maxa ki
tafi tare da Fauxiyya ku siyo min ice da xan yi tuyan awara anjima" Jikin
khadijah na bari suka fita, matan gidan dake ta kallon ikon Allah suka ce
"Yo ke kulu da kike jiran fauxiyya ta kara wayo ki kai ta aikatu kina
samun kudi don me baxa ki kai wnn budurwar da aka kawo maki ba? Ai wannan da
ganinta bbu aikin da baxata iya ba har wanki" Yakumbo tayi shiru tana
kallonsu.
23Ko da suka
dawo gidan firewood kwara biyu kadai khadijah ta riko a hannu, fauziyya kuma ta
rike ya kusa shidda, daga matan gidan har Yakumbo sakin baki suka yi suna
kallon Khadijah da ta ajiye tana haki, yakumbo tace "Meye wannan din kika
dauko?" Da kyar khadijah tace "Firewood, it's too heavy, and it's
pricking me all over" a fusace Yakumbo tace "Kin ma uwar ki Amina turanci
ba ni ba, kuma ke kadai xaki koma ki kwaso duk wanda ga rage fauziyya baxa ta
je ba tunda ba ki da mutunci" korata Yakumbo tayi ta fita ta na share
hawayen dake sakko mata, mai firewood din ganin yanda take hawaye kuma kana
ganinta kasan baxata iya dauka ba ta dauko wani rabanta ta xuba mata su a ciki
ta daura mata a kai tace "Kina kai wa ki dawo min da roba na kin ji"
a hankali khadijah tace "Toh nagode" A haka ta isa gida tayi ta
tsayuwa da roba a kai wai bbu ke sauke mata inji Yakumbo, daga karshe ladi ta
kike ta sauke mata tana cewa "Idan ka xa ki kama jiki ki kama jiki ki
daina ma mutane kamar mara laka a jiki" Khadijah dai bata ce komai ba,
bayan ta juye iccen tace ma yakumbo xata mayar da roban, ko kallonta yakumbo
bata yi ba ta juya ta fita kai ma mai iccen robar ta. Yakumbo ce tsaye tsakar
gida bayan kwana uku da xuwan su Umma, tafi minti talatin banda kumfar baki da
masifa bbu abinda take, ga matan gidan da yaransu a xaune babu mai bata hakuri
sai ma xugata da suke, khadijah kuma na tsaye bakin xaure duk tayi wani duhu ta
rame sosai, idonta duk ya kumbura don kuka ga shatin bulala a jikinta, Ladi
tace "Yo da kinsan haka ne tun farko kema ai baxa ki fara daukarta ba,
meye amfanin yaron da baxa ka amfana da shi ba sai shegen son jiki da iyayi, ai
kadan ma kika mata da kin hada kin fasa shegen bakin turancin da take xagin
mutane da shi a gidan nan" Yakumbo na huci tace "Ai Amina ta cuce ni,
ta yaudare ni... Tasan haka shegiyar yar take xata kawo min ita tun farko, gode
gode da yarinya bata iya komai ba wanke wanke duk ta jika kayan jikinta tayi
awa da awanni a bakin kwararo, shara duk a gantale, gyaran daki gwara ka da
fauziyya mai shekara biyar, aike sai kayi yyi sau uku, har yau ta kasa iya hura
icce, girki dama ba a maganar sa, wa ennan yan mitsimitsi yaran idan na sa ta tayi
masu wanka ta shaka masu sabulu a hanci ko a ido, ni dama tun farko abinda ya
sa na karbeta na yi xatan xan amfana da ita ne, banda haka me xai kai ni kowa
na ta kansa a rayuwar nan gashi gobe ko jibi xa a xo a fitar mana da kaya har
ynxu ban kama wani gidan ba, ni wllh wllh da nasan gidan Amina sai in yi kudin
mota in mayar da ita ta bani kudi na don baxan iya kayan tsiya ba, dama can
Aminar ma ba wani kyautata min take ba uba ne kadai ya hada mu" Salamatu
tace "Ai irin yaran nan kyansu aikatu wllh, a can xa a horasu su
ladabtu...." Katse ta yakumbo tayi tace "Yar da har yanxu bata iya
shara ba xan kai aikatau, ai koramu xa ayi daga ni har ita" Ladi tace
"Yo ke nuna masu xa ki yi bbu abinda bata iya ba ai, a can xa su gyara
mata xama ta iya komai, mutanen da basu san darajar d'an Adam ba, ai tuni
wahalar da xa su dinga mata xai sa ta xage a nan kuma xata koyi komai, wannan
d'an abincin da kike bata ma take kin ci take yawo da yunwa can nema xata yi ta
rasa, hakan xai ladabtar da ita wllh" Yakumbo ta ja kujerar tsugunno ta
xauna tace "Kai amma fa kun kawo shawara, amma...." Sai kuma tayi
shiru ta kalli khadijah dake kallonsu, tsawa tayi mata ta ce "Fita ki ban
waje kije gun mai kanti da hamsin di ta dake gunsa ki amso min barkonu"
juyawa khadijah tayi da sauri ta fita gidan, Yakumbo ta mayar da dubanta gun su
Ladi tace "Toh Amina fa? Kunsan baxa ta yarda ba" dariya Ladi tayi
tace "Ka ji ki, sai ki gaya mata, barin ma yanxu tashi xa ku yi Ku bar
anguwar, shawara a nan shine kada ki kuskura ki gaya ma ko inda kika koma a
anguwar nan, kawai cewa xa ki yi ba ki ma samu gidan ba gidan wata yar uwarki
xa ki kafin ki samu, ke kuwa kije shanono abun ki ki kama ko daki daya ne bbu
wanda yasan inda kike, dama ba waya gare ki ba, har ki tara kudin da xa ki tara
da yarinyar daga nan idan ma mayar da ita gun Aminan xa ki yi sai ki ja mata
kunne ki mayar da ita" Yakumbo tayi murmushi tace "Dadina da ku akwai
shawara mai ma'ana, amma fa har da kudin da xan sa yarinyar a makarantar
gwamnati ta bani, yanxu haka ma da kudin xan je kama haya a shanonon, dubu
hamsin kuma jari xan ja na su omo da sabulu ina siyarwa, ita can na kai ta gun
aiki ana biyanta dubu uku misali, kun ga ni ban ma kai da nisa ba...."
Ladi tace "Toh gaskiya sai kin ba mu dubu dai dai mu da muka kawo shawarar
Ashe ma kudi gare ki har haka" yakumbo ta hade rai tana da ta sanin gaya
masu, rai a bace tace "Dari bibbiyu dai" daga haka ta mike ta shiga
cikin akurkin dakinta, sai ga ta ta fito da sauri tace "Toh yanxu wa xai
min hanya in kai ta gidan aikin, don ni gaskiya baxan tare da ita a sabon
gidana ba, ko yau aka samu gun aikin ba don yamma yyi ba kai ta xan yi, don
haka gobe da safe xan kai ta...." Ladi tace "Akwai wata kawata Habiba
dillaliyarsu ce, xan baki lambarta... Ko kuma ki sa katin dari a wayata mu kirata,
in sha Allah nasan baxata rasa inda xata kai maki ita ba" hakan ko aka yi
Yakumbo ta sa kati ladi ta kira Habiba, suka ci sa'a number ya shiga, bayan
ladi ta gaisa da kawartata tace "Bibalo dama wata yarinya ce da ake son
kai ta gidan aiki to shine muke son ki yi taimako" Bibalo tace "Kai
yanxu haka Ina hanyar dawowa daga kauye na mayar da wasu yara, amma gobe da
safe xa ki gan ni duk da bani da wa enda ke son masu aiki yanxu, amma nasan
kawata Abu baxata rasa ba don ta ma fi ni sanin gidajen manya" daga haka
suka yi sallama ladi ta katse wayar tana kallon Yakumbo don ba sai ta mata
bayani ba tunda a handsfree tasa ita ma ta ji komai, Yakumbo tace "Toh
Allah ya sa a dace, ni wllh ko dubu biyu ma xa a dinga biyanta na yarda"
tagumi tayi tace "Allah gani gare ka, kasa a karbi yarinyar nan ni
kuluwa" Washegari da safe kuwa sai ga Bibalo tare da kawarta da ta fada
Abu, Yakumbo dake ta washe hakora ta gaishesu suka amsa aka xaxxauna kan
tabarma ladi ma ta fito akurkin ta tana masu sannu da xuwa, bayan sun gaisa
Bibalo tace "Toh kinga ni bni da inda xan kai ta amma Abu tace kawarta ta
taba hadata da wata Hajiya mai neman mai aiki, da xata dinga share share da
goge goge sannan wanke wanke, akwai ma wata babbar mai aiki dake girki a gidan,
to Abu taje gidan ya fi sau uku ba a bude mata gate, yanxu ma gwada sa'a xa ayi
kuje har da ke kika wajen, idan sun dauketa to, idan kuma sun ce A'a sai ki
jira har a bukaci mai aiki a wani gidan sai in kai ta" Yakumbo tace
"A'a mu je kawai mu gwada sa'ar mu" Bibalo tace "Toh ki sallame
ni ni xan wuce" Yakumbo ta hade rai tace "In sallame ki? Me kika min
da xan sallame ki" Bibalo ta bude baki tace "Au haka ma xa ki ce, shi
kudin motar da nayi da kuma bata lokacina da na yi na xo nan tare da kawata har
xa ki ce min me na maki" mikewa Yakumbo tayi rai a bace ta shiga ciki ta
fito da dari biyu tana cewa "Ko daukar yarinya ba ayi ba xaki wani ce in
sallame ki idan ba hadama ba" dungura mata dari biyun tayi a gabanta rai a
bace, Bibalo ta dauka ta mike tace
"Ya fi babu ai" daga haka ta yi ma Ladi sallama da Abu tayi
ficewarta, Abu tace "Toh inji kinsan mu dubu daya ce sallamar mu?"
Yakumbo ta hade rai tace "Idan an dauki yarinya ba" Abu tace
"Toh gwara da kika san haka don ni baxan tsaya cacar baki ba, yanxu Ina
yarinyar take?" Yakumbo ta nuna mata khadijah dake ta fama da wanke wanke,
kwalalo ido tayi tace "Warcen da ta fi minti ashirin tana d'an wanke
wanken can, tun shigowar mu fa take wanke wanken kamar ayi kamar baxa ayi
ba" yakumbo ta marairaice tace "Haka take Abu, akwai iya aiki amma ba
sauri ne kawai, amma tana xuwa can nasan xa su gyara mata xama ta xama mai
hanxari" Abu ta tabe baki tace "Toh unguwar da nisa, don can Gra ne,
kuma wllh gidan babban mutane ne, ni dai Allah ya sa su dauketa, yanxu sai ki
tashi ku shirya ta hada kayanta ina jiran ku mu kama hanya" Yakumbo ta
mike da sauri ta shiga ciki tana cewa "Toh bamu minti biyar kacal"
tana shiga dakin ta kwalo ma khadijah kira, khadijah ta mike ta shiga da sauri.
Yakumbo ta jawota tayi kasa da murya tace "Dijangala ta mai gari, ba auren
talaka ba" tana washe hakora ta fadi haka, ita dai khadijah kallon ta
kawai take, Yakumbo tace "Kinsan inda xa mu yanxu kuwa?" Girgixa kai
khadijah tayi, Yakumbo tace "Gidan da xa a dinga biyanki kudi mai yawa in
tara maki in sa ki a boko, kai har in maki aure ma" khadijah tayi shiru
bata ce komai ba, yakumbo ta marairaice tace "Don haka muna xuwa kice kin
iya aikin komai, sai ki bada himma idan an saki aiki ki yi da sauri da sauri,
sannan don Allah Idan mun je gidan khadijah kar ki masu wannan yaran naki na
turanci kin ji koh? Kawai Hausa xa ki masu, idan kuma baki san Kalmar da xa ki
fada da hausa ba sai kiyi shiru abun ki ba sai kin yi turancin ba" yanxu
maxa canxa kayan Ki bari in tusa maki wa encan a jaka tunda basu samu wanki ba
idan kin je can ko ba ki iya wankin ba ki tsoma su a ruwa ki xuba omo ki
shanya" daga haka Yakumbo ta shiga tusa kayanta a wani karamin Ghana must
go, don har ta siyar da jakar da Umma ta kawo mata kayanta ciki, karfe tara da
kusan rabi su yakumbo suka bar gidan tare da Abu bayan ta yi ma yan gidan
sallama suka dinga yi mata Allah ya bada sa'a, tana rike da hannun khadijah
suka isa bakin titi, Abu tace "Amma kinsan ke xa ki biya kudin abun hawa
dai koh?" Yakumbo ta tsuke fuska tace "A kan me?" Abu tace
"A'a mayar da wukar ae dai naga ba xuwan kai na xan yi ba gidan don hka
idan kinsan gidan ke sai ki kai ta, yakumbo ta rikota da sauri tace "Naji,
mu je ya na iya, daga yau ai babu wanda xai xo yace in biya masa kudin napep
dai koh?" Ko tanka ta Abu bata yi ba ta shiga napep din da ta tsayar,
Yakumbo ta shiga ta daura khadijah a cinya. Tafiya ce mai nisa kamar yanda Abu
tace masu, tun da suka bar hayi dama Yakumbo ke addu'ar Allah ya sa a dau
khadijah gidan aikin idan ba haka ba asirinta ya tonu don ta sa rai da kudin da
xa a dinga biyan khadijah, tun da suka shigo anguwan Yakumbo ta saki baki kamar
yawu xai dalalo tana kallon gidaje na alfarma, Abu ta dinga nuna ma Mai napep
din inda xai bai, har suka iso wani cool silent anguwa mai cike da shuke shuke
a ko wani gate, ga bakin kwalta a shimfide daga farkon layin har inda yakumbo
ke tunani karshe ne, bakin wani gate Abu ta sa mai napep din ya tsaya, yakumbo
ta wage baki tana kallon jibgegen gidan da aka yi ma ginin xamani kamar ta sure
ta gudu, gidan ya hadu ne kawai don ita a ganinta duk ya fi sauran gidajen dake
layin haduwa, suka sauka sai kuma Yakumbo aka tsuke fuska da ta tuna kudi xata
bada yanxu, ta dungura ma mai napep din kudin da yace lkci daya kuma tana
hararan Abu, Abu da ko lura da ita bata yi ba tace "Toh Allah ka bamu sa'a
don kwanaki da na xo haka na sha xamana bakin gate rana yayi maganina ban samu
shiga gidan ba... Yakumbo tace "Yana da kyau mutum ya dinga fadin alkhairi
ko yayi shiru, yanxu me ya kawo wannan xancen, in sha Allahu ma sai mun shiga
don haka ki mana shiru" daga haka Yakumbo bta kwankwasa gate din a hankali
kamar me tsoron kada ya fashe don ita fa gani take kamar glass ne a
kauyancinta, ta kwankwasa ya kai sau hudu kafin wani da alamar mai gadi ne ya
bude yana kallonsu, Yakumbo ta durkusa har kasa ta gaishesa, yace "Wa ku
ke nema?" Yakumbo ta mike tace "Matar gidan muke nema ce mana tayi mu
samo mata mai aiki yarinya karama, to cikin ikon Allah gashi mun samo mai
haxaka, shine muke hadaka da Allah yaro ka bar mu mu shiga, mu gabatar mata da
aiken da ta mana" ya girgixa kai yace "Ai akwai mai aiki yanxu haka a
gidan don haka ban ji xa a bukaci warce xa ku kawo" Bakin yakumbo ya fara
rawa tace "Wllh xa su bukata dubeta fa kaga bbu abinda bata iya ba, sannan
Hajiyar da kanta ta sa mu ko daxu mun yi waya da ita tace sai mun xo, haba
yarona ka duba tsufana mana gashi daga hayin rigasa muke wllh" Mai gadin
yace "Toh yanxu ma ku kirata idan tace ku shiga toh shkkn" daga
yakumbo har Abu aka hadiye yawu da kyar don babu mai waya cikinsu, Yakumbo tayi
karfin halin cewa "Wallahi wallahi na mance wayar a gida kaji rantsuwar
musulmi" Abu ta saki baki jin rantsuwar da Yakumbo tayi alhalin taji
Bibalo tace bata da waya.
Post a Comment for "NOOR ALHAYAT 22"