NOOR ALHAYAT 21
Sai kusan
azahar suka dawo gida, Idon khadijah ya kumbura don kuka, Hasana na xaune
tsakar gida tana jajjagen tafasasshen nama da alama dai dambunsa xata yi,
Shafah kuma na daga xaune bakin kofa suna ganin shigowarsu suka yi shiru daga
xancen da suke ko wacce ta hade rai, Umma ta bude kofar ta ta ja khadijah suka
shiga ciki, xaunawa khadijah tayi kan kujera Umma na harararta tace "Duk
kika tsefe kan
nan ke kadai xaki saloon din baxan iya wahala ba, dubi idanuwanki
kamar warce aka yi ma duka, ke ba yarinya ba ki dinga ma mutane ihun
kitso" Khadijah ta kwanta kan kujera bata ce komai ba, Umma ta fita ta
shiga kitchen ta dau indomie biyu ta fito, Hasana ce tace "Gaskiya Abban
fadila ya dawo ya kasa ma kowa indomie ya ajiye a dakinsa tun jiya ake ta shiga
ana daukar indomie abinda yaran gidan ma sai su yi sati basu ci ba, wnn ai
mugunta ce" Umma tayi yar dariya bata ce komai ba ta shiga ciki, dama da
kwai hudu ta dawo gidan, don haka ta girka indomien a daki ta dafa kwan ta tada
khadijah da ta fara bacci ta bata nata sannan ta fita yin alwala, Da daddare
yau ma kamar jiya a karamar cooler shafah ta aiko ma Umma abinci, Tea ta hada
da yake tana da kayan shayin a daki ta fita da kanta ta siyo bread ta ba
khadijah ta ci ba tare da ta bi kan yan gidan ba. A can katsina kuwa neman
duniya kawu da matansa sun ma khadijah amma bbu ita babu labarinta, gidan da
suka fara xuwa kuwa gidansu sadeeq ne, nan mahaifiyarsa ta nuna masu the other
side of her don har sai da suka tsorata kuma tace kada warce ta sake shigo mata
gida, har station kawu yaje da gidan radio, bai taba kawo wa cewa Umma ta san
gidansa ba balle ta xo ta dauke khadijah, Duk da ba wai abun ya wani dame su
Hajiya salaha da Hajiya maimuna ba amma ganin yanda mai gidan nasu ya dage yana
nemanta yasa su ma suka xage, har shawara Hajiya salaha ta bada su kai karar
Hajiya Amina da d'anta, kawu ya gwaleta cike da masifa yace "Kinsan waye
uban yaron?" Hajiya Maimuna tace "Alkali" Kawu yace "Shine
xata dinga magana kamar mahaukaciya?" Ita dai Hajiya Salaha bata ce komai
ba. Washegari da safe Umma ta fita tare da Khadijah don sama mata islamiyyan da
xata fara xuwa, bata yrda ta kai ta wanda yan gidan ke xuwa ba ta kai ta wani
dake gaba da shi sosai, bayan ta biya komai ta wuce kasuwa tare da ita don
yankar mata uniform daga can tayi mata siyayya kananun kaya. Da yammacin ranan
Umma ta amshi girki, tuwon shinkafa da miyar vegetable take girkawa, Khadijah
na xaune kan tabarma bakin kofar Umma tana cin gyadar da Umma ta siya mata a
hanyarsu ta dawowa, da ta bare sai ta jefa ma wani kadangare dake tsakar gidan
yana yawo bawon gyadar, tsawa taji an mata ta waiga da sauri Hasana da
fitowarta kenan tace "maxa tashi ki tsince su don baki da bawa mai shara a
gidan nan" Umma kallo waje tayi daga kitchen din bata dai ce komai ba ta
ci gaba da girkinta, mikewa khadijah tayi ta isa gun da ta ke ta jefa bawon ta
shiga tsince su tana xubasu a shara har ta gama, Hasana ta nuna mata wasu bola
dake kusa da kofar Shafah wai taje ta tsince, Umma ta fito tace "Wannan
kuma ne baki isa ba" kujerar da ke kusa da kofar kitchen ta nuna ma
khadijah tace "Sit here" khadijah ta karasa da sauri ta xauna, Hasana
ta rike ha6a tana kallon Umma bata dai ce komai ba. Umma bata bar khadijah ba
sai da ta tabbatar ta yi bacci sannan ta tafi bangaren Abban Fadila, bata yi
mamakin ganin kishiyoyinta ba a xaune parlorn, da kuma alamar yana shigowa suka
bi sa don bai jima da dawowa ba, har Umma ta ajiye tray din abincin hannunta
kallonta yake, ta xauna ta gaishesa, bai amsa ba yace "Dama kin taho da
yarinyar nan ne don ki ci xarafin mutane Amina?" Umma ta kallonsa tace
"Ban gane ba" yace "Toh daga yau kar ki sake nuna iko a kan ta
Idan ba haka ba ki mayar da ita dangin ubanta, banda janyo yaro ya raina babba
don me Hasana zata sa ta aiki ki hanata, akan me? Meye amfanin xamanta gidan
idan baxa a ci moriyarta ba!" Umma dake saurarensa tayi murmushi tace
"Tun da na shigo gidan nan cikin yaransu akwai warce na taba sa aiki ta
min? Babu.... domin kuwa duk sun hanasu amma na taba kai maka kara? Ni wllh
matan ka basu isheni kishi ba Alhaji, banda kaddara ba lallai su gan ni cikinsu
ba balle su sa ni gaba, ina ce ni ka fara sani ma kafin su? Wllh basa gabana
balle inyi kishi da su, marainiya ce dai na daukota sae dai bakin ciki ya kashe
su tunda ba a kansu xata xauna ba" Tana kai wa nan ta fice daga parlon
idan sun fita sai ta dawo. Ka'ida ce duk safiya a gidan su Fadila ne ke yin
wanke wanken safe da sharan tsakar gida ko ma wacece ke girki kafin su tafi
makaranta, yau kam suna tashi da safe wanka suka yi ko wanne ta tafi ta saka
uniform, Umma bata ce masu komai ba tana ta soya dankalin irish da xa ayi
breakfast da shi a gidan, Khadijah na durkushe kitchen din sai dai ta bude
babban cooler a Umma ta xuba wanda ta soya, Umma ta gama soya Irish din da ta
fere gaba daya ta soya kwai, kananun yaran gidan ne suka dinga tahowa karban
nasu duk ta basu ko wanne sa cup din shayi da ta hada, Khadijah dake ta
kallonsu tace "Umma why are they so plenty?" murmushi umma tayi tace
"Just as the one ur uncles home" Khadijah ta langwabar da kai tace
"Noo, they are nt as much as this" Fadila ce ta taho kitchen din tace
"Anty ina kwana, ina dankalina" Umma ba tare da ta kalleta ba tace
"Idan kin gama wanke wanken can xan xuba maki" juyawa tayi ta wuce
sai ga Shafah ta fito, "Amina ban gane baxa ki ba Fadila kalachi ba, meye
dalili" Ko tanka ta Umma bata yi ba, ta hau masifa tayi mai isarta daga
karshe tace "Bar ta ita ce mayunwaciya Fadila, ta hada da Wanda ta ajiye
ma kanta da agolar da ta kawo su cinye, mu je in baki kudi ki siya kosai da
bredi a hanya, wanke wanken su shekara nan, in dai baxa ta ba ma agolarta tayi
ba" daga haka ta wuce ciki Fadila na biye da ita a baya, daga Hasana har
Shafah bbu warce tayi kalaci da girkin da Umma tayi, duk wainar shinkafa suka
aiki almajiri ya siyo masu a makwabta, Umma kam ko a gyalenta, wanda ya rage ra
kira almajirai ta basu ta hada kayan wanke wanke xata yi, Khadijah tace
"Umma na iya wanke wanke fa yanxu xan yi" da kyar ta amince ta bar
ta, Ganin yanda ta fara jika kayan jikinta Umma ta karbi kayanta ta shiga yi
tace mata ta tafi daki ta kwanta. Da rana cous cous umma ta girka gidan d'an
dai dai, daga ita sai khadijah a gidan don tun misalin goma su Shafah da Hasana
suka fita basu dawo ba, ta dibar ma kananun yaran gidan a warmer ta kai can
dakinta da miyar ta ajiye bayan ta xuba ma Khadijah, ta dawo ta tsaftace
kitchen din ta wanke tukwanen da tayi amfani da su da utensils sannan ta koma
ciki. Sai kusan karfe Uku su Shafa suka shigo gidan Hasana na cewa "Wash
wajen nan ba dai nisa ba Maman fadila, na xata bai fi tafiyar minti talatin ba
fa" Shafa tace "Nima farkon xuwa na na sha wahala sosai, ga hanyar
bbu kyau mutum na mota kamar ya hau jaki duk jikina ciwo yake..." Shiru
Umma taji sun yi suna kallon kofar ta, ita ke ganin su ta labule amma su basa
ganinta, suka kalli juna basu dai ce komai ba, kitchen Shafah ta wuce, can sai
ga ta ta fito tana kallon Maman walida tace "Ke kamar fa bata yi girki
ba" Maman Fadila tace "Bata yi girki ba kuma? Kin ga uban yunwar da
nake ji ga shi bani da kosisi kudin sun kare a kudin motar" Daga labulen
Umma Maman walida tayi suka yi ido hudu, d'an kame kame ta fara da farko, sai
kuma tace "Ba a da niyyar yin girkin rana ne yau a gidan nan ga yara su
kusa dawowa" Umma tace "Ehh" sake labulen tayi ta bar wajen
Maman fadila ta bi bayan ta, tana jin Shafah na jajjage a kitchen xa su dafa
indomie, ita dai tana xaune inda take. Uku da rabi yaran suka dawo kuwa, nan
Umma ta xuba ma kowa abincinsa ta ajiye masu tsakar gida, Shafah dake kan
tabarma ta kalli kishiyarta dake bakin kofar ta ita ma a xaune, yaran suna gama
ci suka fara shirin tafiya islamiyya, Umma ta sa Khadijah ta shirya cikin
dinkekken uniform din da tela ta kawo mata daxu, sai murna take har ta gama
shiryawa, har bakin makarantar umma ta rakata na ranan kadai sannan ta dawo
gida. Umma na kitchen tana girkin dinner ta dinga jin kamar kukan khadijah, ta
mike da sauri ta nufi kofar fita, su Shafah da Hasana dake xaune kusa da juna
suka bi Umma da ido, a bakin kofa ta kusa cin karo da Khadijah ta riko hannunta
tana kkrin cire Hijab din da ta rufe fuskarta tace "Me ya faru?"
Cikin kuka tace "Umma wannan yarinyar dake gidan nan ne ban mata komai ba
na gansu a hanya, she just slapped my eyes and pushed me na fadi a kan wani
dutse" Umma da ranta ya gama baci tace "Wace yarinya kenan?" Dai
dai nan walida ta shigo fuskarta tsuke, Khadijah ta nuna mata ita tana
shessheka, fixota Umma tayi ta wanka mata mari ta ja kunnenta tace "Don
uwarki kika sake taba min 'ya sai na cire maki hakori wallahi, muguwa kawai mai
halin banxa" daga haka Umma ta hankadata, walida ta fasa wani ihu kamar
xata tsaga gida tana kiran uwarta. Mikewa Hasana tayi baki bude tace
"Amina??? Ita walidar kika mara??" Umma ta juya tana facing dinta
tace "An mareta, ki taho ki rama mata, d'a ya fi d'a ne, ai wllh duk
shegiyar da tace 'ya ta baxa ta xauna lafiya ba gidan nan sai dai ita ta rasa
xaman lafiya, me marainiyar ta maku? Ko ba a cin arxiki dama a duniya, kishin
naku ya tsaya iya kai na mana, toh wllh duk ku ja ma 'ya yan ku kunne, duk
wanda ya sake ko da yi ma khadijah kallon banxa ne, sai nayi masa abinda bai yi
xato ba" tana kai wa nan ta tafi daki da Khadijah ta tura ta ciki tace
"Maxa ki canxa kaya" daga nan kuma ta dawo kitchen ta ci gaba da
abinda take rai bace, daga Hasana har Shafah haka suka bude baki suna kallonta
bbu wanda ya iya cewa komai cikinsu. Da daddare Abban Fadila ya dinga kwalo ma
Umma dake xaune kan darduma kira, ta mike ta fita don bata ma ji shigowarsa ba
amma tuni har ya shiga parlon sa, bin bayansa tayi ta shiga parlon tana masa
sannu da xuwa, bai amsa ba ta xauna ba tare da ta yarda ta kalli kishiyoyinta
dake xaune parlorn ga Walida a durkushe a kasa, Abban Fadila yace "Amina,
so nake xuwa gobe ki mayar da yarinyar nan dangin ubanta da kika daukota, I
agree zan yi sponsoring dinta ko tana can din, idan ya so duk bayan watanni uku
ko hudu sai ki je ki dinga dubata, I think that will better, I didn't buy d
idea of her staying here anymore...." Tun da ya fara Umma ke kallonsa a
sanyaye, Hasana da Shafah da aka wani hakikance kan kujera kamar wasu Hajiyoyi
xa a iya ganin murnar dake shimfide fuskarsu, trying hard to control her tears
Umma tace "Saboda me kace haka Alhaji? Kada ka mance yarinyar nan
marainiya ce ba ta da kowa, tun tana yar shekara biyu mahaifiyarta ta rasu,
mahaifinta kuma bai mata gatan nuna mata dangin mahaifiyarta ta ba, da na sansu
da can xan kai masu ita baxan kawo ta ba gidan ka Alhaji" Abban fadila
yace "Kiyi hakuri iyakar taimakon da xan ma yarinyar kenan, ko nawa ne
kudin karatunta xan biya idan ya kama ma da feeding expenses duk xan ba da,
kawai dai gidana ne baxata xauna ba, kuma baki min kara ba da har xaki daga
hannu ki mari diyata a ido don abun su can ya hada su, so tafiyarta xai fi, I
think that's all... Gobe ki hada kayanta ki maida ta inda kika dauko ta"
Umma da hawaye ke xuba idonta a hankali tace "Ina jin da ka sauwake min
kawai in tafi da ita xai fi don ni baxan mayar da ita dangin mahaifinta
ba" yana gyada kai yace "Kema xa ki iya sauwake ma kanki ai Amina ba
sai na sauwake maki ba" mikewa Umma tayi ta fita ta koma bangarenta, ta
shiga daki tayi kukanta mai isarta, duk tausayin khadijah ya cika xuciyarta, to
yanxu ina xata kai marainiyar nan, ita ba ta da kowa mahaifiyarta ta rasu da
sai ta kai ta gun ta tasan xata rike mata ita, bata da wani abun hannu don duk
cutar ta yayyin mahaifin khadijah suka yi a rabon gado bayan ya rasu, domin
kuwa kafin a ankare sun boye abubuwa da dama cikin dukiyarsa, banda haka da ko
boarding sai ta kai khadijah, har gari ya waye Umma bata ritsa ba tana ta
tunanin inda xata kai khadijah domin ta ma kanta alkawari first thing da safe
xata fitar da ita da gidan, yayarta warce suke uba daya dake Kaduna ta fado
mata ta yi shiru tana naxari.
Post a Comment for "NOOR ALHAYAT 21"