RAINA KAMA (BOOK 3) 33 (END)
BOOK 3 👉🏻3⃣2⃣
🔚END!! 😢✋🏻
...............Ban
San yanda zan musalta muku halin dana tsinci kainaba bisa ga wannan tukuyci na
Galadima, saidaifa kafin wani dogon lokaci dukkan Wanda keda alak'a dani yasan
da zaman wannan k'yauta, y'an uwa sai tayani murna sukeyi.
Y'an gidanmu dai saida sukaji wannan
bak'ar al'adar tasu ta hassada, amma sun d'an danne zukatansu sukaimin murna.
Washe gari bayan d'aura auren Sauban da
aunty mimi Galadima yaja gayyar abokansa da yayuna sukaje aka bud'e wajen
saloon d'ina. Akuma ranar ma'aikata suka fara gudanar da aiki, dan a can naje
na iske Galadima ni da tawa tawagar, na gana da dukkan ma'aikatana tare da basu
umarnin duk Wanda ya shigo wajen a ranar amasa abinda yakeso k'yauta, Washe gari
sai a fara na kudi.
Bikin Sauban ya gudana cikin k'ayatarwa,
itadai aunty mimi koda aka d'aura auren shikenan, tace wane biki kuma a
shekarunta, ana gama shagalin na Sauban tareda amaryarsa Ni'imatullah d'iyar
Mom da biyu, itama ta tare gidan mijinta professor Ibraheem Macid'o, musalta
muku yanda mukasha shagali 6ata lokacine.
Bayan bikin da kwana biyu Galadima ya fara
koya min mota, koya motar da taso zama shiririta, wai dole saidai na zauna a
cinyarsa ahaka za'a koyan, banida yanda na iya dole nayi hakan, cikin amincin
ALLAH a sati biyu nagama kwarewa, kwana biyu da faruwar hakan na yaye su
Amaturrahman bisa dagewar Ubansu akan shima k'annensu yakeso, danga Munubiya da
ciki🤭🤣.
Dole nayi wannan yaye yara suka koma wajen
Momma.
Kwanaki 10 cif dayin yayen saiga bak'ona
yazo, karkuso kuga murna wajen Galadima, wai hanyar samuwar ciki ta bud'e.
Ni dai shiru namasa ban tankaba. Randa kuwa
nayi wanka ai babu d'aga k'afa, ALLAH mai iko da falala kuma ya amince masa,
koda wata ya dawo babu jini babu alamarsa, hankalina ya tashi na birkice masa,
sai yayta tuntsuramin dariya da fad'in “Yarinya an fad'a miki nid'in na wasane,
zan zama Abbu a karo na biyu, ALLAH yasa su zama 3+3=6”.
Tashinai nabar masa falon ina
zun6ure-zun6ure, shikam yayta tuntsura dariya.
Nima nayi farin ciki da samuwar cikin,
tunda naga hakan shine burin mijina da farin cikinsa, sai kuma fatan ALLAH ya
sauke mu lafiya, dan wannan karon dai mun sa6a ni da Munubiya.
BAYAN WATA 6
Cikina ya fito sosai, ina samun tattali
da kulawar mijina, kai kace wannan shine cikin farko daza'a Haifa masa, ga
shak'uwa mai yawa dake tsakaninsa da yaransa, abin akwai birgewa mai yawan
gaske.
Ranar wata juma'a kawai mukaga an tashi
da wani gagarumin biki dabamusan na miye ba a masarautar, dama kusan kwanaki
uku kenan bak'i nata sauka, ni dai harna kasa hak'uri na tambayi Galadima,
yace, wlhy shima bai saniba.
Ana sakkowa daga massalaci sallar juma'a
aka hana Galadima shigowa gida, papi ya umarcesa da zuwa ya zauna inda aka
tanada dominsa.
Mamaki ya kamasa ganin gurin dank'am da
jama'a, addu'a kawai aka gudanar papi yabada umarnin fara abinda ya tara
mutane, daga baya koma mikenan jawabi zai biyo baya.
An umarci Galadima da tasowa zuwa saman
daddumar dasu Abie da manyan sarakuna ke zaune, ya zauna a tsakkiya shidai
zuciyarsa na faman tsitstsinkewa da bugun mamaki.
Turaki ya mik'e a tsanake zuwa gaban mai
martaba Sarki Jalaludden Abubakar, yay gaisuwa tare da risinawa sannan ya zare
rawanim dake kansa, gaba d'aga wajen aka d'auki kabbara, Abie yay k'asa da
kansa yana share hawaye, shidai dan anfi k'arfinsane kawai, amma daba yanke
wannan hukuncinba wlhy.
tuni bugun zuciyar Galadima ya k'aru
ganin Turaki ya nufo garesa, zaiyi maganar papi yay masa alamar yay shiru🤫.
Dole ya maida bakinsa ya tsuke yana
had'iyar yawu da k'yar.
Tsohon Sarki Jalaludden ya taso da
taimakonsa Turaki ya cire hular saman kan Galadima aka d'ora masa sabuwa dal,
sannan aka fara nad'a masa rawani akai, jikin Galadima sai tsuma yakeyi, ya
kafe papi da Abie da ido ko k'yaftawa bayayi, shikad'ai yasan a halin dayake
ciki, zufa sai tsatstsafo masa take a kowacce mahudar gashi dake a jikinsa.
Tsaf aka gama nad'a masa rawani jama'ar
wajen suka d'auki kabbara, yayinda za'a saka masa alk'yabba sai dogarai suka
baza riguna ana masa kirari.
Galadima yay k'asa dakai idonsa na
kwararar hawaye lokacin da kunuwansa ke jiyo masa jawabai daga bakin sank'ira.
“ALLAH ya d'auki rawani ya maida bisa kan
matashi kuma adali tsohon Galadima a yau yazama Sarkin wannan masarauta ta
gagara badau bisaga adalcin tsohon Sarki mai murabus a yau, masarautar gagara
badau tayi sabuwar amarya, a halin yanzu Mai martaba Muhammad Sameer Saifudden Abubakar
shine Sarkin wannan adalar masarauta, ALLAH ya tayashi rik'o, yabashi ikon koyi
da k'yawawan halaye irinna manyan wannan gida”.
Tuni waje ya harmutse da surutai, kowa na
fad'in albarkacin bakinsa.
Galadima kam saida papi ya rungumesa a
jikinsa sannan yafara samun nutsuwa, yayinda aka kawo Matawalle shima aka
zaunar aka nad'a masa rawanin wazirci, shine zai zama wazirin d'an uwansa Sarki
Muhammad Sameer Saifudden Abubakar.
Ai tuni guri ya rinca6e, babu maijin
zancen wani, kafafen yad'a labarai da social media duksun d'auka, masu murna
nayi masu bak'in cikin nayi, (kusan shigabanci, dolene kasamu masoya da mak'iya😭).
Mama Fulani da labarin ya Isar mata
zarewa tayi, sai surutai take Wanda ba kowa ke fahimtaba, Gimbiya zulfah kuwa
yanke jiki tayi ta fad'i wanwar, koda aka zuba mata ruwa ta farfad'o saita kama
aman jini zuciyarta yariga ya buga.
Ba'a katse su papi daga abinda sukeba aka
nemo doctor dazai dubata, saidai bata d'auki wani dogon lokaci ba tare ga
garinku nan.
Haka duniya take, lokacin da wani ke zuwa
sannan wani ke ficewa, hakanne ga gimbiya Zulfah, tatafi a randa Galadima ya
zama Sarkin gagara badau.🤴🏿😝😁👍🏻
Ni kaina da labarin zaman mijina Sarki
yau babu zato ya zomin saina rikice, na rud'e, ganin lamarin nake tamkar
tatsuniya ko mafarki, ga ciki, nama rasa murna zanyo ko kuka.
Ban fita a wannan magaginba saiga zancen
halin da gimbiya zulfah take itada mama Fulani, saikuma ga abinda ya girgiza
kowa shine mutuwarta.
***
Koda aka buk'aci jawabi daga bakin
Galadima kasawa yayi, shifa ganima yake a mafarki komai ke faruwa, shima
Matawalle ya kasa cewa komai, sai zirar da hawaye kawai sukeyi Wanda hakan ya
birge kowa da bada mamaki.
Abubuwa sun rinca6e fiye da yanda bakwa zato
a masarautar gagara badau, bayan an sallaci gawar gimbiya zulfah aka kaita
makawancinta na gaskiya y'ay'anta na kuka da y'an uwanta.
Kiri-k'iri ganin mijina ya gagareni har
dare, Abdurraheem sakin k'ulafucin Uba sai kuka yake yak'iyin barci, su Amaturrahman
da sukayi nasu na lallashesu sai suka kwanta, dan sunsaba da yayi sallar isha'i
yana tare dasu, amma yau shiru babu amo babu labari.
Nikam sainaji abin yana cizon zuciyata,
indai wannan mulki zaisa mijina yin nesa dani bana farin ciki, saigani da kuka
rurus.
Sai misalin 12pm Sarki Muhammad Sameer
yasamu rakkiyar zuwa sashenmu.
Ina zaune afalo nayi tagumi naji alamar
mutum tsaye a kaina.
A firgice na d'ago kaina ganin mijina
saina mik'e a firgice tare da fad'awa jikinsa na saki kuka.
Shima rungumeni yayi sosai yana sakin nasa
kukan, sannan ya d'aukeni cak zuwa cikin bedroom d'in ya ajiyeni a saman gadon,
kuma rungume juna mukayi muna cigaba da kukan mu.
Tsawon lokaci muna haka, sannan yafara
dakatar da nashi yana lallashina. “Munaya kinga abinda su papi sukaimin ko, ni
dai banason sarautarnan, amma sunk'i saurarena, wlhy banaso munaya, banaso
nidai”.... Yakuma fashewa da kuka.
Tausayinsa saiya kuma kamani, nakuma
rungumesa tsam a jikina, abinda kaga ya saka Galadima kuka aiba k'arami beneba
kuwa. Daure zuciyata nayi na shiga lallashinsa.
Na kuma rungume sa sosai cikin nutsuwa
ina fad'in, “Mijina ba komai ne ake tuntu6e dashi bisa shiryawa kaiba, wani
abun tunkan kasan tuwarmu gudan tsoka rubutaccene a littafin k'addararmu, babu
wani d'an Adam da alk'alamin k'addararsa ke a tafin hannunsa, gudun zuciya yafi
na k'afafu sauri, idone kawai ke iya banbance fari da bak'i, baki kuwa
d'and'ano kawai yake tantancewa, aikin kunne kuwa jine kawai da banbance k'arar
sauti, baka tunanin duk mutum mai baiwa ALLAH ke ba damar banbancewar? Irinku
kune kuka cancanci mulkin al'umma, domin kuwa bashine burinku ko damuwarkuba,
kune zaku iya adalci da tausayin na k'asa daku, ka amince dayin wannan
sadaukarwar ga iyayenka da al'ummarka, domin samun damar k'ar6ar sakamakonka
wajen adalin Sarki mai tarin rahma da jin k'ai. Zuciya da tunani duk mallakar
gangar jikice, haka gudanar jini da motsin ga6o6i, su papi sune sukasan tayaya
ka cancanta kaida d'an uwanka, har suka d'auki wannan nauyin suka d'ora muku,
Ku kar6i yau d'unku da hannu biyu, domin jiyanku tazama labari, Ku hidimtawa
gobenku domin Ku ribantu da jibinku, wannan shine kawai masalaha mai k'ayatarwa
ga mu ahalinku, masu ganin baka kaiba saisu ajiye makamansu su tabbatar da ka
kai d'in, kazama RAINA KAMA mijina, kosu amince, ko karsu amince kaine RAINA
KAMA”.
Tsam ya rungumeni yana fad'in “kece RAINA
KAMA munaya, domin a dalilinki ne suke ganin nayi feeling, har ake ambaton ni
da sarauta har Abadan, su ganin auren talaka shine k'ask'anci, shine ke nufin
ka koma k'asa, a yak'ininsu saika auri y'ar wani mashahurin Sarki ne darajarka
ke a idonsu, sun manta ba talaucine ya rarrabe tsakaninmu ba, Wanda yafi wani
bautar ALLAH shine mafifici a cikin bayi, su Papi sun tabbatar min kina d'aya
daga cikin manufofinsu na bani Sarauta, sunason tabbatarma duniya da mai
sarauta zai iya auren d'iyar talakawa, basai y'ar mai mulki irinsaba, sunason
duniya tasan shima talaka akwai baiwa da darajar da ALLAH yamasa fiye da mai mulki,
sunason duniya tasan ba mai mulki bane mafi k'ololuwar daraja a cikin bayi,
kowanne Bawa da tarin daraja da baiwar da ALLAH ya masa, kinga kuwa kece RAINA
KAMA my heartbeat, ko ni kin zamemin RAINA KAMA balle su da suke tunani ba
daidaiba”.
Kasa magana nayi, muka rungume juna tsam
cikeda so da k'auna.
An cigaba da gudanar da gagarumin biki na
wannan nad'in sarauta, kwanaki 5 cif akayi anayi, danma mutuwar gimbiya zulfah
ya rage armashin bikin.
bayan lafawar komai da sati biyu mukaje
India Galadima ya maida dukkan harkokinsa nacan ga Sauban daya zama tilas ya
d'auki matarsa su koma can, dole kuma ya ajiye aikinsa duk da sonsa da yake, su
Vijay zasu cigaba da kulawa da komai, idanma suna buk'atarsa zai cigaba da kawo
shawarwari.
Mun dawo da kwanaki biyu aka gama kammala
aikin Company d'insu na nan Nigeria, Wanda dole su Vijay sukazo suka aiwatar da
komai, zuba masa kaya da d'aukar ma'aikata da dukkan abinda yakamata ayi.
Wata d'aya cif a tsakani aka basa
umarnin shirya fara gudanar da mulki, Shiga fada da nad'e-nad'en sarautu da
zaiyi, dakuma Neman matar aure dazai k'ara.🤦🏻♀
Wannanfa Abu ya tayarmin da hankali sosai,
ga cikina ya tsufa, aiko na birkice masa naita kuka, kai wlhy kishiya da ciwo,
duk dauriyarka saikaji babu dad'i, musamman idan kana son mijinka kuma.
ALLAH Sarki Momma Uwa ta gari, itace
taita kwantarmin da hankali da kalamai masu sanyaya zuciya, hakama Galadima
yayta lallashina da nunamin muhimmancin lafiyata kodan tsohon cikin dake
jikina, itama Munubiya da Innarmu haka, nima da naga mijina da kowa na son
ganin kwanciyar hankalina saina kwantar d'in, na kar6a k'addarata da hannu
biyu.
Da farko d'iyar Mom akace ya aura, bankuma
San yanda akayi ya zameba yace yabani wuk'a da nama na za6o masa dukkan wadda
tamin, koya take wlhy zai aura shikuma.
Kusan sati biyu daya bani sainaita
nazari da hasashen wazan za6a masan, haka kawai matashiyar budurwa Hafsat da
muka ta6a had'uwa a jirgi ta fad'omin a rai, lokacin inada cikinsu
Amaturrahman, tamin wani taimako da Galadima ya yaba mata sosai, Wanda harna
kamashi yana satar kallonta, amma a time d'in saiya basar kamar yanda halayyar
tasa take, Nima sai banja maganarba, mukan gaisa da Hafsat miss xoxo time to
time, amma mun dad'e bamu had'uba, inagama tun taron sunan su Abdurrahman da
tazo.
Muna zaune dashi na lalubo hotonta da
mukayi ranar suna tare na nuna masa.
“My king wannan ta makane?”.
Kar6ar Hoton yay yana kallo, yay wata
irin zabura yana ajiye hoton gefe da hararata, “Kina zargin ina sontane komi?”.
Murmushi nayi ina d'auke hoton, nace,
“yanayinka da amsarka kawai ta wadatar dani ranka ya dad'e, danason ma kanason
miss xoxo da tuni na had'a wannan alak'ar wlhy, ALLAH yabamu zaman lafiya”.
Duk yanda yaso bijirewa da nuna ba haka
bane ban sauraresaba, na nunama Momma photo aka shiga binciken miss xoxo. A
cikin sati biyu aka gama komai, duk da itama ta nunamin bata aminceba.
Duk da kishi na cina haka na jajirce
tsakanin borensu, babu 6ata lokaci akasha biki.
Da kaina namata rakkiya d'akin mijinta a
maimakon rakkiyar jakadiya da har yau bai za6aba., nai k'ok'arin danne kishina
nai mana addu'ar zaman lafiya. Na dawo d'aki ina kuka da rungume y'ay'ana,
akuma asubahin farko na farka da nak'uda. Wadda har aka wuce dani asibiti Sarki
Muhammad Sameer bai fitoba, yanacan yana lallashin amaryarsa daya maida
cikakkiyar mace a daren jiya.
Na sauka lafiya na haifi d'a namiji mai
kama dani sak, sai daga baya labari ke kaiwa kunnen Sarki Muhammad Sameer, ya
rikice da murna, gashi babu damar binmu a asibiti, dole ya hak'ura har muka
dawo.
Fad'an farin cikin samun wannan
haihuwa ga Sarki 6ata lokacine, hakama su Abie da tsohon Sarki da a yanzu suka
koma daga gefe suna koyama yaransu dabarun mulki.
Washe garin suna kuma Sarki Muhammad
Sameer ya zauna a fada, tare da yin wasu nad'e-nad'e, hardasu Badi a ciki,
sarkin mota da Sarki k'ofa sunce iya wuya suna tare dashi.
Haihuwar danayi Ce ta d'auke hankalina
daga damuwar kishin mijina da wata, duk da bana nuna kishin dama a fuska balle
Hafsat ta fahimta, dan Alhmdllh tarbiyyarta tasa muke zaune lafiya, saima
k'ok'arin jan yarana da take a jikinta, yarona yaci suna Abdul-fatah, papi
kenan, daga Hafsat kuma Sarki Muhammad Sameer yace ya tsaya, mata biyu sun
ishesa, ALLAH yamusu zaman lafiya.
Rayuwa ta cigaba da gudana cikin
nasarori, wajen saloon d'ina nata ha6aka, da kud'in shigarsa na d'auke kaso
mafi tsoka na nauyin gidanmu, mahaifina ma yasamu sarauta da Sarki Muhammad
Sameer ya nad'ashi, hakan yamin dad'i sosai.
Munubiya itace mai kula da ladies
mirror, office d'inma ita ke zamansa time to time, danni banida wannan damar a
yanzu, fitarma sai wadda ta zama tilas nakeyi.
Sarki Muhammad Sameer nada watanni takwas
akan mulki ALLAH yayma mama Fulani rasuwa, tsakaninta da papi wata 1, wannan
rasuwa biyu ta matuk'ar girgizamu, dan Sarki Muhammad Sameer kusan zarewa yayi
akan mutuwar papi, yabasa gudunmawa mai yawa a rayuwarsa, wadda mantata abune
mai matuk'ar wahala a garesa, mai makon babansu Nuren ya hau mulkin, sai yasa
aka nad'a Nuren d'in. Sarki Nureddin ALLAH ya tayaku ruk'o baki d'aya.
Babu dad'e da nad'im Sarki Nureddin akasha
shagalin bikin Saleem da Feena, bikin dayay armashi sosai, dan itace last mace
dasu innarmu zasu aurar, saura y'an k'ananun y'ay'ansu Aryaan, Aiyaan da Ahmad,
Wanda a yanzu sun zama samari masha ALLAH, dan duk suna sa2 a secondary school,
jirama Sarki Muhammad Sameer yake su kammala ya had'asu da Khaleel su wuce
karatu.
A yau kuma Munubiya ta kawo mana ciyara
da y'ay'anta Meenal, Ameen da k'aramar Ai'sha muna ce mata Islam. Munsha hira
sosai, taita mamakin yanda nake zuba mulkina, yo matar Sarki uwar gida wasace😂👍🏻🤸🏻♀🤸🏻♀.
BAYAN WASU
SHEKARU
Rayuwa ta shud'a ababen dariya
Dana kuka sun faru iri-iri, an haifi wasu wasu sun rasu, hak'urin zama Na yau
da kullum, wataran a 6ata ma koka 6atama wani.
Zuwa yanzu kam munyi rashin wasu daga
cikin iyaye y'an uwa zuwa kakanni, ALLAH yayma Abbanmu rasuwa shida wasu matan
gidanmu biyu, inno ma haka, yayinda innarmu ta gama takaba sai danginsu sukazo
suka tattarata zuwa k'asarta ta haihuwa, muna kuka tanayi hakama jama'ar
gidanmu da y'an anguwa, Dan bamason tafiyar tata, amma hakan gatane a gareta
komawa cikin ahalinta, a gagara badauma kam mun rasa da yawa, tsohon Sarki
jalaludden Abubakar ALLAH ya masa rasuwa sakamakon ciwon hanta, wadda ya dad'e
da ita a jiki Ashe, wannan ma shine dalilinsa na dagewa akan Abie ya kar6a
mulki. Saida rayuwa tazo gangara yake sanar ma Abie d'in Wanda shima zuwa yanzu
girma ya kamashi sosai, Dan yatsufa komai ma sai an masa, danma ALLAH yabashi
gwarzuwar mata Momma, dukda itama girman ya kamata bata gajiyawa da hidimarsa.
Sarki Muhammad Sameer Saifudden
Abubakar, adalin Sarki da talakawa ke alfahari da mulkinsa, musamman ma matasa
da akullum cikin bin hanyoyin inganta rayuwarsu yake, suna zaune lafiya shida
wazirinsa kuma d'an uwansa, babu wani y'an ubanci ko k'iyayyar juna, k'yawawan
zukatansu sun sakasu kawo canji mai yawa a wannan masarauta, da farko su Talba
ne sukaso kawo musu hargitsi, tunda suka fahimci haka sai aka sakasu barin
k'asar tilas suda iyalansu, tun daga nan masarauta tadawo dai-dai.
6angaren Harun ma ya fito tun lokacin
daya cika shekaru goma, amma bisaga karamci Na adalin Sarki Muhammad Sameer
saiyasa aka kawosa fada, yay masa hidima mai yawa, wadda ta sakashi kuka da
gurfana gaban Sarki Muhammad Sameer Neman gafara da nadama akan abinda ya
aikata, Muftahu da ayanzu yake rik'e da sarautar matawalle yay murmushi yanama
Sarki Muhammad Sameer magana da ido akan ya yafe masa tunda yayi laushi, Sarki
Muhammad Sameer ya jinjina kansa yana murmushin nan nasa Na k'asaita da cizar
lips.
Yafewar da Sarki yamasa Ce tabashi damar
Neman gafara ga Uwargida Sarauniya Munaya itama, babu wani ja'inja tace ta
yafe, ba'a barsa ya zauna masarauta ba, anmasa hidima mai yawa da aure aka
sakashi komawa wata k'asa, Dan bawai kowa ya gamsu da tuban nasaba, ayanzu kuma
Sarki da wazirinsa basa buk'atar duk wani mai ru6a66iyar zuciya a kusa dasu.
Sarauniya Munaya uwargidan sarki mai
fad'a aji a wannan masarauta, jarumar mace mai nagartacciyar zuciya,
hamshak'iya wadda ayanzu tazama babbar mace jerin manyan mata sahun faro wajen
dattako da mulki dama dukiyar itada y'ar uwarta Munubiya.
A yanzu yaranta takwas a duniya,
Amaturrahman, Abdurrahman, Abdurraheem, Abdul-fatah, Ai'sha, Zeenah, Saifudden,
jalaludden Auta kenan, Ai'sha da Zeenah da suke kira da Safah da marwah tagwayene,
bayan haihuwar Abdul-fatah tayisu suma, daga nan sai mai sunan Abie, dakuma
auta takwaran tsohon Sarki babansu matawalle konace waziri, ayanzu kam duk
sunzama manya, musamman su Amaturrahman da suke manya duk suna a jami'a, suna
k'asar India tareda uncle d'insu Sauban da ayanzu shima yazama babban mutum,
yazama babban d'an kasuwa bisaga jagorancin dukiyar d'an uwansa, yayinda su
Aiyaan da Khaleel, Aryaan, Ahmad ke taimaka masa, kaga matasan samari abokan
juna kenan, kansu ahad'e yake su hud'unnan, sune yanzu duniya ke yayi take son
gani a fanin na'ura mai kwakwalwa wato Computer, Wanda ayanzu Abdurraheem da
Abdurrahman suke k'ok'arin dannesu, Dan matasan samarin biyu sun zama magada
kwakwalwa irinta mahaifinsu Sarki Muhammad Sameer suma.
Itama Hafsat yaranta hud'u, biyu mata
biyu maza, wad'anda duk suka taso a hannun Munaya, akwai zaman lafiya da
k'aunar juna tsakanin Hafsat da Munaya mai birgewa, Wanda ya kawoma Sarki
Muhammad Sameer kwanciyar hankali da k'yautata musu gwargwadon k'arfinsa, kamar
yanda suma suke k'yautata masa da dukkan iyawarsu.
Yaran Munubiya itama 6, Dan itama 8 d'inne
ta haifi biyu babu rai, Ameen yana tare dasu Abdurraheem, yayinda meenal
takanyi Rabin rayuwartane a masarautar gagara badau, saboda batada k'awa wadda
tawuce Amaturrahman. Inhar basa Masarauta to sunacan gidansu meenal d'in, sun
zama y'an mata ababen birgewa, ita meenal tana masifar son Abdurraheem ne
shikuma k'asaita da muskilanci irinna ubansa Sarki Muhammad Sameer tariga
tazama jinin jikinsa, yata basar da ita kenan, wannan Abu Na cimata rai, amma
aduk sanda ciwonsa zai tashi tafi kowa shiga damuwa, idan kuma taga yanda Ameen
da Amaturrahman ke soyewarsu saita kumajin kanta a damuwa, shikam Abdurrahman
Niger ya tsallaka, Dan d'iyar Sarki Issifa da Sarauniya Ayusher Rabi'a
(Amatullah) yakeso da k'auna, ya rikice sosai, haka kawai saiyayi shiri wai
yatafi yima Inna Hutu, nanko wajen Amatullah yaje.
Wannan hutune Na k'arshen shekara daya
kasance duk yaran suna Nigeria, saboda bikin su Aryaan da akasha babu dad'ewa.
Sarauniya Munaya kishingid'e a kilisarta
hadimanta nata hidima a gareta, matasan samarin y'ay'anta suka nemi ison
shigowa gareta.
Izini ta basu, tareda sallamar dukkan
Hadimanta.
Abdurraheem da Abdurrahman suka shigo,
Kansu d'aya, kamanninsu d'aya, halayyace kawai ta banbantasu, Abdurraheem halin
Sarki Muhammad Sameer ne gaba d'a a jininsa, yayinda Abdurrahman yazama mai
irin halayyar Uncle Sauban da Abie.
Har suka zauna idonta Na kansu, sukai zama
irinna k'asaita suna gaisheda mahaifiyar tasu.
Fuskar Sarauniya Munaya d'auke da Murmushi
ta amsa, takai dubanta ga Abdurraheem dashi ko kad'an bashida yawan magana.
“Abdurraheem saunawa zan maka magana akan
aske sumarnan ne?”.
Lips d'insa ya cije (d'an gado kenan😂) yanad'an 6ata fuska.
“A gafarceni Ummu, wlhy zan Aske, jiya
nafita zanje shagonki askin sai takawa yayi kirana ya Sani wani aikin, amma
Ummu shima Abdurrahman kimasa magana ya yanke wannan k'umbar, ALLAH
k'yank'yaminta nake.......”
Harara Abdurrahman ya zuba masa, zaiyi
magana Sarauniya Munaya ta katseshi tana tashi zaune, “Abdurrahman naga
hannunka”.
“Ummu karki yarda da gulmar yaronnan
ALLAH, yatsa biyunefa”. Ya k'are maganar da kuma harar Abdurraheem daya ta6e
baki ya cije lips.
Sarauniya Munaya tace, “Yimani shiru,
nabaku nanda dare wlhy kowa ya cire k'azantar jikinsa, ina kuma fata anje an
bama Abie magungunansa?”.
“Eh Ummu, Abdul-fatah ya bashi, yanzuma
daga sashensu muke barci yakeyi, amma su Amaturrahman nacan sun cikama Momma
kunne da surutunsu Na tsiya itada Meenal”.
Murmushi Munaya tayi, Dan ita babu abinda
take gani tattare da Abdurraheem sai Mijinta, shikuma Abdurrahman rashin iya R
kawai ya gado shida Safah da Marwah duk basu iya R ba, to ga Saifudden nanma
akwai k'asaita tsiya, d'an k'arami dashi sai mulkin tsiya, ga jarabar son
girma, bawani girman jalaludden yayiba amma inkaga yanda yake basa umarni
saikaci dariya, hakama yaran Hafsat.
Sarauniya Munaya tacigaba da hira da
yaranta da musu nasihar tsare mutuncin Kansu kamar yanda ta saba.
Wayarta da sak'o ya shigo ta d'auka tana
dubawa.
Sarkine da kansa.
Gaskiya ina buk'atar jin d'umin my mata.
Murmushi Sarauniya Munaya tayi tana
kallonsu Abdurraheem da suka satar kallonta, idan kaga irin wannan murmushi ga
mahaifiyarsu to akan Abbun sune kawai.
Tad'an hararesu tana fad'in “Takawa ba yana
fada ba?”.
“A'a yana turakarsa, Dan zamu shigo nan
mukaga fitowarsa daga fada”.
Nanma murmusawa Munaya tayi kawai, ta
tashi zaune tana gyara zaman alk'yabbarta, “Kuje Sweetheart Na nemanku, amma Ku
dawofa da wuri, kunsan yau ranace ta musamman da takawa ke zaman hira damu,
karkuyi sakacin dazata wuceku, akwai sak'o a d'akina saman mirror Ku d'auka
akai mata, zan kirata namata bayani”.
A tare suka amsa da to Ummu.
Ta mik'e ta shiga bedroom d'inta, mintuna
kusan biyar saigata ta fito tabi wata hanya da zata sadata da sashen Sarki
Muhammad Sameer kai tsaye batare da kowa ya gantaba, wannan tsarinsane, Dan
baya buk'atar wata jakadiya a tsakaninsa da matansa, yace suke rura munafunci a
tsakanin matan Sarki.
Kallon juna Abdurraheem da Abdurrahman
sukai, sukayi murmushi tareda tafawa, soyayyar iyayensu Na masifar kashesu,
burinsu shine suyi koyi, tafawa sukayi sannan suka mik'e domin cika umarnin Na
zuwa wajen gwaggonsu Munubiya, Dan ita kad'ai ummunsu take kira da Sweetheart.
Sarki Muhammad Sameer Na kishin gid'e a
k'ayataccen falonsa dayaji kayan more rayuwa, lap-top yake sarrafawa hankalinsa
kwance, sai tataccen ruwan tuffa dake ajiye a gefensa, k'amshin matarsa
gimbiyarsa komansa da yajine ya sakashi d'ago k'yawawan idanunsa yana kallon
k'ofa tareda amsa mata sallamarta yana zare medical eyeglasses d'in idonsa.
Tunda ta shigo ya dakata da danna lap-top
d'in ya zuba mata ido kawai, cikeda tafiyar k'asaita ta isassun mata ta k'araso
gareshi. Zata zauna gefe ya kamo hanunta yana tashi zaune sosai ta zauna saman
cinyarsa, su duka ajiyar zuciya suka saki, ya sark'e idanunsu a waje d'aya yana
mata murmushin da ita kad'ai take samun ganinsa a fuskarsa, cikin matso da
fuskarsa gab da tata ya hura mata iska tafara farfar da idanu.
Lumshe idonsa yayi yana cijar lips, a
hankali ya furta I love you my Queen, my Everything? ”.
“i love you too my king”. Munaya tafad'a
a hankali itama cikeda salo.
Bashida za6in daya wuce had'e bakinsu,
dukda girma ya kamasu harda manyan y'ay'a da zasu iya aurarwa soyayyarsu bata
tsufaba, tun anayi a afalo harya d'auka abarsa suka shige bedroom.
Bayan wasu y'an lokuta suka fito wanka
fuskarsa kowanne d'auke da murmushi, Munaya ta kalli mijinta cikeda so da
k'auna.
“My king miya faru kabaro fada da wuri
haka?”.
Murmushi Yamata mai saka zuciya nutsuwa,
ya zauna kusa da ita yana kwantota jikinsa, cikin magana rad'a yace, “kewarkice
kawai, jinai bama Na fahimtar komai da ake a fadancin, sai gizo kikemin kawai,
shiyyasa Na buk'aci shigowa Na huta, bagashi Na huta d'inba?”. Yay maganar
cikin d'age gira d'aya da kashe min ido d'aya”.
Murmushi nasaki ina kuma shigewa
jikinsa, nace “Anya kuwa a tarihin masarautar nan anta6a Sarki irinka?”.
Murmushi Sarki Muhammad Sameer yayi
yana d'ago fuskarta da sark'e idanunsa cikin nawa, “miyasa kika fad'i haka?”.
Murmushi nima nayi ina shafa k'irjinsa,
“Kaine Sarki Na farko dakan gana da iyalansa aduk lokacin da yaso, babu maganar
jiran dare, kaine Sarki Na farko dakan ware wasu ranaku Dan zaman hira da
dukkan iyalansa kawai amatsayi Na Uba ba sarkiba, lamarinka akwai k'ayatarwa
yalla6ai”.
Hararta yayi dajan hancina, “bazaki
manta da sunannan ba ko?”.
Dariya mai d'aukar hankali nayi ina
fad'in, “kaida sunanka, yalla6ai Na yalla6iyarsa”.
Shima dariyar yayi yana kuma rungumeni a
jikinsa, “Wlhy kin zuba rashin ji sosai My mata, bak'aramar wahala nashaba
lokacin auren Contract d'in nan, naga alamar tsiwarki Safah ta gado gaba d'aya,
yarinyarnan batada tsoro ko kad'an, ga iya magana, tafi Marwah wayo sosai”.
“Ai Marwah miskilanci da gatan da Hafsat
ke musune ke d'awainiya da ita kawai, yarinyarnan miskilancinka ta gado itama,
itada Abdurraheem da Saifudden da Khadeeja (d'iyar Hafsat) wlhy duk
hallayarkace, rashin son hayaniya, miskilanci, k'asaita da basar da Abu tamkar
bai damesuba, rashin iya r, ga salon cizar lips irin naka da Abdurraheem keyi
shida auta jalaludden, nifa saidai naita kallonsu idan sunayi, Dan kai nake
hangowa gaba d'aya a zamanin k'uruciya, musamman Abdurraheem ”.
Sarki Muhammad Sameer yay murmushi da
sumbatar goshina, a hankali yace, “my mata k'yan d'a......?”.
Nace, “yagaji ubansa”.
Yace “kin gama magana Sarauniyar sarakuna,
time d'in barci yayi”.
Bai barni nak'ara maganaba ya jani saman
gadon tareda ja mana bargo mara nauyi.
Har barci ya kwashesa ni nakasa nawa, Na
zuba masa idanu ina tuna abubuwa masu yawan gaske da suka faru a tsawon shekaru
25 da aurenmu, Galadimana Muhammad Sameer yanzu yazama Sarki Muhammad Sameer,
mutum mai tarin k'asaita, mulki, k'yawawan halaye masu nagarta, hak'uri, kawaici,
dattako, iya zama da mutane, tausayin Na k'asa da shi, k'yauta da k'ok'arin
tsare gaskiya, wad'annan duk halayyarsace dake kuma k'aramin k'aunarsa da
addu'ar y'ay'anmu koyi dashi, Na matsar da fuskata kad'an ina manna masa Sumba
a la66a, yad'an bud'e ido yamin murmushi dakuma sanyani a jikinsa. Daga nan
nima barcin yay awon gaba dani.
Sai bayan sallar la'asar sakaliya Na
baro sashen Takawa, nafito sainaji sha'awar lek'a Hafsat, Dan duk yau bamuga
junaba saboda tayi bak'i a yammacin jiya, tsakaninmu ma akwai k'ofar dake
sadamu da juna batareda rakkiyar kuyangi ba, saidai abinda yasaka jikina
sanyaya iske Hafsat a k'aramin falonta tareda bak'inta suna zugata akan
zamanmu, ta mik'e tsaye karta yarda Na cigaba da mulkarta, kowa yasan nama fi sarkin
mulki, Dan sai abinda nace yakeyi koda a fada, itako tazama tamkar wata sa
d'akarsa.
Fushin daya tasominne yasani daka musu
tsawa.
Bilyn Abdull da Hafsat suka rikice, ko
kad'an basusan da zuwan Sarauniya Munaya falonba, hakama Maman kadee da Aysha
DanSabo da Rano, party zarah, Ummu Basheer, khaleesat hydar, Ummi Ai'sha, Faxy
fashion, Zee Bawa, zee Yabour, Ayusher Muh'd, Mamugee, Asmy b Aliyu, Silmzy,
Feedohm, Bily galadanci, Safiyya Huguma, kdeey duksun rud'e, Dan dama sune
bak'in Na Hafsat miss xoxo.
Hafsat ta mik'e tana nufar Sarauniya
Munaya datayi fushi zata fita, “Please gimbiya ki saurareni, ko kad'an niban
d'auki zugarsuba, dama jira nake su gama Na kora musu bayanin bakina”.
Jin wannan magana sai Sarauniya Munaya ta
tsaya cak, sannan ta juyo da baya tana danne fushinta da maye gurbinsa da
murmushi.
Dawowa tayi ta zauna duk tana kallonmu,
cikin sanyin murya tace, “kunason sanin yanda aikai nasamu dukkan fada da
matsayi a zuciyar mijina Sarki Muhammad Sameer fiyeda kowacce mace bayan
mahaifiyarsa?”.
A tare suka amsa da eh.
Tai murmushi da zame hular alk'yabbarta
tayi baya, sannan ta kuma gyara zama da nutsuwar maida dukkan hankalinta garemu
tafara bamu labari tun daga kan harmutsi da halayyar gidansu zuwa yanzu damuke
tare da ita a yanzun.
Wannan shine mak'asudin fitowar labarin
RAINA KAMA ga sauran Fan's.
Gaba d'aya sai jikinmu yay sanyi, domin
labarin ya girgizamu, Sarauniya Munaya ta cancanci fiyema da hakan ga Sarki
Muhammad Sameer Saifudden Abubakar, babu abinda zamuce saidai binta da fatan
alkairi, itama k'awarmu Hafsat miss xoxo mu bita da addu'ar samun k'auna ta
musamman a zuciyar Sarki Muhammad Sameer, dukda itama Alhmdllh tana samun
dukkan kulawa a garesa.
Mun bama Sarauniya Munaya hak'uri da
Neman yafiyarta akan jahiltar abinda bamu saniba, lallai idan kaga mace Na
mulkin gidanta karka zargeta, Dan bakowacce bace take zama Sarauniya a gidan
miji bisaga bigiren kauce hanya, wata k'yawawan hallayartane suka siyamata
wannan matsayin da girman da soyyar ga mijin da ahalinsa, domin ayau labarin
Munaya ya tabbatar mana da haka, hardajin sha'awar kasantuwa masu koyi da
k'yawawan halayyarta.
Mun yarda lallai Mahaifansu Munaya Inna da
mama Rabi'a RAINA KAMA ne, Galadima, kuma a yanzu Sarki Muhammad Sameer shima
RAINA KAMA ne, Munaya & Munubiya suma RAINA KAMA, Momma RAINA KAMA. Abie
RAINA KAMA, kai jama'a dayawa a wannan labarin sun zama RAINA KAMA KAGA GAYYA!!
😁👍🏻
Atake a wajen tace ta yafe mana, takuma
gayyacemu zuwa sashenta inda tasa aka had'a mana beta ta musamman😋😋, dazan Baku labarin garar arzik'i da
abinda wad'anan guys d'in Na HASKE sukayi dakunsha dariya, saidai ina tsoron
suburbud'a alk'ur'an🤣🤣⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀.
Abin kallo bai k'are manaba sai da
daddare, bayan sallar isha'i kai tsaye sashen Sarauniya Munaya akayo masa
rakkiya, Dan wannan rana tana cikin ranakun dayakan kasance da iyalansa ba a
matsayin sarkiba, matsayin miji ga matansa, sannan uba ga y'ay'ansa.
Yanda ya zauna yana wasa da dariya dasu,
kowa Na k'ok'arin fad'ar abinda ke bakinsa, yayinda matansa suka sakashi
tsakkiya da yaran 12 cif, k'ananun duk suka a jikinsa kowa farincikin ganin
Abbu Na tare dashi, sunci sunsha a tare, zuwa k'arfe 10 suka d'unguma sashen su
Momma, acanma hirar ta gudana mai cikeda farin ciki ga wannan ahali, murmushi
ya Gaza d'aukewa a fuskokinsu, kowanne yanajin tsantsar so da k'aunar junansu a
cikin jininsa da ayukansa..........✍🏻🔚
Kamar yanda Nina k'aunarku da kewarku ta
mamayeni a lokaci d'aya😭.
Tammat bi
hamdullah.
Na godema
Ubangijin al'arshi daya horemin dama da kwarin gwiwar kai wannan labari k'arshe
dayay ta tafiyar hawainiya tamkar bazai k'areba😁, kuskuren danayi ALLAH ya yafemin, abinda Na fad'a dai-dai ALLAH ya
taramu a ladan Baki d'aya, bakina bashida Kalmar furtawa agareku masoyana, kun
nunamin d'unbin k'auna da soyayya akan wannan labari, ina rok'on ubangiji ya
amfanar damu da alkairan dake cikinsa, kuskuren kuma mu watsar dashi gefe domin
girman ALLAH, Dan kunsan d'an Adam azijine, Nina ina a layinsu ni bilyn Abdull,
ALLAH kabamu ikon koyi da k'yak'yk'yawa, ya nisantamu daga mummuna, ALLAH yasa munada Rabin sake had'uwa a buk Na
gaba.😭🙏🏼
ALLAH ka
gafartama mahaifina, kakai rahma da Ni'ima kabarinsa, ka azurtashi da
yalwatacciyar rahman tareda dukkan sauran y'an uwa musulmai da suka kwanta dama😭🙏🏼.
ina Neman
afuwa ga dukkan Wanda Na 6atamawa a yayin rubuta wannan littafi da Sanina ko'a
rashin sani, Nima Na yafema duk Wanda ya 6atamin, ALLAH ya yafe mana Baki
d'aya.😭🙏🏼
Akwai
kuskuren danayi a salon wannan labari, domin kusan Munaya ke bada labarin ga
k'awayen miss xoxo, amma mantuwa kansani shiga ciki, hakan tafaru bisa d'an
rikicewa bayan dawowata daga hutun azumi, ina fatan zakumin afuwa, kuma zakuga
gyara anan gaba insha ALLAH, domin wani lokacin gazawama nasarace, saika Gaza
kake d'aukar hanyar gyara, ALLAH ya ganar damu baki d'aya, Rufaida Umar ina
godiya sosai, Dan kece kika farkar dani kafin kowa😊😘😘👍🏻
Takuce sai
BILKEESA IBRAHEEM MUSA
(Bilyn Abdull😉👌🏻)
ALLAH ya
sake had'amu da alkairinsa.😁🙏🏼
I love you
wijiga-wujiga, mazga-mazga, manya-manya, irin trillions d'inan my sweet fans😘😘😘😘😘😘❤❤❤❤❤❤😁👍🏻.
I miss you
wlhy✋🏻😭
SANARWA
Yakamata y'an uwana musulmi mu farga
wajen yawan binciken lafiyarmu akai-akai, Dan cutar ciwon HANTA ta yad'u a
cikinmu sosai, gashi mafi yawanmu bamu saniba😭, sai taci k'arfinmu muke farga saboda bamuda yawan kulawa Na binciken
lafiya sai ciwo ya kwantar damu, gashi anata d'aukar ciwo ta hanyoyi da dama,
wlhy wani abokin mijina suna hirar yanda a yanzu idan anzo tantance matasan da
aka d'auka aikin Uniforms mafi yawan matasanmu Na arewacinmu suna d'auke da
ciwon basu saniba, Dan ALLAH ki lalla6i mijinki kuje a abincika lafiyarku data
y'ay'anku domin sanin halin da kuke ciki, ALLAH ya cigaba da bamu lafiya yakuma
tsaremu baki d'aya, ciwone mai had'arin gaske da ake kamuwa dashi harta hanyar
toilet. Karmuyi sakaci domin ALLAH😭🙏🏼.
Ya RABBI ka
gafartama kakanninmu da iyayenmu baki d'aya, yayyenmu, k'annanenmu, y'ay'anmu,
k'awayenmu, mazajenmu damu kanmu😭🙏🏼
Post a Comment for "RAINA KAMA (BOOK 3) 33 (END) "