RAINA KAMA (BOOK 3) 32
.................Randa
sukaje gidanmu ai munsha kallo da mamaki, yau ga babban Sarki har cikin gida,
dan Sarki cewa yay saiya taka har d'akunan y'an uwansa, hakan yayma Innarmu
dad'i, koba komai jama'ar gidanmu zasu kuma ganin martabarta.
Aiko sun gani, dan ko rantsuwa nayi babu
kaffara wasu saisunyi kukan fili bama na zuciya kawaiba. Ranar anguwarmu cika
tayi mak'il da jama'a.
A wannan zuwane Innarmu ta fara taka nawa
d'akin itama, dan tana zuwa gaida ahalinta masarauta saboda anan aka saukesu,
dan haka Galadima yake sakawa a d'akkota duk bayan kwana 2 susha hirar zuminci,
duk da Sarkine dawasu manyan y'an rakiyarsa ne kawai a masarautar, sauran mata
dasu Badeerah duk suna gidanmu, wasu kuma gidansu Ayusher. Kwanansu goma ciff
aka d'aura auren Yarima Issifu da amaryarsa Ayusher, wannan aure yasaka kowa
farin ciki da annashuwa, anyi biki na kwanaki biyu anan muka shilla Niger
kaita, a can kuma aka d'auro auren Badeerah da Yaa Fadeel, kwanakinmu Biyar
anashan shagali maiban mamaki da birgewa, muka d'akko amaryar Yaa Fadeel muka
dawo gida.
Koda muka dawo babu zama, dan kuwa hidimar
bikin aunty salama muka shiga, Wanda yanemi had'ewa Dana Muftahu da Matawalle,
zakusha mamaki idan nace Muku Samha Ce matar Muftahu😁, wannan had'i ALLAH yayishine bisa umarnin Momma,
kowa kuma ya kar6a da hannu biyu yay addu'a, koda Samha taso bijirewa bisa ga
soyayyar Gopal nice naita tausarta da mata nasiha harta kwantar da hankalinta.
Munsha shagali kam iya shagali, babu abinda
zamucema ALLAH sai godiya dakuma bin amare da angwaye da addu'a.
Aiko wad'annan bukukuwa sai suka tada
tsumin Nuren shima, yace aure shima yakeso, kai tsaye kuma ya kawo Farhat
d'iyar Minister a matsayin za6insa, su Papi basuk'iba, domin nagartar
mahaifiyar yarinyar ya cancanci a aureta, hakan kuwa akayi, shima aka sanya
bikinsa kusa, mukasha biki kuwa cikeda nishad'i da farin ciki.
*****
Bayan kammala wad'annan bukukuwa mukajema
Aunty Salamah gaisuwa, da tayata murna ta musamman ni da Munubiya, tarba tamana
mai k'yau da mutuntawa, a hirar da muka gudanar nake mata tambaya gameda
mitasani ga Galadima?, dan naga yaranta sun kasance yaransa na wajen aiki.
Murmushi tayi tana sakama Meenal pampas,
“Babu wata alak'a tsakaninmu, Ameer k'aninane uwa d'aya uba d'aya, sanan mu
y'ay'ane ga Baba Rabilu da zakiji yana fad'a, har akayi aurenki da Galadima
bansan akwai alak'a tsakanin Mahaifina da shiba, duk da nasan kad'an daga cikin
labarin mahaifina, sai a dalilin satar Muftahu da mukayi, ta wannan hanyarne
kuma mahaifina baba Rabilu yasamu ganawa da Galadima ma, akuma wannan lokacinne
duk muka San komai gameda abinda yafaru, ashema yanakan Sani ya saka Ameer
aikin C.I.D, bisa tsatstsauran bincike daya dad'a yanayine ya gano Galadima
yanama hukumar DSS aiki, shiyyasa yatura Ameer ga hukumar dan neman kusanci
dashi, wannan shine kawai abinda na sani”.
Daga ni har Munubiya munsha mamaki da
girmama hukumar Ubangiji, dan shine ya sanya alak'a tsakaninmu da aunty salamah
batareda sanin junaba ko wani dalili, ni dai ALLAH yariga ya k'addara nice dama
matar Galadima, shiyyasa ya kulla bisaga hikimarsa wadda wasu wawaye suka kalla
a matsayin nasararsu.
Satinmu biyu da zuwa gidan aunty salamah
mukaje India ni da Galadima, halattar bikin Akash da Doctor Erfan Fahad, abin
mamaki da al'ajab saiga Radha a matsayin matar Akash, matan Dana ta6a had'uwa
dasu a shagon kayan yara na Galadima, lokacim inada cikinsu Abdurrahman, masu
yara Vishnu, Ashe ita k'anwar Maman Vishnu d'ince. Aiko muka rungume juna cikin
tsantsar farin ciki da annashuwa, ashema munsan juna, vishnu ya k'ara girma
abinsa, sai dai bai ganeniba ma😊.
Ana gama bikin Akash muka nufi Kashmir
bikin Dr Erfan Fahad da tashi amaryar shima, nanma mun rakwashe mun kwalla
kamar babu gobe. Daga nan muka dawo India muka baje kolin soyayya, duk da ni
yanzuma banajin dad'in gidan babu su Momma, sainaita k'iyasta rayuwar damukayi
aciki a baya, wani nayi kuka wani dariya, Ashe 6angaren Galadima ma hakance
yafaru, rayuwa kenan tsarin ubangiji.
Mune har k'auyen su Khumar, shima kuku
munje nasu gida.
Saida muka kwashe kusan watanni biyu a
wannan zuwa sannan muka dawo bisa samun labarin rikicewar jikin innaro.
A lokacin su Amaturrahman suna rarrafensu
ko ina, harma sukan gwada mik'ewa tsaye, dan suna wata na 10 ne, danma tafiyar
kamar tamusu nauyine.
Isowar dare mukayi, dan haka washe gari
tunda safe muka nufi asibitin da aka kwantar na innaro.
Hankalina yatashi ganin yanda Innaro ta
koma, dukta tsotse takuma tsufa. Na zauna bakin gadon ina kama hannunta da
share hawaye, dukkan ahalin gidanmu mazata da mata na ma'auri suna asibitin.
Innaro ta kalleni tana murmushi k'arfin
hali, da ido taima Innarmu magana akan tazo kusa da ita.
Innarmu ta share hawayen idonta ta k'araso
gaban gadon ta durk'usa, hannuna innaro ta saki ta kama na Innarmu.
Ahankali ta fara fad'in, “Ai'sha ki
gafarceni, nasan na aikata miki kurakurai da zalunci iri-iri, na manta da
duniya bakomai bace a wajen Bawa balle kayan cikinta, idan babu mutuwa akwai
tsufa, babu abinda ke dawwama sai ALLAH, duk yanda ka d'auki kanka hakan kake
kasancewa, ko a auren yaranan da y'ay'an alhaji halluru na zalunceki, amma nayi
nadama tun a auren su da mazajensu na yanzu, y'an biyu dan ALLAH Ku yafemin
kuma, amatsayinku na jikokina ban muku adalciba, son zuciyane kawai da rashin
hangen nesa, yafiyarku itace babban gatana, ina kuma rok'onku kumin Afuwa domin
ALLAH”.
Atare ni da Munubiya da Innarmu muka
had'a baki wajen fad'in, duk mun yafe miki Innaro, ALLAH ya yafe mana baki
d'aya, kin Isa damune ai, kuma Bawa baya zartama k'addararsa da bitar
rubutaccen littafinsa tundaga cikin uwa. ALLAH ya baki lafiya dai.
Innaro tayi murmushi mai ciwo tana hawaye,
ta juya ga y'ay'anta su Abbanmu da gwaggo Safiyya suma tana Neman gafararsu.
Suma duk d'urk'ushewa sukai a k'asa suna Neman tata gafarar, matan gidanmu
duksai jikinsu yay sanyi, suma suka durk'usa suna Neman gafararta, ta rok'esu
akan suma su canja Dan ALLAH.
Cikin awannin dabasu gaza biyuba mai
afkuwa ta afku, dan kuwa ALLAHn daya bamu Innaro yau ya d'auke abarsa, ta koma
garesa tafiya mai nisan zango, saiga su baba k'arami na kuka da idanunsu,
mahaifiya dabance, komai mugun halin mutum idan giji tazo dolene ka saduda
dajin k'aunarsa ta musamman, kuka kam mun cisa tamkar babu gobe, yau gidanmu
saiyay tsitt.
Gwaggo Safiyya ta mata wanka a d'akinta,
aka sallaceta a k'ofar gida da raka gawarta gidanta na gaskiya, hardasu
Galadima kuwa, Wanda shima saida ya share hawaye, halayyar tsohuwar kan sakashi
nishad'i haka kawai, danshi bayajin haushin masifarta, saima birgeshi da
takeyi, musamman idan ta kafe akan Abu, bayan tasan gaskiyane amma tace sam ita
ba hakaba.
Ranar a gida muka kwana harsu Fauziyya, washe
gari aka cigaba da kar6ar gaisuwa, a kwana na biyu saiga dangin su Innarmu daga
Niger, harda Ayusher dake fama da tsohon ciki.
Ranar addu'ar uku saiga su Abie da mai
martaba sunzo gaisuwa suma, dasu akayi addu'ar uku ma.
Aranar duk muka koma gidajenmu cikeda
kewar innaro.
***
Ranar addu'ar bakwai d'in Innaro muka
samu shiga wajen baba mai kanwa ni da Galadima.
Mun iskeshi shima dai lafiyar sai a
hankali, dan yanzu ko fitama bayayi, muka gaidashi cikeda girmamawa, ya amsa
mana da fara'a, harda tsokanarmu da cewar, “Sai yau nake ganin ango da
amarya?”.
Duk murmushi mukayi cikin jin kunya.
Shima ya kuma murmusawa da fad'in, “Mi
kukeson Sani y'ay'ana?”.
Nace, “Baba mai kanwa abinda ALLAH ya
baka ikon Sani game damu”.
d'an Murmusawa yakumayi yana gyara zaman
hularsa, ya nisa cikin sauke numfashi. Yace, “Da farko dai niba maye bane,
bakuma muguba kamar yanda wasu sukasha fad'a tun ina yaro, saidai ina tare da
wasu aljanu da bansan ta Yaya suka kasance daniba tun k'uruciya. Tun farkon
zuwan kakanninki gidan Malam fharuku aljanun dake tare dani suka sanarmin da
dukkan asalinsu, harkuma suka rasu da matsalolin da mahaifiyarku taita fuskanta
ga marigayiyya, abinda yasa na barsu ban ta6a maganarba saboda komawarsu a
wancan lokacin bashida amfani, ina tausayinsu kuma k'warai da gaske, aljanuna
sunsha d'aukata su kaini har cikin masarautar su Ai'sha, kullum cikin bibiyar
musu ko ansamu canji nake, amma ba'a daceba har ta samu haihuwarku. Abinda yasa
lamarin Galadima ya shigo rayuwaki a labarin shine, Maharbi daya taimaki Badi a
jeji ranarda ya bama Auwalu babanki abin d'aukar hoto ne. Ba mutum bane wancan
maharbi, aljanine yazo masa a suffar mutane, kuma har Badi yabar wajensa shima
bai saniba, wannan aljani shine ya ta6a taimakonka a India lokacinda ciwonka ya
tashi ka fad'i a titi, shine kuma ya kwad'aita maka wasu zantuka akan matar
dazaka aura, a lokacin shekarun su Hussaina 12 kacal a duniya😊, badan yasan itace matar takaba ya fad'a, saidan maka
fatan hakan, dan yata6a sanarmin akwai al'amari mai k'arfi dake tattare da y'an
biyun Ai'sha, kuma bisa dalilin abinda akabama Auwal abin yake, sai dai shima
baisan mineneba, saidai mujura hukuncin ALLAH. tun daga wannan lokacin wannan
aljani ya baza y'an uwansa aljanu suna kula da dukkan motsinka Muhammad Sameer,
suma su Hussaina haka itada y'ar uwarta har suka kai adadin shekarun girma.
Yafara zuwama Hassana a mafarki, amma saiya fahimci batada k'arfin zuciyar da
zata iya shan gwagwarmayar rayuwa dakai, hakanne ya sakashi komawa kan
Hussaina, amma ita sai aka dace, wannan shine mafarkin da kuka dingayi keda
y'ar uwarki Hussaina, nikuma na cigaba da d'oraki mataki-mataki akan kar6ar
Muhammad a matsayin miji, Haidar da kike gani yazo har aka saka ranar aurenku
ba mutum baneba, aljanine dagashi har iyayensa da sukazo neman aurenki”.
Ba k'aramar zabura nayiba, hartaso bama
Galadima da baba mai kanwa dariya.
“Kinga kwantar da hankalinki, ai ko driver
dayay masu Muhammad aiki akan satoki ba mutum bane ba, k'arfin jini da ALLAH
yabaki kikaso fahimtar hakan kuma, daga ke har Muhammad kunsha mu'amulla da
aljanu a matsayin mutane ai har lokacin da ALLAH ya k'ulla igiyar aurenku, aiko
cikar taron d'aurin aurenku akwai d'unbin aljannu da suka Halarta a ciki,
dukkan bayanan danai muku yanzu zan baku tabbaci, wani turaren tsinke ya d'aga
lamusashshiyar katifarsa ya zaro, ya k'yarsa ashana ya kunna, dandanan hayak'i
da k'amshi ya gaurasye d'akin, saiga sallama munji a k'ofar d'aki.
Matashin saurayi ya shigo, Wanda Munaya
bazata ta6a mance fuskarsaba, wato Haidar, hakane ya sakata zabura ta
mak'alk'ale Galadima.
Haidar yay murmushi kawai yasamu waje ya
zauna, saiga kuma dattijo da Galadima yata6a had'uwa dashi a India, shima dai
da kallon k'urilla ya bishi, basu fita a mamakiba saiga Driver daya ta6a d'akko
Munaya lokacin dayace suyi auren Contract shima ya shigo, saikuma mabanbanta
fuskoki Wanda sun had'u dasu a mabanbanta gurare, harda masu zuwama Munaya a
k'awaye, saida duk suka zauna suka nutsu sannan suka gaisa da baba mai kanwa,
Galadima ma dai a d'arare ya yarda yabasu hannu sukayi musabaha, nikam uwar
y'an tsoro ai ina mak'ure a bayansa, ALLAH ma yasoni banzo dasu Abdurraheem ba,
suna gidanmu.
Baba mai kanwa ya nuna manasu yana
fad'in, “Ina fata duk kun ganesu?”.
Duk muka amsa da eh a d'arare.
Dattijon daya had'u da Galadima a India
ne yafara magana a nutse, “Muhammad Sameer ya bayan rabuwa da gwagwarmayar
rayuwa?”.
Galadima ya amsa da “Alhmdllh”.
Tsoho mai sihirtaccen k'yawu zam jinin
indiawa yace, “ka tuna na fad'a maka matarka Ce fitilarka? zuwa yanzu ka
tabbatar?”.
Galadima ya gyara zama yana Murmushi har
hak'waransa na bayyana, yace, “Lallai ban mantaba kaka, saidaima nabama wasu
labarin, nakuma mik'a godiya ta musamman agareku da fatan ALLAH ya had'amu daku
a aljanna, ya kuma biyaku da mafificin alkairi bisaga taimako na mussaman da
kuka bama rauwarmu ni da matata, duk da kasancewarmu ba jinsi d'ayaba”.
Gaba
d'aya suka amsa da amin, haidar ya nema izinin Galadima domin Neman afuwar
Munaya. Galadima ya bashi izini.
Haidar yace, “ki gafarceni bisa ga kalmomi
masu zafi dana fad'a a gareki a wancan lokacin, hakan ta farune bisa k'ok'arin
janyo hankalin mijinki domin jin tausayinki, kasancewarsa mutum mai tausayi da
gudun shigar wani matsala ta dalilinsa”.
Munaya ta murmusa tana kallonsu. Tace,
“na yafe maka wlhy, kuma komai yawuce, fatana ALLAH ya tabbatar da addu'ar
mijina a garemu baki d'aya”.
A tare aka amsa da amin. Mun dad'e muna
tattauna abubuwa da dama, kafin daga bisani sumana sallama su tafi, Wanda bai
saniba saiya d'auka da gaske mutanene, baba mai kanwa yay mana doguwar nasiha
mai ratsa jiki, wadda harta d'arsa tsoro a ranmu, yakuma ja mana doguwar
addu'ar. Galadima ya ajiye masa alkairi mai tsoka mukayi masa sallama muka
fito, bamu dad'e a gidanmuba muka koma gida jikinmu a sanyaye da abubuwan da
suka faru tsakaninmu da baba mai kanwa da su Haidar.
Kwanaki uku da faruwar haka labarin
rasuwar baba mai kanwa ta riskemu, mutuwarnan itama ta girgizamu k'warai da
gaske, munkuma jema iyalansa gaisu.
Manyan dake kula da matsalolin gidanmu
duk Ubangiji ya d'aukesu, yau babu Innaro babu baba mai kanwa.
Zuwa yanzu kam ko ina su Amaturrahman zuwa
sukeyi, sunyi wayo sosai da girma, hakama yaran Munubiya danasu Safara'u datai
hak'uri takoma gidan mijinta suke zaune lafiya da kishiyarta da haihuwa yau ko
gobe.
Ayusher ta haihu namiji, dan haka muka
d'unguma Niger suna k'wanmu da kwarkwata, hardama y'an gidanmu Wanda wanannne
zuwansu na farko, sunkuma gano abinda yafi k'arfin shirmensu kuwa, yayinda
girman Innarmu yakuma yawaita a zukatansu.
Mun dawo da kwana hud'u Aunty Salamah da
Badeerah matar Yaa Fadeel suka sauke, babu nisa tsakaninsu Farhat d'in Nurenma
ta juye, Saiga Samha ma ta haife yaranta y'an biyu duk mata, hakama matar
Matawalle. Kai wannan abun dad'i da yawa yake, munsha shagulgula sunan kam babu
k'arya.
A lokacin ne kuma Galadima yafara k'orafin
na yayaye su Abdurrahman wai kona samu nima. Dan gatan da ALLAH yay mana ni da
Munubiya muna jerin mata da al'ada ke d'auke musu bayan jinin bik'i har sai sun
yaye, amma nasan murzar da Galadima ke min da tuni k'ila ciki na uku na d'auka🤭🤣.
Yanzuma danake kwance a jikinsa dariya
kawai nayi. Nace, “su Abdurraheem basu gama yin k'wariba my king, inama laifin
sud'anyi 4years haka?”.
Harara ya zubamin da fad'in, “yarinya
kinma isa, insha ALLAH gab kike da d'aukar wasu ukun”.
Bance komaiba sai dariya da nayi ina
sumbatar goshinsa domin kauda zancen, dan inhar yay zurfi zai zama rigimar da
muka sabane kawai, nikuma bana buk'atar hakan.
★★★★★★★★★
Rayuwa ta cigaba da gungurawa dai-dai
gwargwadon iko, yau da dad'i gobe babu, soyayya nida mijina ba'a magana.
Shekarun Abie biyu kenan da dawowa cikin
ahalinsa, yayinda kunnen kowa na masarautar gagara badau yake a bud'e dan
sonjin makomar sarautarsa. Saidai kuma tsit babu wani bayani.
Yay shiri yaje har prison wajensu Harun
jikin su Alhaji Mansur yayi sanyi matuk'a, Wanda sukaso ya k'are rayuwarsa
tamkar gawane a gabansu, lallai duk saurin Bawa da son nuna k'arfin iko sai ya
jira ALLAH, Abie baice dasu komaiba ya juyo ya fito, shiruma maganace ga mai hankali.
A 6angaren mai martaba sunata fafatawa ne
shida mama Fulani tun dawowar Abie, yanason tado da maganar sarauta amma mama
Fulani ta kasa ta tsare, ta hanashi.
Yayinda gimbiya zulfah keta k'ulunboton
asirce-asirce agefe dan kar mulki ya koma wajen Abie, duk da batada wata fawa a
masarautar yanzu, saboda tunda wancan abun ya faru mai martaba ya hanata shiga
turakarsa, babu kuma wani Abu dayake mata a matsayin matarsa, bai kumace ya
saketa ba, dan kowa yasan Sarki a k'asar Hausa baya saki, saidai idan mutuwa ta
raba. Da farko tashiga damuwa tamkar tayi nadama, amma dawowar Abie saita kuma
birkicewa, musamman da Matawalle yay aure matarsa kuma ta haifi mace, duk zugarta
dason 6ata Galadima a wajen y'ay'anta Matawalle baya d'auka, saima yakuma
kusantar Galadima suka d'inke waje d'aya, su
wambai ne dai ma sai kuma rura k'iyayyarsa suke a ransu, har Momma da
Abie haushi sukeji, duk da jansu a jiki da sukeyi a banza, uwarsu da mama
Fulani sun rigada sun hure kunnuwansu.
Ganin abin zai kwa6e mai martaba ya
shirya taro na manyan masarautar, harda gayyar papi Wanda ayanzu shima lafiya
take Neman yimasa k'aranci, saboda girma, dan yanama shirye-shiryen yin murabus
ya d'ora mahaifinsu Nuren.
Mama Fulani batasan da wannan taronba ko
kad'an, dan mai martaba bai nuna mataba ko da a fuska.
Galadima na kwance a tsakkiyar falonsa
yana wasa da yaransa daketa hawa jikinsa yana musu doki, ni dai ina gefe zaune
ina danne-danne a laptop. Nakan kallesu nai dariya idan sukai masa wani Abu.
Wayarsa dake kusa dani tayi ring, d'auka
nayi na mik'a masa, ya sauke Amaturrahman dake saman fuskarshi yana duba wayar,
ganin mai martaba sai ya mik'e zaune sosai yana musu alamar suyi shiru.
Duk da ba wayone dasuba yariga ya koya musu
hakan, duk kuwa sai suka rik'e bakinsu. Ni dai dariya nayi kawai na kauda
kaina.
Galadima ya amsa kiran cike da
girmamawa.
Yana yanke wayar ya mik'e.
Kallonsa nayi da mamaki, “My king lafiya
kuwa?”.
“Duk'owa yay ya sumbaci goshina sannan ya
zauna a hannun kujerar da nake zaune. yace, “Mai martaba ne ke buk'atar ganina
wai yanzunnan”.
“Tofa ALLAH dai yasa lafiya?”.
“To amin, bara na kimtsa naje naji”.
Na amsa masa da to.
Yaran duk suka mik'e zasu bishi na
kamosu ina lalla6arsu. “Haba my sweetness kuzo kuji, Abbu wanka zaiyi kunji”.
Abdurraheem ya kwa6e fusaka zaiyi kuka,
danshi duk yafi sauran y'an uwan k'ulafucin uban, ko barci yake Galadima yay
magana saiya farka, gashi bashida yawan kwaramniya, yanda Amaturrahman da
Abdurrahman zasu saki jiki suyi wasa Abdurraheem bayayi, idan har Galadima na
gida to yana manne dashi.
Koda ya fito zai tafi sai suka sanya kuka,
lalla6asu yayi yay musu wayo ya gudu, amma Abdurraheem saiya saka kuka harda
shashsheka yana shid'ewa, dole Galadima ya dawo da baya ya d'aukesa suka fita.
Nikuma naita lallashin su Amaturrahman har suka saki jikinsu kuma.
Abdurraheem yana ganin Abie sai kuma
ya mak'ale masa, ya d'aukesa ya d'ora a cinya yana murmushi.
'Dakin taron yayi tsit kowa yana sauraren
Mai martaba.
Cikin nutsuwa da halin dattako yafara
jawabi kamar haka.
“Inama kowa fatan alkairi, nasan kowa
zaiyi mamakin wannan taro na gaggawa, wasu dalilaine suka saka yinsa tilas, tun
bayan kama mutane da suka cutarmin da d'an uwa babu wani zama da mukayi ko
magana akan wannan matsalar, duk da kasancewar akwai namu mutane a ciki, waziri
da d'ansa, da kuma sirikina, sai mahaifin mahaifiyata wato kakana kenan, tabbas
abune da musalta bak'in cikin da mukayi 6ata lokacine, amma mun tura komai ga
Ubangiji ya musu hukunci dai-dai da yanda suka aikata mana, a kullum kuma cikin
yaba k'ok'arin d'anmu mukeyi bisa ga jajircewa akan tonuwar asirinsu, ALLAH ya
albarkaci rayuwarsa da ta zuri'arsa, akwai wad'anda suka bashi taimako sosai,
amma bamuyi musu komaiba. Bawai mun manta dasu baneba, sunan cikin zukatanmu.
To a yanzu dai mak'asudin zamanmu anan shine inason maida sarautar dake kaina
ga d'an uwana, tunda ALLAH yabashi lafiya, sai a d'ora daga inda aka tsaya”.
Cikeda mamaki Abie ya kalli mai martaba,
cikin Dakatar dashi ya d'aga masa hannu yana 6ata fuska. Sannan ya yunk'ura ya
mik'e yana mik'ama Galadima Abdurraheem dayay barci, har yanzu bawai ya dawo
normal bane, da taimakon sanda yake tafiya. Yace, “Ku gafarceni bisa katse
hanzarin d'an uwana danayi, maganar gaskiya bazan kuma wani mulkiba, akwai
iyayenmu anan yakamata su dubi lamarin bisa ga idon basira, har zuwa yanzu
bawai lafiya Ce ta gama isataba, saidai muce Alhmdllh domin Ubangiji yamana
dukkan Ni'ima, ai ko lafiyata k'alau zan iya sauka a wannan shekarun nawa na
bashi dama, munyi maganarnan ni da shi nace yabarta anan, amma saida ya kawota,
to wlhy, wlhy kunji dai na rantse ko, bazan sake hawa karagar mulkiba, kwanan
nanma nake shirin komawa India ni da iyalina, dan ALLAH wannan maganar ta tsaya
iya haka, karmu sake jayayya a kanta”.
Shiru kowa ya kasa motsi, domin wannan
rikici yazama na manya, hakanne ya saka papi mik'ewa ya sallami kowa, ya rage
daga shi sai mai martaba da Abie a d'akin taron.
*****
Na fito wanka na iske Galadima zaune a
bakin gado hannunsa dafe da kai, da sasaarfa na k'araso dan nasan akwai matsala
kenan, musamman da acikin y'an watannin nan sau biyu ciwonsa na tashi, duk da
akowane bayan watanni uku sai munje India ganin likita shida Abdurraheem,
dayake yanzu hankalinsa yana nan Nigeria akan Company da suketa k'ok'arin
ginawa, zuwa India saiya zame masa sai time to time kokuma wani gagarumin Abu
ya taso daya zama tilas saiyaje.
Laimar ruwa da yaji a jikinsa ya sashi
d'agowa da hanzari ya kalleni, kafin nace wani Abu sai kawai ya rungumeni tsam
a jikinsa, sai kace zai maidani cikine, kusan mintuna 3 muna a haka, sai sauke
tagwayen ajiyar zuciya yakeyi, nikam ina shafa gadon bayansa a hankali.
Nutsuwar daya samu ta sakashi d'ago muka
zubama juna ido, murmushi mai kashe zuciya namasa ina shafa sajensa, cikin
sanyin murya nace, “Waye ya ta6amin Barden gagara badau ne?”.
Lips d'insa ya ciza yana rik'e hannuna,
cikeda damuwa yace, “Munaya sosuke kawai sudawo da abinda ya wuce”.
Nace, “Mikenan?”.
Ya sauke nannauyan numfashi ya zamewa
ya kwanta, kansa bisa cinyata muna kallon juna yacigaba da fad'in, “Akan mulki
mana, tun sanda Abie ya dawo na fuskanci Abba nason maida masa mulki, amma mama
Fulani na hanashi, sannan a gefe mahaifiyar su Matawalle tana nata
k'ulle-k'ulle, dama kwanaki mun fara maganar ni da Momma da Abie, saboda
rikicin dake Neman 6arkewa tsakanin mama Fulani da mai martaba, a lokacin
bansan kuma miya dakushe lamarinba, sai yau da rana tsakarnan mai martaba yace
zai maidama Abie sarauta, wannan shine mak'asudun zaman gaggawar, kinsan kuwa
wannan kujerar itace ke hana kowacce masarautar zaman lafiya da
hargitse-hargitse, harta kai ga asarar rayuka, shiyyasa da Sarki yafara ciwo
burin kowa ya mutu hattada y'ay'ansa da matarsa mai manyan y'ay'a saboda burin
y'ay'anta su gaji mulki? Wlhy ina cikin tashin hankali, hankalinmu ya kwanta
kowa yasamu nutsuwa a masarautar nan gawani bala'innan zasu 6alloma mutane,
inaga kawai zamu tattara mu koma India harsu Abie da zaran anyi bikin Sauban.
Da aunty mimi”.
“Ina bayanka wlhy my king, wannan itace
babbar mafita kawai, domin cigaba da samun zaman lafiya mai d'orewa, hukuncin
daka yanke yayi sosai”.
Ya lumshe idanu da shafo fuskata saboda
jin dad'in goyon bayan dana bashi, domin k'ara masa nutsuwa saina d'ora bakina
akan nashi nashiga masa wani salo mai cikeda kwarewa fiyeda yanda ya koya min,
tamkar jira yake ya birkicemin, kafin kicemi labari ya canja salo, saigani da
sake sabon wanka babu shiri.🤭
Tun daga ranar bamu sake jin
maganarba daga bakin manya, sai munafunce-munafunce da sukaita wanzuwa, bakuma
mujiba daga bakin Abie ko papi, dan aranarma ya koma inda ya fito, wannan
dalilin Galadima ya samu yafara shirin komawarmu India da Zarar an kammala
bikin Sauban daya rage sati biyu kacal.
Ana saura kwana biyu d'aurin aure ya zauna
da bayin ALLAH da suka hidimta masa akan su tanderu.
Baffi, Baba Rabilu, Badi, Muftahu, Nuren,
Saleem, Sir isa, su Ameer.
Dukansu ya bisu da k'yauta ta girma, tare
da musu godiya ta musamman mara iyaka, yakuma y'anta Badi tare da k'yautar
muhallin zama mai nagarta a cikin masarauta, hakama sarkin mota, ya basu
hak'uri bisa ga jinsa shiru, abaya tattalin arzik'insa ya raunana ne, koyace
zai karramasu bashida k'arfin hakan, amma yanzu kam alhmdllh komai ya
dai-daita.
Suma sun masa godiya ta musamman a garesa
da k'yak'yawar Addu'a, daga k'arshe ya kaisu ga Abie da Momma, sunci abincin
rana tare da adalin tsohon Sarki wato Abie, sannan suka sha hira, dama kowa
yasan Shiba mutum bane mai girman kai, ga yawan tsokana, shima yamusu k'ayuta
ta musamman, hakama Momma tayi nata.
Washe gari ana gobe d'aurin aure kenan da
tashin hantsi yasakani shiryawa wai namasa rakiya wani waje.
Kamar ko yaushe Sarkin Montane ke
Jammu, yayinda dogaransa ke binmu a baya.
Mun Isa wani waje kusada birnin gayu
plaza, wajen ya had'u iyakar had'uwa, a da shagunane kawai a wajen, amma yanzu
kamar an rushe anyi wani gini na musamman. An saka k'aton allo mai d'aukeda
hotunan kayan gyaran gashi dana kwalliya, an rubuta LADIES MIRROR da manyan
haruffa, hakama jikin k'ofar wajen dayasha glass, an saka babban allo a sama
mai kawo wuta da d'aukewa, shima dai irin rubutun farkone a nan, wato ladies
mirror, abin ya k'ayatar dani, yana rik'e da hannu na muka shiga.
Ashe wajene na musamman na gyaran irin
duk Wanda mace take buk'ata, gyaran jiki, saloon, kwalliya, kunshi, dakuma waje
na musamman da kayan shafe-shafe na kwalliyar mata ake siyarwa, da glasses aka
rarraba shagon, kowanne da 6angarensa, bayan ka fara iske reception a farko,
sai office dayaji komai zam dake can k'arshen shagon, shima dai duk glass
d'inne, amma daga ciki zagaye yake da labuloli, ba'a buk'atar ganin Wanda zai
zauna a ciki kenan.
Bayan mun gama zagaya ko ina muka Isa
Office d'in, Galadima ya saka hannu ya yaye wani allo da aka lullu6e da farin
k'yalle.
Kallonsu nayi da mamaki, saiya nunamin
rubutun jikin allon..
“Wannan tukuycine a gareki my mata,
badan biyanki hidimar da kike daniba, dan idan biya zanyi abinda na mallaka kaf
bazai iya biyankiba matata abar k'aunata, bugun zuciyata komaina Munaaya”.
Da tsantsar mamaki na d'ago ina kallonsa,
yad'an ta6e baki da d'agamin kafad'a alamar gaskiyar kenan.
Kawai jinai hawaye sun gangaromin, na
fad'a jikinsa ina sakin wani kukan farin ciki.
Hannu biyu ya saka ya rungumeni yana
murmushi, sannan ya jani muka zauna bisa sofa guda d'aya dake a office d'in,
ban tsaya wata-wataba na manna la66ana saman .....🤭.
Caraf ya cafke tamkar dama jira yakeyi, gaba
d'ayama mun manta a inda Muke, mun tsunduma duniyar masoya wad'anda suka soyu a
soyayyarma, saida naji yana Neman kauce hanya sannan na dawo hayyacina.
Na kuma rungumarsa tsam ina jero masa
godiya wadda nama rasa wace iriya zanyi masa yasan naji dad'i.
Ya rik'e fuskata cikin tafin hannunsa
yana bina da kallo, “My mata babu godiya a tsakaninmu, inma akwaita to nine ya
cancanci nayi miki, domin kinmin abubuwa da baki bazai iya lisafosuba, kedai
kawai ki rik'eni Amana ni da yaranna da k'anensu masu zuwa, idan kinkai hakan
kin gamawa Muhammad Sameer komai, na haramta miki yimin godiya inhar akan
wannan d'an wajenne”. Ya kamo hannuna yana zaro key d'in mota a aljihu ya
d'oran a hannu.
Kallonsa nayi sannan na kalli hannayenmu,
ya d'aga min gira da cije lips sannan ya mik'e.
Tamkar sokuwa haka na bisa da kallo, gaban
loka k'arama dake office d'in ya nufa, ya kwaso wasu file ya dawo inda ya barni
tamkar wata gunki, d'ayan hannun nawa ya kamo yana d'oran files d'in, “Wannan
sune bayanai da form na ma'aikatanki, angama d'aukar kwararru a kowanne fanni,
wannan takardun wajene da kowanne lasisinsa, ko gobe kika shirya ma'aikata zasu
fara aikinsu.................✍🏻
ALLAH ya
gafartama iyayenmu😭🙏🏼
Post a Comment for "RAINA KAMA (BOOK 3) 32"