RAINA KAMA (BOOK 3) 31
...............Da
asubahi na tashi jikina cike da gajiyar tafiya da wadda boss ya k'aramin, daga
sallar asubahi bai samu dawoba, Dan ana fitowa salla dukan ahalin gidan mai
ruwa da tsaki sun hallara ne ga yima Abie
barka da zuwa dakuma tabbatar da
gaskiyar zancen, domin tabbatar musu da kokwantonsu mai martaba yabasu damar
ganin Abie d'in tareda shelar Sank'ira. Wannane dalilin yad'uwar zancen dawowar
ta Abie har a wajen masarauta.
Dukda gajiyar dake tare dani bansamu
komawa barciba, nashiga k'imtsa gidan iya bedrooms d'inmu zuwa nashi sashen da
babu wata baiwa dakeda lasisin shiga. Sauran guraren zuwa kitchen kuma bayina
dasukayo asubancin zuwa sashen saboda jin nadawo ne keta k'ok'arin gyarawa.
Na fito da nufin komawa d'akina na tashi
yara na musu wanka cikin bayina d'aya ta zube Guywoyinta a k'asa tana fad'in
“Ranki ya dad'e ga sak'on kayan abincin salla nan daga sashen mama fulani”.
Cikin d'an mamaki Na kalleta tareda kayan
abincin dake jibge, sai naman kaji cikeda k'atuwar roba irin wadda ake tarama
mai jego ruwan wanka. Katsemin tunani tayi da kuma fad'in,
“Ki gafarceni ranki ya dad'e, wannan
al'adar mama Fulani Ce, a duk daren salla takan aikama kowanne sashe Na
y'ay'anta da manyan gidannan irin wannan kayan, yanzu zama a k'araso da sauran,
kowane sashe dasu yake abincin salla”.
Kaina Na jinjina tareda zama bisa kujera
ina d'ora k'afa d'aya kan d'aya da kallon baiwar dani nama mance sunanta a
yanzu. Nace, “Oh, yama sunanki?”.
“Ranki ya dad'e Umimi”.
“To Umimi wace shugabar hadiman sashen
nan?”.
“Nice rankai ya dad'e”.
“Ok, ya zamuyi kenan? gashi mun kasance
lokacj a k'ure, Dan yanzun kinga kusan 6:23am, bamuda isashen lokacin abincin
salla kenan”.
“Ranki yadad'e ki gafarceni, zamu iyayi
insha ALLAH, tunda kinga ai munada yawa”.
Shiru nayi inad'an nazari, saikuma Na
sauke numfashi ina mik'ewa damata nuni muje kitchen d'in.
Alhmdllh inada kaso mafi yawa Na buk'ata,
saidai abinda ba'a rasaba, Umimi nasaka ta tattaro sauran suka shigo da kayan,
Dan danan suka fara rage aikin, ni kuma Na fito nad'an rubuta sauran abinda
nake buk'ata nabama baiwa d'aya da kud'i takaima Sarkin Mota yabama wani ya
sayomin.
Badansu Abdurrahman sun tashiba Na tadasu
duknai musu wanka, shirin sune yad'an jani lokaci abinka daba d'ayaba, gashi
sunfara wayo, sauk'i nama d'aya Umimi babbar macece kuma Na yaba da tsaftarta.
Duk da dai namusu gargad'in jira nazo Na had'a komai da kaina. A gurguje nayi
wanka nasaka simple gown dabazata takurani wajen aikiba, nasaka k'aramin hijjab
Na fito nabarsu Abdurraheem a d'akin, insha ALLAH bazasuyi kukaba, Dan saida
cikinsu yay taf sannan Na fito.
Naji dad'in iskesu sunci rabin aikin, to
kusan su 15 kowa da abinda yakeyi. Dannan nasaka hannu nima wajenyin abinda
yakamata ace ni nayi d'in, Dan Sarkin Mota yakawomin sak'ona tuni. Sannan
ankawo sauran kayan daga sashen mama Fulani.
8:00am dai-dai Galadima ya shigo sashen,
saboda yazo yay shirin massalaci, mamaki ya kamashi jin k'amshi ya baje ko'ina,
shidai yasan bai tanadi komai d'aya danganci abincin salla ba.
Yana cikin tunanin Sauban ya shigo d'auke
da k'atuwar ledar kayanda zai saka, Wanda tun muna India yabada umarnin a
dink'a masa su.
Tare suka shiga sashensa da tunanin ko
inacan, dukda yasan bazanbar y'an aiki akan girkiba, Dan yakula inada son komai
naima kaina musamman girki.
Babu abinda ke tashi sai k'amshi mai dad'i
anan d'inma, ga ko ina yayi k'al gwanin sha'awa da birgewa, saidai kuma tsit
alamun babu kowa.
Sauban ya Shiga bedroom d'insa da kayan
shima yana biye dashi.
Cikin sigar tambaya Galadima yace, “to ina
take itada yaran?”.
K'aramar dariya Sauban yayi, yace, “Yaa
Sam kasan halin auntyn tamu dai, Na tabbatar k'amshin girkinnan daga sirrin
iyawartane, kaga kenan tana kitchen ”.
Hararsa Galadima yayi, Sauban ya rufe
baki Dan tuna ta6argazar da yayi.
Ina cikin aikin Sauban ya shigo, bayin
duk suka zube suna gaisheshi, da farko nama zata ko Galadima ne, saida Na waigo
naga Sauban.
Bayan ya d'aga musu hannu dabasu izinin
tashi ya kalleni yana fad'in “Aunty gimbiya kinsani jin yunwa mai yawa da
wannan k'amshin girkin naki”.
Murmushi nayi kawai ina wanke hannayena,
nace “ALLAH Yaa Sauban akwaika da tsokana, ya gajiya”.
“Ai tabi gado wlhy, tare muka shigo da
Yaa Sam fa”.
Nace, “Ok". Coffee Na had'a masa a
k'aramin filas Na d'ora a tire mai k'yau da mug daduk abinda zai iya buk'ata.
Kar6a Yaa Sauban zaiyi nace, “A'a kabarsa
Na hutar dake nikam”.
Yay murmushi, “shikenan Aunty, inagafa
nima zuwa zanyi Na shirya yau idin Na musamman ne ga jama'ar masarautar gagara
badau”.
“Gaskiyane Yaa Sauban, ALLAH yasa yau
asamo mana amaryarmu”.
Dariya yayi yana yunk'urin fita,
“lallaima Aunty d'an k'araminnan dani wazai ban y'arsa?”.
Ban samu bashi amsaba ya fice, Nima
sashen Galadima Na Shiga INA murmushi.
Babu kowa a falon, Dan haka Na wuce
bedroom d'insa.
Sallama nayi kawai Na shige. A bakin
gado Na iskeshi zaune d'aure da towel, da alama wanka zai Shiga. Murmushi
mukaima juna. nace, “Afuwan my King, aiki ya d'auke hankalina bansan ka
shigoba”.
Murmushi ya kumayi yana wani lumshe ido,
Na ajiye tiren saman k'arim copy table d'in gabansa sannan Na zauna kusa dashi
Na kwantar da kaina gefen kafad'arsa bayan Na sumbaci damtsen hannunsa”.
Shima saiya karkato fuskarsa gareni ya
shafa tawa fuskar da tattausan hannunsa, cikin magana rad'a-rad'a yace, “miya
kaiki aiki keda ke tare da gajiya?”.
Idanuna na d'ago na kallesa ina
murmushi, nace, “my king ai yakamata ace anyi abincin salla a sashen Galadima,
wannanfa shine karon farko da zakayi bikin salla da matarka a masarautar nan,
bai kamata ace anyishi babu wasu alamuba ai OK?”.
Yanda nai maganar da kashe ido d'aya
saida tsigar jikinsa ta tashi, yad'an lumshe ido da sumbatar goshina, sannan ya
rad'amin “ALLAH yay miki albarka” acikin kunne.
A saman la66a na amsa da “Amin”.
Ya tambayeni yara nace, “suna d'akina,
maybe ma sunyi barci. Bamu tsaya 6ata lokaciba muka Shiga na taimaka masa da
wanka, sannan muka fito nahau shiryashi, dukda lokaci yaja a nutse nake masa
komai, danshi ma'abocin son komai a nutsene, bayason gaggawa ko yawan sauri
koda a magana ne kuwa.
Inamasa shiri yana shan coffee, kaga d'an
gatan Munaya.😂
Tsaf na shiryashi cikin farar shadda
daduk salla yakanyi amfani da ita wajen idi, nakawo babbar riga na saka masa
sannan na fesheshi da turare, ajiye mug d'in hannunsa yayi yana d'aukar hularsa
zanna bukar daketa maik'o yay mata kari ya kafa bisa kansa yana dai-dai tawa.
Alk'yabbar dazai sa nagama feshewa da
turare sannan na matsa ina kwantar masa da sajensa dayasha gyara da cumb,
shikuma yana saka link d'in hannunsa.
Kusan tare muka gama, na kama hannunsa na
d'aura masa agogon dabai San da shiba.
Da mamaki ya kalleni amma saina janye idona
ina murmushi da fad'in “Happy salla nane nida triplets d'inka”.
Rasama mi zaice yayi, sai kallon agogon da
koshi da kansa iya mak'urar za6ensa kenan. Yakai hannu zai rik'oni nai baya
kad'an ina girgiza masa kai, Dan nasan makomar rik'onin.
Cikin marairaice face nace, “please kabari
saika dawo kawai”.
Wani miskilin murmushi yayi yana cije
lips.
Nima na murmusa da nuna masa Alk'yabbar.
Kansa ya girgizamin a hankali yana mai shafa
agogon Dana d'aura masa da d'ayan hannunsa. “kibarta zasumin nauyi da yawa,
idan zamu fita gaida Governor zan saka”.
Ido d'aya na kashe masa da had'e yatsuna👌🏻alamar yayi.
Ya murmusa shima yanamin jinjina👍🏻.
Ban barsa ya fitaba saida namasa photo
biyu, sannan na rakoshi har falon k'arshe, inda Muftahu da Matawalle ke
jiransa, suma sunsha wanka mai birgewa, tamkar ka sacesu ko anguna ranar
aurensu.
Galadima ya kareni da bayansa tareda min
alamar na koma. Baya buk'atar su ganni kenan. Nima saina juya ciki kawai.
Yayinda nake jiyosu suna masa Sheri da kod'a wankan nashi.
Na lek'a yara naga barci sukeyi, Dan haka
na koma kitchen muka cigaba da aikin da fatan mu kammala akan lokaci.
Tunda matasan samarin masu d'anyen jini suka
fito sai kallo ya koma sama, bayi sai zubewa suke suna gaishesu, sukam sai
d'aga hannu dad'an murmushi.
Haka kawai sai Galadima yaji kewar Harun,
aduk irin wannan ranar shike zuwa ya fiddoshi daga sashensa, amma yau gashi
bak'in halinsa yasa a gidan yari zaiyi tasa bikin sallar dagashi har ubansa. Ya
k'aunacesa saboda ALLAH ashe shid'in ba haka bane a tashi zuciyar.
Motocin da aka tanada domin su suka shiga.
Wambai da talba haushi ya kamasu, ganin
wai yau d'an uwansu matawalle ne zai tafi salla tareda Galadima.
Oho, daga matawallen har Galadima basusan
sunayiba.
A 6angaren Abie da mai martaba shiga
sukayi iri d'aya, Abie ya fito a ainahin sarakinsa na asali, sai rama wadda
kayan jikinsa suka 6oye, idan ka gansu bazaka ta6a banbanta wanene sarkin ba.
Mai martaba ya fito rik'eda hannun d'an
uwansa Abie, nanfa aka fara ruwan cameras dukda dogarai na karewa ma, cikin
lullu6esu da manyan riguna da musu kirari da busar algaita suka shiga mota
d'aya.
Masallaci yacika mak'il da al'ummar manzon
ALLAH (s.a.w), isowar Sarki da tawagarsa kawai ake jira.
A dai-dai k'ofar baya ta musamman motarda
ke d'auke dasu Abie ta tsaya, mai martaba ya taimaka masa ya fita suka shige
cikin massalaci.
Nan take aka d'auki kabbara bisa umarnin
liman domin nuna godiya da al'ajabin hikimar ubangiji na dawowar tsohon Sarki
cikin k'oshin lafiya, bayan tsahon shekaru daya d'auka baya k'asar. Duk
matashin dake k'asa da shekara talatinma bai sanshiba.
Mak'iyan 6oyefa da sukaga tabbas sai tsoro
ya kamasu, ashedai zancen daya karad'e gari gaskiyane, yau ga Sarki Saifudden
Abubakar a gabansu ko sunaso ko basaso kuwa.
An gabatar da Kud'uba tamkar yanda
addini ya tanada, mai ratsa jiki da 6argo, mai k'arama muminin kwarai imani da
tsoron ALLAH.
Su Galadima suna jerin sahun farko, saidai
na kusada su Abie ba.
Alhmdullah, sallar idi ta gudana bisaga
farincikin kasantuwar bayin ALLAH wannan rana da ko yaro k'arami ke d'okantuwa
da zuwanta, bare su Galadima da jama'ar masarautar gagara badau da farin cikin
ya had'e musu biyu.
Bayan idar da salla akaja addu'a mai tsayin
gaske ga Abie, sannan aka bashi microphone daga zaune yay bayani mai gamsarwa
da ratsa jini da jijiyoyi Wanda yasaka mafi yawan jama'ar dake massalacin
hawaye.
Hatta da Galadima k'asa kawai yayi dakai
yana murmushi da share hawayensa da handkerchief.
Yau dai kam ai saida aka kai kusan 11:30 a
massalaci kafin a sallami jama'a.
Yayinda manya kuma suka samu yin
gaisuwa ga Abie da masa murna da addu'a.
A can kuwa jama'ar gari kowa ya gumtsi
labari yatafi fesarwa, hakama y'an jarida masu zuwa kallon zahiri, kafin kace
mi labari ya cigaba da shiga lungu da sak'o, hakama hotunan Abie da nasu
Galadima.
Bisa ga wannan labarine su Ahmad tahowa
Masarauta dukda basuda tabbacin ganin Galadima d'in.
K'arfe 12 aka shirya liyafar cin abincin a
masautar, wadda har governor zai halarta, itace madadin hawa da akeyi zuwa
gaida Governor.
Duk yanda Galadima yaso komawa ga iyalansa
hakan ta gagara, yawan jama'a ya hanashi matsawa konan da can, kowa soyake ya
nuna masa kansa a jerin masu tayasa murnar dawowar mahaifinsa cikin k'oshin
lafiya.
****
Alhmdllh munsami kammala komai, Na barma
su Umimi sauran aikin suka k'arasa, niko nanufi tsaftace jikina kafin mijina ya
shigo, dukkan abincin da za'a fita dashi kuwa nabama su Umimi umarnin kaisa duk
sashen daya dace.
Galadima daya tuna da batun abincin da
Munaya keyi yad'an fita daga cikin mutane yana kiran sarkin Mota, Umarni
yabashi akan zuwa birnin gayu ya kar6o drinks wajen manager, yanason kiran
Munaya amma babu dama, Dan dawuyama idan ta maida layinta Na 9ja bisa waya,
gashi bashida damar tsallakewa ya taho gareta.
****
Sosai Momma take samun tattali ga mama
Fulani, ita abinma mamaki yabata, saida aka sakko idi sannan aka kaita sashe Na
musamman da akayi aikin gyarawa da safiyar, zasu d'an zauna anan itada Abie
kafin asan abinyi gameda sarautarsa dake kan d'an uwansa.
A tsorace mama Fulani take, dukda
kaffa-kaffa da take dasu Momma, ko kad'an batason mulkinan yabar hannun d'anta,
har yanzu burinta jikokinta su gaji masarautar gagara badau.
Amma dai taita danne zuciyarta Dan karta
nuna hali.
******
Bayan mai martaba da Abie sun huta aka fara gudanar da liyafar cin
abincin a babban d'akin taro Na masarautar.
Wanda yasamu halartar manyan mutane dake
cikin binin, duk wani mai fad'a aji ya garzayo masarautar Dan kar ayi babushi,
kokuma ya shiga black list.
Matawalle ya kalli Galadima dayak'i
cin komai sai drink yake sha. “Lafiya kuwa Sameer?”.
Galadima ya kallesa da alamar tambaya,
amma baice komaiba.
Da hannu Matawalle ya nuna masa abincin
gabansa.
Murmushi Galadima yayi yana shafa
kumatunsa, cikeda k'asaitarnan tasa yace, “Bazaka gane bane d'an uwa, my mata
tayi abincin salla, idan naci wannan cikina ya cika naje can kuma babu space ai
sai a hanani.......”. Sai yay shiru bai k'arasaba.
Mi Matawalle da Muftahu zasuyi inba
dariyaba, har mutanen dake d'an gefensu suka juyo suna kallonsu.
Galadima kam murmushi kawai yayi ya maida
eyeglasses d'insa a ido yana kallon inda su Abie ke zaune.
Anci ansha kowa yay mak'il cike da
godiyar Ubangiji, daganan aka fara gudanar da
jawabai Na godiya ga ALLAH bisaga ni'imar dawowar Abie.
Mai martaba shine ya fara, sannan Abba
hayatudden.
Maganarsu ta ratsa zukatan mutane da dama,
domin sun nuna k'auna mai yawa da farincikin dawowar d'an uwansu, hakan ya k'ara
musu kima, dan sunture zancen nan Na mutane a zuciyarsu, wato y'an ubanci
dayafi komai ruruta wutar k'iyayya a masarautunmu Na Hausa Fulani.
An buk'aci ganin Galadima shima.
Ya mik'e cikeda takun izza da zagayawar
jinin Mulki a dukkan sassan jikinsa, k'asaita da kwarjinin yarinta Na
d'awainiya dashi. Yanda akaita zubama su mai martaba hototuna shima hakanne. Da
yawan mutane dake wajen ya burgesu, koda haushinsa kakeji kwarjininsa ya Isa
jin ka k'aunacesa lokaci d'aya. Ya gyara
tsayuwarsa yana wani k'asaitaccen murmushi mai tsada da nuna halin dattako,
cikakkiyar sallama ya musu suka amsa, sannan yacigaba da magana yana zare
eyeglasses d'insa.
Hawaye cike da idonsa yace, “A watannin
da bazasu cika shekara ba Na tsaya a gabanku kamar haka ina kuka da kausasan
kalamai ga dukkan mai hannu a ciwon mahaifina, a ranar d'aurin aurena hakan ta
faru, nasan kuma dayawanku dake nan suna a wancan zaman, sai dai bisa ga
hukuncin Ubangiji yau nine tsaye a gabanku ina kukan farinciki da tausasa
harshena Na Neman afuwa, na godema Ubangiji da yaymin dukkan sutura ta rayuwa,
ina fatan samun ta gaba inda yafi gidan duniya, badan nafi kowaba yaymin
wad'anan ni'imomin, sai Dan hak'uri da juriya da kar6ar k'addara aduk yanda
tazoma bawa, bara nabaku wani labari kad'an, Wanda yana d'aya daga cikin babbar
riba dabazan manta da itaba har k'arshen numfashina. Doctor Arjun shine likita
na farko daya fara duba Abie, shine kuma yacigaba da kulawa dashi har nakai
wayo, shi mabiyin addinin Hindu ne, sanann daga wannan k'abila ya fito,
shekarar dazan shiga jami'a sai ALLAH ya jarabcesa da ciwo rana tsaka, yanama
cikin aiki a asibiti ya yanke jiki ya fad'i, y'an uwansa doctors sun bashi
dukkan taimakon gaggawa harya farfad'o, a daren ranar saiya buk'aci d'aya daga
cikin doctors d'in daya kira masa ni. Ina tare da Momma da Jakadiya kiran ya
iso gareni, munyi mamaki kwarai da gaske, dan bamu dad'e da duboshiba, lokacin
salla dayayine yasakamu baro d'akin dayake ma. Haka Na tashi natafi amsa
kiransa. Awajen doctor Arjun Na iya yarensu na Hindu, tunda Na shigo saiya
shiga muk'omin hannu alamar nazo garesa, nabi umarninsa Na zama kusa dashi
tareda rik'e hannayensa cikin nawa, muryarsa cike da rauni yace___”.
“Sameer Kasan miyasa nace a kiraka
kuwa?”.
“Kaina na girgiza masa alamar a'a. yayi
murmushi idonsa Na cigaba da tsiyayar da hawaye, yakuma damk'e hannuna a cikin
nasa yana cigaba da fad'in___”.
“Sameer kune Muslims na farko dana ta6a
mu'amulla mai tsayo dasu, daga gareku na fahimci wasu k'yawawan halaye da kullum
duniya kefad'in baku dasu, lallai duk mai ambatar wannan addini da addinin y'an
ta'adda ya jahilci fahimta da sanin halayyar d'an adam, kun kasance masu
hak'uri wajen samu da rashi, kar6ar rayuwa a dukkan halin data zo muku, kun
kasance masu yawan k'yautata zato, mutane da yawa sunsha zuwa duba mahaifinka,
amma duk d'unsu ban yarda dasuba amma Ku sainaga babu wani kokwanto a Kansu, da
zuciya d'aya kuke k'ar6arsu da mu'amulantarsu, dukda zukatanku sunada yak'inin
dolene a samu mugaye a cikinsu, a duk daren duniya idan nashiga duba mahaifinka
nakan iske mamanka tana salla ko karatun littafinku, ahankali sai wad'annan
abubuwan suka fara kwad'aitamin wani abu daban, tun ina kokawar turewa harya
fara zama babban 6angaren tunanina dayay tasiri mai girma a dukkan kuzarina, da
farko tsoro nakeji, Dan kaf ahalinmu babu wani mabiyin addinin musulunci ko
kiristanci. Amma kasan duk miye matsayar wannan labarin danake baka a yau?”.
“kaina Na girgiza masa jikina a sanyaye,
yayd'an murmushi da cigaba da fad'in__”.
“Inason biyan ko nawane domin Shiga addininku, a yau bana tsoron kowa
yasani koya ganni a ciki, inason ribantuwa da k'yawawan halayenku”.
“A lokacin kunsan miya faru?”.
Jama'a suka amsa da a'a. Galadima yay
murmushe da share hawayensa da Handkerchief.
“Na tsinci kaina cikin zumud'i da firgici
dukda k'ananun shekaruna, Dan lokacin bazan wuce 17years ba nake tunani, hawaye
Na zuba a idona nace da gaske zaka musulinta Doctor?. Cikim jinjina kai ya
tabbatar min. Ban tsaya 6ata lokaciba nace doctor addinin musulunci ba'a biyan
ko sisi domin kasantuwa a cikinsa, imani da ALLAH da yarda da manzonsa shine
babban farashi mafi daraja a duniya. Yace to a ina zan samo imanin?. Nai dariya
da fad'in ta hanyar ambaton Kalmar la'ilaha illallah muhammadurrasulullh. Yace
to ya shirya. Duk da k'arancin shekarunan nawa baiyi Girman kaiba ya kar6a
kalmar shahada yana mai jaddadata a harshensa har saida tari ya sark'esa,
rikicewa nayi Na mik'e da nufin nemo doctor amma saiya hanani, yamin nuni dana
bashi ruwa, haka nadawo na bashi ruwan, kur6arsa hud'u ya janye kansa yana
fad'in___”.
“Sameer, tabbas yauce ranar tafiya koda
shiri ko babu, ina rok'onka koda sau d'ayane ka gudanar da salla a kaina,
sannan karka yarda wani d'an uwana ya san da musuluntata, badon komaiba sai Dan
gudun tozarta ku, ka sanarma Anania ina matuk'ar k'aunarta, karta manta dani”.
Daga nan ya shiga maimaita kalmar
shahada yana wata irin zufa maiban tsoro, na rik'ice inata ambatar sunansa da
girgizashi, sai kawai naga jikinsa ya saki. Sakinsa nai Na fita da gudu kiran
doctor sai mukaci karo da Momma dataji shirun yayi yawa tabiyo sawuna. Rik'eni
tayi tana tambayar lafiya?, jikina Na rawa nasanar mata abinda yafaru da Hausa.
Dan nasan mawuyacine asamu maijin yaren a kusa damu, hanani kiran doctor tayi
taja hannuna muka k'oma d'akin tana share hawen farin ciki Dana kewar Dr Arjun,
tai addu'a mai yawa akan gawarsa sannan tace Muh'd zaka iya masa wanka?. Bak'aramin
tsorata nayiba, jikina Na k'yarma nace Momma wankafa?, nidai tsoro nakeji. Ta
dafa kafad'ata cikin k'aramin kwarin gwiwa tace yarona karkaji tsoro, tunfarko ubangijine ya za6eka ya k'addara Dr
Arjun ta hannunka zai zama musulmi, ka daure ka cika masa wasiyyar daya barmaka
ta sallatar gawarsa, Dan kasandai su ahalinsa ba irin wannan jana'izar zasuyi
garesa ba, ina tare dakai kaji. Bisa Umarnin Momma da koyarwarta naima gawar Dr
Arjun wanka, itakuma tana bakin k'ofa tanamin gadi, Ubangiji kuma saiya ara
mana dogon lokaci harna gama na maida masa Uniform d'in asibitin a jikinsa,
sannan na sallacesa ina kuka. Saida muka gama komai sannan muka fito mukabar
gawarsa cikin d'akin, bamukoyi nisa da k'ofarba mukaga doctor ya shiga d'akin
da hanzari, mintuna kad'an da shigarsa maganar rasuwar Dr Arjun ta fara Shiga
kunnuwan Mutane. Wannan rasuwa ta matuk'ar ta6a zuciyata, har a yau d'innan da
nake gabanku ina jinta, kuma ban gaza wajen yimasa addu'oin samun rahama ba”.
Galadima ya share hawayensa dake zirara
tamkar fanfo, ya kalli mutane yana fad'in “kakannina, iyayena, yayyena da
k'annenna kunsan hikimar baku wannan labarin kuwa?”.
Jiki a sanyaye, wasuma hawaye sukeyi suka
amsa da a'a.
Galadima yay murmushi yana kuma share
hawayensa da gyara tsayuwa, “Wannan labarin yana mana nuni muzama masu nagarta
aduk inda muka tsinci kanmu, babu irin k'yawawan halaye da addininmu bai koyar
damuba, amma son zuciya da burukan duniya saisu sauyamu, miyasa muke mantawa
damu su waye? Ina kuma zamu koma?, dalilin ruk'o da gaskiya mahaifina ya fad'a
hali mai tayar da hankali na tsawon shekaru, babu wanda ya ta6a tunanin sake
ganinsa anan, amma kuma sai gashi, kunsan wane irin hali mai firgici da ciwo da
muka tsinci kanmu kuwa? Mahaifiyata itace silar komawata jarumi, da taimakonta
nazama jajirtacce, a halin k'uruciya har tunani nake anya kuwa tana sona? Ajiye
sosayyar nan ta d'a da uwa tayi ta kutsani cikin talakawan daba yarena ba, ba
addinina d'aya dasuba, ba k'asa d'aya muka fitoba, naringa wahalhalun koyon sana'oi
da gwagwarmaya ta fahimtar rayu, ga karatu, ga damuwa da ciwon mahaifina, ban
fahimci gata taminba saida na iya d'aukar nauyin ciwon mahaifina da hidimomin
ahalina, na kammala karatuna bisa bigiren danake buri, iyaye mata wlhy kuzamto
masu koyi da halayen mahaifiyata, matasa y'an uwana kuzama masu koyi da
rayuwata, dukda ana ganina d'an ganta ban zauna gata yamin komaiba, saina tashi
da k'afafuna da gumina na gina kaina, muzama masu k'yawawan halayya koda daraja
martabar addininmu ga wad'anda basu fahimcesa ba, Dan k'yawawan hallaya da
nagarta yaja hankalin Dr Arjun kwad'aituwa da addinin Islam, Yakuma mutu a
cikinsa bisa amincewar ubangijin al'arshi, da mugayen hallaya mukeyi saidai
doctor Arjun ya k'yamacemu dajin kuma k'yamar addininmu, son zuciyoyinmu shike
maidamu bayan baya a Kullu yaumin, ba tarin dukiya ko gata ko k'yawune abin
birgewaba, Nagarta, nagartar samun k'yawawan halaye da d'abi'u shi ake kira
jarumta, matata ta ta6a fad'amin Hak'uri shi ake kira NASARA, saida hak'uri ake
zama jarumi, sai an jure zafi ake tsintar kai a sanyi. Kusan shekarunta nawa
kuwa?, ashirin, inhar mace mai k'ananun shekaru irin wannan tanada hikimar
zance da nazari mai amfanar da wani irin haka miyasa tunaninmu ke d'aukar mace
mai k'aramar kwakwalwane?, nabaku satar amsa kaje ka mu'amullanci matarka ta
nagartacciyar hanya kaga yanda zaka amfanu da tagomashin tunaninta, kunga mata
biyunan sun zamema rayuwata wata ginanniyar Katanga, mahaifiyata da kuma matata
da auren shekara d'aya kacal zamu cika, kakata yayata k'anwar mahaifiyata
rumface su dake kare martabata da zamana cikakken mutum, ina mai farin ciki mai
tsanani da samun lafiyar mahaifina, da godiya mai yawa ga wasu ke6antattun
mutane wadda gudunmawar suce silar ganina a gabanku, ALLAH ya albarkaci rayuwar
ahalinsu ya cika musu burukansu na alkairi, Yakuma had'amu a aljanna gaba
d'aya”.
Duk suka amsa da amin suna binsa da
tafi.
Daganan sauran jama'a sukaita bayani
d'ai-d'ai, taro dai bai tashiba sai kusan 3:00pm.
Cikin farin ciki Galadima ya shigomin, ko
kunyar su Ahmad dake zaune da Sarkin mota ya shigo dasu bai jiba ya rungumeni,
saida na ankarar dashi sanann ya sakeni yana susar gefen wuya alamar yaji
kunya, yayi farin ciki da ganinsu kuwa, yaran sun shiga ransa sosai, duk da
abinda yayma mahaifansu basu tsanesa ba, saima zuminci mai k'arfi daya k'ullu a
tsakaninsu.
Ranar sashenmu saiya koma na matasan
samarin masarautar, Dan shima Sauban nan ya kawo gayyarsa cin abinci, gasu
Yassar kuma, itama Samha saiga tata gayyar, saikuma ga matasan gidanmu da
y'ammata da banyi zaton ganiba, harda Zarah da Siyama, dad'i tamkar xai karni
kuwa.
duk yanda Galadima yaso ke6ewa da matarsa
abin ya gagara, dansu Matawalle da Nuren da suka iso dawasu samarin masarautar
suma duknan suka nufo, tsakaninsa da Munaya sai dai y'ar satar kallo, dan
kwalliyarta tagama narkashi.
Baniba kosu Amaturrahman sunji a jikinsa
raranar, d'auka dai sun shata harsun gode ALLAH, bankuma samu damar shayar
dasuba sai madara suka sha. Har dare babu wata damar samun ke6ancewa da juna.
Washe gari kuma aka gudanar da hawan salla
mai k'ayatarwa, wanda a tarihin masarautar gagara badau an dad'e ba ayi irinsa
ba, saboda manyan sarakuna na garuruwa daban-dabanne da Governors harda uban
gayya president da senators da sukazoma Abie barka da dawowa suka halarci bikin
hawan sallar.
Misalta muku k'yawun kwalliyar jarumin
naku Galadima ai 6ata lokacine, ammafa komai zamm, y'ammata da yawa sun k'yasa,
balle yau fuskarsa washe take da murmushi na musamman Wanda jama'a basu ta6a
ganiba.
Su Abbana ma sunzo gaida Abie, sun sami
k'yak'yk'yawar karramawa mai ban mamaki, wadda tasani farin ciki mai tsanani
dajin k'arin k'aunar Ahalin Galadima.
**
Saida shagalin bikin salla ya lafa nasamu
zuwa gidanmu da zagaya dangi, kowa yayi farin cikin ganina, musamman ma
Munubiya da Innarmu, su Aiyaan da sauran jama'ar gidanmu, jikin Innaro yayi
tsanani, dan harma ana shirin kaita asibiti, ciwon k'afa ya takura mata ainun.
Sati biyu dagama bikin salla tawagar
masarautar su Momma sukazo daga Niger, a masarautar gagara badau suka sauka,
kasancewar harda uban gayya Sarki.
Wani k'warya-k'waryar biki zuwan nasu
yazama a masarautar, tareda k'ulla alak'a mai matuk'ar k'arfi wadda ada babu
ita, da safe Matan suka koma gidanmu akabar Sarki da jiga-jigansa anan.
A wannan zuwane aka nemi auren Ayusher,
saima Abbansu ya tak'aita musu wahala akan a d'aura auren kawai baki d'aya kowa
ya huta.
Kowa yayi murna da hakan k'wai da
gaske..............✍🏻
ALLAH ya
gafartama iyayenmu😭🙏🏼
Post a Comment for " RAINA KAMA (BOOK 3) 31"