RAINA KAMA (BOOK 3) 30
.................Gaba
d'aya sun kasa yin breakfast, suna cikin zaman jigum-jigum suka jiyo bud'e gate
da shigowar mota. Samha ta fita da hanzarinta danson ganin wanene, fitowar tata
tayi dai-dai da fitowar Galadima daga cikin mota fuskarsa d'auke da wani irin
k'ayataccen murmushi daya fidda sirrin k'yawunsa.
Da gudu ta taho garesa, yakan mata fad'a
akan son rungumarsa ko Sauban amma yau saigashi ya bud'e mata hannu dakansa
tazo ta shige jikinsa.
Ihun murnartace tasaka su Momma fitowa da
hanzari suma
Ganin Galadima ai sai duk sukayo kansa
itada aunty Mimi, itadai munaya gefe ta tsaya tana sharar hawayen farin ciki.
Abie dake kallonsu daga cikin mota ya saki
murmushi yana share hawaye, yana k'asa d'aya da iyalansa amma bai ta6a sanin
muhallinsu ba sai yau, dukda bai shigaba gidan yamasa k'yau.
Galadima ya ture Samha daga jikinsa ya
rungume Momma da aunty Mimi yana sakin wani irin kuka daya matuk'ar tada
hankalinsu.
Da sauri suka d'agosa hankali tashe suna
tambayarsa mike faruwa? Kodai ALLAH yayima Abie rasuwane?.
Cikin kuka da dariya yace kowa ya rufe
idonsa .
Babu musu sukabi Umarninsa, har Munaya
dake gefe.
Yace, “kun tabbatar kowa ya rufe?”.
A tare suka amsa masa da eh.
Ya murmusa da goge sauran hawayensa sannan
ya juya ga motar ya bud'e, hannun Abie ya kama da taimakonsa ya fito rik'eda
sandarsa mai k'yau dazata dinga taimaka masa wajen tafiya, Dan har yanzu
tafiyar batai kwariba.
Saida Abie ya jingina jikin Mota ya tsaya
da k'yau sannan Galadima yace, “Kowa ya bud'e idonsa”.
Har rige-rigen bud'ewa suke.
Akusan tare Aunty Mimi da Munaya da Samba
suka kwalla k'ara, Momma kam sai tayi luuu sai gata a k'asa kawai ta sume.
Abie da Galadima dasu Munaya duk kanta
sukai suna kiran sunanta, shima Abie ya tuzgud'e zai fad'i, Dr Ajay daya kawosu
yay hanzari rik'esa yana fad'in “A sannu dai Sir, k'afafunka basukai k'warin
wannan hanzarinba”.
Da gudu Munaya takoma ciki sai gata da
ruwa, ta zuba a hannu tana shafama Momma, da k'arfi takawo Numfashi.
Bin yaran nata tayi da kallo tana fad'in
“mafarki nakeyi ko yarana? Nasan irin mafarkin dana sabane dama, ba takawa Na
bane ba”.
Cikin dariya da kuka Aunty Mimi tace,
“Wlhy shine Momma, shine agabanki ba mafarki kikeba, Momma Abie d'inmune wlhy
tallahi kinji Na rantse”.
Zumbur Momma ta tashi daga jikin Aunty
Mimi, Abie dake tsaye har yanzu bisa taimakon su Galadima ya murmusa yana
fad'in “Zeenah ki cire kokwanto, da gaske wannan Saifudden d'inkine ba Wanda
yasaba zuwa miki a mafarkiba kinji”.
Tasowa Momma tayi garesa, ta shafa
fuskarsa domin tabbatarwa, takuma binsa da kallo tundaga sama har k'asa, lallai
da gaske wannan Saifudden d'intane bana mafarkiba, Ai sai kawai ta rungumeshi
babu kunya ko tunawa dasu Galadima a wajen.
Sai duk'ar da Kansu duk sukai suna
Murmushi.
Gaba d'ayansu kowanne soyake ya nuna
ajintarsa ga Abie domin nuna masa gamsuwa da farincikin samun lafiyarsa, aka
kawo masa y'an Uku ya had'a duka ya rungume yana maijin k'aunarsu har cikin jininsa, Khaleel ma yana nanik'e dashi.
Munaya dai nadaga gefe bata zak'eba.
Idon Abie ya sauka akanta, Murmushi
yamata yana fad'in “'Diyata zo mana”.
Takowa tai cikeda jin kunya tazo gabansa
ta durk'usa, cikin girmamawa ta gaisheshi da masa addu'ar k'arin samun lafiya
mai d'orewa.
Ya amsa yana mai k'ara jin farin cikin
kadancewarta suruka agaresa uwa ga jikokinsa.
Galadima ma yakasa d'auke ido daga
gareta, sai yaga tamasa y'ar rama tsakanin jiya da yau.
Breakfast d'in dabai samu shigaba d'azun
aka baje domin ci, amma shi Abie kasancewar an hanashi cin wasu Abubuwan Kuku
yay azamar tanada masa Wanda yake buk'ata.
Daka gansu kasan suna tareda matsanancin
farin ciki .
Koda suka kammala Galadima ya taimakawa
Abie shiga d'akin Momma, shima ya haye sama shida matarsa.
Tun'a falo ya d'auketa cak yana juyi da ita
cikin hajijiya, babu shiri Munaya tahau k'yalk'yata dariya da k'an k'ame
wuyansa da hannayensa tana cusa kanta cikin k'irjinsa.
A haka suka k'arasa cikin bedroom, ya
jefa abarsa saman gado yabita tareda jan bargo yay musu runfa.
An hanani ganin abinda akeyi🤨, sauk'inma inada mijin Nima😏🙄.
Farin cikin da wannan ahali suka tsinci
Kansu wlhy 6ata lokacine, Momma kam sai ko ganinta bama ayi🤭🙈.
A gurguke please🥺😔.
Walwala da farin cikin wannan gida
tadawo kam, ga nutsuwa mai saka zukata samun damar yawan ibada, ko yaushe suna
manne da Abie, sai idan time d'in hutunsa ne yayi, Galadima yayma kowa gargad'i
akan sanarda tashin Abie, burinsa kowa
yaga abin mamaki, 100% Momma ta yarda da shawararsa, hakama Abie.
Yanzu dai kam sun yanke shawarar Isa
k'asarsu ta haihuwa ranar salla k'arama, zasu azumi na kwanaki 20 a india, su
biya Saudiyya suyi Umrah ta kwana goma su isa Nigeria a ranar salla ayi idi
dasu.
Gaba d'aya azumi saura kwanaki 6 a farashi.
******
AZUMI
Alhmdllh kowanne musulmi yau ya tashi da
azumin watan Ramadan mai mai albarka, saidai irin masu ak'idar saimun gani da
suka kasance k'alilan acikin wasu k'asashe irin namu Na yankin Africa.
Duk da shayarwa hakan bai hana ni zama
cikin jerin masuyiba, dan raino dai bani nakeba, tsakanina da yarannan idan
sunji yunwa, koyaushe suna tare dasu Momma, sunyi 6ul-6ul dasu tamkar y'an watanni
6, amma har yanzu suna cikin wata Na hud'une ma kacal.
Tunda safe Galadima ya fice, Na d'an
tashi nai gyaran saman sannan Na sakko, yau babu maganar shiga kitchen, Dan
tunda Abie ya dawo nakoma nike mishi girkin abinda zaici, wataranma nakan had'a
da namu muma, babu abinda zan cema wad'annan mutane sai godiya, soyayya dai mai
cike da k'auna ina samunta a garesu, ni da mijina kam ai sai hamdala, yana
tattalina da tarairayata, saidai d'an sa6ani Na yau da gobe Wanda baka Isa raba
ma'autara da Shiba, shima kuwa bai wuce wasu awanni muke shiryawa ba, inko Momma
ta lura ma takan kiramu tamana Nasiha, hakama Aunty Mimi.
A falo Na iske Abie daga can gefen falon
inda wasu kujeru biyu suke da kanta mai d'aukeda buks Na karatu, tundaga kan Na
addini har zuwa Na makaranta dadai sauransu, zaune yake yana nazarin wani
littafi da banga sunansa ba saboda tazarar dake a tsakaninmu.
Sai Samha dake falon kwance a kujera tana
kallon film, zaman gyalena Na gyara, Na taka a nutse zuwa garesa, saida Na
durk'usa a gabansa sanann nace “Barka da safiya Abie”.
'Dago k'yawawan idanunsa da Galadima ya
gado yay yana kallona, ya zare medical eyeglasses d'in idonsa yana Murmushi,
“'Diyata barka dai, kin tashi lafiya?”.
Kaina a k'asa ina murnushi nace, “Lafiya
lau Abie, ya ibada da k'arin k'arfin jiki?”.
“Alhmdllh d'iyata, ai jiki kam sai
godiyar Ubangiji, Muhammad fa?”.
“Ya fita tunda safe”. Na fad'a cikin kuma
duk'ar dakai.
Murmushi Abie yayi, ya maida eyeglasses
d'insa yana fad'in “ALLAH ya dawo dashi lafiya to”.
A saman la66a Na amsa, sannan Na mik'e da
k'yar zuwa d'akin Momma.
Abie ya bita kallo zuciyarsa cikeda
k'aunar wannan yarinya, irinta yaytama y'ay'ansa addu'ar samu amatsayin
abokiyar rayuwa, Alhmdlh Ubangiji ya amsa masa, saura Sauban kuma.
Nidai nashiga Na gaida Momma, Na iske
tanama su Amaturrahman shiri, da alama wanka tamusu, Na gaisheta cikeda
girmamawa kamar yanda Na saba, itama ta amsamin da kulawa tareda d'an jana da
hira tamkar yanda ta saba, nad'an jima a d'akin, harta fito tabarni Na gyarashi
tsaf kamar yanda nakeyi tun bayan dawowarmu, Dan tuni Na dakatar da Samha ni
nakeyi.
Na fito da nufin shiga Na gaida aunty Mimi
saina isketa tama fito falo, anan muka gaisa Na zauna muka d'ora da hira tamkar
yanda muka saba, mafi yawama firar ta Sauban Ce, Dan kowa yayi missing d'insa,
yace azumi da kwana 3 zai zo sai salla zai koma, Galadima bai hanashiba, dukda
yana tareda tattalar kud'i a tsakaninnan saboda sun masa k'aranci, to saima
papi ya d'auki nauyin zuwan Na Sauban da komawarsa.
Mund'an ja lokaci Muna hira barci yafara
rinjayata, mik'ewa nayi Na gudu sama, nad'an rage kayan jikina Na haye gado sai
barci.
Kusan 10am saiga Galadima ya dawo, bai iske
kowa a falonba, da alama barci suke kokuma suna harkokin gabansu a ciki, kai
tsaye d'akin su Momma ya nufa, yay knocking aka bashi izinin shiga.
Abie Na zaune saman abin salla ya idar
da sallar walha, yayinda Momma ke zaune bakin gado tana bama Abdurraheem Magani
saboda zazza6in dake jikinsa.
Galadima ya zauna a saman sofa yana
gaidata da tambayar miya sami Abdurraheem d'in?.
Cikeda kulawa ta amsa masa tana gogema
yaron inda maganin ya 6ata masa a wuya da fuska.
“Tunda muka tashi yau Na kula bayajin
dad'i yaronnan, inagafa yakamata ka kaishi a bincikasa, basai mun zauna wata 6
ta cikaba, tunda kasan ciwon yana zama iri daban-daban, karmuyi tunanin ko irin
nakane azo ba hakaba, Dan Na kula yafika yawan laulayi shikam, Abdurraheem baya
had'a sati biyu da isashsshiyar lafiya”.
Jin jina kai Galadima yayi, tausayin d'an
nasa Na ratsashi, ya had'iye abinda ya tsaya masa a mak'oshi da k'yar yana
amsar Abdurraheem d'in daga hannunta.
Abie daya shafa addu'a ya maido hankali
garesu.
Mik'ewa Galadima yay yakoma inda yake yana
gaisheshi, Abie ya shafa kansa hakama Abdurraheem, cikeda tsokana yace, “Like
Father like son”.
Dariya Momma tayi, yayinda Galadima yay
Murmushi mai k'ayatarwa har hak'oransa Na bayyana.
Yace, “Abie ai dakai suke kama duka,
Amaturahman cema tad'an d'ebo mamansu kad'an”.
[8/19, 6:14 PM] 🙇🏻♀Da Rarrafe🙇🏻♀: Abie yay Murmushin jin dad'i, yana
shafa kan Abdurraheem da yay barci, gaskiya Galadima ya fad'a, dan shima tun
randa yafara ganinsu ya lura da haka.
Sund'an ta6a hira, har Galadima ke kawo
maganar Aunty Mimi akan yakamata tayi aure hakanan, domin zaman bashida amfani
haka, ko wani yamaka k'yak'yk'yawar fahimta wani bazai makaba, tunda ba wuce
auren tayiba.
100% iyayensa sun gamsu da zancensa,
sunkuma amsa masa da isha ALLAH zasu zama Na musamman da ita.
Kwantar da Abdurraheem yay musu sallama
akan zaije yad'an rage barci.
Tunda ya shigo yay tozali da Munaya
barbaje a gado, murmushi yad'anyi yana cire Bottoms d'in rigarsa harya k'araso
cikin d'akin, hanging d'in rigar yay sannan ya zauna saman sofa yana cire
takalmansa, mitsawar da Munaya tayi tana juya kwanciya yad'ago ya kalleta,
aransa yace hajiyata ko an farajin azuminne?.
Harya gama hidimarsa yazo gefenta ya
kwanta bata saniba, dayake ba motsi mai k'arfi yay tayiba, Dan yasan batada
nauyin barci, gudun karta tashi yay tayin komai a sannu.
*****
Duk musulmin ALLAH Na k'warai daya
wadatu da ibada inhar lokacin salla tayi ko barci yake saiyaji a jikinsa,
kokuma yayta mafarkin ana sallar, hakance ta kasance ga Munaya da Galadima,
kusan atare suka farka, kowanne bakinsa d'auke da addu'ar tashi barci.
mamaki ya kamani ganinsa gefena, Dan
bansan yama dawoba, ya min murmushi nima Na mayar masa da murtani ina shafa
fuskarsa.
Cikin lumshe ido nace, “Yaushe ka dawo?”.
Hannunsa ya d'ora saman nawa dake kan fuskarsa, yad'an rufe ido ya bud'e
akaina, murya k'asa-k'asa yace, “Tun d'azun mana, kinata barci abinki”.
Yatsine fuska nad'anyi ina zame hannuna da
k'ok'arin tashi. Nace, “Wlhy barci bai wani isheniba shiyyasa nad'an rage yanzu
kafin time d'in shiga kitchen”.
Shima tashi yay zaune yana jinjinamin
kai.
Shiya fara shiga wanka, saida ya fito
sannan nima Na shiga nayo.
Koda ya fita salla ya dawo bai koma
cikiba, sai suka zauna a harabar gidan shi da Abie suna hira, dayake kullum
Galadima cikin bashi labarin abubuwan da suka dingi faruwa yay lokacin yana
jiyya, wani yay murmushi, wani dariya, wani kuka, yana kuma yabama Galadima
bisa ga gwarzan takar dayayi ta kare mutuncin ahalinsa da rik'e martabarsa.
Har time la'asar suna zaune a wajen, da
taimakon Galadima Abie yataka zuwa massalaci, dan inhar yana gida haka sukeyi,
bayan sun dawo awajen suka sake zama, Galadima ya kirani nabama Samha System
d'insa takai masa.
Da to Na amsa, Na hau sama Na d'akko
nabata.
K'arfe biyar dai-dai muka shiga kitchen ni
da Samha da kuku, sai Hadiman gidan guda biyu dake taimaka mana da wasu
ayyukan.
Cikin nutsuwa muka gabatar da dad'ad'an
abincin bud'a baki, wasu namu Na Hausa wasu kuma Nan.
Gab da
magrib muka gama, munbarsu k'arasa komai Na k'imtsa kitchen d'in da shirya
abincin.
Wanka nakesonyi ga Amaturrahman Na kuka,
Momma kuma tace babu inda zani saina shayar da ita.
Dole Na zauna ina dungure kanta. Oho
batasan ma inayiba, itadai taji abinda take buk'ata a baki kawai. Ganin
tad'ansha na d'auketa muka haye sama dan karma Momma tace saita k'ara.
Na iske Galadima yana wanka, ni bammasan
ya shigo cikiba, Na kwantar da Amaturrahman Na kuma sauka, nasan dole yana
d'akin za'a kira salla, dabino da ruwa Na d'oro a k'aramin tire nazo Na ajiye,
ina ajewa kuwa yana fitowa.
Sannu da aiki yamin, Na amsa ina manna masa
Sumba a hannunsa dana kama, nai saurin shigewa bathroom.
da kallo ya bita yana murmushi, ya kalla
hannunsa data sumbata shima ya sumbaci wajen.
Fitowata wanka yay dai-dai da cikar
lokacin kiran sallar magrib, a bakin gado Na iskesa zaune Amaturrahman Na
kwance kusa dashi tana wuntsil-wutsil da k'afafu, idonta nakan hasken globe,
shikuma yana kallonta yana murmushi da video d'inta awaya.
Batare danayi tunanin komaiba Na k'araso
garesa da nufin bashi dabinon, amma saiya jawoni nafad'o jikinsa, dukda laimar
ruwan dake jikina.
Babu wani k'arin bayani ya d'aura bakinsa
saman la66ana, idanu Na waro masa Na tsorata da mamaki, amma saiya kashemin ido
d'aya da cigaba da abinda yake.
Kusan mintuna biyu nasamu ku6ta. Ina
yunk'urin tashi ya kuma hanani.
“O ALLAH, azumi fa kakai my King, shine
kafara da jan magana mai makon Neman ruwa ko dabino?”.
Wani miskilin murmushi yayi da huramin
iska saman ido. Farfar Na fara da idanu.
Yakuma Murmusawa, “Bazaki ganeba babie na
nayi missing d'inkine, kinga ai lada biyu, gatakai azumi gata d'abbak'a sunna,
ni ai ga dabino Na nan, yawunki kuma shine ruwana”. Ya k'are maganar yatsansa a
la66ana.
Tura kaina nayi a jikinsa ina Murmushi.
Ya rungumeni da shafa bayana shima yana
murmushin.
K'arshe dai sai a d'akin mukai sallar
magrib sannan muka sauka k'asa shan ruwa.
Jinai gaba d'aya kewar y'an gidanmu
tazomin a yau, Na tuna yanda muke had'uwa k'wanmu da kwarkwata a runfa shan
ruwa, murmushi naita saki dajin kewarsu mai yawa da d'okin son ganinsu.
Aunty Mimi data lura dani tace, “My K'anwa
yadai?”.
Nakuma fad'ad'a fara'ata ina cewa “Na
tuno gidane kawai Aunty”.
Murmushi duk sukayi, Galadima dake
gefena ya mintsini cinyata kad'an, d'agowa nai Na kallesa ina d'an 6ata fuska,
gwalo yay min kad'an yana d'auke kai cikeda basarwa tamkar bashi yayiba.
Saida na tabbatar bamai kallonmu sannan
nima na rama, aiko zafin yasakashi kad'an garage ya 6arar da kunun da yake sha,
yay saurin rik'ewa.
Sannu muka shiga masa, na Fiske abina
tamkar banyi komaiba.
Muna had'a ido ya cije lips da min
gargad'i da ido akan zai kamanine.
Nima gwalo namasa.
Abinda basu saniba tun farkon fara
lamarin Abie da Momma suna kallonsu, dan
haka yanzu sai suka kalli juna suna murmushi.
A gurguje
please⛹🏻♀😏
★★★★★★★★★
Kwan uku da fara azumi Sauban ya iso
India, bak'aramar birkicewa yay da ihun ganin Abie ya samu lafiyaba, hardasu
kuka rurus, Abie ya rungume Autansa d'aya zama sangamemen Saurayi yana mai jin
farin ciki da k'aunarsa. A ranar sai sabuwar murna ta tashi kuma, haka muka
wuni cikin farinciki biyu, na zuwan Sauban da gimama farincikin daya riska.
Haka azumi yacigaba da gangarawa, kullum
saina kira su Abbanmu da sauran jama'ar gidanmu namusu barka da shan ruwa,
hakama y'an uwana sunta turomin sak'on massages kenan kulum namin barka da shan
ruwa.
Azumi na kwana 15 muka kai Abdurraheem
Asibiti, Yakuma samun binciken kwararrun Likitocin zuciya, suka dubashi da
k'aramin dabaru wajen kula da rainonsa, sai magunguna da zai iya sha a
matsayinsa na yaro k'arami.
Dukkan sayayya da Galadima zaiyi ya
kammalata, harma ya tura mana kayanmu ta jirgin ruwa.
A kwanakin bashida wani sukuni, yawan
shigi da fici na damk'a amanar harkokinsa kawai yake ga mutane, dan zai jima a
9ja bai dawoba a yanda ya hasaso, inma ya shigo India bazai dinga wuce sati biyu
zuwa uku ba zai barta, shima saboda Company nasune, danma yanata k'ok'arin
ganin sunzo sun kafa reshe a Nigeria dan shima yabada gunmawa ga k'asarsa.
Muma dake cikin gidan bawani zaman mukeba,
munata kimtse-kimtsen kayan gidan waje d'ayane. Da sallama da mak'wafta da
abokan arzik'i da akai sabo.
A wannan yanayinne na gane Ashe yayan
Dhibya Gopal soyayya suke da Samha, wannan ne kusancin dake k'ara k'arfi
tsakanin Dhinya da Samha, ban sanarma kowaba, haka itama ban mata maganaba,
tunda gashi ALLAH ya kawo sanadin da zasu nisanci juna cikin sauk'i, babu yanda
za'ayi aure ya iya yuwuwa a tsakaninsu, yaudarar juna kawai sukeyi, Su Dhibya
y'an k'abilar Hindu ne, kuma mabiya wannan addini masu tsananin ak'ida,
Galadima ya ta6a sanarmin iyayensu sun dad'e basu saki jiki dasuba saboda
kasancewarsu musulmai kawai, Gopal kusan sa'anni suke dashi amma babu wata
shak'uwa tsakaninsu. To tayaya suke tunanin k'ulluwar aure a tsakaninsu inba
Gopal musulunta zaiyiba, hakan kuma abune mai wuyar gaske, dukda ba'a yanke
hujunci da ikon ALLAH.
Ana gobe zamu wuce saudia Galadima ya
sallami Khumar da kuku, wad'anda suke kuka da idanunsu na bak'in cikin rabuwa
damu, muma kuma hakanne, sai da Galadima yamusu bayani akan badan shima bayason
rayuwa dasu ya sallamesuba, sai dan karya tauye hak'insune, yabasu Dama suje su
nemi wasu ayyukan, duk sanda ya shigo k'asar zai nemesu su dawo kan aikinsu
insha ALLAH.
Sunyi murna sosai da bayaninsa, haka muma
munji dad'in hakan, domin kuwa dai ba'a rabuba kenan.
KOMAI YAY
FARKO...😭👎🏻
Zai iya zama k'arshe watan watarana,
yau ga Abie daya shigo India cikin tsananin ciwo da fidda rai daga rayuwa zai
barta cikin farin ciki da k'warin gwiwar rahma da falalar ubangijin al'arshi.
Fuskokinmu kawai sun isa shaida maka muna cikin farin ciki muma.
Mun tafi cikin kewar India da jama'ar
cikinta, musamman ma Momma da Abie da tunda suka shigota sai yaune zasu barta.
Tunkan mu Isa Galadima ya sanya Sultan
nema mana masauki.
Muna sauka kuwa cikin mutunci akazo aka
d'aukemu zuwa matsakaicin gida dazai d'aukemu babu wata takura.
Har kuka saida nayi a 6oye ganina a inda
ban ta6a zato ko tsammaniba, kasa mai tsarki.
Hutun wannan ranar kawai muka samu, washe
gari muka duk'ufa ibada da godiyar Ubangiji bisa ga ni'imomi dayay mana badan
munfi sauran bayinsa da komaiba.
Tsawon kwana goma muna bautar Ubangiji, a
randa ake saran ganin wata jirginmu ya d'aga zuwa k'asarmu ta haihuwa, Abie da
Momma sunfi kowa zumud'i da k'aguwa.
Babu wanda yasan da zuwanmu sai Sarkin
Mota, shima kuma bashi da tabbacin dawa za'azo d'in, Galadima dai yace ya saka
a gyara masa 6angarensa da inda su Aunty Mimi ke sauka.
*****
Jirginmu ya sauka 9ja k'arfe 11:30pm.
Mu muka fara fitowa, Abie da Galadima suka zama k'arshe.
Abie na sauka a jirgin yana Murmushi da
hawaye, tareda shak'ar iskar k'asarsa daya bari tsawon shekaru, yama fidda
ransa da kuma dawowa cikinta har Abadan.
Sarkin Mota da dogaran Galadima suna
zaune a airport d'in suna jiran isowarmu.
Ganinmu da yawa yabasu mamaki, amma
saisuka zube suna gaishemu, a cikinsu babu Wanda ya gane momma da Abie, Bama
zai yuwu su ganesu d'inba, tunda sanda yabar k'arsar duk basa a wannan
matsayin, sai dai iyayensu, wanda a halin yanzu mafi yawa acikinsu duksun rasu
ma.
Dole saida muka k'ara da motocin haya,
Momma da Abie suka shiga wadda sarkin Mota ke ja, Ni da Galadima da Samha muka
shiga ta haya d'aya, Aunty Mimi da Yaa Sauban da yara suka shiga d'aya.
Mun Isa Masarautar tsit babu yawan
hayaniya alamar mafi yawan al'ummar cikinta sun nutsu waje d'aya, sai wasu
tsirarun hadimai dake kai kawo mussamman masu tsaro.
Duk muka fito amma banda su Momma,
Galadima ya nufi mortar dan son taimakawa Abie fiwo, Sarkin Mota kuma na
k'ok'arin biyan masu motarnan kud'insu.
Fir Abie yak'i fita, yace d'an uwansa
mai martaba ne kad'ai zai fiddashi a motar, duk rok'on da sukai masa fir yak'i,
gashi yanata sharar hawaye da handkerchief.
Galadima yasan yanzu Mai martaba ya
shiga ciki, maybe ma matar dake dashi taje.
Rasa yama zaiyi yayi.
Momma Ce tabashi shawarar kiran wayar mai
martaba, cikin damuwa Galadima ya kar6a wayan Sauban dabe dad'e da barin
k'asarba, sim card d'insa zaifi saurin aiki fiye da nashi.
Hadiman gidan sund'an fara fuskantar akwai
matsala gameda tsayuwar su Galadima, dan wannan ba halinsa bane.
ALLAH ma ya taimaka Mai martaba baiyi
barciba, yana zaune ne yana duba wasu takardu, matarsa ta biyu na tare dashi
dan yau kwanantane. Ya dad'e yana kallon wayar da nazarin mai kiransa, dan ba
kowane keda Number mai martaba, sai jiga-jigai irinsu Galadima d'in.
Tamkar bazai d'aukaba yad'ai d'auka tana
gab da katsewa a kira karo na biyu.
Cikeda girmamawa Galadima ya gaishesa
sanann yay masa bayanin shine.
Da farko mai martaba tsorata yayi, dan
babu Wanda yasanar masa Galadima ya dawo, cikin hikima da girmamawa Galadima
yayma mai martaba bayanin yafito yaga abin mamaki a k'ofar sashensa.
Sosai mai martaba yayta juya kalmar abin
mamakin, hakama matarsa, alk'yabba ta d'akko masa ya saka sannan suka fito a
tare.
Jakadiya na niyyar tafiya makwancinta taci
karo da mota a k'ofar turakar mai martaba, mamaki ya kamata, zatayi magana
saitaga Galadima dake tsaye a jikin motor, ta rusuna tana gaisheshi, kamar
yanda yasaba ya d'aga mata hannu cikeda izzar mulki.
Bata fita a mamakinba taga mai martaba da
matarsa sun fito.
Galadima baice komaiba sai bud'e murfin
motar da yay yana nunama mai martaba ciki da hannu.
Jikin baiwar mama Fulani mai kai mata
rahoton motsin kowa na rawa ta nufi sashenta, hartayi shirin barci ma ta
sallami Kuyanginta, amma dayake baiwar tanada fada sosai a wajen ta saita mata
knocking k'ofa.
Cikeda masifa da izza mama Fulani ta bud'e
k'ofar, jikin baiwarnan na rawa ta zube k'asa tana fad'in “Ki gafarceni ranki
ya dad'e, abinda nagano yafi k'arfin barinsa zuwa safiya, yalla6ai Galadima ya
shigo fada shida sauran iyalan tsohon sarki, maimakon yawuce sashensa tamkar
yanda ya saba saiya nufi turakar mai martaba kai tsaye, gashi can naga yana
nuna masa Abu amota, ban tsaya ganiba na nufo gareki ya uwar gijiyata”.
Ai mama Fulani bata tsaya bata amsaba ta
figi alk'yabba ta saka tana fitowa, baiwarnan ta take mata baya.
A can kuwa Mai martaba da mamaki ya
kalli Galadima, amma sai Galadima ya girgiza masa kai yana sake nuna masa cikin
motar.
Matsawa mai martaba yayi sosai domin ganema
idonsa abinda d'an d'an uwansa keson ya gani, Momma ta kunna fitilar dake motar
dukda haske mai k'ayatarwa daya haske ko ina na masarautar.
Koda mai martaba ya lek'a saiyay baya a
zabure, cikin rawar baki da nuna motar yace, “Sameer yaushe kuma ka fara shirya
min wasa da hankali har irin haka?”.
“Ka gafarceni ranka ya dad'e, abinda
kagani zahirin gaskiyane, wannan d'an uwankane ya dawo gareka cikin k'oshin
lafiya da hukuntawar Ubangiji”. Galadima ya k'are maganar da rank'wafawa ya
taimakama Abie ya fito, itama Momma ta fito.
Hakan sai yayi dai-dai da isowar mama
Fulani wajan. Da fuskar Momma mai d'auke da k'asaitaccen murmushi tafara
tozali, ta k'araso gabanta da sassarfa tana rik'o hanunta da fad'in “Zeenah!”.
A take Momma ta juya gareta, dan ko a
mafarki bazata manta mai wannan muryarba, batareda tunanin komaiba ta
rungumeta.
Yayinda shima takawa ya rungume Abie daga
can.
Tun a wannan daren labari yafara karad'e
masarautar, wasu kan basu aminceba kwata-kwata, burin kowa gari ya waye yayi
kallon zahiri ba jita-jita ba.
Dole matar mai martaba ta koma sashenta,
dan mai martaba yace Abie a sashensa zai kwana, jiyake idan ya barsa zuwa wani
sashe tamkar da safe zai wayi gari yaga ba hakaba.
Itama Momma a sashen mama Fulani ta kwana
tilas, yayi da mukuma muka nufi namu da yasha gyara ko ina yake need tamkar
muna k'asar.
Yau dai kam na murzu wajen Galadima,
acewarsa murnar sallah ce, dukda gajiyar tafiya darashin samun isashen barcin
da muka tara a Saudia bai d'agan k'afaba, a cewarsa yamayi k'ok'ari, kwana
nawa.
WASHE GARI
A Washe gari antashi da farin ciki guda
biyu a masarautar gagara badau, Murnar Salla da dawowar Abie.
Dan zuwa safiya kam tabbataccen labari daga
bakin sank'ira ya isa kunnen kowa, harma da k'yak'yk'yawan albishir na halattar
sallar idi tareda Abie.
Kafin kace mi labari yafara fita wajen
masarautar, su papi ma tun a Daren Galadima ya kirasu da wayar Sauban dake
hannunsa.
Batareda sanin ya akayiba saiga magana
tafara shiga kunnuwan jama'ar gari da y'an jarida, wasu gidajen TV Dana redio
suka fara sanar da wannan zance dawasu ke k'arya tawa kansu
tsaye................✍🏻
ALLAH ya
gafartama iyayenmu😭🙏🏼
Post a Comment for " RAINA KAMA (BOOK 3) 30"