RAINA KAMA (BOOK 3) 27
♦RAINA KAMA...!!♦
(Kaga gayya)
.................Momma
dai ta kasa ta tsare ta hanani hawa sama, idan abu Galadima ke buk'ata saitace
Samha ta kai masa, tsakanina dashi saiya sakko gaidasu ko zaije massalaci, ya
kumak'i nuna hakan ya damesa, sosai mamaki ya kamani, dan kwanakinmu hud'u
kenan da dawowa, da farko na d'auka kawai shariyar tasa ta
k'asaitace ta motsa,
amma zuwa yau dayake shirin zuwa Kashmir sai abin yafara bani tsoro, dan ina
zaune bakin gadon Momma ina shayar da Abdurraheem ya shigo, Momma ta fita
kitchen.
'Dago ido nayi ina amsa masa sallamar
da yayi, amma saiya d'auke kai tamkarma bai ganniba, ya k'araso kusa dani ya
rissina ya d'auki Amaturrahman dake kwance tana motse-motse.
Duk'owar dayay saitasa k'amshin
turarensa bugomin a hanci sosai, na lumshe idanuna sannan na bud'e akansa,
magana yake ma Amaturrahman ahankali cikeda k'asaitarnan tasa, saikace wata
babba.
Da kamar nima zan shareshi, saidai na
daure nace, “Ina kwana”.
“Lafiya”. Ya amsa batareda ya kalli
inda nakeba.
Hakan yamin ciwo a rai, na dangwarar da
Abdurraheem d'in akan gado batareda ya k'oshiba, aiko saiya saka kuka, banbi
takansaba na shige bathroom abuna.
Da kallo Galadima ya bita cikeda takaici
harta shige, ya cije lips nashi tamkar zai huda da hak'ori, idanunnan harsun
kad'a da 6acin rai. Yana k'ok'arin tashi ya d'aukeshi Momma ta shigo d'auke da
k'aramin Kofi ma Magani daza'a basu. K'arasowa tai dad'an hanzari tana fad'in
“shikuma wannan mi akai masa?”. Ita bama ta lura da Galadima ba, amma taji
k'amshin turarensa.
Kwafar da yayi yasaka Momma juyowa ta
kallesa bayan ta d'auki Abdurraheem d'in. “Wai dama kana d'akin amma yake kuka?
Ina Munayar ne?”.
Baice komaiba sai bayi ya nuna mata da
hannu, hakan yasata fahimtar ransa a 6ace yake, ta zauna tana shafa bayan
yaron, yayinda shikuma ya daina kukan.
A kausashe Galadima yace, “Momma idan
bazata iyaba na nemo masu kulamarmin da yara, dan bazan d'auki wannan
wulak'ancinba, ta k'auracemin na k'yaleta tayi duk yanda ta gadama, shine yanzu
kuma abin akan yarana zai dawo, nifa wlhy......”
Dakatar dashi Momma tai ta hanyar d'aga
masa hannu, “ya Isa haka Muh'd, Munaya dai matarkace, kuma lafiyar ALLAH kuka
dawo k'asarnan, aganina tun washe garin dawowarku kaga batazo inda kakeba
yakamata ka tambayeta miye dalili? Amma ka share tamkarma hakan bai damekaba,
shin mulki haukane Muh'd? Indai kace zakaima mace izza da mulki wlhy kana tare
da wahala, dan ba kowace mace bace zata d'auka, gaka da zuciyar tsiya saikace
kuturu, ni nasan minene matsalarkune balle na sasantaku? Kuka Sani, inma zaku
shekara a hakane kuyita zama babu ruwana wlhy”.
Shiru Galadima yay yakasa magana,
zuciyarsa sai zafi take masa.
Momma kam ta d'auki Abdurraheem da
maganinsu tayi ficewarta tabar musu d'akin, sumaci Kansu ita babu ruwanta.
Kansa ya dafe cike da takaici, shi yarasa
gane kan Munaya, da farko yabartane yaga iya gudun ruwanta, a tunaninsa ko
kunyace, amma daga baya saiya fahimci ba haka bane, wani tsirin ne kawai take
Neman k'irk'ira, kud'i ya ajiye mata shima ya fice d'auke da y'arsa a kafad'a.
Munaya dake a bayi tana kuka ta wanke
fuskarta ta fito danjin alamun ya fita.
Kwanciya tayi saman gadon wasu hawayen na
zirarowa, itafa koma mizaiyi tana akan bakanta, dolene saiya kar6a laifinsa
sannan koda zai sameta yanda yakeso.
A can falo Samha yabama Amaturrahman
yay musu sallama ya fita.
Shareshi momma tayi, sai aunty Mimi ce
tace, “Dan ALLAH Momma Ku tsaida shirinan naku keda mom, kubashi matarshi,
yanzune hankalinsa ya kwanta yadace yasami cikakkiyar nutsuwa da iyalinsa, amma
kunbi kun kankane, haba dan ALLAH Momma ”.
Da 6acin rai Momma ta kalli Aunty Mimi,
“To mai d'an uwa, yanzu ke idan Sauban ne a matsayin Munaya zakiso wani yazo ya
auresa a sigar da d'an uwan naki yayi? Miyasa kukeda son kanku, wlhy kinji na
rantse inhar bai gane kuskurensa ya nemi yafiyartaba ta yafe masa bazan ta6a
bashi itaba, idan yagadama ya cika gidannan da fushi, kuma aiga y'ay'ankunan
mata kun haifa, ba kuma zakuso a aikata hakan agaresuba ince?”.
Aunty Mimi ta tausasa murya ganin
ran Momma ya 6aci, “tokiyi hak'uri Momma, ni aganina a zaunar dashi a karanta
masa laifinsa, kinga shi yanzu dukma baisan dalilinkuba wlhy”.
Banza Momma Tamata, ta ajiye
Abdurraheem ta tashi takoma d'akinta.
Binta kawai da kallo aunty Mimi tayi, tasan
akan gaskiya su Momma suke, to amma sai a tausayama Sameer ai shima, akuma
sanar dashi laifinsa, tasan halin Momma akan son kwatarma mai gaskiya
gaskiyarsa, bakuma zata ta6a tank'waruwa ta sauk'iba, balle ga mom a gefe na
angizata.
******
Ran Galadima a 6ace yay wannan tafiya, sauk'inma da yaje yaga jikin Abie
ne sai nutsuwa ta saukar masa, har yanzu yanata samun kulawa ta musamman,
bakuma a shiga inda yake, amma kullum Dr Erfan cikin ma Galadima albishir yake
akan cigaban da ake samu, yauma sosai ya labarta masa komai gameda ga66an Abie
da ayanzu zasu iya fara aiki, zasu barsane yad'an k'ara kwanaki domin k'arfin
jikinsa da abinda ba'a rasaba, dama ciwo shike shiga lokaci d'aya, amma sauk'i
sai a hankali.
Kwanan Galadima biyu yadawo new Delhi.
Ranar kamar wasa Munaya da Samha suka
shiga kitchen wai zata koya mata tuwo, har Momma na musu dariya da tsokanarsu
yau zasuci tuwon y'an gayu.
Daga abin wasa sai Munaya ta zage tayi
nutsetstsen tuwo da miyar ganye, tamusu juns na kayan itatuwa, gamawarsu kenan
sukaje zasuyi wanka, Momma da Aunty Mimi na zaune afalo suna jiran suyi wankan
azo abasu tuwo suci, su Abdurrahman duk suna tare dasu aunty Mimi na yanke musu
k'unba, Yayinda jakadiya ke tayata, babu Wanda ya sanarma zaizo, sai kawai
sukaga ya shigosa da sallamar nan tasa ciki-ciki.
Duk juyowa sukai suna kallonsa da mamaki,
jakadiya ce kawai tasami damar amsa masa, sai Khaleel dake wasa ya tafi da gudu
yana masa oyoyo.
'Daukar yaron yay ya d'aga sama, dukda
yayi girma masha ALLAH.
Ya k'araso cikin falon Jakadiya na
gaisheshi, amsa mata yayi da kulawa, sannan ya zauna a kujera yana rik'e da
hannun Khaleel.
Momma tace, “wai dama kana tafe?”.
“Wlhy kuwa Momma”. Yafad'a cikin sauke
numfashi, itama ya gaisheta.
Itama aunty Mimi suka gaisa, tana masa
sannu da tambayarsa jikin Abie.
Cikin fad'in “Alhmdllh” ya amsa musu,
yabasu labarin cigaban da aka samu, farin ciki na manaye zukatansu.
Ajiye ruwan da baiwar tamasa yay dai-dai
da fitowar Munaya cikin matsakaiciyar kwalliyar data k'ara mata kwarjini da
cikar haiba, dan zani da rigane na atanfa, ta fito asalin bahaushiyarta jinin
buzaye tawani fannin.
Lokaci d'aya idonsa ya sark'e cikin na
juna, kowanne sirrikan kewar d'an uwansa na fita daga cikin nasa, Munaya tafara
d'auke kanta, yayinda shima Galadima ya janye nasa cikeda basarwa. Jitai tamkar
karta k'araso, amma kowa yarigada yaganta, tadai k'araso tana masa sannu da
zuwa. Amsawa yay cikin halin ko in kula.
Ita Momma dariyama suka bata, hakama
aunty Mimi data maidasu television.
Ajiye Abdurraheem d'in yayi yatashi wai
zaije ya watsa ruwa.
Munaya tabisa da kallo a sace, sanye yake
cikin k'ananun kaya, wando ruwan toka da farar riga mai d'ishi-d'ishin ruwan
goro.
Tad'anyi 6oyayyar ajiyar zuciya tana
kauda idonta lokacin daya juyo, dan jiyay a jikina kallonsa akeyi, aiko
saigashi ya kama yalla6iyarsa dumu-dumu.
Baki yata6e ya ida hayewa yana sak'ama zuciyarsa
matakin daya shirya d'auka akanta.
****
Ba'a zauna zaman cin tuwonba saida
Galadima yay wanka ya sakko, duk suka hallara wajen cin abincin, Momma tama
Munaya nuni da ido tayi saving nashi.
Babu musu tabi Umarnin Momma, yanata latsa
waya tamkarma baisan hidimar da sukeba, ga fuska cinkus babu walwala, dukda
zuciyarsa na kwad'ayin fara cin abincin da k'amshin ya addabi hancinsa tun
d'azun.
Tana gamawa takoma mazauninta da Samha
ta shiga tsakkiyarsu, ya ajiye wayar yana kuma wani d'aure fuska dacin Magani,
yayi mamakin ganin tuwo, dukda dai Dama akanyi musu amma sai time to time,
shiyyasa yake sonsa sosai.
Hannunsa ya wanke a ruwan da aka ajiye
masa, baici da tsokalin data ajiyeba. Tun a laumar farko kunnensa ya nemi
tainkewa, 100% yaji yakamata ya baima mai wannan girkin maki.
Momma da Aunty Mimi dai kam kasa hak'uri
sukayi, suka shiga santi da yaba wannan tuwo, Galadima dai yayi tsitt, sai a
zuciyarsa yake yabawa, cikeda tsokana Momma tace, “wasuma dai santin nasu na shirune,
suna tsoron yin magana dad'in ya yanke”.
Dariya su aunty Mimi sukayi, Munaya ta
saka d'ankwali ta kare bakinta tana murmushi, dan kowa yasan dashi Momma take.
Galadima da yasan dashi Momma take
shima saiya murmusa yana satar kallon Munaya.
Saida suka gama tsaf Momma ke cewa lallai
d'iyata sannu da k'ok'ari, rabon danaci tuwo irin wannan mai dad'i tunna inno,
har k'yauta yau saina miki”.
A kunyace Munaya tace, “godiya nake
Momma”.
Dukda Galadima ya fahimci girkin
Munaya tayishi baice k'alaba, saima ya d'auki waya yay kira, ya mik'e ya fice
harabar gidan.
Aifa nan suka shiga gulmarsa suna dariya,
Samha harda cewa tana ganinsa yana lumshe ido lokacin fayakecin tuwo.
Aiko mizasuyi inna dariyaba.
Koda yagama wayar bai koma cikin
gidanba, saiyay ficewarsa saboda gabatowar lokacin salla.
9:30pm
Galadima ya sakko daga samansa, fuskarsa
kawai zaka kalla kafahimci yana tare da damuwa, sanye yake da kayan barci
farare sol, wandon yaje har k'waurinsa amma baikai k'asaba, sai k'amshi mai
sanyi yakeyi.
Cikin sand'a ya tura k'ofar Momma yad'an
lek'a kansa, Munaya kad'ai ya hango zaune abakin gado tana tofama yaran addu'a
a tafin hannunsu tana shafa musu a jiki, ya kalli ko ina babu alamar Momma
saiya ida shigewa.
Shigowar Mutum kawai Munaya ta gani,
tsorata tayi, ta kware baki zatayi ihu yay azamar saka tattausan hannunsa ya
toshe bakin, k'amshin turarensa ya sakata fahimtar shine, d'aukarta yay gaba
d'ayanta tanata mutsu-mutsu da k'afafu dason yin magana amma babu dama.
Yanufi k'ofa da ita zai fice Momma ta
fito daga bayi, daga bayansa kawai yaji ance,
“Sannu shugaban masu iya satar mutane,
to saika ajiyeta ai”.
Fad'uwar gaba da kunya dukta lullu6eshi
a lokaci d'aya, ya dire Munaya yana susar k'eya saboda kunya, yama kasa kallon
Momma d'in.
Itakam bata kuma cewa dashi komaiba tazo
ta gabansa ta fita d'akko abu.
Yana ganin Momma ta fita saiya juyo ga
Munaya da hanzari. A matuk'ar fusace yay kanta, “K! y'ar rainin hankali ALLAH
yau saikin sanarmin minayi miki, inba hakaba a d'akinan zan kwana, bar ganin
Momma ta tsaya miki”.
Ja da baya Munaya tayi ganin yana Neman
maketa, idonta cike da kwalla tace, “Ai kaima kasani”.
Hannu ya d'aga tamkar zai maketa saikuma
ya fasa, ya dunk'ule hannun, “ke wai wace irin mutumce birkitacciya?, ba'a ta6a
zama dake lafiyar ALLAH?, kinsan ALLAH wannan karan Abban zan kira Na sanarmawa
idanni kin rainani.......”
Cikin kuka munaya ta katseshi, “Dama
kasanar masa ai shine ya kamata, kaga shima zaisan tayaya ka aurar masa
yarinya, Papi da mai martaba zasusan Neman auren shekara biyu sukaje suka nema
kuma suka d'aura.....”
Kansa ya dafe cikin tsantsar takaici,
miye kuma nadawo da wannan maganar bayan ta wuce? Kai yarinyarnan y'ar
matsalace. Duk a zuciyarsa yake zancen.
Momma da dama duk cikin shirinsune ta fita
tai saurin shigowa tana fad'in “Minakeji haka? Waye yayi auren shekara biyu?”.
Duk kasa magana sukayi, munaya Na kuka
shiko kunya da nadama dukta rufeshi.
“Waishin bakujini baneba?!”. Momma tayi
maganar a tsawace.
“Momma please cool down”.
“Nayi cool down a ina Muh'd, dama abinda ka
aikata kenan bamu saniba? Yanzu nan da hankalinka da iliminka Na addini da
tarbiyyar da muka baka zakaje kayi auren yarjejeniya da d'iyar mutane? Shekara
biyu ta cika kasaketa saboda son zuciya? Wannan d'abi'ar daga ina kuma ka
samota? Danba koyarwar addininmu bace balle al'adarmu”.
Jiki a sanyaye Galadima ya zauna a bakin
gadon kansa a dafe, itama Momma saita zauna tana kiran Munaya data mak'ure
jikin bango tana kuka maiban tausayi. Takowa tayi tazo inda take, saita zauna a
k'asa kusada ita.
Momma ta kallesu dukansu, saima suka
bata tausayi, Dan takula kowannensu yakamu dason d'an uwansa Na gaskiya,
tad'anyi gyaran murya tana fad'in “Muh'd!”.
Kallonta yayi idonsa ya kad'a zuwa jaa
kad'an, jijiyoyin kansa da gashin jikinsa duksun mik'e saboda damuwa, sai faman
cizar lips yakeyi.
Momma datasan bazaiyi magana ba tunda
yahau sama saita cigaba da maganarta, “Muh'd ka fad'amin gaskiya ya akayi ka
auri Munaya?”.
Kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru
yana kallon Munayar da kanta ke a duk'e tana kuka har yanzu.....
“Ba kallonta nace kayiba, amsar tambayata
nake buk'ata”.
Zamansa ya gyara a sanyaye yace,
“Momma ku gafarceni, dama nasan duk daren dad'ewa wannan ranar saitazo, nasan
nayi kuskuren aikata abinda Addinina bai koyar daniba, hakama al'adata idan
taji zata k'yamaci hakan, saidai wlhy a wancan lokacin banida za6in daya wuce
hakan, ban ta6a tunanin son wataba, damuwar mahaifina da ciwonsane kawai
agabana, banta6a kallon mace dawata siga ta soyyayaba balle tunanin aure, dukda
fad'a da kukemin akan nayi aure a kullum. Bayan jaridar nan ta fita saina shiga
rud'ani da zargin an aikotane dama gareni, wannan daliline yasani tunani sakawa
a satomin ita Na ajiyeta harsai ta sanarmin wanene ya sata, amma sai Muftahu ya
nunamin Sam hakan ba mafita baneba, dama kawai Na aureta, maganarsa ta sakani
d'aukarsa mahaukaci, Dan haka namasa gargad'in karma ya kuma yinta, nidai kawai
a d'akkomin ita Na tuhumeta. Shikuma yace Sam bazai bani goyon baya bisaga
wannan gangancinba, k'yalesa nayi da nufin zan nemo Wanda zaimin aikin. Saidai kuma Nureddin kawai gareni, shikuma a
time d'in yana Italy. Kwatsam sai wani tunani yazomin a zuciya da gamsuwa da
shawarar Muftahu, Dan gaskiya yafad'amin, inhar wani yasan tana hannuna duniya
zata d'auka abinda yafaru a jaridar nan gaskiyane Na aikata d'in, amma idan
aurenta nayi bakin kowa zai mutu, inada kuma ikon sata tayi komai takuma
sanarmin Wanda ya sata. Wannan ne dalilin dayasani bincike akanta, har nasamu
aka d'akkomin ita Na sanar mata buk'atata. Da farko k'in abincewa tayi, amma
daga baya bansan dalilinta Na amincewarba. Wlhy Momma kinji Na rantse ban
aureta dannaci zarafinta ba, kuma harga ALLAH banso kutse cikin mutuncintaba,
wlhy Muftahu ne ya zuba mana pills a hollandia muka sha, ALLAH kuma ya k'addara
zuwan yarannan ta wannan silar, tundaga randa Na aikata mata abinda babushi
acikin yarjejeniyarmu nayi nadama, nakuma gane kuskurena, tunkuma a lokacin
nafara tausayinta, tsakanina da ALLAH badan Na amfanu da itaba Na aureta,
saidai nasan koda fad'a mata nayi bazata aminceba, zata d'auka bisa wancan
dalilinne nace ina sonta, amma nasha nuna mata inason nata, saita dunga
sharewa, bansaniba ta fahimcenine kokuwa bata fahimtaba, wlhy Momma tsakanina
da ALLAH nakeso Munaya, kuma nayi nadamar aikata abinda Na aikata, na tabbatar
bazanma ALLAH wayoba, ikonsane ya aikata yanda yaso a lokacin dayaso d'in”.
Momma tayi murmushinsu na manya tana
kallon Munaya, “Na fahimceka Muh'd, amma adalci d'aya zan maka bisaga wannan
gangancin naka, adalcin kuwa shine ka saki Munaya a warware auren Contract,
saika koma ka kuma Neman aurenta na gaskiya ga iyayenta, ka kuma sanar musu
mika aikata musu a farko, kanemi afuwarsu, shima takawa da mai martaba kaje ka
sanar musu abinda ka aikata, nikuma namaka alk'awarin zan tsaya maka wajen
ganin dawowar Munaya gareka”.
Kasak'e yay yana kallon Momma da wannan
tsarin nata, toshi mahaukacine dazaiyi wannan gangancin? Ai kowane irin hukunci
zai d'auka amma banda na saki wlhy.
“wai kobaka jini bane?”. Momma ta katse
masa tunani.
Narke mata fuska yayi tamkar zaiyi
kuka, “Haba Momma Dan ALLAH, yanzunan dakanki kike fad'ar haka? Nidai kimin
dukkan hukunci dakikeso amma wlhy banda na saki, bazan iya aikata wannan
gangancinba, nayi kuskuren farko amma na biyu kam yana dai-dai daku rasani baki
d'aya, wlhy inason matata ina k'aunarta har cikin raina, ni na amince zanje
nasami su Abba da papi na sanar musu, nakuma nemi afuwarsu amma banda maganar
saki please ”.
Shiru Momma tayi tak'i tanka masa,
saikuma yabama Munaya tausayi, ita dama burinta ya amince yayi kuskurenne.
Haka yaytama Momma magiya amma tak'i
tanka masa, shikuma ya nace.
Saida Momma ta tabbatar yayi ligif sannan
tace, “To ga adalci na biyu tunda ka nace, idan Munaya ta amince ni banida
matsala ai, nabaka minti goma kacal zanje na dawo”.
Tashi Momma tayi ta fita tana gumtse
dariya, saida ta fita tayita sosai, dama akwai randa Muh'd d'inta zai risina
irin haka akan mace, Muh'd dazai aikata laifi bada hak'uri ya gagaresa koma
yafi Wanda yayma laifin zuciya da fusata, itakam babu abinda zatace da ALLAH
sai godiya, Munaya tagama mata komai data zama sanadin canjawar yaronta mai
masifar tauri da tsauri.
A d'aki kam Momma na fita Galadima ya
sakko k'asa wajen Munaya, matsawa tayi baya, ya bita, takuma matsawa, yasake
binta, sai kawai ta saka masa sabon kuka.
Kansa ya dafe yana fad'in “O ALLAH, Munaya
please and Please kiyi hak'uri, nasan nimai laifine amma ki gafarceni, wlhy tun
kwananki biyar kacal dakikayi a gidana nayi nadamar aurenki ta sigar
yarjejeniya”.
Cikin kuka Munaya tace, “saboda kashiga
mutuncina ba”.
Huci Galadima ya furzar, “Haba Munaya
yakike fad'ar haka? Ke shaidace dagani har ke babu mai nutsuwar banbance wani
Abu a waccan ranar, sai wahaltuwa da mukayi muduka, wlhy kinji namiki rantsuwa
badan na lashi zumarkiba nafara sonki, a lokacin nadamar auren contract da
mukayi nayi, amma soyayyarki tafara tsiro da yad'one a zuciyata tamar yanda
tushiyar bishiya keyi, wasu k'yawawan halayyarkine suka jani a k'aunarki,
rashin tsoronki da d'aukar raini, dukda kasantuwata a gidan dana fito baki
amince na takaki yanda nasoba, hakan ya tabbatar min bak'ya cikin mata masu
kwad'ayi dason wani Dan d'aukakarsa ko dukiyarsa, yawan ibadarki ya tabbatar
min da tarbiyyarki, babbar mallakata da kikayi shine damuwa da ciwon mahaifina,
wannan Ce babbar hanyar dakika cusan k'aunarki cikin sauk'i, Munaya kin bada
gudunmawa a arayuwata wadda bazan ta6a mantawa da itaba, aduk lokacin da raina
ya 6aci kafin shigowarki rayuwata nakan azabtu da motsawar ciwona, na fita
hayyacina, bana sauraren kowa sai damuwata, amma kece kika canja wannan
matsalar tawa ta k'yak'yk'yawar siga, cikin hikimarki da ilimin da ALLAH
yabaki, da kasancewarki mai tarbiya, Dan kowanne tsuntsu da gaske kukan gidansu
yakeyi, nasha gwadaki akan abubuwa daban-daban amma kina cinye wannan gwajin
nawa saboda zuciyarki a tsarkake take, please ina rok'onki a karon farko ki
yafemin, kiyi hak'uri kiyi hak'uri kiyi hak'uri, nimai laifine amma mai nadama,
tabbas zanji ciwon wani ya k'ulla alak'ar aure da Samha ma ba Amaturrahman ba
ta sigar dana k'ulla dake, amma wlhy inhar kince naje gabansu Abba na sanar
dasu komai zanje, nidai karki bari aurenmu ya girgiza koda da igiya d'ayane,
namiki alk'awarin samuna fiyema da yanda kike tsammani matata”.
Idanu Munaya ta d'ago tana kallonsa, ya
jinjina mata kai da lumshe idanu alamar tabbatarwa.
Batace komaiba ta maida kanta k'asa.
Hanunta ya saka anashi yana matsawa, a
marairaice yace, “Kokinason Muhammad Sameer yamiki kukane Munaya? Sannan ki
yarda nayi nadama? Wlhy nayi nadama da gaske”.
Jikinsa kawai ta fad'a takuma sanya masa
wani kukan, shima ya rungumeta yana sakin wasu mugayen ajiyar zuciya, jiyake
kamarma ya had'iyeta gaba d'aya ya huta, suzama abu guda d'aya kawai.
Momma dake bayansu tashiga tafi tana
takowa cikin d'akin. Da sauri Munaya tabar jikinsa tana 6oye fuska, shikansa Galadima
yaji kunya, yay k'asa da ido tana murmushi.
Momma ta zauna tana fad'in “Alhmdllh ya
Ubangijin talikai na gode maka, ALLAH ka d'orar da wannan zama har'a aljanna”.
A saman la66a Galadima ya amsa da amin.
Munaya dai kunya ta hanata kallon kowa.
Momma tace, “Nima yau zan sanar muku
abinda baku saniba”.
Daga Galadima har Munaya kallonta duk
sukayi.
Ta gyara zamanta tana murmushi. Tace,
“Tun farkon Aurenku nasan komai”.
Da mamaki duk suka kalli juna sannan suka
maida kallonsu ga Momma.
Murmusawa takumayi, “Lokacin da Muh'd ya
yarda zai auri Munaya amatsayin auren contract Muftahu ya sameni ya sanarmin
komai, danshi burinsa Muh'd ya Auri Munaya ne aure na gaskiya tamkar kowa, a
lokacin kuma yasan cewar Gimbiya Zulfa itace ta saka aka muku wannan 6atancin,
domin 6atama Muh'd suna, abinda yasa Munaya ta shiga matsalar ranar da kuka
had'u a filin idine, shikuma Erfan dayazo miki da suna Fu'ad an sakashi sakama
Muh'd idone, saikuma ya ganku tare, duk zatonsa akwai alak'a a tsakaninku
shiyyasa yayta bibiyar lamarinki harya kaiku plaza, saidai kuma ya rikice
yagaza banbanceku lokacin daya fahimci sewar Ku y'an biyune, shi Muftahu a
lokacin bazai iya tunkarar Muh'd da ainahin gaskiyar abinda ya saniba gameda
Gimbiya Zulfa da Harun, shiyyasa yayta cusamasa ak'idar aurenki a zuciyarsa,
Dan aganinsa hakan zai girgiza zuciyarsu gimbiya zulfa, maybe su aikata abinda
Muh'd zai iya farga dasu, ammashi sai rashin yardarsa ta tsiya ta hanashi
aminta dake kanki. Gudun karta kwa6e agaba yasaka Muftahu zuwa ya sanarmin
komai, yakuma fad'amin nagartarki data ahalinki, ya tabbatar min sai kowa yayi
alfahari dake acikin masarautarnan, dansu suna ganin idan Muh'd ya auri y'ar
talaka zai k'ask'anta bazaiyi sarauta ba, sun manta ALLAH shine mai komai da
kowa. Muh'd yanada tausayi sosai Na tabbata inhar wani Abu ya shiga tsakaninku
bazai ta6a sakinki ba, wannan dalilin ya sakani bama Muftahu pills ya saka
muku, Dan ta wannan hanyar ne kawai zaku iya zama Abu guda”.
Munaya da Galadima duk suka kalli Momma
da mamaki, saikuma sukayi k'asa da kai saboda kunya.
Murmushi Momma tayi. Tace, “Yes nice
nabashi danna kafeku a waje d'aya, nakuma san Munaya zata iya bore akan ka
saketa, shiyyasa a washe garin faruwar abin nasaka ka tilas ku taho nan, wannan
shine mataki na biyu, mataki na uku saka Munaya tak'i kwantar maka dakai
dannasan halinka da bak'in rashin yarda Muh'd, wannan na kula itakuma bata
d'aukar saita kwana, shiyyasa abin yamin dai-dai, nadad'e da fahimtar son
dakake mata, amma na shareka harsai ka gano dakanka ka fad'a mata. Cikin Munaya
shine babbar ribar danaci, wadda nakema ALLAH godiya akowace dak'ik'a ta
rayuwata, nake kuma jin k'aunarta har cikin jinina, badan na rabaku na rik'e
Munaya ba, nayine dama danna tabbatar da nadamarka, itama ta kuma tabbatar da
lallai da gaske kana k'aunarta, ta daina kokwanto a ranta, ALLAH yayi muku
albarka, ya k'ara baku zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba, yabama Sauban mace
tagari shima irin Munaya, itama Haneefa yabata miji nagari kamar mijinta daya bar
duniya koma Wanda ya fishi, jikata Samha itama ALLAH yabata miji nagari Wanda
zai rik'e mana ita”.
Atare muka amsa da amin.
Galadima zaiyi magana Momma tace, “kaga
d'auka matarka ku tafi dare yayi, da safe ma k'arasa, nikam barci nakeji”.
Kunya ta kama Galadima da Munaya, amma
Momma saitayi tamkar batasan sunaiba.
Tamkar munafukai haka suka mik'e sum-sum
suka fice a d'akin, yanda basuyi yink'urin d'aukar yaro ko d'ayaba haka Momma
bata tuna musuba itamaπ€£ππ»...................✍π»
Masoyan
Raina kama amin afuwa dajina shiru, wlhy abubuwane sukaimin yawa, amma Alhmdllh
yanzu nafara daidaita, kuma zanyi k'ok'arin gamawa nan kusa da izinin ALLAH,
ina muku barka da salla baki d'aya, inakuma jiran naman layyaπ
π€Έπ»♀π€Έπ»♀.
wad'anda suka tura hoto kuma Na yafe
muku wlhy har zuciyata, wancan write up nayisane lokacin raina a matuk'ar 6ace,
yanzu kuma Na huceπ
, nayi HAK'URI bisa koyarwar manzon
ALLAH, Maman Haneefa ngd kema sosai ALLAH yabar zuminci, yakuma yafe mana baki
d'aya, dama raina ya 6acine saboda bansan iya inda hotunan zasu kaiba, idan
wani ya gani da k'yak'yk'yawar zuciya wani zai iya munanani ta mummunar hanyar
dabanjiba ban ganiba, duk mace tagari bazataso pictures nata suke yawo a social
media ba, musamman ma mai aure, kobaka da aure mace darajane da ita, saikuma
mutunta kanka ALLAH zai kareka, masu ganin Abu kuna yad'awa jikinku Na rawa
kubari wlhy, kokad'an hakan bashida k'yau, Dan kuma bazakuso hakanba, ALLAH ya
k'ara mana hak'uri baki d'aya.ππ»ππ
ALLAH ya
gafartama iyayenmuπππ»
Post a Comment for "RAINA KAMA (BOOK 3) 27"