NOOR ALHAYAT 34
34🌸🌸🌸🌸✨ *NOOR-AL-HAYAT* ✨
Pharmacy Aliyu ya tafi ya siya mata drugs ya dawo gidan,
bedroom din mumy ya shiga ya bata ledan maganin tace "Toh ni nasan
prescription dinsu Aliyu, ka tasheta ka bata mana" yace "Ohk"
sannan ya fita xuwa dakin baby, baby na xaune kan study table din ta tana
solving mathematics din, Ya karasa kusa da gadon yana
kallon khadijah, kallon
baby yayi yace "Je ki tambayi mai aiki a downstairs ko ta ci abinci"
Baby ta fita ba a dau lkci ba ta dawo rike da plate din abincin ta ajiye a kasa
tace "Tace bata ci ba" Yace "Tell her to make a cup of tea"
baby ta juya ta fita, da cup din shayin ta dawo ya karba ya ajiye sannan ya
tada khadijah, mikewa xaune tayi tana murxa ido ya dau shayin ya mika mata, ta
girgixa masa kai tace "Am not hungry" yace "I know you are not
Hungry, kafin in dawo kin shanye shayin nan" daga haka ya fita, Baby ta
taho da sauri tace "Kawo in taya ki sha kafin ya dawo" khadijah ta
mika mata, baby ta fara shan shayin don ba xafi sai da ta yi rabi ta mika ma
khadijah, ta bata fuska tace "It's till plenty" baby ta sake kafa kai
bata sauke ba sai da ya rage mitsitsi, ta mika ma khadijah ta karba, ta bar gun
da sauri tana goge baki ta ci gaba da abinda take yi a study desk dint,
khadijah ta shanye sauran ta ajiye cup din, xata kwanta sai ga shi ya shigo
yana kallon cup din dake ajiye, hade rai yyi baby sai satan kallonsa take ya
juya direction dinta tayi saurin dauke kai, kallon khadijah yyi yace
"Shayin kika bata ta shanye kenan" ko rufe baki bai yi ba baby ta fice
daga dakin da gudu, ya bi ta da ido, daukan cup din yyi ya mika ma khadijah
yace "Tafi ki kai a sake hada maki wani da kanki" kamar xata yi kuka
tace "Ni ba yunwa nake ji ba" ya wani hade rai yace "Tashi ki
fita" ta mike da kyar ta dau cup din xata fita yace "Ina jiran ki
fa" Rabin cup ta sa kyauta ta hada mata shayin ta dawo dakin yana tsaye ta
shanye sannan ya bata magungunan da bottle water, da kyar ta shanye su har da
kukanta, ya wani hade rai, xata kwanta ya hanata ya dauko textbook din da baby
take assignment yace "Solve it now ba sai kin kwanta ba" karba tayi a
hankali yana kallonta ta fara solving maths din, yace "Idan kin gama ki
kawo min downstairs" tace "Toh" sannan ya juya ya fita, dinning
ya koma ya xauna, saleem dake xaune parlor bai ce masa ba shi ma bai ce masa
ba, bayan kusan minti sha biyar khadijah ta sakko rike da textbook da note book
din baby, gun Aliyu ta nufa ta ajiye tace "Na gama yayanmu" ya dau
book din yana kallon abinda tayi, after sometime yace "Good, shine kike
son a sa ki jss2" ta d'an yi murmushi ce "A jss2 nake ai, it's just
that lesson teacher dina back then at home yana koya min karatun jss3"
Aliyu bai ce komai ba ya rufe books din, ganin tana ta tsaye ya daga kai yana
kallon idonta da suka rine yace "Toh tafi" juyawa tayi xata tafi
dakin kyauta ya kirata, ta dawo yace "Tafi dakin baby kiyi kwanciyar
ki" Sama ta kalla tayi shiru, yace "Tafi na ce" juyawa tayi ta
nufi stairs din, saleem ya bi ta da kallon gefen ido, tana kwanciya dakin baby
bacci ya dauketa. Tun daga wannan lokacin khadijah ta koma dakin baby da kwana
ba don kyauta ta so ba, baby da kanta tace ma Mumy ta gaya ma kyauta ta dauko
kayan khadijah a kawo ta saka a cikin press dinta akwai space, duk wannan abun
Anty khadijah na nan ta sa masu ido abun na cin ranta wai khadijah ce har sama
dakin baby... tabdii, sai dai bata ce wa kowa komai ba da yake har lkcn bata
magana da Aliyu, Mumy ma ko shiga dakinta ta daina yi, yanxu saleem ne nata da
siyama da Aneesah a gidan, sai dai fa ita kadai tasan kudurin dake ranta, kusan
a dakin Anty Khadijah Saleem ke yini, da yake ba wani shiri suke yi da Abbansu
Aliyu ba bata fara ce masa komai kan khadijah ba, tun da ta ki xaman aure domin
kuwa aurenta yyi uku ko ga maciji basa yi da shi idan ba yanxu da ta ja6e a
gidansa ba take gaishesa don dole, idan ta ga yanda yake faram faram da
khadijah sai taji abu ya makale mata a makogwaro, a haka daddy ya koma germany
bayan sati daya shi kadai ba tare da saleem ba, Kusan kullum sai Iklima ta
tsokani khadijah a gidan har da xagi tamkar dai uwarta ke sa ta, Amma ko sau
daya khadijah bata taba kulata ba, tun da mumy tace kar ta sake ta kulata,
hakan yasa fadanta yawanci da baby take yi, wani lkcn har da dambe, wanda ba
haka Anty khadijah ta so ba, ta so ne ace da khadijah iklima ke wannan abun toh
da bata samu fuskar su yi fadan gun khadijah ba yasa ta makale ma baby suke
fadan, gashi baby ta nakada mata duka hakan bai sa kuma ta daddara, islamiyya
mumy ta sa saleem ya kai Iklima, sanin ikliman ba gaida Aliyu take ba har
sannan yasa Mumy bata ma sa shi ya kai ta ba, Ranan litinin da asuba mumy ta
kira saleem ta basa cash na kudi tace "Gashi anjima idan yara xa su
makaranta, ku tafi tare da Iklima kayi mata registration, ita ma tace jss3
take" Saleem yace "Toh Mumy,
har da uniforms?" Tace "Eh Abbanku ne ma ya bada kudin" fita yyi
dakin bayan ya amshi kudin ya kirga. Mumy ta bude kofar dakin Anty Khadijah don
tare suke kwana da 'ya tata da take ji kamar ta mayar ciki, tun da ta ga
Khadijah na kwana dakin baby ta hana iklima shiga dakin, Anty khadijah ta dauke
kai ganin yayarta hade da daure fuska, Mumy ta tabe baki tace "Sai ki
tashe ta daga baccin ta shirya xa su makaranta tare da su Siyama" daga
haka Mumy ta rufe masu dakin. Aliyu na bedroom dinsa yana shiryawa da safen
ranan baby ta shigo sanye da Uniform tana turo baki tace "Yayanmu kaga
wannan ikliman mai shegen tsokanar mutane mumy tace xata fara school din mu yau
kuma same class muke da ita da Iman koh, yaya a schl ma tsokanata xata dinga yi
ni bana son ta xo schl dinmu Allah" yana karashe buttoning shirt dinsa
yace "Toh ki je ki gaya ma Mumy mana" ta turo baki tace "I told
ya Saleem yace xai mare ni, he is always supporting the dirty girl" Aliyu
ya tabe baki bai ce komai ba, Baby ta karasa gun sa ta nuna masa takardan
hannunta tace "Yaya.... Iman ce tayi solving din math din nan, I told her
it's wrong ta ki ta yarda" karba yyi ya juyo yana kallon book din, ya
langwabar da kai yace "Where is she?" Juyawa baby tayi sai ga ta sun
dawo tare da Khadijah, khadijah ta tsayema bakin kofa ita ma tana sanye da uniform
tace "Yayanmu ina kwana" yace "Lafiya lau, where u sleeping when
solving dis?" Ta xaro ido tace "Aa idona biyu" ya mika mata yace
"Toh it's wrong" karasowa tayi ta karba tana kallon baby, tace
"but I told her to solve it let's see kuma taki yi fa, and tare muka yi
wannan" Aliyu yace "Don't worry ku yi submitting haka, learn not to
be afraid of failure..." Khadijah tayi murmushi tace "ohk thank
you" daga haka ta fita baby ma tace masa thank sannan ta bi bayanta. Tun
dawowarsu makaranta iklima ke ta ba uwarta labarin makarantar da ta fara ranan,
Anty khadijah dake saurarenta fuskar nan a yamutse tace "Yanxu ajin ku
daya da annobar can kenan?" Iklima ta tabe baki tace "Ehh mana, class
din mu daya, kuma ko wani tambaya aka yi a class din ita ke bada amsa, Iman ma
ake kiranta a class, she is always bragging she knws everything, in the
afternoon ya Aliyu ya xo school din ma...." Katse ta Anty khadijah tayi da
sauri tace "Wajen wa?" Iklima ta kara tabe baki tace "Water
colour naga ya kawo mata da Math set, may be she told him since yesterday,
lokacin muna break ma ya xo" Anty khadijah da ta wangale baki tace
"Haba...." Iklima tace "Wllh, kuma yyi kamar bai gan ni ba har
bin wajen motarsa nayi" kamar xata yi kuka ta kare maganar, Anty khadijah
da idonta ya kankance tace "Ita kadai ya kawo wa ko har da baby??"
Iklima tace "It seems baby tana da shi, ita kadai naga ya kawo ma"
shiru Anty khadijah tayi tana naxari iri iri a ranta, can tayi kwafa hade da
murmushi. Baby ce tsaye a class tana kyakyata dariya har da rike ciki, Khadijah
dai murmushi kawai take tana kallon sheet dinta na quiz da suka yi ranan over
20 both math and English gaba daya kuma ta cinye, Wata yarinya ta karbe script
din baby dake ta kyalkyale dariya taga 15 gare ta, Baby ta sake satan kallon iklima
dake can gefe tsaye tayi keeping strong face ta linke script dinta ta boye,
baby ta kara rushewa da dariya har da kwanciya, har sanusi ya xo daukansu ranan
baby da ta saci kallon iklima sai ta kwashe da dariya, Siyama da ke kusa da
iklima ta kalli baby tace "Dariyar me kike ke kuma" Baby tayi keeping
innocent face tace "Nothing" a nan ne ta fiddo script dinta a jaka
tana murmushi ta mika ma Siyama tace "Quiz da muka yi daxu a class, I got
15 over 20, Iman kuma scored 20/20" Aneesah tace "Iklima fa?"
Baby ta danne dariyarta tace "I don't really knw" Siyama ta kalli
Iklima tace "Ke meye score din ki" Iklima ta tsuke fuska tace
"16" wani kara baby tayi tana xaro ido tace "Wllh karya take she
scored 3 over 20 I saw it with my two naked eyes" Iklima ta cakumota ta
kunduma mata xagi tana huci tace "Ke kika ban 3 din, munafuka
shegiya" kokuwa suka fara yi cikin motar har sai da Sanusi yyi parking,
Siyama ta fito da baby daga cikin motar, sai da Sanusi ya sa baby ta dawo gaba
sannan fadan ya lafa, amma sai xage xagen juna suke baby na kiranta olodo har
suka isa gida, Iklima ta fice daga cikin mota ta shige gida da gudu ta rushe da
kuka tana kwala kiran Uwarta, Da gudu Anty khadijah ta fito tana tambayarta
menene da yake Mumy na gun aiki bata dawo ba, cikin kuka Iklima tace "Su
baby ne ke ta tsokanata suna kirana olodo tun a school mumy bana son same class
with dem, gwara a mayar da ni jss2..." Baby ta shigo parlorn tana turo
baki Anty Khadijah tace "Baby me ya hada ki da 'yar uwarki, uban waye ya shiga
tsakanin ku har yake neman raba min kan ku?" Baby tace "Anty ita ce
take dambe da ni a mota, just because she scored 3 over 20, ni bani nayi
marking din ba da take fada da ni" Anty khadijah bata ce komai ba ta ja
Iklima xuwa daki ta kulle kofar tace "3 over 20 iklima garin yaya"
iklima ta turo baki tace "Toh the questions where very hard" Anty
khadijah ta bude baki tace "Toh ita babyn me ta ci?" Iklima ta tabe
baki tace "Wai 15" Anty khadijah tace "kina me iklima, to ita
shegiyar yarinyar can fa" Iklima ta kara turo baki gaba tace "She
scored everything, mumy kuma na ji suna cewa xa su nuna ma ya Aliyu xai siya
masu wani abu" hawaye cike idonta ta kare maganar, Anty khadijah tace
"Ba kwa xuwa makarantar ne a can gida!" Iklima tace "Ina xuwa"
Anty khadijah ta dungureta tace "Amma kin kunyata ni Wllh, yanxu da wani
ido xan dubi yan gidan nan, yar iskar can xata iya cinye duka quiz din ke me
kike da baxa ki iya ba" Iklima sai matsar kwalla take, Anty khadijah tayi
shiru tana cixan yatsa, can tace "Tafi kije dakinsu ki dauko min script
din shegiyar da sauri" da gudu iklima ta fita dakin, ta je dakin baby tayi
sa'an ba kowa ta bude jakar Khadijah ta dau takardan quiz dinta ta fita ta kai
ma Anty khadijah, yayyage papern Anty khadijah tayi ta bude window ta watsar
tace "Tafi kiyi wanka ki je ki karbi abincin ki" cike da murna Iklima
ta wuce bayi. Da daddare babu irin neman da Khadijah bata yi ma takardanta ba
baby na taya ta xa su kai wa Ya Aliyu, Baby tace "Ni nasan Iklima ce ta
sace maki script, she openly showed she is jealous tun a schl," daga haka
ta fice ta tafi ta gaya ma ya Aliyu dake dakinsa, shiru yyi yana kallonta.
Post a Comment for "NOOR ALHAYAT 34"