NOOR-AL-HAYAT 36
36🌸🌸🌸✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨
Khadijah ce kadai
xaune daki da daddare tun bayan incident din daxu da rana ta ki fita dakin,
Baby ta shigo daga dakin Mumy tana kallon Khadijah tace "Iman you look sad
since afternoon, ko don abinda anty Khadijah tayi maki ne a schl?" Khadijah ta girgixa mata kai tace "A'a am not feeling fine ne" Baby ta buda ido sosai
tace "Toh ki gaya ma Mumy mana, or you can tell Yayanmu
that is a doctor" Khadijah tace "I will be alright in sha Allah"
juyawa baby tayi ta fita, dakin ya Aliyu ta shiga ta xauna gefensa har ya gama
wayar da yake sannan ya kalleta yace "What happen" tace "Yayanmu
Iman ce naga she is sad all day, I asked what's wrong tace min she is not
feeling fine" ya kalli kofa kamar xai tashi sai kuma yace "Ta fi ki
kira min ita" Mikewa baby tayi ta fita ta koma dakinta, "Yayanmu yace
in kira ki" abinda ta fadi ma khadijah dake kokarin kwanciya kenan,
Khadijah ta hade dai tace "But I didn't tell you to announce I am
sick" baby tace "What ever... Ko ince masa baxa ki xo ba" daga
haka ta juya ta fita, mikewa khadijah tayi ta sa Hijab ta bi bayanta, dai dai
fitowar Anty khadijah daga dakinta xata sauka downstairs, da da ne tana ganin
Iman tayi hanyar dakin Aliyu irin ko ya kira su tare da baby xata mata mugun
kallo ta hanata shiga dakin, yanxu kam sau daya ta kalleta ta dauke kai tayi
wucewarta, a sanyaye khadijah ta shiga dakin don tuni baby ta shiga, ta tsaya
daga bakin kofa tace "Ga ni Yayanmu" yace "kika ce baki da
lafiya, what's wrong?" Ta kalli baby tace "Kawae I told her am nt
fine, ba wai bani da lafiya ba" Baby tace "Ke ma kina son ki fara
karya kamar iklima koh?" Murmushi Khadijah tayi, Aliyu ya kalli baby yace
"You can leave" mikewa tayi tace "Ohk" sannan ta fita, yana
kallon khadijah yace "Come over Iman" karasawa cikin dakin tayi, ya
jawo study chair dinsa ya ajiye mata, ba musu ta xauna tana facing dinsa, a
hankali yace "But I told you not to worry koh?" Ta sunkuyar da kanta
cikin sanyin murya tace "I am without worries" shiru yyi yana kallonta,
ta ki dago kanta, murya can kasa yace "Iman" dagowa tayi da manyan
idonta tana kallonsa, yace "Tel me when you lost ur parent" lkci daya
hawaye ya cika idonta, ya girgixa kai yace "Noo ban ce kiyi kuka ba"
ta gyada masa kai tana fidgeting fingers dinta a hankali tace "My dad told
me I lost my mum when I was just 3, we where together tun daga sannan, shi yake
kai ni schl da islamiyya, I love my dad... He took good care of me, kullum a
eatry Abbana ke siyo mana abinci, I mean all the 3 daily meals, but there is
always custard, cornflakes, golden morn, ice-cream in the fridge and different
biscuits and chocolates at home all for me, duk sanda Abbanmu xai je trip
abroad he always go together with me, not until he married my step mum when I
was 8 years old, and she took over from where he stopped, my step mum is more
than kind, tana so na, she does to me what ever I like, ko Abbanmu na nan ko
baya nan, muna tare har na kai 14 years...."
Katse ta Aliyu yyi yace
"Ita yaranta nawa step mum dinki?" Tayi murmushi tace "Ni kadai
ce yarinyarta, she never gave birth with my dad" Aliyu ya gyada kai yana
kallonta, ta d'an yi shiru, sai kuma a hankali tace "One faithful Friday
Abbanmu xai je port Harcourt wajen junior brother dinsa da aka kira sa ba shi
da lafiya ya xo ya tafi da shi, we bade him fare well har parking lot da Asuba
tare da Ummata" ta fashe da kuka tace "That was the last time we saw
him, sai aka kira Umma aka ce yayi accident and he is gone" kamo hannunta
Aliyu yayi murya can kasa yace "Allah ya ji kansa, yayi masa rahama, dont
cry pls" cikin rawar murya tana gyada masa kai tace "Ameen" yace
"After that?" Ta xame hannunta tace "We cried a lot da ummata,
but at the end tace in daina kuka saboda my dad won't be happy with me idan ina
masa kuka ban masa addu'a ba, and from then ban sake kuka ba don bana son
abbana yyi fushi da ni, ko da yaushe addu'a nake masa Allah ya basa aljanna, we
stayed for plenty months tare da Ummata a gidan mu kadai, kawai ranan sai ga
uncle dina ya xo wai xa a yi sharing property din Abbanmu, I don't knw how but
at the end, kawai ummata tace min ita xata tafi gidansu ni kuma uncle dina yace
xai tafi da ni gidansa in xauna a can, a week after kuma ya sake dawowa... A
ranan muka rabu da ummata ya rufe gidan, ya tafi da ni katsina gidansa ita kuma
ta tafi gidansu ita ma" Aliyu sai kallonta yake ko kiftawa bai yi, labarin
rayuwar wahala da tsangwama da tayi gidan kawunta ta shiga basa, da irin
hidiman da sadeeq ya mata da yanda Mahaifiyarsa ta hanasa daga karshe har xuwa
ranan da Umma ta xo ta gudu da ita ta kai ta gidan sabon mijin da take aure a
kano, nan ma duk ta basa labarin 3 days stay dinta a gidan da abubuwan da suka
faru kafin Umma ta kawo ta nan Kaduna wajen step sister dinta yakumbo, bata
boye masa duk kalan wahalan da ta sha gidan yakumbo ba da irin duka da xaginta
da take, har daga karshe makwabtan ta suka dinga xuga ta a kan ta kawo ta gidan
aiki, har dai yakumbo ta kawo ta nan gidan tare da Abuuu.... Khadijah tayi
shiru tana kallon Aliyu da ya kasa kallonta, kai kana ganinsa kasan tausayinta
ne kawai ya cika sa, jin tayi shiru ya dago da kyar yace "Kiyi hakuri
Iman, all this will come to past one day it's just a matter of time" ta
gyada masa kai kawai, Ya shafa kansa yace "Kuma ki dinga hakuri da abinda
Anty Khadijah ke maki, wataran baxata yi ba kin ji" a hankali tace
"Toh" yace "And Saleem babu ruwanki da shi, soon xai tafi
Germany ki kwantar da hankalin ki kin ji" nan ma tace masa "Toh"
yyi mata murmushinsa mai kyau ya lakaci hancinta yace "Good girl" ita
ma murmushin tayi ta sunkuyar da kanta, yace "Yanxu islamiyya xa ku dinga
xuwa from morning to evening tunda ba schl kuma" kallonsa tayi bata ce
komai ba, yace "Toh tashi ki tafi kar ki kara sa ma kanki damuwa
kinji" kai ta gyada masa ta dau wasu novels guda biyu da ta gani kan study
desk dinsa tace "Can I read them" yace "Noo, I will get you the
one to read tomorrow" tace "Ohk" sannan ta juya ta nufi kofa ya
bi ta da kallo. Bayan kwana biyu Mumy na daki ranan asabar misalin karfe sha
daya da yake babu aiki, Su siyama, Baby da Khadijah har Iklima duk sun tafi
islamiyya, Anty khadijah ta shigo dakin Mumy a shiriye rike da yar karamar
jaka, daga nan bakin kofa tace "Anty fati xan je gidan wata kawata dake
nan Zaria bata ji dadi ba, in sha Allahu xan yi kwana biyu xuwa uku kafin in
dawo" Mumy tace "Zaria kuma, wace k'awa gare ki a Zaria, amma baki
taba ce min kina da k'awa a Zaria ba, kuma ni tun da kika xo gidan nan ban taba
ganin wata k'awa ta xo wajen ki ba, hasali ma ce min kike ba ki da
kawaye...." Katse ta Anty khadijah tayi fuska a murtuke tace "Toh
karya nayi kenan Anty fati, da can na taba ce maki xan je gidan k'awa ta?
yanxun ma lalura yasa xan je wajenta, kuma da ba a Zaria take ba a Abuja take a
anguwar mu, aiki ne ya mayar da mijin ta Zaria" Mumy tace "Toh Allah
ya kyauta, Allah ya kiyaye" Anty Khadijah tace "Ameen, Anty fati don
Allah ki sa ido kan Iklima kin san ba wai can take son cin abinci ba" Mumy
ta harareta tace "Baxan sa ba" Bata ce komai ba ta juya ta fita daga
dakin, Aliyu ne kadai xaune parlor, ko kallonsa bata yi ba ta nufi kofar fita,
ya bi ta da kallo kafin yace "Allah ya kiyaye hanya" ficewarta tayi
ta rufe kofa ba tare da ta tanka sa ba. Karfe biyar na yamma bayan Aliyu ya
dawo aiki ya kira baby ta shigo dakinsa yace "Me ya hana ku xuwa
islamiyya" ta xaro ido tace "Yayanmu na safe fa muka je yau"
yace "Ohk je ku shirya da Iman mu fita" cike da murna tace
"Waow, su siyama fa Yayanmu?" Yace "Ban da su" juyawa tayi
da sauri ta fita baki har kunne, a dakin Mumy ta tarda Khadijah dake fiddo ma
Mumy turarrukan da ta aiki driver ya siyo mata a shopping mall, Iklima kuma na
xaune saman gado tana kallo, Baby tace "Mumy wai Yayanmu yace ni da Iman
mu shirya xa mu fita anguwa" Mumy tayi shiru bata ce komai ba, can tace
"Toh ku je ku shirya" iklima ta sakko saman gadon kamar xata yi kuka
tace "Mumy ni ba dani xai je ba kenan" Mumy tace "Toh ni na sa
ki ki dinga masa fitsara? Wannan kuma ya rage na ku ke da shi" Fita iklima
tayi dakin tana kuka, Baby ta fiddo atamfar da Mumy tayi masu iri daya da
khadijah da mayafi tace "Wannan xa mu sa Iman" ita dai khadijah bata
ce komai ba, baby ta kyalkyale da dariya tace "Allah sarki ban da
iklima" Khadijah tayi murmushi tace "Yayanmu has a very good heart
nasan xai je da ita" Baby tace "Tab kinsan yanda Yayanmu ya tsani mai
rashin kunya" Khadijah bata ce komai ba ta fara sa kayan da baby ta dauko
masu. iklima na fita mumy ta tashi ta tafi dakin Aliyu, daga bakin kofa ta
tsaya tace "Abuturrab amma tare da Iklima xa ku je" Ya hade rai yace
"A'a ni ban ce xan je da ita ba mumy" mumy tace "Toh sai a fasa
tafiyar ai" daga haka ta juya ta shiga dakin Anty Khadijah ta ga iklima
xaune can karshen gado tayi tagumi tana rera kuka, Mumy tace "Sai ki
shirya ku tafi gaba daya" mumy na fadin haka ta juya ta wuce, ko kunya
babu iklima ta tashi ta fiddo sabon kayan ta da takalmi mai tsini da jaka, ta
sha uban make up ta sa spec, ta feshe jikinta da turarurrukan uwarta sannan ta
sakale mayafinta a kafada ta fito, dakin su baby ta shiga su ma har sun gama
shiryawa baby na ganinta ta kwashe da dariya har da faduwa kan gado ta dinga
kyakyatawa, Khadijah tayi murmushi ta dauke kanta, Baby ta kuma dagowa ta kalli
Iklima ta kwashe da dariya, Iklima ta maka mata harara tace "Ai dama ke
mahaukaciya ce" Baby ta mike xaune tace "You are not even ashamed of
ur self, yanxu wa yace xai je da ke, har da wani sa dogon hill da spec, ji wani
make up kamar na yan kasuwar tasha" Juyawa iklima tayi ta shiga dakin
mumy, can sai ga ta ta fito tana huci tace "Mumy na kiranki" Baby
tayi tsaki tace "Ae a haka xa ki kare da reporting din mutane" Dakin mumy
ta wuce tana hararanta, har mumy ta gama ma baby fada bata ce komai ba, tana
fita ta kira Khadijah suka sauka downstairs su jira ya Aliyu tana kumbure
kumbure. Babu yanda Aliyu ya iya haka ya tafi har da iklima, baby ce gaban
motar, iklima da Khadijah kuma a baya, babu abinda ya fi ba Aliyu takaici irin
shegen make up din da tayi a fuska. Smart kids ice cream spot ya nufa da su,
bayan ya siya masu ice cream da pizza da fries ya mayar da su gida duk da ba
haka ya so ba amma saboda iklima ya fasa duk abinda yyi niyya. Ranan lahadi da
daddare Anty khadijah ta dawo gidan, Mumy da Aliyu dake xaune parlor suka bi ta
da kallo ganin yanda ta yi wujiga wujiga, bata yarda ta tsaya parlor ba sannu
da gida kawai tayi ma yar uwar tata ta wuce sama da sauri, Aliyu ta kalli Mumy
yace "Daga ina take mum?" Mumy tace "Allah kadai ya sani"
Anty khadijah na shiga daki ta bude press dinta ta tura jakarta sannan ta rufe
ta tube kaya ta shige bandaki, sai da tayi wanka ta sauya kaya sannan ta fito
tana kwala ma siyama kira ta xo ta xuba mata abinci, xaunawa tayi parlor, Mumy
dake ta kallonta tace "Lafiya na gan ki haka" da sauri ta kalli mumy
tace "A ya kika gan ni?" Mumy tace "Atoh, kinga wani duhu da
kika yi kamar warce taje kauye" Anty khadijah tace "Kauye kuma, Zaria
fa nace maki xan je, kuma gashi har naje na dawo" Mumy tace "Toh
Allah rufa asiri" Sai a sannan Aliyu ya gaisheta, fuska a murtuke ta amsa can ciki, ya mike yyi
wucewarsa sama, tana kallon mumy tace "Ina d'a na saleem?" Mumy tace
"Ya je Abuja jiya da kika tafi, ina jin daga can ma xai wuce Germany, toh
wai ke da kika ce kwana biyu xa ki yi Khadijah ya aka yi kika dawo yau, jiya da
safe fa kika tafi?" Anty khadijah ta hade rai tace "Kai Anty fati, to
kwana biyun bai yiwuwu ba" daga haka ta mike ta wuce kitchen don xuba
abinci ganin siyama bata sakko ba. since afternoon, ko don abinda anty Khadijah tayi maki ne a schl?" Khadijah ta girgixa mata kai tace "A'a am not feeling fine ne" Baby ta buda ido sosai
Post a Comment for "NOOR-AL-HAYAT 36"