Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

NAJEEB 43

Kaman granny tasan abunda ibtisam ke tunani, tace ibtisam zaki ga kaman bana goyan bayanki, ba haka bane, yanzu duniya ta canza, komai ya canza, idan mace batai hakuri gidan mijinta ba inta fita bata san wanda zata aura ba, kinga gwara tayi hakuri ta zauna da Wanda tasan halinsa, saita dinga kiyaye wa, amma yanzu in mace
ta nemi saki , inhar mijinta ya saketa bata san wa zata fad'a mawa ba, sai yasa ake cewa hakuri shine gaba da komai, kuma Mai hakuri yana tare da Allah, wlh ibtisam ban taba ganin laifinki ba gaba d'aya na najeeb ne, domin ke aka cuta amma gashi ina rokanki akan kiyi hakuri wata rana insha Allah za kiyi dariya


2gnovel

4medicals

Smidris

Ibtisam nidai burina in ganku tare har abada, shine Fata na, indai kukai haka zan mutu cikin salama......

Da sauri ibtisam ta rungume Granny tana kuka tare da fad'in insha Allah bazaki mutu ba Granny

Granny tayi murmushi tare da fad'in ai mutuwa ta zama dole ibtisam, lokaci kawai ake jira, amma dole ce ko Ana so ko ba'a so

Ibisam tace toh nidai Granny abar maganan mutuwar nan dan Wlh ba son jinta nake ba, gaba d'aya

Granny tace Indai kam baki Sonta saiki koma ma mijinki, yanda zaki sani farin ciki

Ibtisam tace Granny ni Kinga Wlh yunwa ma nake ji, Sosai mai kuka dafa ne Inci

Granny tace ja'ira wato canza firan zakiyi koh??  Yayi miki kyau ai

Ibtisam tashi tayi ta nufi kitchen inda ta dibo abinci domin taci, tana cikin ci sai ga Ummi ta shigo cikin d'akin tana fad'in ah Ashe y'an karanta an dawo

Ibtisam cikin fara'a da murna take fad'in eh Ummi tun dazu na dawo bakya nan

Ummi tace Mun fita da Maman fati ne, ya karatun an Gama jarabawan kenan?


Pls Kuna mana click na ads

Ibtisam tace eh mun gama zamu sha hutu Mai tsawo harna wata d'aya da sati Biyu

Ummi tace Kai Aiko zaku dad'e a gida Sosai Allah ya taimaka bari inje in watsa ruwa duk na kwaso rana, Ummi ciki tayi tabar ibtisam da Granny





*AMERICA*

najeeb ne zaune yana karanta al'qur'ani domin gaba d'aya yanzu ya iya had'a ba'ki, abun har mamaki yaba malamin yanda yayi saurin iyawa, gashi najeeb baya dad'ewa ya gane Abu, wanda yawanci tun a k'aramin shekaru mutum yake saurin haddace Abu haka, amma sai gashi Abun mamaki shi najeeb da girmansa yana haddace Abu da wuri

Malamin ne yazo inda najeeb yake yana fad'in gaskiya najeeb ka gode Allah, wlh komai naka Abun sha'awa babu wuya ka haddace Abu, nan da nan wlh kana da kwakwalwa sosai

Najeeb saida yakai karshen Aya sannan ya kalli malamin Bayan ya ajiye al'qur'ani yace malam ba komai bane yasa kaga Ina saurin haddacewa ba sai Dan Ina son in koya wanda Allah yaga zuciya ta, duk abunda nake da Wlh Ina aikatawa ne ba tare da sani na ba, sannan yanzu dana gane nake son in koya in iya dole in dage, aikina gaba d'aya na dau hutu dan in nemi ilimin addini, inta Kama ma Wlh ajiye aikin zanyi, duk da nayi yunkurin yin hakan amma suka d'age akan bazan ajiye ba, inje inyi hutu, shine nace na d'auki hutun 5mnt

Malamin yace hakan ma yayi tunda gashi yanzu ko wata biyu bamu yiba amma harka iya abubuwa da dama, ko a haka ka tsaya aika gode Allah, domin wani wanda ya taso tun yana yaro yayi karatun ban tunanin zaiyi aiki dashi akan Kai yanda kake aiki dashi, yanzu nima tafiya ta Kama ni dole zan tafi saudiya, domin mahaifina baida lafiya, Kaga bazan zauna ba har inyi wata ukun da Nayi alkawari ko a haka na Barka Alhmdlh Nasan ka koya abubuwa da yawa

Amma idan naje naga yanayin jikin nasa inda hali zan dawo.....

Najeeb yace a'a karka damu, nida kaina zan biyo ka saudiya, zanje Nigeria insha Allah daga nan Zanzo harda iyayena domin su ganka, ku gaisa

Malamin yace haka yayi, tare dayi MA NAJEEB addu'an samun nasara a rayuwa

Najeeb Bayan ya koma gidansa gaba d'aya baya son zama shi d'aya sai yaji gidan yayi masa girma, kwanciya yayi akan kujeran falon inda ya lumshe ido, lallai sai yanzu yasan yana rayuwa, a da yana rayuwa ne amma kaman matacce, domin bai San yanda zai bauta ma Allah ba, gaba d'aya wannan canjin daya samu ya sameshi ne ta sanadin rayuwarshi da ibtisam ta shigo

Ya fara tunanin yasan mai yasa shan giya ya zama haramun da zina, lokacin da tace mishi duk manyan laifin da Allah ya hana kana aikatawa, tun daga ranan ya fara tunanin sanin Mai yasa ya zama laifi har yakai shi ga kiran malam, wanda gashi yanzu gaba d'aya rayuwarshi ta canza, sai dai abu d'aya da yake fatan shima ya canza

Lokaci d'aya ya tashi ya nufi bedroom d'inshi inda ya fad'a toilet yayi wanka ya fito daga shi sai boxer da singlet Kai tsaye kitchen ya nufa inda ya Tarar damai mishi aiki yace ta Kawo mai coffee, yana fad'in haka ya juya falon ya zauna yana danna wayarshi dake hannunsa

Bayan Mai aikin ta kawo mai coffee ta ajiye Mai akan center table har zata wuce najeeb yace ta tsaya tare da fad'in gobe zani Nigeria so zaki iya d'aukan hutu, but amma ki dinga zuwa kina duba gidan coz ban son in dawo inga datti ko k'ura

Ta amsa da OK sir

Najeeb d'aukan coffee din yayi inda ya fara sha.....

Washe gari kaman yanda yace hakan ko ta faru domin kuwa jirgin k'arfe 10 yabi inda ya tafi Nigeria Kai tsaye a abuja ya sauka inda aka turo mai driver yazo ya d'auko shi,.

Bayan sun k'arasa gida, Zarah da saurinta ta nufeshi tana fad'in Wlcm bros

Murmushi ya sakar mata tare da kallonta yace ya gida da skul?  Yana ganki a gida??

Tace lafiya bros munyi hutu ne

Yace OK

Nan suka shiga ciki abunda najeeb bai taba yiba yau yayi gaida iyayenshi cikin girmamawa, gaba d'aya daga Dad har Mum sunyi mamaki tare da kallon juna

Najeeb ya lura da hakan sai yayi murmushi tare da fad'in kai am so tired I need to rest hope d'aki na a gyare yake??

Mum tayi murmushi tare da fad'in eh my only son, a gyare yake, AI ban barin dakinka da datti, domin Nasan yaron nawa baya son kazanta, amma before ka huta Aida kaci abinci koh

Yace Mum bari in huta na gaji Sosai wlh, nayi missing food d'inki amma tunda kika ga na kasa ci, toh na gaji ne

Tace OK a huta dakyau

Yayi murmushi tare da shiga d'akin nashi wanda yana shiga ya fad'a gado ya kwanta sai bacci

Mum da Dad sukam zama sukayi inda Dad yake fad'in kinga yanda yake gaidamu cikin girmamawa, gaba d'aya harta magananshi ya canza kaman bashi ba

Mum tace Wlh kuwa abun ya bani mamaki, bari dai ya tashi muji ya akayi





Ibtisam ce zaune tana ta wanke underwear d'inta, a wajan fanfo din dake waje, a tsakar gidan

Granny ta fito tana fad'in in banda kazanta mutum saiya tara su wando da skirt da yawa Kafin ya wanke, ai wannan kazanta ne

Ibtisam tace kazanta?? Lallai Granny Wlh kina shiga sabga ta da yawa, d'ago wani pant d'inta tayi tare da nuna mata da tace ina kika ga alaman kazanta a nan??  Kuma pant d'in ga sunan gudu biyar ne duka amma kina wani kiramun kazanta, salan wani yaji kisa a d'auka haka nake

Granny tace toh aji mana, AI gaskiya na fad'a Inba Kazami ba, taya mutum zai dinga tara pant da yawa haka babu wanki, ko ni da nake tsohuwa bana irin haka saike yarinya karama saboda lalaci.

Ibtisam tashi tayi tana d'iban kayan domin ta gama zata toilet ta shanya tace Kedai kika sani, nidai banda lokacin wannan surutun dake inada abunyi da yawa

Granny tace ai kyace haka mana t.....  Wani irin K'ara ta saki tare da yin k'asa, da sauri ibtisam ta saki roban dake hannunta ta nufi Granny tana fad'in Granny lafiya kuwa? Maiya sameki tana tambayar Granny tana kuka

Ganin granny bata ko motsi yasa ta nufi d'akin ummi dake bacci da gudu tana fad'in ummi Ummi kizo mukai Granny asibti na shiga uku Granny ta fad'i k'asa

Ummi dake bacci sai taji kaman tana mafarki da sauri ta tashi amma sai taji ba mafarki bane domin dai dai lokacin ibtisam ta shigo d'akin Tana fad'in ummi Granny ta fad'i muna cikin magana Dan Allah mu kaita asibti ki kira abba

Da sauri Ummi ta tashi tare dasa hijab tana fad'in maiya faru da ita?? Kai tsaye waje suka nufa inda suka tarar har yanzu tana nan kwance a k'asa tana nishi sama sama

Nan Ummi tace maza su kamata su kaita asibiti, hakan ko sukayi ibtisam ta fita ta kira Mai adai daita sahu inda suka Kama Granny ita da Ummi sukai motar da ita, direct asibiti suka nufa da ita inda aka amsheta akai emergency da ita domin a duba lafiyarta

Ibtisam kuka take Sosai, domin a duniya Tana son Granny, ko kad'an bata son taga wani abu ya sameta

Ummi sai a sannan ta kira abba Inda ta fad'a mishi halin da ake ciki, ko minti 30 baiyi ba ya garzayo asibitin Kai tsaye inda ya Tarar dasu suna zaune ibtisam nata faman kuka

Abba yace maiya sameta??  Nan ibtisam ta Fara fad'a mishi Abba muna fira na tashi inje inyi shanya tasa ihu tare da faduwa

Abba yace Toh ya isa mana kibar wannan kukan Mai Dr yace ??

Ummi tace baice komai ba, har yanzu Dr bai fito ba

Nan Abba ya zauna suna jiran fitowan Dr din

Wayar abba ce tayi K'ara d'auka yayi yaga Dad ne Bayan sun gaisa Dad yake cema Abba d'anka ya dawo yau

Abba yace a Barka da fatan ya dawo lafiya

Dad yace lafiya

Abba yace gamu a asibiti Mama bata da lafiya

Nan Dad yace Subhanallah maiya sameta??

Abba yace gamu nan dai har yanzu Dr bai fito ba

Nan Dad yace bari yanzu mu kamo hanya

Abba yace kai yamma yayi fah

Dad yace ya zamuyi dole mu tawo

Nan Bayan sun kashe wayan Dad ya kalli Mum yace mama bata da lafiya yanzu zan kama hanyar Kano

Mum tace maike damunta?

Dad yace wlh ban sani ba, Tadai fad'i ne kuma ance Dr bai fito ba

Mum tace amma daka bari gobe saimu tafi gaba d'aya koh??

Yace a'a yau zani ku saiku tawo gobe

Nan Zarah tace zata bishi

Yace Toh kiyi sauri muje kin San ban son jira

Zarah tashi tayi da gudu taje ta zuba kayanta a akwati tare da abun bukata sannan ta fito suka Kama hanya ita da Dad, mum dai tace ita da najeeb gobe zasu tawo

Bayan fitan su Dad saiga najeeb nan ya fito ya tashi Daga bacci.

Mum tace harka tashi

Yace eh mum Ina Dad ya fita ne??

Tace ya tafi Kano yanzu

Yace yanzu da yamma haka? Lafiya kuwa??

Mum tace granny ce aka kwantar a asibiti, shine ya tafi shida Zarah Nima gobe zamu tafi

Yace Subhanallah maike damunta??  Kai ni bamma taba ji ance tana ciwo ba sai yau

Mum tace Wlh bata ciki ciwo ba, gashi wanda bai ciwo inya tashi yi bai iyaba

Najeeb yace Allah ya Sawake, nima da Ina nan Aida nabi Dad munje tare

Mum tace gobe saimu tafi da safe ai, kaci abinci ko saina zuba maka ne??

Dariya yayi tare da fad'in tunda y'ar autarki bata nan yau nine autan sai a zuba min din kawai

Mum tayi dariya tare da zuba mai, nan suka zauna suna ta fira Inda NAJEEB yace Mum yanzu nasan ina rayuwa wanda da gaba d'aya ba rayuwa nake ba

Mum tace kaman ya??..

Yace Nasan addini na, Mum da gaba d'aya Ina amsa sunan ni musulmi ne amma ban San miye addini ba, amma a yanzu Alhmdlh Nasan abubuwa da dama kuma ina kan koya

Mum cikin mamaki tace najeeb a Ina ka koya??..

Murmushi yayi tare da bata labarin abubuwan daya faru Bayan tafiyar shi

Mum wani hawaye ne ya zubo mata tare da tashi ta rungumeshi ta baya tana kuka tare da fad'in Alhmdlh Alhmdlh Alhmdlh  yau nafi kowa murna yau Ina cike da farin ciki d'ana ya fara neman ilimin addini, najeeb Wlh baka ga yanda naji dad'i ba, abunda yake ranmu kenan akan muyi maka magana sai gashi kaida kanka ka Fara koya Wlh ji nake yau kamun anyi min kyauta Mafi girma a duniya

Najeeb yayi murmushi tare da fad'in Mum nima yanzu baki ji yanda nake jin dad'i ba, nasan miye rayuwa nasan yanda zan tafiyar da rayuwa domin samun tsira wanda da duk ban sani ba yanzu kam Alhmdlh

Mum tace najeeb Allah yayi maka albarka

Tashi yayi tare da kamo hannun Mum Ya ri'ke tare da fad'in mum plz ina son duk wani abu dana miki na rashin tarbiya ki yafe min, Dan Allah domin na gane da ba'a akan dai dai nake ba

Mum ta rungumo shi tare da fad'in na yafe maka duniya da lahira, Wlh najeeb komai kayi min ban taba ri'keka ba cos ni uwa ce sannan nasan duk wannan abunda kakeyi ina maka uzuri duba da irin kasar daka taso a cikinta

Wani irin hawaye ne ya zubo a fuskanshi wanda yayi sauri ya goge, lallai uwa uwace, shida kanshi yana jin kunyar abubuwan daya musu baya amma gashi yanzu tace bata rik'eshi ba, Allah sarki rayuwa duk Wanda bai mutunta iyayenshi ba yayi Asara, kun dai ga irin abubuwan da najeeb yayi amma Mum tace bata ri'ke shi ba, waye Zaima wannan inba Uwar data haifeka ba

Jin kiran sallah magrib yasa najeeb nufa masallaci

Su dad sun k'arasa Kano wajan karfe 9 da wani abu, kai tsaye asibitin suka nufa wanda koda Dr ya fito baiyi musu wani bayani akan abunda yake damunta ba, yadai ce jikin da sauk'i sannan suna kan gwaje gwaje akan abunda ke damunta, sannan har yanzu bata farka ba

Hankalin kowa ya tashi da wannan ciwon na Granny, ibtisam gaba d'aya sai kuka take, inda Zarah take ta rarrashinta, wajan k'arfe Goma Ummi tace ya kamata su tafi gida ita zata kwana da Granny....


Nan ibtisam tace ina, ita zata kwana da ita, saida ummi tayi dagaske Kafin ibtisam ta yarda harta suka wuce suda Zarah da abba inda Dad ya tafi hotel shima Bayan ya sai musu su madara ruwan roba da duk wani abu da zasu bukata sannan yaba Ummi kud'i yace ko za'a bukata

Koda su ibtisam suka je gida sai kuka take tana fad'in Wlh Ina jin tsoran wani abu ya samu granny ina matukar Sonta da yawa, Wlh baki ji yanda nake jiba na shiga uku Granny na

Zarah tace haba ibtisam babu abunda zai sameta addu'a za muyi mata, ki daina fad'in haka insha Allah komai zai wuce sannan granny zata warke Kinji

Ibtisam shuru tayi tana sauraran zarah

Zarah tace ki tashi kije kiyi wanka, kinga duk Fuskanki ya tashi idonki ya kumbura kaman wacce tayi shekaru gidan yari

Ibtisam tace hmm zarah Wlh hankalina a tashe yake ban son wani abu ya samu granny Wlh ko kad'an

Nan zarah tace babu abunda zai sameta maza tashi kije kiyi wanka Kinji

Ibtisam tashi tayi ta fad'a toilet tayi wanka, koda ta fito zarah bata d'akin can saiga zarah tazo da tea a hannunta da kazan da abba ya siya musu

Ta ajiye ma ibtisam tace gashi Nima Bari inje in had'a nawa tea din

Tashi tayi ta nufi kitchen inda itama ta had'o tea d'inta ta dawo ta Fara sha ibtisam kam kasa sha tayi

Zarah tace wai miye haka ibtisam kisha mana, ibtisam tace Wlh zarah bana son sha

Zarah tace Indai baki shaba Nima Wlh bazan shaba.....

Ibtisam tace ke nifa bana jin yunwa gwara kici

Zarah tsaki tayi tare da fad'in kinga saida safe
.ganin dagaske take yasa ibtisam fad'in zo kici Nima zanci

Jin haka yasa Zarah ta zauna tare da d'aukan cup din tea din ta farasha tare da kazan

Bayan sun kammala, itama Zarah wanka tayi tazo ta kwanta

Washe gari tunda sukai sallah asuba suka shiga kitchen inda suka d'aura abinci domin sukai asibti, Bayan sun kammala sukai breakfast suka nufi asibitin Wanda suka tarar har yanzu Granny bata farka ba ga oxygen ansa Mata.

Ibtisam hawaye ta farayi domin tausayi, taji Granny ta bata, tare da furta ciwon lokaci d'aya jiba jiya Uwar haka lafiyanta kalau amma kalla yanzu ko numfashi saida aka sa mata oxygen, kai ikon Allah, fita tayi waje tana kuka domin tausayin halin da Granny d'inta ke ciki

Zarah ce ta biyota inda ta zauna kusa da ita Tana fad'in ibtisam hakuri zakiyi kibar wannan kukan, inba haka ba kanki ne zaiyi ta miki ciwo....

Zuwan Dad ne yasa Zarah fad'in Ina kwana dad? Da fatan an tashi lafiya

Dad yace lafiya yamai jiki??

Tace da sauki

Itama ibtisam gaida Dad tayi inda yace har yanzu kina wannan kukan mamana

Ibtisam hannu tasa tare da share hawayen idonta

Murmushi Dad yayi sannan yace yauwa gwara kibar wannan kukan

Dad ya kalli Zarah yace Mum d'inki bata k'araso ba??

Zarah tace eh

Dad yace a'ah tace min fah tun d'azu sun shigo Kano bari in kirata d'auko wayarshi yayi yana k'okarin kira Zarah tace ga sunan

Nan Dad ya nufesu inda sukai gaba shida mum bayan ibtisam ta gaidata, d'ago kanta tayi sukai ido biyu da najeeb wani irin faduwan gaba taji wanda bata taba jiba sai yau, najeeb kam kallo d'aya yayi mata ya kauda kai tare da kallon Zarah yace yamai jiki hope da sau'ki??

Zarah tace toh har yanzu bata farka ba dai.....

Mum ce tazo tana fad'in ibtisam kuna ina kuzo Granny na kiranku NAJEEB kaima tawo

Da gudu ibtisam ta nufi d'akin inda taga Granny tana kallon sama hawaye na zuba a idonta, jin muryan ibtisam yasa Granny kallonta ibtisam nufan Granny tayi tana kuka tare da kamo hannunta

Granny cikin murya tana hardewa tace ina na je bu

Mum tace najeeb jeka mana

Najeeb kusa da gadon yaje inda Granny ta Kamo hannunshi Tana mishi murmushi, shima murmushin ya sakar mata, had'a hannunshi tayi dana ibtisam ta Fara magana najeeb Ina son ku kasance kaida ibtisam a haka har karshen rayuw..... Kallon mum tayi tace fad'a mishi abunda nake fad'a nan Mum ta Fara fad'a mishi abunda Granny take fad'a.....  Granny tace naso inga yaranku amma Allah bai nufa ba.....

Ibtisam cikin kuka tace Granny ki daina fad'in haka dan Allah na ro'keki

Granny tace ibtisam ni nasan bazan tashi ba, wannan ciwon bazai barni ba, dan Allah najeeb ku koma ku zauna kaida ibtisam hakan zaisa koda na mutu in mutu cikin salama, wlh Ina takaicin rashin jituwan ku,, ina so kumin alkawari zaku zauna a tare har abada......

Da sauri najeeb yace I promise Granny kin gani tare da K'ara matse hannun ibtisam duk mum na fassara Mata

Granny wani irin murmushi tayi lokaci d'aya ta saki hannunsu Tana salati wanda dai dai lokacin oxygen din da aka saka mata yake k'okarin d'aukewa.......



Plz I don't tin gobe zanyi posting coz gobe gaba d'aya Ina busy sai yasa na muku yau but inna samu time may be inyi koda babu yawa










Post a Comment for "NAJEEB 43"