AZIZA DA AZIMA 41-50
*PAID.*
🅿️=4️⃣1️⃣↪️4️⃣2️⃣
Mai gadi ne ya leƙo jin ana kwankwasa kofa ya ga bafulatana tana tsaye kanta a duke,
"Baiwar Allah lafiya kuwa?" cewar Mai gadi,kuka Azima ta saka tana fadin ya taimaka ya yi mata magana da masu gidan,mai gadi ya ce
"Baiwar Allah zan gaya miki gaskiya,me wannan gidan baya ma kasar gabadaya! Ya jima baya nan,iyayensa ne a gidan,idan kuma wani neman taimako kikeyi to wallahi ba zaki samu komai a wajansu ba,dan basu kyauta" Azima ta ce
"Ina da bukatar yi musu aiki ne,don Allah kayi mini magana dasu, ni ba kudinsu nake so ba"
Ganin yadda ta dage yasa Mai gadi fadin "to ɗan shigo daga ta ciki sai nayi miki magana dasu" Azima tana sa kafa a gidan gabanta ya bada dammmm!! Da karfi sai da ta danne saitin zuciyarta,mamakin faduwar gaban nata take yi, a kan benci mai gadi ya nuna mata ta zauna shi kuwa ya nufi babban parlourn gidan da sallama, wata mata ce zaune a hakimce a kujera ta ɗora daya a kan ɗaya tana danna waya,sallamar mai gadi ya sakata ɗagowa tana kallonsa da kyar ta amsa,
"Allah ya taimakeki ranki shi daɗe"
"Lafiya kuwa Ɗan'Bala?"
"Wlh Hajjaju wata 'yar fullo ce a waje take ta faman kuka a taimaka mata tana neman aiki, ina ga irin wa inda 'yan fashi suke kai musu farmaki rugarsu ne, su kashe musu kowa su kwashe shanukansu, wlh Hajjaju abun tausayi" shuru Hajjaju ta yi kafin ta kalli Dan'Bala ta ce
"Je ka shigo da ita" Ɗan'Bala ya amsa da to sannan ya fice da sauri ya zo ya samu Azima dake zaune ya ce
"Zo mu shiga Hajjaju na kira" ba tare da Azima tayi magana ba ta tashi ta bi bayansa, suka shiga parlourn, sosai Hajjaju ta karewa Azima kallo sannan ta kwala kiran wata mai aikinsu
"Hadiza! Hadiza! Hadiza!" wacce aka kira da sunan Hadiza ta amsa da na'am da fito da sauri ta duƙa a gaban Hajjaju, Hajjaju ta ce
"Hadiza je ki yiwa Maman Hanan magana ki ce mata da sauko kasa yanzu" Hadiza ta amsa da to,sannan ta hau da sauri, a tare Hadiza suka sauko da wata dakekkiyar mata wacce ita ma da ka ganta zaka san ta yarda da kanta, tana tafiya a gaba Hadiza na binta a baya,tana saukowa ta ce
"Lafiya kuwa Maman Beenah?"
"E lafiya lau mai aiki ce dama za a dauka shine nace a kiraki tukunna"
"E ya kamata ai, idan yaso sai ta dinga gyara su dakuna tana sharewa da gogewa dan aiki ya masu Hadiza yawa"
"To shikenan sai mu kirasa anjima mu gaya masa mun kara daukar mai aiki dan ya tanadi kudin biyanta ita ma"
"Ah to shine magana ai,idan bai kashe mana kudin ba munyi wadaka yadda muke so ma wa zai yi ma wa? Tunda Uwar da Uban duk sun mutu" Maman Beenah ta yi murmushi ta ce
"Ai muyi kokari da ya dawo mu haɗa masa kannanmu ya aura dan mu ci gaba da tatsarsa"
"Wannan magana taki haka take, Hadiza shiga da wannan ki nunnuna mata abunda ya dace, su dakuna zata dinga gyarawa, dakin su Hanan da Beenah da Hanif sai kuma namu dakunan, sai idan *AL'MAZEEN* ya dawo zata dinga gyara masa nashi dakin dan haka har part din Al'mazeen zaki nuna mata amma ba yanzu ba"
"Tukunna ma ya sunanki?"
"AZIMA BANJU!" cewar Azima kanta a duƙe
"To kin dai ji aikin da zaki dinga yi mana ko? Za a dinga baki dubu goma a wata"
"Na gode sosai" cewar Azima, Maman Hanan ta ce
"Kuje da ita Hadiza"
"To Hajiya,Azima zo muje ki ga dakinmu" da kyar Azima ta miƙe dan tun lokacin da aka kira sunan *Al'mazeen* ta nemi natsuwarta da karfin halinta ta rasa, a zuciyarta take tambayar kanta waye shi Al'Mazeen din? dole ta ga waye shi dan daga kira sunansa sai jikinta ya yi sanyi? anya zata iya zama a gidan kuwa? daga fara saka kafarta a gidan tayi tuntube da faɗuwar gaba,yanzu kuma an kira suna zuciyarta ta tsinke, jin babu kuzari a gangar jikinta yasata b'allan gashin kanta ta sa a baki ta lumshe ido tukunna taji ta dawo dai-dai, Hadiza ce ta nunnuna mata abubuwa dasu dakunan da zata dinga gyarawa a sama da kasa,amma bata haura da ita part din Al'mazeen ba, kasancewar an ce mata ba yanzu za a nuna mata ba,Azima kuwa tace ba zata iya jira ba ko da yaya ne sai ta shiga part din ta gani.
🍃🍃🍃🍃🍃
Yau kwanan Azima biyu a gidan,kuma cikin ikon Allah babu wanda ya shiga hidimarta kamar yadda bata shiga tsabgar kowa, sunan wanda ake kira da AL'MAZEEN shine ya tsaya mata a rai, ga shi bata san part dinsa ba,kuma ba zata iya tambayar su Hadiza ba,dan bata son yawan magana , Beenah har kyautar kaya suka mata,kuma babu wanda ya taba yi mata magana a kan rufe fuskarta da take yi kasancewar ansan kunya gado ce ta fulani, ko Hanif da yake namiji baya shiga hidimar Azima,idan kuma gyaran daki ne tana shiga zata hura iska ta bakinta dakin shi da kansa zai gyara kansa,idan ta shiga daki ko minti goma bata yi zata fito da an shiga za a gansa fesss! shiyasa daga Maman Hanan har Maman Beenah suke jin dadin zama da Azima,ita kuwa Azima yanzu tunanin kisa ya fita a ranta sai son ganin waye AL'MAZEEN.
🍃🍃🍃🍃
A kwana biyu kuwa Aziza ta ɗan sake dasu Mom da Sultana barin ma Sultana da bata nuna mata ƙyama tana janta a jiki, ranar da ta cika kwana biyar a gidan ganin jikin nata da sauki sosai yasa Sultana zuwa wajan Mom tace Mom ta basu kudi zata kai Aziza wajan gyaran gashi, Mom tayi murmushi sannan ta bata kuɗi ta ce driver ya kai su.
Bayan sun je shagon salon din za a buɗewa Aziza fuska ta hanyar kwashe mata gashi tayi saurin saka tafin hannunta a fuskarta dama da kyar ta yarda ta cire hijabinta, dariya Sultana ta sa tana fadin
"Duk rowan da kike mana na ganin fuskarki yau dai dole ki bude" da kyar mai salon ta lallaba Aziza tana kwashe gashin Aziza tayi saurin rufe idonta gam, kan aka hau wanke mata kai ɗin, Sultana na zaune a gefe wayarta ta yi ƙara tana dubawa ta ga Brother da sauri ta daga tace
"Assalamu alaikum, Brother ina kwana?"
Daga can ya sauke ajiyar zuciya ya ce
"Lafiya lau Sultana ya kuke? Ina Mom? Na kira wayarta bata ɗaga ba,ki gaya mata yau ina hanya"
"To Brother sai dai nima na kirata a wayar"
"Sabida me? yau ba saturday ba ai ba skull, ko kina skull din ne?"
"A'a Bro ina shagon salon na raka Aziza ne a wanke mata kai" jin sunan da ta kira yasaka shi katse wayar da sauri, dan tun ranar da ya buge yarinyar nan yake mafarkin tana neman taimakonsa,tun abun baya damunsa har ya koma damunsa, da fari ya yi tunanin ko dan ya bugeta ne amma a yanzu ya kasa fahimtar halin da yake ciki, da ya ji Mom tace ta dauketa aiki har cikin ransa bai so ba amma dai bai ce komai ba.
Sultana kuwa mamakin katse wayar ya yi tayi,daga baya kuma ta ce
"Uhum Yaya kenan" wayar Mom ta kira bata ɗaga ba itama, ta kalli mata mai salon din ta ce
"Dan Allah Anty ki gama mata da sauri zamu tafi gida Yayana wai yana hanya"
"Ai gashin nata ne dayawa wlh ga tsayi ga cika tabarkallah Ma sha Allah!" Sultana ta yi murmushi.
Kusan mintuna talatin aka kwashe ana wankewa Aziza kai idonta kuwa yana lumshe ko da wasa bata buɗe ba, bayan an gama ne aka busar mata da kai din aka shafa mata mayuka masu kyau da ƙamshi aka taje mata shi sannan aka sa ribbom aka daure mata shi, Ma sha Allah! shine Abun da Sultana ta faɗa ta ciro wayarta tana daukar Aziza hoton wacce ta yi saurin maida hijabinta tana rufe fuskarta,bayan Sultana ta biya kuɗin mai salon suka mata godiya suka fice tana ta yabon kyawun Aziza da dogon gashinta,ita dai Aziza tana murmushi ne kawai sama-sama, bayan sun shiga mota Sultana ta ce
"Yanzu mu fara biyawa mu karbo kayanki na wajan tela, yawwa dama ina so na tambayeki,kin iya karatu?"
Aziza ta gya ɗa kai ta ce
"Nayi sauƙan al'kur'ani mai girma a kauyenmu, sannan na karanta litattafai da dama,na iya rubutu kamar irinsu ko da wasika idan Baffanmu zai rubuta idan rubutun tayi masa yawa ina tayasa rubutawa amma ba da irin rubutunku ba, da harafin su Alif kamar ajimi haka"
Sultana ta ce
"Ahh Ma sha Allah ki ce malama ce" ta faɗa a mamakince dan kuwa ta sha mamaki ɗin sosai, murmushi Aziza ta yi ta ce
"A'a ina dai kan neman ilmin"
To shikenan zan koya miki karatun hausa da turanci ta yadda zaki iya duka,idan har kina ganewa da wuri zan cewa Yayana ya nema miki skull mafi kusa da saurin ganewa,sannan matsalar idonkin nan ya nema miki medicalglass"
"A'a Anty Sultana karki gaya masa,ki bari kawai idan kika koya mini ma ya isa, idona kuma haka yake haka aka haifeni dan Allah ko wa Mom ne karki ce mata komai" Sultana ta yi murmushi ta ce
"To shikenan"
Bayan sunje sun karbo kayan suka koma gida a daki suka samu Mom, Mom tace "sannunku da dawowa 'yan matana har kun dawo" Aziza ta duka kasa Sultana kuma ta zauna a gefen gadon Mom, ta ce
"E Mom mun dawo barka da gida, dazu muna shagon salon Yaya ya kirani wai yana hanya mun kiraki baki daga ba"
"E munyi waya da shi daga baya,kema na kiraki bai shiga bane, lokacin da ya kirani ashe na tashi na bar wayar a parlour shiyasa, yanzu dai ku tashi kuje ku gyarawa Yayan naku dakinsa, idan kun gama sai ku shiga kitchen" dan mom bata yarda da lalaci ba dan babu irin girkin da Sultana bata yi shiyasa da shike basu da yawa a gidan kuma ba yara garesu ba shiyasa mai aiki daya kawai suke dauka, suka amsa da to, Aziza ce ta fara tashi ta fita, Sultana ta ce "zo muje part din Yayan" tayi gaba Aziza na binta a baya, suna fita sai ga wani ɗan ƙofa madaidaici Sultana ta buɗe suka shiga,parlour a kasa har da step wani sashene mai zaman kansa a wajan tabbas an tsara parlourn ya tsaru, Aziza matowa tayi da kallon parlour,idonta ne ya sauka a wani pic babba a parlourn shi daya da kuma wani a gefe su biyu, dukkansu fuskarsu babu murmushi,tabe baki Aziza ta yi,dan ita bata ga abum gyara a wajan ba,ganin yadda take kallon hoton ne yasa Sultana fadin "wannan shine Babban Aminin Yaya baya da wani sama da shi, a tare suke a america tare suka yi karatu gabaɗayansu kuma likitoci ne, karki ga fuskarsu haka a haɗe barin ma yadda kika ga na Abokin Yaya,to wlh yafi Yaya Nawaz sauƙin kai,kawai dai shi magana ce bai cika yi ba da dariya,amma idan kina neman zafin zuciya kika samu Yaya Nawaz kin gama" jinjina kai Aziza tayi ba tare da tayi magana ba,suka hau sama yadda k'asan ya tsaru haka ma saman ya tsaru haka de ta dinga bin Sultana har suka gama suka saka masa turaren wuta sannan suka wuce kitchen suka hau girki, dama Sultana na koyawa Aziza yanayin girkinsu,duk abunda ta koya mata sau daya kuma cikin ikon Allah ta riƙe kenan babu mantuwa, idan tazo yi kuma sai tayi wanda yafi na Sultana daɗi, haka suka yi girki a tare suka gama duk da ba wani hira sukeyi ba,tunda Sultana ta fahimci Aziza bata son yawan magana yasa itama bata takura ba,ita kuwa ba zata fahimci tashin hankalin da take ciki bane,bata fata su gano cewa ita ba mutum bace macijiya ce har su rabu tinda zama dasu na wucin gadi ne, bayan sun gama girki Sultana ta ce
"Aziza je kiyi wanka ki canza kaya, sai ki kwanta ki huta idan kika huta da dare sai mu fara karatun ko?"
"Dazu fa kafin muje wajan wankin kai nayi wanka"
"E na sani,ai ita tsafta bata yawa sai dai tayi kaɗan, zaki dinga yi ne dai-dai gwargwaɗon iyawarki,kuma gwara ki saba da shi tun daga yanzu dan bamu sani ba watakila Mom ta samu surki a nan garin" wani wawan faduwar gaba ne ya ziyarci Aziza ta sake maimaita kalman sirki a ranta, da kyar tayi murmushin karfin hali ta amsa da to a sanyaye sannan ta wuce daki,itama Sultana sama ta haura, Aziza na shiga daki ta wuce toilet, tana shiga ta maida kofa ta rufe ta rintse idonta ya sake komawa fari, fatar jikinta ma fari yana sab'ulewa, daga ƙasarta ta fara rikiɗewa nan ta zama rabi mutum rabi macijiya sannan ta zauna a gefen bath din wanka ta hau kuka, tunowa da maganar Arɗo da Baffa Mandi, na cewa ba zata warke ba har sai sunyi aure, kuma ita warakanta yana tattare da Azima wacce bata ma san a wani duniya Azima take ba, sai bayan da ta gama shan kukan nata kafin ta yi wankan ta fito.
🍃🍃🍃🍃
Sai huɗu Nawaz ya samu damar isowa, ko da ya iso wajan Mom ya nufa nan take masa sannu da zuwa tare da fadin
"Nawaz sai yanzu?"
"Wlh Mom motata ce ta ɗan samu matsala a hanya sai da aka mata gyara"
"Subhanallahi! Karfen nasara babu tabbas Allah ya kara kiyayewa"
"Amin Mom bari na samu na ɗan watsa ruwa sai na fito na ci abinci,ina Sultana?"
"Ba mamaki tana dakinta,bata ji shigowarka ba ai da ka ganta da gudu" murmushi ya yi kawai ya fice, part dinsa ya shiga ya samu na tashin kamshi bai tsaya wani bata lokaci ba ya yi wanka ya shirya ya fito, ji yayi ba zai iya komawa babban parlour ba dan haka ya kira Sultana ta kawo masa abincin part dinsa.
*PAID.*
🅿️=4️⃣3️⃣↪️4️⃣4️⃣
Da sauri Sultana ta fito tana kwalawa Aziza kira, fitowa Aziza ta yi ta ce
"Gani Anty Sultana"
"Yawwa Aziza dan Allah zo ki tayani kwashe tray zan kai wa Yaya abinci ashe ya dawo"
"Oh har ya dawo?"
"Nima wlh ban sani ba sai da ya kirani a waya"
"Ayye" cewar Aziza ta duƙa tana daukar tray din da Sultana ta gama jera su plates, sannan itama ta dau ɗaya tayi gaba Aziza ta rakata a baya.
Da sallama suka shiga Sultana ce a gaba sai Aziza dake binta a baya kanta a duƙe cikin hijabi gabanta na faduwa, yana kwance a dogon kujera yana sanye da jallabiyya, amsa sallamar tasu ya yi yana tashi zaune, da sauri Sultana ta ajiye tray din hannunta ta zauna kusa da shi tana masa sannu da zuwa,kanta ya shafa cikin kulawa yana amsawa, duƙawa kasa Aziza ta yi bakinta na rawa ta ce
"Ina wuni *HAMMA NAWAZ* ya hanya?" rassrassras! gaban Nawaz ya faɗi ya ƙura mata ido amma ta gefen ido yana kallon yadda take rirriƙe yatsun hannunta jikinta na rawa daga nesa yake karantar yanayinta duk da ta boye fuskarta cikin hijabi sai saitin ƙaramin bakinta da yake iya hangowa wanda shi ma ke b'ari,
"HAMMA NAWAZ!" yake ta nanatawa a ransa, Aziza kuwa jin bai amsa mata gaisuwarta ba alhali ya amsa na kanwarsa yasa ta tashi a hankali jiki a sanyaye zata fita, watakila baya amsa gaisuwar masu aiki, har ta kai bakin kofa sai taji Sultana na faɗin Aziza ina kuma zakije?"
"Amm dama Anty Sultana dama akwai kayan da ban....kwa. She...ba...ina...so..ne...naje....na kwashe" ta karasa maganar da in-ina tana fita da sauri, cikin fuskar tausayi Sultana ta juyo ta kalli Yayanta ta ce
"Bro,wlh Aziza bata ji dadi ba, ta gaisheka baka amsa ba fa,kuma kamar ma naga tsoronka takeji"
"Za ki yi serving ɗina ne ko zaki cika min ciki da magana?" ya faɗa ba tare da ya kalleta ba, kasancewar tasan halinsa yasa ta zuba masa abincin ta ajiye masa komai sannan ta fice itama,tana fita ya dauki spoon zai kai abincin bakinsa sai ya tsinci kansa cikin rashin jin dadin amsa gaisuwarta da bai yi ba, HAMMA NAWAZ! ya faɗa a fili ya saki murmushi jin yadda ta kira cike da harshen fullaci kuma sai sunan ya yi daɗi a bakinta, da kyar ya lallaba ya ci abinci dan kuwa yaji dadin abincin sosai yaci yasha zobon da suka haɗa ya yi hamdala, nan ya zauna suna waya da amininsa yana gaya masa ranar thursday In sha Allahu yana hanya zai bi jirgi amma sai ya ƙara komawa ta abuja, Allah ya kawo shi lafiya ya yi masa,yana kan waya har aka kira sallar magriba dan haka yace masa za shi masallaci suka yi sallama akan cewa sai sunyi waya anjima, alwala Nawaz ya yi ya tafi masallaci bai dawo ba sai da ya haɗa da isha'i, ko da ya shigo gida babban parlourn gidansu ya wuce da sallama ya shiga a lokacin Aziza na riƙe da kaskon turaren wuta ita kadai ce ma a parlourn, jin sallamarsa yasa jikinta ya dauki rawa wanda bata san dalilin hakan ba, cikin rawar murya ta amsa sallamar ta shi ta ajiye kaskon hannunta tana shirin shigewa daki da gudu taji muryarsa kamar daga sama
"Ya kike? ya jikin naki? Yanzu babu inda yake miki ciwo ko?" ya faɗa lokaci daya,cak Aziza taja ta tsaya,a iya saninta Sultana da Mom suna sama,to kenan da ita yake yi? take tambayar kanta, bata amsa ba bata juyo ba sai da taji ya sake fadin
"AZIZA baki ji ina miki magana ne?" sai a sannan ta juyo murya na rawa ta ce
"Alhamdulillah na warke" tana gama fadi ta shige daki, shuru ya ɗan yi yana nazartan yarinyar daga baya kuma ya yi tsaki ya hau sama,dakin Mom ya je ya kwanta a gadonta suna hira, Mom ta ce
"Bana ma kenan a kasar waje zaku sake yin Azumi ga Azumi ya ƙarato, meyasa ba zaka sa amininka ya dawo nigeria kuyi azumi a gida ba? Bana dai ace kunyi sallah a kasarku tare damu"
"Mom kema kin san ba zai dawo ba ko da na faɗa masa, azumi kuma In sha Allahu mai zuwa idan rai ya kaimu ai muna nan a gida In sha Allah" Mom ta sauke ajiyar zuciya ta ce
"Ai ya kamata,ni na ƙagu ku dawo dan ku nemo matar aure ku aura,barin ma Son yana da bukatar mata wacce zata kula da shi"
"Ai ya samu Mom"
Mom ta ce
"A'a gwara dai fa ya samo mai tarbiyya da natsuwa da hankali" Nawaz ya tabe baki ya ce
"Humm wanda yake fadin zai aura ni kwata-kwata bata min ba,bamu shiri da ita ko kadan amma shi yace zai aureta,kuma abun takaicin fa Mom shima ba sonta yakeyi ba"
"To ina ruwanka? kai fa matsalarka Nawaz zafin zuciya" Mom ta fada tana kallonsa
"Mom ai ba zan can ina ruwana bane ko zafin zuciya,magana ce ta gaskiya,kuma ai abunda ya shafesa ya shafeni"
"To kawai ka tayasa da addua shine babban soyayyar da zaka ci gaba da nuna masa"
"In sha Allah Mom" daga haka suka ci gaba da hirarsu,bai baro dakin Mom ba kuwa sai sha biyu na dare yana fitowa ya shiga dakin Sultana bata nan,tana can dakin Aziza tana koya mata karatu,cikin ikon Allah Aziza ke ganewa, da bai ganta a dakin ba ya yi tunanin ko tana toilet ne dan haka ya wuce part dinsa ya kwanta, sai sha biyu da rabi Sultana ta miƙe tana fadin
"To Aziza bari mu dakata da karatun haka sai Allah ya kaimu gobe kuma, yanzu akwai wani horror series film din da nake kalla, 12 ake farawa a gama 1:30 ga shi yanzu har sha biyu da rabi sai dai na kalli karashi,ko zaki zo muje ki kalla ne?" Aziza ta ce
"Me hakan ke nufi? shi horror din" sai da Sultana tayi dariya kafin ta ce
"Ina nufin fina-finan dodanni, kamar irinsu abun tsoro haka da film din macizai!" rassssss! gaban Aziza ya buga ta yi sauri dago fuskarta ta kalli Sultana ta tsakiyar gashinta da ya rufe mata fuska,Sultana ta kwashe da dariya ta ce
"Matsoraciya kawai,daga faɗa miki har kin firgita, wlh kuma fa Yaya ya hanani kalla har cewa yake min ranar da na fara ganinsu a zahiri zan sani, yanzun ma inada tabbacin ya tafi part dinsa,kinga sai da safe" tana fadi ta fice ta bar Aziza da zare ido tana tunanin ranar da Sultana zata ganta a macijiya mai zai faru? Saurin kau da tunanin ta yi tana fadin "taya ma hakan zata faru?" ajiye tunanin tayi a gefe ta shiga ta ɗauro alwala ta tada sallah,ta jima tana addua tana kuka tana neman taimakon mahaliccinta.
🍃🍃🍃🍃🍃
Kwana a tashi ba wuya a wajan Allah, Azima duk hankalinta ta karkata shi wajan sakawa su Maman Hanan da Maman Beenah ido ganin manaƙisan da suke kullawa wanda bai ji ba bai gani ba, ta sha jin haushin kanta a kan ƙutse da take yiwa wanda bai san da ita ba kamar yadda itama bata san da shi ba, ga shi duk sadda ta yi yunkurin barin gidan sai taji kamar an ɗaure mata kafafu,wannan gida ya zame mata karfen kafa.
🍃🍃🍃🍃
Ana gobe Nawaz sai tafi abuja jibi kuma zai wuce america ya yi wani mugun mafarkin da ya gigita duniyarsa, Aziza ce ya gani a jejin da yafi na kullum muni tana kuka tana miƙa masa hannu ya taimaketa, kar ya tafi ya taimaka mata,ƙiri-kiri ya ganta a macijiya.
🍃🍃🍃🍃
A Lallaba yau aiki yamin yawa🏃🏻♀️
MOMYN AHLAN✍🏻
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_
🍃🍃🍃🍃🍃
🍃🍃🍃🍃
MOMYN AHLAN✍🏻
GARKUWAR MACIZAI🐍😂
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_
🍃🍃🍃🍃🍃
*PAID.*
🅿️=4️⃣5️⃣↪️4️⃣6️⃣
Hakika wannan mafarki ya tayar masa da hankali, ko da ya farka da washe gari jikinsa a mace, da kyar ya gama shiryawa ya fito ya yiwa Mom sallama da shike driver ne zai kaisa ya dawo, shiyasa zasu yi fitar wuri, bayan sun gama sallama da Mom suka rakasa har bakin mota, sai ware ido yake yi inda zan hangi Aziza amma bai ganta ba, kallon Sultana ya yi ya ce
"Ina Aziza ne?"
"Ina ga tana dakinta bari na dubota"
"Noo leave her" ya faɗa yana jan murfin mota Mom tana kan yi masa addua yana amsawa da amin, Mom da Sultana basu koma cikin gida ba har sai da motar ta fice a gate gabadaya aka ja gate din kafin suka koma,ko da suka shiga Sultana ta wuce dakin Aziza ta sameta zaune tana ninke kayan Mom da ta wanke, Sultana ta ce
"Aziza baki fito kinyiwa Yaya Allah ya kiyaye hanya ba har sai da ya tambayeki wlh"
"Ayye ban san ya fita ba da shike ina nan ina ninke kayan Mom ne" ta faɗa ba tare da ta dago ba, alhali taji sadda suka sauƙo dasu Mom har sadda ya shiga mota duk tana tsaye tana leƙensu ta window, sai da ta ga motar ta fice a gidan kafin ta koma daki, Sultana ta ce
"To ke miye haɗinki da kaya ina Buba yake?"
"Wlh jiya ne yaji ciwo a hannu shiyasa na karba kayan na wanke"
"Subhanallahi! Allah ya kiyaye gaba amma ai sai ki faɗa ba wai ki wankesu da kanki ba da an nemo mai wankewa,yanzu dai ki gama ɗin sai ki zo muje Mom ta aike mu karbo kulolin azumi wanda ake abincin sadaka dasu gidan wata kawarta a nan malali"
"To Anty Sultana bari na karasa gani nan zuwa"
"To kiyi sauri ki shirya, saura kuma wlh ki zunduma hijabin kin nan, dan Allah ki nemi abaya ki saka ki yafa gyale akwai gidan da zaki rakani mu shiga tare Mom ta bamu sako ma a gidan" da to Aziza ta kara amsa Sultana, Sultana tana fita Aziza ta sauke ajiyar zuciya tana fadin "Allah ya kaika lafiya Hamma Nawaz, ba mamaki ba zaka dawo ka sameni ba" ta fada tana mai lumshe ido, saurin kwashe kayan ta yi ta kaisu dakin guga, sannan ta koma ta shirya shap-shap tasa doguwar abaya baƙi ta dauki ash'color din gyale taja gashin kanta ta nannaɗesa ta daure a tsakiyar kanta ta dau hula ta saka kafin ta dauki mayafin ta yi lullubinta kamar kodayaushe,ko da ta fito parlour Mom da Sultana suna parlour Mom tana kara ba wa Sultana saƙo, itama ta yi shigar bakin abaya, tana fitowa Sultana ta ce
"Yawwa ko ke fa" murmushi kawai Mom tayi ta ce
"Ma sha Allah 'yan matana, Allah ya kawo miji na gari,kodayake ma yanzu kam sai dai nayiwa 'yata Aziza dan ita Sultana rana kawai za a saka"
A sanyaye Aziza ta ce
"Lahh Anty Sultana shine baki gaya mini ba? To Allah ya kaimu Allah ya sanya alkhairi" Mom ta amsa da amin Sultana kuwa ta dukar da kai tayi tana murmushi,bayan Mom ta gama basu saƙon ta ce
"Dan Allah karku kai magriba,Sultana karki ga dan Nawaz baya nan ku kai magriba kin san dai ko da wani lokaci kiran waya yake yi,da ya kira kuma zai ce ina kike, dan haka kuyi ku dawo"
"In sha Allahu Mom" suka faɗa suna ficewa, duk inda aka aikesu nan suka je, har gidan surakanan Sultana, a gidan kuwa wani ƙaninsa ya ga Aziza sai kallonta yake yi, har sai da ya biyo Sultana yana faɗin
"Anty dan Allah wannan fa?"
Murmushi Sultana ta yi tana faɗin
"Kanwata ce,kana ciki ne?"
"E wlh Anty ina ciki"
"Lallai kam to sai ka gayawa Yayanka"
"To Anty shi da baya kasar ki kirasa ki fara gaya masa,kinga ma sai a haɗa bikin da naku"
"Ahh lallai Walid baka da kunya, wato ma a haɗa da namu?"
"E mana Anty,kodayake ma ku da ba a saka ranar ba, sai a fara namu kafin Yaya ya dawo ke kuma kin gama skull kafin nan kema kin kara girma Anty" ya faɗa cikin tsokana, Sultana ta ce
"Wlh Walid ka rainani,zan haɗaka da Yayanka kuwa"
"Allah ya baki hakuri Anty,ni dai dan Allah ki fara min kamu" banza da shi Sultana ta yi ta shiga mota ta cewa driver yaja su tafi,basu tsaya ko ina ba sai gida,suna isa Mom ta musu sannu da dawowa tace musu idan sun huta su shiga kitchen suyi girki suka amsa da to.
@@@@
Da washe gari sai dare Mom ta samu damar yin waya da Nawaz ya shaida mata cewa ya isa lafiya, Mom ta ce
"Ma sha Allah haka akeso,Allah ya taimaka ka gaishemin da son"
"Zaiji Mom,ina Sultana?"
"Suna can daki ita da Aziza suna karatu, dama kuwa ni ina son yi maka magana a kan yarinyar inaso zan nema mata makaranta, tana da kaifin basira, wlh basu kai sati da fara karatu ba amma karka ga yadda kanta ke ja,abun mamaki" Shuru Nawaz ya yi na dan wani lokaci har sai da Mom ta kuma cewa
"Nawaz bakaji me nace bane?"
"Naji Mom duk yadda kikayi dai-daine, Allah ya baki lada"
"Amin Nawaz" hira suka ɗan taba kafin suka yi sallama da shi.
🍃🍃🍃🍃
Bayan sati biyu da tafiyar Nawaz abubuwa da yawa sun faru daga ciki kuwa harda fara azumi da aka yi, sosai a wannan wata ta ramadan Aziza ta dage da addua Allah ya takaita mata wahalar neman yar uwarta su samu su koma gida, dan ta ƙosa ta koma ta ga iyayenta,kullum da Hajja take kwana take tashi a ranta har ma da Baffanta, ta maida lamuranta ga Allah.
Ta bangaren Azima kuwa ta kasa gane meke mata dadi, dama duk azumin duniya ita kam ba yinsa take yi ba, to wannan din ma haka ta kasance dan ko daya bata yi ba, sosai kuma take sakawa su Hajjaju ido, duk wani ƙullin da suke yiwa AL'MAZEEN.
Ana azumi lafiya da yardan Allah, tunda Nawaz ya bar nigeria ya kasa samun natsuwa, ga mafarkin Aziza da ya gallazawa rayuwarsa wanda ya rasa ya zaiyi da wannan mafarki, ga shi ya kasa gayawa kowa, wanda hakan har rama ya fara saka shi, wanda da an tambayesa zai ce azumi ne kuma ya haɗa masa da ba a gida yake yi ba shiyasa.
Ana saura kwana uku sallah Sultana ta kai musu dinki wajan telarta inda ya cire musu zuƙa-zuƙan dinkuna na gani na fada, laces kala biyu, atampa kala uku, sai shadda da material kala ɗaɗɗaya, da gyalensu da takalminsu dasu sarƙa da ɗankunne, da komai da komai, hakika Mom ta yi kokari,Sultana kuwa ta yi bajinta wajan zabo musu kaya masu kyau, ita ma Azima anyi mata, amma sam basu gabanta dan bata saka a ranta zata yi wani kwalliyar abu sallah ba.
Ana gobe sallah sai aikin suke yi dukkansu a kitchen har da Mom, Sultana ta ce
"Mom wlh zan yiwa Walid ba dadi, kinga yadda ya takura min wai yana son Aziza?" Mom ta yi murmushi ta ce
"Kai yarinta, duka-duka nawa kike bare kuma Walid? to kuma aje ga maganar Aziza wacce take da 15, Aziza ki maida hankalinki a kan karatunki kinji ko? In sha Allah bayan sallan nan zaki fara zuwa university dinsu Sultana tunda Allah ya baki kwakwalwa karki biyewa shirmen Walid kar ma ki fara kulasa, idan Khalil yaji ma ransa ne zai b'aci" Aziza a ranta ta ce
"Ina kuwa nake da lokacinsa,da yasan wacece ni ba zai so kara yin magana da mai irin sunana ba ma" a fili kuma ta ce
"Ni Mom ina da burika da yawa bana da lokacin kulasa"
"Yawwa Azizata" cewar Mom suka ci gaba da aiki har karfe sha biyun dare kafin suka tattara suka kwanta, da washe gari tunda sukayi sallar asuba basu koma bacci ba, abinci sukayi dukkansu har da Mom, karfe takwas da rabi suka gama, Sultana ta ce
"Aziza kiyi wanka da sauri ki zo muje masallaci" Aziza ta amsa da to.
Wanka sukayi suka saka shaddarsu, sannan suka saka hijabansu mai alkebba da takalmansu, suka fito har da Mom itama da ta dake cikin lace dinta, gabadayansu zasuje masallaci dan Mom tace abu daga shekara sai shekara nan ma sai mai tsawon rai wanda Allah ya nufesa da gani.
Haka akayi idi lafiya, sai fatan Allah ya amshi ibadunmu na alkhairi ya yafe mana kurakurenmu amin.
@@@@@@
Bayan sun dawo gida, nan yan uwa da abokan arziki suka hau zuwa ana yiwa juna barka da sallah, masu kawo abinci suna kawowa wa inda ake kai musu ana kai musu, Mom tana haɗawa tana bayarwa ana miƙawa bayin Allah, dasu lemuka da purewater, da kuɗi haka Mom ta dinga rabo, Sultana kuwa tana cikin yan uwanta ana shan su pics ana gaisawa an dade ba a hadu ba, Mom ce ta shigo babban parlour ta kira sunan Sultana ta ce
"Sultana ina Aziza ne kam?"
"Wlh Mom tun da muka dawo inaji bayan mun gama hada abincin da za a fita da shi ban ƙara ganinta ba, dan tun sadda baki suka fara shigowa ban ganta ba" Mom ta ce
"Kin san Aziza bata son mutane kamar ma kunyarsu takeji yanzu haka to ba mamaki tana daki"
"Wlh kam Mom kunyar mutane takeji,ko mu a gida Aziza bata gama sabo damu ba bare kuma yau ta ga mutane ai ba zata fito ba,amma bari naje na fito da ita dan yau yawon sallah zamu je a ga yan uwa da abokan arziki" Mom ta ce "dubota to, sai ku shirya ku fita nima zanje gidan Hajiya Hauwa(gidan sirkan Sultana, Hajiya Hauwa ita ce Mamansu Khalil wanda zai auri Sultana) dan yau muma zamuje ziyara ne"
"To Mom" Sultana ta faɗa tana tashi da sauri ta yi dakin Aziza a lokacin ta gama kukanta tana tunanin wan can sallar tana gida tare da Hajjanta da Baffanta, Sultana tana shigowa Aziza na fitowa daga toilet ta wanke fuskarta, Sultana ta ce
"Ohh Allah Aziza, sabida kinji gidan a cike shine kika boya a daki? To maza ki shirya, zamuje yawon sallah"
"A'a Anty Sultana bana son fita,bazan je ba"
"Wlh sai kinje, Mom ma fita zata yi,yau ranar zumunci ce, yau fa ranar farin ciki ne amma ke na ga kamar ba baki farin ciki ko mun yi miki wani abu ne?"
Aziza ta girgiza kai,
"To idan har ba mu miki komai ba ki shirya yanzu ki canza kaya ki saka atampa,bari nima naje na canza kaya" Aziza ta gya ɗa kai, Sultana ta fice.
har Sultana ta shirya ta sha makeup ta kashe ɗauri ta yi pics ta turawa Khalil dinta, sannan ta fito dauke da handbag dinta ta shiga dakin Aziza ta sameta ta canza kaya amma tana zaune tana riƙe da ɗankwali a hannunta, Sultana ta ce
"Ba kiyi kwalliya ba?"
"A'a Anty Sultana ba zan yi ba"
"A yau sallan? Wlh baki isa ba" Sultana ta fada tana daukar powder ta hau gogawa Aziza a fuska, sannan ta shafa mata red lipstick, duk da fuskarta taki bari ya fito sosai amma ta yi kyau, sannan Sultana ta kashe mata ɗauri, Subhanallahi! Aziza ta yi kyau sosai, nan Sultana ta daukesu hoto, duk da Aziza bata ɗago fuskarta sosai ba, sannan bata ɗaga idonta ba.
Bayan sun fito parlour suka sake yi da Mom, sannan suka fice a gidan, a mota Sultana ta turawa Nawaz pics din tare da rubuta masa HAPPY SALLAH BRO NAWAZ.
Ko da Nawaz ya buɗe ya ga hotunan yan uwa da abokan arziki, Allah Sarki gida dadi,ya fada yana murmushi a ransa, wani hoto ya bude ya ga Mom sai da ya sumbaci hoton, sannan ya sake buɗe wani ya ga Sultana ta yi kyau sosai ya ce "nice sis" ya sake bude wani ya ga da Mom da Sultana ya yi murmushi yana faɗin
"My world" wani hoton ya sake buɗewa ya ga Sultana da Aziza amma bai ganeta ba, sai da ya kara buɗe wani ya ga tana dukar da kai kamar amarya kafin ya ganeta, sun sha lalle kuwa, wani hoton ya sake buɗewa Aziza na zaune a mota bata ma san sultana ta dauketa ba, lumshe ido Nawaz ya yi yana karanto adduar masifa dan Aziza ji yake yi ta zamo masa masifa, kansa ne ya hau sara masa sai da ya ɗan ji dai-dai kafin ya fita dan yaje ya samu amininsa su ɗan fita suma.
🍃🍃🍃
Kwana hudu su Sultana suna yawo,kullum kuma idan suka yi wanka sai Sultana ta musu hoto ta turawa Nawaz, tun yana buɗewa har ya daina buɗewa,dan ganin hoton shike kara masa mafarkai a nasa ganin kenan.
🐍🐍🐍
Ta bangaren Azima ko kaɗan bata yi wankan sallah ba bare shigar sallah, haka ranar sallar ta wuni tana jin haushin kowa,kiris ya rage abincin sallar ma bata watsa masa dafi ba, dan haka kawai ta ga kowa na murna da farinciki ita kuma tana ji kamar zuciyarta ya fashe da baƙin ciki da takaici, haka aka gama cin sallah Azima bata yi shigar sallah ba illa kayan fulaninta da ta dinga yawo da shi har satin sallah.
Bayan komai ya daidaita haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, bayan sallah da sati biyu Aziza ta fara zuwa university din su Sultana, bata shiga hidimar kowa kasancewar tasan ita din ba mutum ba ce,haka zata je ta dawo,idan kuma Sultana na da paper su kan je tare su dawo tare, tana nan tana tara kuɗinta har ma da wa inda ta samu da sallah dan tace kwanan nan zata bar gidan.
🍃🍃🍃🍃🍃
"Innalillahi wa inna ilayhirrajiun! Dan Allah Jauro ka taimakawa ƴata kar mayyar nan ta kasheta!" ya faɗa yana mai riƙe kafar Jauro, Jauro ya ce
"Wlh Malam Halliru na kasa yiwa 'yarka magani, wannan mayyar tana da taurin kai" Salti dan gidan Jauro ya ce
"Wlh Baffana baya da baiwa irinta Baffa Magaji, dama wajan Baffa Magaji kuka je da yanzu ta samu sauki, amma ku fara zuwa kuyi kamun kafa da Sarki Chubaɗo"
"Wlh zanci ubanka Salti! Zaka fita mini ka bani waje ko sai na bazar da kai da sanda?" Salti ya miƙe yana kunkuni yana fadin
"To dan na fadi gaskiya kuma Baffa" Salti na fita, Malam Halliru ya ce
"Hakika munyi kuskure, dole wajan Magaji zamu je neman taimako"
🍃🍃🍃
MOMYN AHLAN✍🏻
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_
🍃🍃🍃🍃🍃
*PAID.*
🅿️=4️⃣7️⃣↪️4️⃣8️⃣
Wajan Sarki Chubaɗo Malam Halliru yaje yana kuka yana ba wa Sarki yankin fulanin kwana hakuri a kan ya taimaka yasa baki ya yiwa Magaji Bawa magana ya taimaka ya duba masa 'yarsa, Sarki Chubaɗo cikin tunzura ya ce
"Ayhoo!! Ashe ku kuna son yaranku, shi da ku ka kora masa nasa ya yi yaya kenan? har kwanan gobe Jumala bata magana bata um bata um-um,nan ku ka daure Aziza kuna shirin kasheta! anyi haka ko ba a yi ba?" cikin kukan nadama Malam Halliru ya ce
"Munyi kuskure ranka ya dade! Amma ba laifinmu bane Jauro ne ya zugamu ya sa mana tsoro da shakku, dan Allah a taimaka mini" Sarki Chubaɗo ya ce
"Idan Jauro ya ce ku faɗa wuta zaku faɗa ne? idan har Magaji zai taimaka maka a nasa ra'ayin farillahi hamdu! amma idan ya ƙi wlh daga nan fada babu wanda zai saka baki" Malam Halliru ya amsa da ya yarda shi dai ayi masa izini yaje gidan Baffa, Sarki Chubado ya daga masa hannu alamun yaje godiya sosai Malam Halliru ya yi ya tashi da gudu har yana tuntube, bayan Malam Halliru ya tashi Wazirin kwana ya ce
"Ranka ya dade bana tunanin Magaji zai ƙi taimakawa Malam Halliru" Garkuwan Fulanin kwana ya ce
"Tabbas haka ne maganarka Waziri, Magaji Bawa Allah ya masa kyakkyawar zuciya,yana da tausayi da hakuri, yanzu haka sai ka ga ya taimaka masa" Sarkin Fadar kwana ya ce
"Ai Halin Magaji Bawa sak wannan Yarinya tasa Aziza, amma ka ga wannan shaiɗaniyar Azima hummm!" Sarki Chubaɗo ya ce
"Barewa ba zata yi gudu ɗanta ya yi rarrafe ba, itama Azima Banju ke rayuwa a jikinta,ba zamu iya tantace ya halayyarta yake ba har sai an rabata da Banju wanda yake rayuwa a jikinta,ko kun manta da komai na jikinta yake rayuwa? Azima fa ba Azima ba ce BANJU ne, amma ni dai nasan Ɗawisu ba zatayi k'yal-k'yal banza ba" Garkuwa ya ce
"Tabbas hakane, ranka ya dade, an fa ja watanni rabon da su Azima da Aziza a wannan yankin, wlh har bana son haɗuwa da Magaji sabida tausayin da yake bani, ga shi dole mutum ya dinga tunanin yaran suna lafiya ko akasin haka! Babban abunji ma ita ce Azima,mu nan da muke yankin jeji ne ya muka iya da ita,bare kuma aje ga mutanen cikin birni da suke da yawa ɗin nan"
"In Allah ya yarda suna lafiya, Allah kuma shi zai ƙare bayinsa daga sharrin Banju, ina da kyakkyawar zato wa yarinyar nan Aziza, zasu dawo In sha Allah, sannu-sannu baya hana zuwa sai dai a daɗe ba aje ba, duk tsawon watanni ko shekaru su Azima da Aziza zasu dawo" cewar Wazirin kwana,Sarki Chubado ya ce
"Haka shima Magajin yake faɗi, zasu dawo In sha Allah,yanaji a jikinsa yaransa suna nan lafiya, kuma zasu dawo garesa"
"To Allah ya dawo mana dasu lafiya,ni kam ma Azizan nake son haɗawa da ɗan wajena" cewar Garkuwa, Waziri ya ce
"Kai yanzu Garkuwa a tunaninka ɗanka Garbiyo zai yarda ya auri Aziza ne? Ai kai ɗanka bai yi halinka ba sam, tsoron bala'i garesa sai kace ba bafulatani ba" Sarki Chubaɗo ya yi dariya ya ce
"Wlh ko cewa akayi Azima da Aziza sun warke bana tunanin Garbiyo zai yarda ya auri Aziza" Garkuwa ya yi murmushi ya ce
"Garbiyo kam ai sai a hankali amma idan ya samu Aziza rayuwarsa zata yi kyau dan na yaba da halin yarinyar sosai wlh"
"Hakane kam, yanzu dai adduar shine Allah ya dawo dasu lafiya" aka amsa da amin.
@@@@@@@
Baffa na zaune a bukka yana lazimi, Hajja kuwa ta samu zaman kofar bukka a kan tabarman kaba,idonta kamar kullum a bakin kofar gida, sallah ce kawai yake tayar da Hajja sai kuma tsakar dare idan zata shiga ta kwanta,duk da bacin sai dai sama-sama, ta ajiye idonta a bakin kofa tace ba zata gaji da jiran dawowar yaranta ba, zasu dawo gareta tanajin hakan a jikinta In sha Allah.
Sallamar Malam Halliru ne ya fargar da Hajja, amma bata amsa ba, sai Baffa da ya fito yana amsawa, Hajja ta jawo mayafinta tana gyara lullubinta, Baffa ya bada izinin shigowa, Malam Halliru ne da matarsa da 'yarsa a hannunsa suna kuka, suka zube a gaban Baffa, shuru Baffa ya yi yana kallon Malam Halliru kafin ya ɗora idonsa a kan 'yar dake hannun Malam Halliru,yana ganinta ya gano matsalar dake damunta, shuru Baffa ya yi ba tare da ya yi magana ba, Malam Halliru cikin kuka yake fadin
"Dan Allah Magaji ka taimakeni, wlh ita kenan mini yarinyar,na jima kafin na samu haihuwa ga shi Mayya tana shirin kashe mini ita ka taimakeni Magaji"
Shuru Baffa ya yi na wasu lokuta kafin ya ce
"Nima su kenan gareni, ɗaya ta gudu da kanta daya kuma kun kusa kasheta,inda daga karshe na koreta da kaina!"
"Hakika munyi kuskure Magaji kayi hakuri" shuru Baffa ya yi bai yi magana ba,ganin haka yasa matar Halliru zuwa ta kama kafar Hajja tana kuka, kallonta Hajja ta yi cikin sanyin muryarta ta ce
"Na san abunda kike ji a ranki a matsayina ta uwa na fahimci hakan, Baffan Biyu ka dubata dan Allah, su ci albarkacin macizai" Hajja na gama faɗi ta miƙe ta shiga bukka, Baffa kuma ya duƙa ya kama goshin yarinyar ya matse, ya rintse ido, ya gane mayyar dake jikinta, tana ɗaya daga cikin wa inda suka gudu ranar da ya haƙo kayansa, jin Magaji a kanta yasa ta hau kururuwa,Baffa ya ce
"Ai kin sake kawo kanki" cikin gurnani ta hau bai wa Baffa hakuri, Baffa ya ce
"Tun asalinki dama ke annoba ce, a wan can karan da ban ƙonaki ba dan na rufeki ne,yanzu kuma ƙonaki zanyi, dan idan na barki ban san wa inda zakiyi kokarin kashewa ba" Baffa na faɗin haka ya rintse ido tare da ɗora wa yarinyar wani farin dutse a kirji, ta sake ihu mai cike da amo, kafin ta koma tayi shuru zuwa wani lokaci aka ji ta ɗiff! Malam Halliru ya ce
"Magaji ba dai 'yata ta mutu ba?"
" 'yarka bata mutu ba Malam Halliru amma ta samu lafiya In sha Allahu, ku tafi gida, ga wannan kuma idan ta farka kuyi mata hayaki da shi" hawaye Malam Halliru ya goge ya ce
"Tabbas mutane irinka basu da yawa a wannan duniyar namu Magaji, dan Allah ka yafe mini, wlh Jauro ne, kayi hakuri dan Allah, Allah kuma ya dawo da Azima da Aziza lafiya" Baffa ya amsa da amin, Malam Halliru da matarsa suka fita suna kan yiwa Baffa godiya, Baffa kuma bukkar Hajja ya shige ya sameta zaune a bakin gadon karanta, ta yi shuru, zama ya yi kusa da ita ya ce
"Jumala?" hannu Hajja ta daga, ta ɗan yi shuru kaɗan kafin ta ce
"Karka damu Baffan Biyu,na rungumi kaddarata,amma ka san ita zuciya bata da ƙashi sai tsoka, duk yawan watanni ko da an shekara ni kullum abu daya nake gani" tana gama fadi ta tashi ta fice, Baffa ya ce
"Duk inda kuke Allah ya kareku, hakika idan har na kama Banju kisan da zan masa wannan karon ƙare ba zai tona ba, dama irin wa innan hatsabiban aljanun basu gane rarrashi , nima zan nuna masa waye ni!"
🍃🍃🍃🍃🍃
*Bayan wata biyar.*
Abubuwa dayawa sun faru a wata biyar din nan, daga ciki kuwa har da 'yar gayu da Aziza ta zama turanci a bakinta raɗau, ga shi shaƙuwa mai karfi ta shiga tsakaninta da Sultana,haka ma Mom bata nuna mata bambanci tsakaninta da Sultana, lokuta da yawa Aziza ta sha yunkurin guduwa amma sai ta kasa hakan, sakamakon yardan dasu Mom suka yi da ita, ga shi ita ba zata iya gaya musu gaskiya a kan ƙaryar da ta musu ba, ta rasa yadda zata yi, ga shi a wannan lokacin tana da bukatar ta canza wani gari ko Allah zai sa a dace.
akwai ranar da suke hira da Sultana take gayawa Aziza zasu je zaria bikin ƙawar Sultana din, to yanzu shirinta idan suka je bikin daga nan kawai ta gudu,idan har ta duba bata ga Azima a zarian ba, to zata sake canza wani gari, dan yanzu alhamdulillah ko da Mom ba ta bata kudin aikinta ba, a kudin da take samun alkairi ya isheta yawatawa neman 'yar uwarta, bare kuma alkairin da su Mom suka mata yafi abunda zasu bata sau dubu dari.
Ta bangaren Azima itama tana nan ta zama wata iri da ita, sai faɗi take yi ta shigo gidan da ya dameta duk sadda ta shigo gidan taji kamar an ɗaureta, ga shi duk yadda ta ci burin hawa can sama part din AL'MAZEEN abun ya ci tura, ala dole ta yi hakuri tana jiran dawowarsa,dan ta fara jin ƙishin-ƙishin a bakinsu Maman Hanan cewa nan da wata shidda AL'MAZEEN zai dawo, dan haka Azima ta koma tsumayin jiran dawowar Al'mazeen.
@@@@@@
Yau saura kwana uku su tafi zaria, Aziza na zaune Sultana ta shigo da sallama da waya a kunnenta hannunta dauke da kaya ta zuba a kan cinyar Aziza,kaya ne kala shidda kala uku iri daya, Aziza ta hau ɗaga kayan tana mamaki, zama a gefen gadon Sultana ta yi, tana ci gaba da wayarta bisa alama kuma da ƙawarta wanda za ayi aurenta suke waya, sai da ta gama wayar tsaf ta tabbatar mata cewa gobe da wuri zasu fito kana suka yi sallama,sannan ta waigo wajan Aziza ta ce
"Azizi baby, ga anko ɗinmu fa"
"Ankonmu kuma?" Aziza ta faɗa tana cikin mamaki tana ɗaga kayan, Sultana ta ce
"E mana, zamu je biki ne ba tare da kinyi anko ba? Wlh muna zuwa zaki zama kamar bare, shiyasa da na tashi na cewa Bros Nawaz ya turo mana da kudi nayi mana mu biyu" shuru Aziza ta yi sai kuma ta sa kuka, Sultana ta ce
"Miye haka kuma Aziza?" cikin kuka Aziza ta ce
"Anty Sultana, anya dawainiyyar ba zaiyi yawa ba? aiki nake muku amma kun maidani tamƙar yar gida, ni kuwa dame san saka muku? Sai dai na bi ku da addua ke da Mom,Allah ya saka muku da mafificin alkairi" hannu Sultana tasa tana sharewa Aziza hawaye ta ce
"Ni da Mom kawai? Shi kuma Yaya ɗin fa! Yana yawan tambayarki wlh idan muna waya da shi, Aziza kin riga da kin shiga ranmu ne wlh, muna jinki ne a jikinmu, shekaran jiya Mom ke faɗamin cewa ita tana miki kallo ne tamkar ita ta haifeki,kuma tana tausaya miki na rashin iyaye da yan uwa da kika yi, tace ba zata taba wulakantaki ba, dama wulakanci mu ba halinmu bane, duk wanda ya riƙe maraya tsakani da Allah,Allah zai ba shi lada, In sha Allahu ko neman aurenki aka zo yi ba zamu taba cewa ke ba yar gidan nan bane, Allah ne ya saka mana kaunarki a ranmu, sabida hankalinki da natsuwarki, wlh Aziza ina jinki tamkar kanwata uwa daya uba daya, a rayuwata ina son na ganni da ƙanwa, amma ana haifata Allah ya dauki ran mahaifinmu, har kwanan gobe Mom taki kara aure, Yaya shike mana komai da shike Allah ya dafa masa, idan har Allah ya baka dama da dukiya amfaninka shine kai ma ka taimaki wa inda basu da shi, dan haka ki daina sa damuwa a ranki ki saki jikinki nan gida ne, bari naje nayi waya da My Khalil" share hawayen da ya sake zubo mata Aziza tayi ta ce
"Na gode sosai Anty Sultana, Allah ya shayar daku ruwan alkausara, Sultana ta amsa da amin tana fadin
"An fa fara maganar tsaida aurena,wlh ana maganar sai da naji zuciyata ta buga"
"Kai Anty Sulty waya gaya miki?"
"Nima ba gaya min akayi ba,dazu ne zan shiga dakin Mom naji suna magana da Hajiyar su Khalil, akan cewa za a tsaida lokacin bikin"
"To shi da baya kasar ma?" Aziza ta faɗa tana ninke musu anko din, Sultana ta ce
"To nima dai naji Mom na cewa a bari sai Yaya ya dawo, kin san fa sun kusan dawowa gida gabaɗaya, shima Khalil din ya kusan dawowa, wai ko kuma a tsaida ranar sai ya kasance lokacin da zasu dawo kar bikin ya wuce saura wata biyu, na dai ji Mom na cewa wata takwas ko wata tara,kafin nan sun dawo dukkansu kuma sun huta" Aziza ta gya ɗa kai tana fadin
"Allah ya tabbatar mana da alkairi"
"Amin ya Allah, da bikina fa ke ce zaki yi min babbar ƙawa wlh" Aziza na shirin magana wayar Sultana ya dauki ruri tana dubawa ta ga Khalil ɗinta, da sauri ta miƙe tana fadin
"My love ya yi kira sai anjima" tana fadi ta fice da gudu, Aziza kuwa ware idanunta tayi tana jinginuwa da bango sabon hawaye na sake zubo mata, komai yana shirin kwab'e mata, kawai mafita shine zatayi addua Allah ya zaba mata abunda yafi mata alkairi,bata so sam Nawaz ya dawo ya sameta a gidan, dan haka taja akwati ta haɗa kayanta tun daga yau, anko din kuma dakin guga ta yi dasu idan aka goge sai ta miƙawa Sultana nata.
🍃🍃🍃🍃🍃
Yau ce ta kama ranar da zasu tafi zaria, gaban Aziza ke dukan uku-uku tun farkawarta bata da kuzari,ganin haka yasa Mom cewa Aziza meke damunki ne?
"Ba komai Mom"
"A'a Aziza karya ba halinki bane, karki fara meke damunki?" a sanyaye ta ce
"Kaina ke ciwo Mom"
"Subhanallahi! Idan ba zaki iya tafiyar ba ki bar shi ki huta abunki ita mai biki sai ta tafi" nan Sultana ta yi tsalle ta dira da cewa wlh Aziza bata isa ba,kawai dai son mutane ne da bata yi, Mom ta ce
"A'a Sultana baki zo da gaskiya ba, yarinya tace miki bata da lafiya kice bata isa ba,kinga wuce ki tafi kawai Allah ya kiyaye hanya" Sultana tace ita kuwa idan har Aziza ba zata je ba itama ta fasa, Aziza ta ce
"To ba kin riga da kin gaya mata yau kina hanya ba?"
"Sai na ce mata na fasa😏, kuma ai ba ina hanya nace mata ba muna hanya nace mata"
Aziza ta yi murmushi ta ce
"A'a ba za ayi haka ba Antyna ta kaina tashi mu tafi" Mom ta ce
"Ki biyewa Sultana ki kashe kanki"
"A'a mom ai nasha magani, ciwon kan zai sakeni"
"To Allah ya kiyaye hanya, a gaida su Hajiya Habiba, ai da ace zaku biya ta kano da na baku sako wa su Hajiya Lawiza" haɗe rai Sultana ta yi ta ce
"Gaskiya Mom ba zamu kano ba, daga zaria sai kaduna In sha Allahu" ganin yadda Sultana ta haɗe rai yasa Mom dariya ta ce
"To shikenan Allah ya kare" ta faɗa tana rakosu har jikin mota, ta ce
"Ina dai ba zaku wuce kwana biyun ba ko?"
"In sha Allah Mom ba zamu wuce ba,ai ba zamu je mu zauna mu barki ke ɗaya ba" daga haka driver ya jasu ,Mom tana ɗaga musu hannu.
Kasancewar tsakanin kaduna da zaria ba nisa nan da nan suka isa aka hau shagali dasu, haka sauran ƙawayen amarya Sulaiha suka ja Aziza a jiki, amma matsalarsu daya da ita shine rufe fuskar da take yi, sai da Sultana tace musu ai ko a gida ma haka take wuni fuska a rufe kasancewar tana da matsalar ido, daga haka suka fara yi mata fatan sauki, sai yaba kyawunta sukeyi da dogon gashinta,ita dai Aziza nata murmushi da godiya, dan duk tunaninta ya raja'a a ta hanyar da zata bi ta gudu, dan suna isowa zaria bata yi kasa a guiwa ba ta duba amma bata ga Azima ba, yanzu garin da take hari taje shine garin da Mom tace zata aiki Sultana idan har zasu je, wato KANO.
Ranar da suka zo anyi party da washe gari asabar aka ɗaura aure, bayan an daura aure da daddare akwai dinner daga wajan dinner za a wuce da amarya gidan mijinta da washe gari kuma sai su koma kaduna, a daren yau idan suka je dinner shine Aziza tasa a ranta zata gudu.
@@@@@
Sun sha makeup dinsu, suka cakare cikin net dinsu kalar sky blue sunyi kyau sosai,ita dai Aziza taƙi yarda ayi mata makeup har amarya Sulaiha take fadi cikin wasa ai ita da kyau ɗinta ba sai an mata kwalliya ba tunda bata so a barta.
Suna can babban hotel din da aka kama ana ci gaba da gudanar da abunda ya tara jama'a, Khalil ya kira Sultana a waya kasancewar bata ji a ciki yasa ta fito waje tana wayar.
Wasu maza ne su uku a wajan gate din hotel din suna cikin mota sai aikin busa hayaki suke yi, wani ne ya daga ido daga cikinsu ya sauke a kan Sultana dake waya, sai da ya kara goge idanunsa kafin ya ce
"Kaii Ɗan Gidan Alhaji? Wa nake gani a can kamar kanwar Doctor Nawaz?" wanda aka kira da sunan Ɗan Gidan Alhaji ya dago yana ƙarewa Sultana kallo ya ce
"Jar Uba! Ita ce wallahi! To me ya kawota zaria?" ɗayan ya ce
"Ko ma me ya kawota, lokaci ya yi da zamu rama abunda Yayanta ya mana a kanta" Dan Gidan Alhaji ya ce
"To yanzu ya kuke ganin zamuyi?" dayan ya ce
"Ah mu kwamusheta kawai,muje mu huta da ita, ya ɗanɗani abunda mukaji sadda yasa aka kullemu a kan wasu banzan talakawa!"
"Lallai Shaho ka kawo shawara, kuma dabadin Baban Ɗan Alhaji ba wlh da mun ƙare rayuwarmu a kurkuku" Dan Gidan Alhaji ya ce
"Yanzu ku daina wannan maganar tunda ba mutane yanzu a kusa ku fita ku dauko mana ita" sai da suka leka suka leka kafin suka fito daukar Sultana wanda hankalinta ya yi nisa sosai a wayar da take yi da Khalil.
Aziza na zaune cikin kawaye da ta waiga ido bata ga Sultana ba ta tashi a hankali tana fadin
"Ki yafeni Anty Sultana zan tafi, ba zai yu ba rayu daku ba danni ba mutum bace,zanje neman yar uwata dan mu koma duniyarmu!"
Da wannan tunani zuciyarta babu dadi kamar karta tafi dan an saba, ta fito saɗaf-saɗaf.
Fitowar Aziza ya yi dai-dai da lokacin da su Shaho suka roɗa ma Sultana katako a bayan kai a kan idon Aziza,ihu Aziza ta saka tana fadin
"Antyyyy Sultanaaaa!!!" ganin haka yasa Ɗan Gidan Alhaji Faɗin su haɗa da Aziza su kwamuso.
🍃🍃🍃🍃🍃
MOMYN AHLAN✍🏻
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_
🍃🍃🍃🍃🍃
_GOOD MORNING😄_ ☕☕🍵🍵
*PAID.*
🅿️=4️⃣9️⃣↪️5️⃣0️⃣
Dan haka suka bugawa Aziza katako a kai sau daya,jiri ne ya ɗibeta amma bata suma ba, ta hau kokawa dasu dan ta kwace Sultana daga hannunsa, Shaho yasa katako ya dinga sauke mata shi a gefen kai har ta suma kanta ya fashe yana zubar da jini, sannan suka daukesu suka saka a mota.
Basu zarce ko ina dasu ba sai wani gidan Ɗan Gidan Alhaji da Babansa ya gina masa, suna zuwa su Shaho suka fito dasu Sultana da Aziza wanda suke sume, suka shige dasu, suna shiga dasu suka kwantar dasu a parlour, D'an Gidan Alhaji ya ce a bari su farka, Shaho yace ba sai an jira sun farka ba dan babu lokaci, a yayyafa musu ruwa kawai su farka, ga wannan yarinyar ba mamaki ita ma kanwarsa ce dan naji ta kiran wannan da Anty, wai cakwai kenan gata kirjinta a cike yake,yaran dai za a shana fa" Dan Gidan Alhaji ya yi murmushi yana lashe baki tare da binsu da kallo, Shaho ne ya kawo ruwa cikin bokati ya shekawa su Sultana da Aziza tun daga kansu har kafarsu, a firgice Sultana ta farka ita ce ta fara dawowa hayyacinta tana riƙe bayan wuyarta dake mata tsami, ware idanunta ta yi a kan Ɗan Gidan Alhaji, tayi saurin ja da baya tana girgiza kai,tana juya idonta ta sauke shi a kan Aziza wacce bata riga da ta farka ba, a razane Sultana ta hau jijjiga Aziza tana kuka tana kiran sunanta ganin yadda jini ke b'ulb'ula a kan Aziza, cikin kuka Sultana ta ce
"Wlh idan Yayana ya sani dukkanku babu wanda zai tsira" D'an Gidan Alhaji ya ce
"Kafin nan Ubana ya min biza na bar kasar, kuma ko da zai sani sai mun miki mummunar tab'o,ko nace sai munyi muku mummunar illa!" Ya fada yana sa hannu zai damki Sultana Aziza ta cafki hannunsa gam tana daga kwance dan duk taji abunda yake fadi, cafka bana wasa ba Aziza ta yiwa hannun Ɗan Gidan Alhaji, da mugun mamaki Sultana ke kallon Aziza wacce take kwance idonta rufe ga jini, cikin rawar murya Sultana ta ce
"A....ziii.....zaaa...! dan Allah ku kai min ƙanwata asibiti kar ta mutu, baku da imani!! Ku azzalumai ne!!" Shaho ya yi kan Sultana yana zuwa zai kai mata mari Aziza tasa kafa ta tokaresa sai da ya yi sama kafin ya bugu da bango ya faɗi kasa, da sauri Dan Gidan Alhaji ya ce
"Kai wannan yarinyar fa na ga alama tana ji da kanta, ga shi ta riƙe min hannuna kamar zata b'alla, ke dan uwarki da Ubanki! Sakar min hannuna" ya fada yana jan hannunsa da karfi amma Aziza ta ƙi sakewa, Sultana kuwa tana takure a jikin Aziza tana kokarin yadda zata tsaida jinin da ke fita akan Azizan.
"Shaho, yarinyar nan fa taƙi sakina!!" Shaho wanda ya sha ƙasa ya miƙe a fusace yana fadin
"Wannan yarinyar sai fa mun nuna mata cewa ni cikakken dan iska ne, ban taba kisan kai ba, amma inaji zan fara a kanta, dan naga tana fama da tashen balaga, ko dazu bugu ɗaya nayi wa dayar ta suma amma ita sai da na mata biyar! dan haka ba zata sakeka ta dadi ba,bari ka gani" Shaho ya faɗa yana jan wani karfe a bayan windown labule, ganin haka yasa Sultana fasa ihu dan ta ga gadan-gadan ya nufi Aziza dake kwance, a haukace Sultana ta hau faɗin
"Dan Allah Aziza ki sakesa, ba danni ba Dan Girman Allah, kinga munyi sallama da Mom lafiya-lafiya kar a koma mata da gawawwakinmu, dan Allah Aziza ki sakesa! Ki sakesa nace!!" Sultana ta faɗa da karfi a tsawance, sake masa hannu Aziza ta yi, tana sakinsa ji ya yi tamƙar kashin hannunsa ta tsatstsage,a hankali tasa hannu a tsakiyar gashin kanta ta dafe,da kyar ta miƙe zaune sabida jirin dake dibarta dan ta bugu sosai a kai,inda yake saurin musu illa kenan shine duka a kai, amma duk sauran jiki dan sun bugu aikin banza ne.
Kanta a duƙe tana riƙe da kai da hannunta daya, dayan hannun ta yi musu nuni da yatsarta manuniya cike da gargaɗi ta ce
"Duk wanda baya so Uwarsa! ta haifi wani, to kar ya kuskura ya sake ya taba mini Antyna, ku maidamu inda kuka dauko mu!" dariya Shaho da ɗan Gidan Alhaji da ɗayan suka yi, ƊAN GIDAN ALHAJI ya ce
"Zamu maidaku bayan mun yaga muku rigar mutunci! Ke kuma mai bamu umarni kar mu tabata, Yayanta ne yasa aka kullemu watanmu biyar a kurkuku da kyar mahaifina ya fiddomu, dabadin shi ba ma da har yanzu bamu fito ba, ai kema bamu san kanwarsa ba ce! Mun daɗe muna neman hanyar fansa! Sai ga shi ta kawo kanta har zaria, abun ya bada kala fa, dan haka ke ki fara zuba ido ki ga yadda zamu mata kafin a gama da ita a zo kanki, Shaho ku banƙaremin ita!" kukan tashin hankali Sultana ta saka tana kokarin kama Aziza su Shaho suka fizgota suka bajeta a kan carpet ɗaya ya riƙe mata hannaye ɗaya ya riƙe mata kafafu, kuka Sultana take yi tana ambatar sunan Allah da Yayanta da Mom da Aziza da Khalil, Aziza sai yunkurin tashi take yi ta kasa, ganin Ɗan Gidan Alhaji ya fara sa hannu yana tattaro doguwar rigar dake jikin Sultana yana yin sama da shi rintse ido Sultana ta yi, ta sadaƙar kawai,ganin haka yasa Aziza ware gashin kanta tasa hannu ta b'alli daya tasa a bakin, wani gurnani ta saki tare da hucin Maciji🐍, jin hucin maciji yasa Sultana buɗe ido da sauri dan tasan irin wa innan abubuwan tunda tana yawan kallonsu, saurin juyowa suma Ɗan Gidan Alhaji da muƙarrabansa sukayi suna kallon Aziza wacce take tsaye gashi ya rufe mata fuska, kwashe gashin ta yi ta tattare ta maida shi baya ta ƙulle,bata da wani mafita wanda ya wuce haka, idan har ta bari tana kallo aka yiwa Sultana fyaɗe ba zata yafewa kanta ba, dole Sultana tasan asalin wacece ita a yau, tana tsaye jini na kan wanke mata fuska, dama idonta a rufe yake,hannu tasa ta shafe kanta nan take aka nemi ciwo aka rasa, bama iyakar Ɗan gidan Alhaji da mutanensa ba, harta Sultana ware ido ta yi kamar zasu faɗo kasa yayinda zuciyarta ya yi wani mugun tsinkewa, Shaho ne ya yi karfin halin faɗin
"Waike wacece ke!?"
"MACIJIYA🐍, AZIZA MACIJIYA!!" tana faɗi ta buɗe idonta nan take ta rikiɗe ta sama katuwar Macijiya fara sol sai kyalli takeyi, ba shiri Su Shaho suka saki Sultana wanda ganin Aziza ta koma Macijiya ta saki ihu tana sumewa.
neman hanyar guduwa su Shaho suka hau yi, Aziza ta naɗosu da jelarta, sannan ta koma rabin mutum rabi macijiya, kafin ka ankara masu sakin zawo a wando da masu fitsari duk sunayi, cikin tashin hankali da kiɗima da ɗimauta Shaho ya ce
"Dama ke ba Mutum ba ce?"
" *RUWA BIYU*" (taken Hajiya Azima kenan).
"Ku godewa Allah bana kisa,bana fata kuma ranar da zanyi kisa! Inaso ne na muku gargaɗi da kakkausar murya, babu ruwanku da Hamma Nawaz shi da familynsa, sannan duk ranar da dayanku ya ƙara aikata abu marar kyau zan maida shi kwaɗo, sannan idan har ku ka ba wa wani labarin abunda ku ka gani yau a take zaku mutu, kuna jina!!?"
"E wallahi Mamanmu mun ji ki,mu dai dan Allah kiyi hakuri!" suka haɗa baki wajan faɗi, watsar dasu Aziza ta yi, sannan ta zama mutum, su kuwa da mugun gudu suka watse nafsi-nafsi kowa ya yi ta kansa.
Da sauri ta yi kan Sultana yayinda hawaye ya hau wanke mata fuska, zata tab'ata kuma sai ta fasa, zata tashi sai koma ta kara komawa tasa hannu ta shafi inda aka buga mata katako a bayan wuya, sannan ta mike zata tafi taji Sultana ta riko hannunta, ganin haka yasa Aziza hura mata wani farin hayaki, nan take Sultana ta buɗe idonta, tana buɗe ido ta saukesu a kan Aziza, nan ta saki wani kuka tana fadin
"Dan Allah kice min film nake kalla,ko kuma duk abunda ya farun nan ki ce min mafarki ne ba gaskiya bane" tana maganar ne a ruɗe tana juyi ta rasa inda zata sa kanta dan firgici ganin haka yasa Aziza ɗora hannunta a goshin Sultana, lokaci daya ta samu natsuwa, hawaye ne ya zubowa Aziza ta ce
"The game is over Anty Sultana! da,fari naso nayi tafiyata ba tare da kun san wacece ni ba, amma ke Allah ya nufa zaki sani, ba zan iya yarda na watsar da yardan da kuka mini ba,ko ba komai yanzu idan na tafi zanyi farin ciki idan kika koma zaki gayawa Mom cewa ni ba mutum ba ce,bazan taba manta alkairinku a tare dani ba, hakika Anty Sultana ni ba mutum ba ce MACIJIYA CE!!"
Girgiza kai Sultana ta hau yi tana fadin
"Gaskiyan Yaya ne da Mom wata rana sai na fara ganin abunda nake kalla a gaske, to ko dai na samu tab'in hankali ne sabida dukan da aka min? Amma taya mutum zai ga maciji a zahirance irin haka?" hannu Aziza tasa ta kamo fuskar Sultana ta ce
"Kalli cikin idona!" ɗagowa Sultana ta yi ta sauke idonta a cikin na Aziza nan ta ganshi sak idon mage mai fari-fari
"Wannan shine dalilin da yasa bana buɗe fuska sabida idona! Ki yarda Anty Sultana ni ba mutum ba ce,duk labarin da na baku a kaina karya nake yi, wannan shine asalin gaskiyata, ni macijiya ce,na zo neman 'yar uwata ce ta biyuna, shine dalilin da yasa na shigo cikin gari, idan kinason jin labarinmu ba zan boye miki komai ba, ki kasa kunne ki sha labari" Aziza ta fada tana gyara zama,ita dai Sultana banda rawa da jikinta ke yi sai b'arin baki babu abunda takeyi tana yiwa Aziza kallon tsoro, nan Aziza ta dauko mata labari tiryan-tiryan a natse take warwarewa Sultana zare da abawa, bata boye mata komai ba ta gaya mata komai tsaff! Wani gauron ajiyar zuciya Sultana ta sauke ta ce
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Ai ko a fina-finan da nake kalla ban taba ji ko na gani ba, to meyasa baki gaya mana gaskiya ba?" murmushi Aziza ta yi ta ce
"Babu wanda zai zauna da macijiya, da ace a lokacin na gaya muku zaku koreni,idan kuma baku koreni ba zaku dinga tsorona, na zauna shuru a gidanku ne dan na tara kudin da zan nemi yar uwata mu koma al'karyarmu, dan Allah ki ba wa Mom hakuri idan kin koma, sannan ki nema mini yafiyarta idan na mata abu a rashin sanina, haka ma dan Allah ki nema min yafiya a wajan Hamma Nawaz, sannan kema ki yafe mini" Aziza na gama faɗi ta fashe da kuka ta tashi da sauri zata fita,sultana tace
"A yau kin ceci rayuwata, da ace ba dan ke ba, abunda nake yiwa gidan mijina tanadi da yanzu an karbe shi, bani da sauran wani mutunci da kima, da na koma matatta ko da ina raya, a yadda naji labarinki ke abun tausayi ce ba abun gudu ba daga ke har Baffanki da Hajjanki da kuma yar uwarki! Ai ke ba abun a gujeki bane Aziza, dan ke din mai tausayi ce, idan har kin yarda dani kuma kin yarda munyi miki halacci ba ki so ki saka mana da butulci to ki biyoni gobe mu koma kaduna,nayi miki alkawari zan tayaki neman yar uwarki gari ya gari, idan har kin yarda dani fa amma" wani kuka ne ya sub'ucewa Aziza ta ce
"Anty Sulty?" rungumeta Sultana ta yi ba tare da tsoro ko fargaba ba,
"Dama akwai mutane irinku a duniya? Tabbas duk lalacewar mutanen duniya na Annabi basu ƙarewa" cewar Aziza tana kuka, Sultana tana bubbuga bayanta ta ce
"Ni dai ki min alƙawari ba zaki gudu ba,kuma karki kara tunanin guduwa,Mom mutum ce mai zargin kanta a koda wani lokaci zata dinga zargin kanta da bata miki riƙon tsakani da Allah bane shiyasa kika gudu, dan Allah karki saka mata da haka"
"In sha Allah Anty Sulty babu inda zani" daga haka Sultana taja hannun Aziza suka fice a gidan ga dare ya tsaga ana neman gaff kiran sallan assalatu, fitowa bakin titi sukayi, Sultana ta ce
"Muna waya da Khalil yan iska sun bugeni wayar ta faɗi, na san za a nemu kam kuma hankalinsu zai tashi" Aziza ta ce
"Nima takalmina kafa daya ya fadi, yanzu ya za ayi kenan?"
"Kawai ki daukemu mu b'ace muje gida" zare ido Aziza ta yi ta ce
"A'a Anty Sulty,mu nemi wani hanyar dai" suna nan tsaye har aka kira assalatu, Aziza tace mu zauna a nan mu jira har ayi sallar asuba nasan a lokacin motoci zasu fara wucewa sai mu wani wanda zai kai mu gida, tunda bamu sallah ba da sauki ai"
"Yan iska mutanen banza! Da yanzu sai su mana fyaɗe muna period ko?"
"To suna tsoron Allah ne, ai basu tsoron Allah" zama Sultana ta yi a kasa tana fadin
"Ai shikenan" itama Azizan zama ta yi, nan kuwa aka yi asuba kafin motoci suka fara gilmawa da kaɗan-kaɗan har suka tare mai taxi, Sultana ta gaya masa unguwar da zai kaisu ya daukesu.
A gate din gidan mai taxi ya ajiyesu, suna fita suka samu harda yan sanda, mutane ana tsaye cirko-cirko daga ciki kuwa harda amarya da ango, wanda jiya da aka tashi a wajan dinner amadadin ayi gida ai sai hankali ya tashi, kuma ga wayar Sultana da suka samu a gate din da kafar takalmin Aziza guda daya, shiyasa suna gani suka sa a ransu ai kawai an sace su Sultana ne, sai kuma ya haɗe da Khalil da yake ta faman zabgawa wayar Sultana kira dan yaji lokacin da Aziza ta kwala mata kira sadda aka buga mata katako a kai wayar ta fadi kasa,kuma yaji sadda suke cewa a dauko da Aziza, itama aka dinga buga mata katako, sannan sun ga jini a wajan, jinin kan Aziza wanda ya fashe.
Hajiya Habiba mahaifiyar amarya Sulaiha ganinsu yasa ta ta tarosu da kuka tana tambayar lafiyarsu, nan suka tabbatar mata da suna lafiya, aka tambayesu me ya faru,nan Sultana tace daukesu aka yi, yan sanda suka tambayesu waye suka ce basu gane mutanen ba, dan sun rufe fuskarsu,
"Taya aka yi kukayi escaping daga hannunsu?" Sultana ta ce
"Ashe bamu zamu dauka ba, su da kansu suka sakemu, a bakin titi muka kwana kasancewar dare ya tsaga, sai da akayi asuba muka samu mota ya kawo gida"
"Ina dai basu muku komai ba ko" cewar Hajiya Habiba
"E Ammi basu mana komai ba"
"Na godewa Allah, da me zan cewa Hajiya yara daga zuwa biki ni Habiba,tana can hankalinta tashe wallahi, dan ma dai tana da karfin zuciya" nan aka shiga jajinta lamarin, aka ce su shiga su huta Sultana tace sam ai yanzu kam gida zasuyi, anyi-anyi su bari sai anjima tace sam,ganin haka yasa Hajiya Habiba cewa to jami'an tsaro su rakasu har kaduna har cikin gida, kayansu kawai aka fiddo musu aka sa a both, Sultana ta rungumi Sulaiha ta ce
"Ƙawata kuyi hakuri fa jiya hankalinku ya tashi ga shi ko gidanki ba a kai ki ba"
"Haba Sultana ba dole ba"
"To shikenan ai muna lafiya, kiyi hakuri ba zan samu zuwa gidan ba amma na miki alkawari zan zo idan an kwana biyu, a sha amarci lafiya" daga haka sukayi sallama wata ƙawar Sulaiha ta mikawa Sultana wayarta da kafa ɗayan takalmin Aziza,bayan mota suka shiga jami'an tsaro suka rakasu a baya, har kaduna.
@@@@@@
Suna isa da gudu Sultana ta shige gida,Mom tana tsaye a parlour ta kasa zama, Sultana na shigowa ta ce "MOM!?" da sauri Mom ta juyo tace
"Sultana" rungumeta tayi, cikin hawaye Mom ke tambayar lafiyar Sultana, shigowa Aziza da yan sanda sukayi, Mom na ganin Aziza ta yi saurin zuwa ta rungumeta tana tambayar lafiyarta,jikin Aziza ne ya kara sanyi, da yanzu ta gudu wani tashin hankali zasu shiga? Da yanzu wannan abun bai faru ba da shikenan ta b'ata rawarta da tsalle, hakika zamanta dasu akwai wani babban sirri da Ubangiji ya boye, shin yanzu su gayawa Mom gaskiya ne ko yaya zasuyi?" Mom ce ta shafo fuskarta tace
"Kina lafiya 'yata?"
Aziza ta gya ɗa kai,nan yan sanda suka kara yiwa Mom bayani kafin Mom ta musu godiya suka fice,suna fita Hajiya Habiba na kira,nan Mom ta shaida mata ta kwantar da hankalinta sun zo gida lafiya, dama tsautsayi ai baya wuce lokacinsa Allah ya kiyaye na gaba kawai, daga haka suka yi sallama aka rabu lafiya, Mom ta kallesu tace
"Bakuyi wanka ba ko?" suka gya ɗa kai
"Kuje kuyi wanka ku kwanta ku huta idan kuka tashi sai ku ci abinci, tunda yanzu ana neman shaɗayan safe ne" suka amsa da to, Aziza a sanyaye ta shige dakinta, Sultana kuma ta haura sama, sai da ta yi waya da Khalil dinta ta tabbatar masa tana lafiya dan hankalinsa ya tashi bai rintsa ba jiya, ta ba shi labarin ai Aziza ce ta taimakesu, amma bata gaya masa komai a kai ba, dan tayi alkawari ko wa Mom ne ba zata gaya ba har sai Aziza ta yarda, wanka ta yi sannan ta bi lafiyar gado dan bacci takeji sosai, haka ma Aziza ita ma wankan ta yi ta kwanta zuciyarta a cin kushe, ga tunani fal a cikin ranta,ji take kamar kanta zai fashe, ta ɗau minti talatin tana juyi kafin bacci ya kwasheta.
Basu farka ba kuwa sai hudu na yamma,Mom ma bata tashesu ba, ta dai musu odern abinci, bayan sun farka ruwa suka sake watsawa kafin suka ji sun watstsake, kasancewar suna fashin sallah dukkansu shiyasa basu wani damu ba, Sultana ce ta fara fitowa ta shiga dakin Mom ta sameta suna waya da Nawaz,sai da suka gama Mom tace
"Kin tashi? Kinyi sallah?"
"A'a Mom ina fashin sallah, Aziza ma haka"
"Yaushe kuka fara?"
"Ranar da muka isa zaria"
"Ok ya yi kyau,banda shan zaƙi dai da abu mai sanyi"
"To Mom"
"Kije ki ga idan Azizan ta farka,ku ci abinci"
"To Mom, amm Mom Khalil yace zai dawo a satin nan"
"Lafiya dai ko?"
"Nima ban sani ba, amma yace ya fasa cike sauran watannin" gya ɗa kai Mom tayi ta ce
"Nima maganar da muke yi kenan da Nawaz yace zasu dawo, jin abunda ya faru yace gwara kawai ayi auren kwanan nan a kaiki hankalinsa da nawa ya kwanta nima kuma nayi na'am da abunda yace, dan haka yace zasu dawo dukkansu shi da Son,idan suka dawo sun dawo kenan, nan da wata daya" shuru Sultana tayi dan bata so haka ba, ba tare da tayi magana ba ta fice, kasa ta sauko bata ga Aziza a parlour ba dan haka ta zuba musu abincin tayi dakin da sallama Aziza na zaune a bakin gado, tana sallaman Aziza ta amsa tana shirin rufe fuska, Sultana tace
"Babu amfani ai tunda nasan komai, zo muci abinci" ta fada tana zama kan carpet, zamowa daga gadon Aziza tayi ta kalli Sultana ta ga jikinta a sanyaye Aziza ta ce
"Anty Sultana yana ganki haka akwai matsala ne?"
"Babba ma kuwa Aziza, Khalil jin abunda ya faru yace zai dawo a cikin satin nan, Yaya kuma yace shima zai dawo nan da wata daya dan ayi aurena hankalinsu ya kwanta shi da Mom,kuma Mom tace shi da amininsa zasu dawo, dama yanzu dawowa mai gabadaya zasuyi" Aziza ta ce
"A'a bangane ba,ina da tambaya, shin Hamma Khalil ba shi bane abokin Hamma Nawaz ba wanda suke kasa daya?" dariya Sultana tayi ta ce
"Taya? Khalil fa shi yana paris ne, su Yaya Nawaz kuma suna america ne, sunan babban aminin Yaya ba Khalil bane, ke yanzu duk zamana dake baki san my husband to be ba? sunan babban aminin Yaya Nawaz *AL'MAZEEN NE* shi kuma ɗan Kano ne ba dan kaduna bane,gidansu ne Mom tace zata aikemu nace bazan je ba.
🍃🍃🍃🍃
Post a Comment for "AZIZA DA AZIMA 41-50"